Showing 1 words to 3000 words out of 84412 words

Chapter 1 - YARDA Book Complete by Maman khady.pdf

12 Jul 2025

2599

[YARDA.

1



Zaune suke cikin cikin ajin nasu,Su kadaine azaune sabida anfita break adaidai lokacin.
Kuma janyemata hannu tayi akaro na uku kamin tace" Zahra yakamata kidaina wannan
tagumin ki gayamin matsalarki,Kindaisan duk fadin makarantarnan babu Wanda nake kulawa
saike bansan damuwarki sabida Allah yagani NA YARDA dake to damme ke bazaki saki jiki
daniba?Ko kina tunanin har yanzu bankai matsayin da zansan damuwarki bane?
"Ajiyar zuciya ta sauke me k'arfi kamin ta kamo hannuwan me maganar ta farko" Wallahi ba
haka bane Jidda kema kinsan NA YARDA dake kilama fiye da yanda kika daukeni amma
matsalata ta cikin gidace nakuma rasa ta yanda zan bulloma damuwar saidai inaso ki tayani da
addua Dan Allah idan Allah ya kaimu wani lokaci zan gayamiki komai ammadai yanzu kifara
tayani da addua tukunna kinji?

"Kwace hannuwanta tayi tana hararar zahra din kamin tace dalla ni kyaleni indai bazaki
gayamin matsalarkiba to wallahi babu ruwana dake.

" Murmushi tasaki tana kuma kamo hannuwan jidda din kamin tace"yi hakuri sahiba Dan Allah
wallahi dama matsalar dady ce yana cikin takura sannan muma muna buk'atar wadda zata
dinga kula damu amma yakiyin aure,Jiya naji abokinshi yanamishi fada akan ya daina yima
kanshi allurar kashe sha'awa tun kamin ta cutar dashi Amma nasan bazai dainaba hajiya kaka
ma kullun saitamishi fada Amma yaki ji,Shine sai indingajin hankalina yanatashi wlh.

"Eh gaskiya akwai damuwa zahra amma ni sai inga kisameshi kimishi magana mana idan
kika nunamishi kinaso yayi aure ai kila yayi nasandai damuwarshi bazata wuce kadda ya auro
wadda zata cutar dakuba danhaka ke zaki nunamishi abinda kukeso tunda yanasonku kuma
yanajin maganarki ko? Murmushin jin dadi tasaki kamin tace eh hakan yayi nagode sosai wlh insha Allah yau
dinnan zanyimishi magana komekenan zuwa gobe idan munzo makaranta sainaimiki bayani
nagode jidda.



Yarane kusan sa'annin juna wanda shekarunsu bazasu wuce 15-16 ba sabida jidda ta Dan
dara ita zahra din dakusan shekara daya amma kuma Kansu daya.
K'awancene tun farkon fara karatunsu Wanda har iyayensu sun san da zaman amintarsu.


Tsaye suke aharabar makarantar lokacin anata zuwa daukar yaran wasu amotoci wasu

amashina,Sukuma suna tsaye har lokacin agefe duk da cewa tuni direban dake daukar jidda
yazo amma dayake yasaba ko'ajikinshi hasalima yana zaune cikin mota yanashan rake,Dan
yasan indai ba mezuwa daukar su zahran yazoba to jiddan bazata yadda tabishi konan da can
ba.
" Zahra Dan Allah ki yima yarinyarnan kitso cikin satinnan kalli yanda kitson duk ya zanzare
Allah da wuya idan ba k'azanta zakiyiba zuwa nan gaba.

Wani uban tsaki zahran taja kamin tace amma kin rainani jidda,Wallahi haka kan Mimi yake
duka yaushe dady yaimata wannan din nifa dama kinsan ban iyaba shiko ya iya tunda yanama
momee kamin ta rasa nima bejima da dainaminba sabida beso muje ko ina wannan inyamurar
ke zuwa tanamin saiya biyata,Itako Mimi kukan tsiya shiyasa yace inbari kawai ya dinga mata
amma zan tsefemata anjima tunda babu islamiyya.

Da gudu Sadiq da faruk suka shige cikin motar bayan kowa ya mannama dadyn nasu Sumba
akunci yayinda Mimi ta saka ihun kuka sabida sunrigata zuwa wajan dady din.
Dole yafito daga motar yana dariya tare da daukarta duk zata iya kaiwa shekara biyar
amma tsabar gata yasa saikai tunanin bata wuce shekara biyu zuwa ukuba.
Gaidashi mukai tare nida zahra sannan ya wuce yasata gaban motar domin dama nan dinne
wajan zamanta,Sallama mukai sannan nima na wuce wajan Wanda yazo daukata.
So daya ya kalleta ta madubi yaga Sam yau bata da walwala danhaka shima saiyaji
hankalinshi yatashi,Shifa behada yaranshi da komaiba na duniya.

Kasancewar yau alhamis babu islamiyya shiyasa abincin safe kawai suka girka kamin sutafi
danhaka yanzu data huta zatafara Neman abinda zatayimusu kamar yadda tai dadyn ya horata
akai.
Saidai yau damuwardatake ciki saita saukar mata da kasala Allah yasama tai sallah
amakarantar danhaka kawai saita haye gado bayan ta kwabe kayan jikinta.

Mimi tashigo dakin da kukanta tana shafa cikinta da alama dai kuka n yunwa takeyi.

Harararta tayi kamin tace"To sarkin fitina ai mundawo gidan yanzu zaki hana uban kowa
kwanciyar hankali me akaimiki kike kuka?
Hawayenta ta share kamin tace yayanmu Abinci zanci ni bansan tea.

Harararta tayi kamin tace wuce bani wuri yau banda Lafiya sai zuwa anjima zanyi girki duk
uban ciye-ciyen da kikayi dazu amma yanzu Dan kar mutun ya zauna Lafiya zakice yunwa
wuce tai wajan dady.

Hannunta ya rike suka nufi falo domin dama yana tsaye kofar dakin yana sauraren
mesukeyi,Da kanshi ya shiryamusu indomie danshima yunwar yakeji.
Saida yaga yaran sun natsu sannan ya yakoma ya jingina da kujera tare da lumshe manyan
idanunshi wata irin kewar matarshice ta dabaibaye zuciyarshi jiyake kamar yasaka kuka

kozaisami sukunin zuciya.
Tashi yai ya nufi dakin zahra Dan beso damuwa tai tasiri cikin zuciyarta da gangar jikinta.

Gabadaya ya rungumota jikinshi yanajin zuciyarshi na tsananta bugawa,Bubbuga bayanta
yafara kamin yafara magana ahankali cike da lallashi"Bansan damuwa zahra kinfi kowa sanin
hakan shiyasa nabaki dama akan komai Wanda yashige miki duhu gayamin menene ya
canzaki?
Rungumeshi tayi tana kuka"Dady mungaji da ganinka hakanan Dan Allah kayo aure musami
wacce zata dinga debemana kewar mahaifiyarmu bazai yiwu ace koda yaushe Kaine komai
dinmu ba kaima kana bukatar hutu kamar kowane mahaifi.
"Karki damu inshaAllah zanyi matsalar banso in dauko wadda zata zamemana matsala
danhaka ki kwantar da hankalinki zanyi aure amma ba yanzu ba idan kuma kinada wacce ta
kwantamiki arai to nabaki zabi Zahra.



Maman khadija







NA maman khadija.
Page 2


Tajima cikin halin tunani bayan barinshi cikin d'akin saidai tuni zuciyarta tafara kawo Mata wani
kyakykyawan tunani,Wani mayen murmushi tasaki tare DA sakin k'aramin ihu murna fal cikin
ranta lallai kakusa angwancewa my dady.

Duk da yanajin kamar zai iyayin danasani saidai ya Hana tunanin hakan tasiri cikin
zuciyarshi musamman idan yai tunanin cewa yo wa zahra tasani balle hartayi abotar da zata iya
bashi YARDA irin wannan shi bumma saiya bashi dariya danhaka tuni ya saki wani lafiyayyen
murmushi saman kyakykyawar fuskarshi kai dady fa badai kyau ba.


Bayan nakoma gida wanka kawai nayi bataredana nemi abinciba danni abinci bawani
damuna yayiba musamman idannacika cikina da cibanza ci wofi amakaranta,Kwasar
littattafaina nayi na nufi falo jin muryar Yayana Usman dan shine ke kuma koyamin dukkan

abinda akaimana amakaranta matukar yana gida.
Kayan dayagama cin abincinakwashe nakai madafa sannan nadawo kusa dashi na lafe
Dan Allah yayoni dason jikin masifa.

Janyeni yayi daga jikinshi yana hararata"To mage sarkinson jiki waike bakisan kibar mutun
ya hutabane? Indai baki tashi daga jikinaba Allah kwallo zantafi yanzu inbarki.

Bakina na turo gaba tare da d'an dagamishi jiki kamin in koma dannariga nasaba rayuwa
dashi.

"Haba Usman waikai Dan Allah meyasa kacika mitar masifane sabida Allah yarinyar nan
idanbata rabekaba wa kakeso taje ta raba?Nifa bansan kana takurata da shegiyar mitarka ta
gado,Kakarmu hajiya hauwa itace tai wannan maganar tanayi tana watsa hannu Dan ita Sam
bata yarda kowaya tabaniba. Be kulataba dan yasan kadantake jira yanzu ta taramishi mutanen dake kofar gida indai
akan jidda ne

Ina kwance ajikinshi yaimin k'arin bayaninduk karatunan sannan yatashi zai fice,Rikeshi
nayi ina kyafula manyan idanuna alamar kuka zan sakarmishi.
Waigawa yayi yaga gabadaya hankalin hajiya yana kan labaru datake kallo danhaka saiya
koma ya zauna tare da zaunar Dani gefenshi gayamin menene kinji sweet sis?
Cikin yanayin muryatadatake me sanyi ga shagwaba nace pls Yayana kaje Dani Dan Allah.
Dama yasan fitinar bata wuce ta hakan danhaka saiya rungumeni jikinshi cikin muryar wayau
yace yanzu zanje indawo bawani jimawa zanyiba zantaho miki da ice cream me shegen dadi
kinji ko
Samu yai ya fice yanajin dadi cikin zuciyarshi godiya yake kumayima Allah dayasa berasa
kanwarshiba kamar yadda ya rasa iyayenshiba.


Washe gari.
Can muka hade da zahra wadda yau naganta fayau da ita cikin farinciki sabanin jiya da take
cikin damuwa da rashin walwala.
Rungume juna mukayi da ita kamar yadda muka Saba sannan sukuma suka gaidani.

Saida akaimana break kowa Yakama gabanshi sannan nazaro kular da hajiya ta zubomin
dambun nama mukafaraci bayan na dibarma kannen zahra kamar yadda nasaba.

"Uhum saiwani murmushi kikeyi har yanzu kinkicemin komai KO dady yasami matar ne?
Dan tsaki taja kamin tacemin kinjiki saikace wani Wanda yarasa mashinshini aidama shi
dady akwai masu kaunarshi da yawa kawaidai yaki basu dama ne amma jiya munyi magana
dashi kuma yabani wuk'a da nama Zan zabamishi matar aure kalar wacce ta dace dashi wadda
nasanta nasan halinta sannan na YARDA da ita fiyema da yanda ita ta yarda Dani.

Murmushi kawai nayi kamin ince amma naji dadi Allah yasanya alkhairi kinga nima wataran
saiki ganni nazo gidanku yini tunda akwai mace amma yanzu danace zanje sai hajiya tace a a
wai sai dadynku yayi aure.
"Murmushi itama tasaki kamin tace ki kwantar da hankalinki har kwanama zakiyi,Am yau
juma'a sonake in nufi wajan hajiyakaka muyi shawara kome kenan zan taboki cikin wayar hajiya
kokuma inzo ranar asabar.

"To babu damuwa Allah ya kaimu Lafiya.

Anan hirar tamu ta tsaya har akatashi bamu tsaya jiraba yau Danni yayana Usman yazo
daukata sukuma tuni dama dady na jiransu.


"Wannan k'awar taki daga gani itama sarkin rikicice kamar ke ko? Cewar dady,Wanda ke
farimciki ganin walwalar yarannashi duka.

Dariya tayi sosai kamin tace"Kai dady babu wani rikici damukedashi itakam gatane yai Mata
yawa amma kuma bame cutarwaba kasan bata da iyaye duk sun rasu saidai yayanta da
kakarta hajiya saikuma sauran dangi kowa yana sonta sunajin tausayinta shiyasa take
shagwaba Amma wallahi dady jidda tayi saima ka zauna da ita gashi ta iya girki kamar kamar
me kowane iri shiyasa nake kaunarta har cikin raina.

"Kuma dady tanasonmu sosai kullun saitabamu abinda dadi dama zata dawo
gidanmu,Cewar Mimi wadda ketajan jelar kitsonta.

Wani irin murmushine ya kwacema zahra din Wanda har saida dadyn ya kalleta.



*********

Da ciwon Mara na isa gida duk da saida muka biya ya Usman ya saimin magani Wanda tun
cikin mota yabani nasha Amma tsabar sangarta da kuka nashiga gida.

Da sassarfa tafito zaninta ahannu tana salati da sallallami kamin ta Dora da to keda
ubanwaye wani shegene yatabaki incimishi uwa? Hajiya kenan iyayen rikici shiyasa nima nake
sonta wallahi bata hada soyayyata da komaiba.

Jikinta nashige ina shesshekar kuka kamin ince hajiya marata ke ciwofa.

Saida ta lissafa kwanakin wata taga daidaine sannan ta furta"Wayyo Allah na sannu wallahi
na manta da yaune zuwan abun muje ki wanka saiki kwanta kihuta ai ki kwantar da hankalinki
akwai hisabi tsakaninki da wannan ciwon.

K'annen mahaifina na tadda zaune afalon sunacin dambu Wanda hajiya tayi abunta da kanta
dan itafa har yanzu jinta take garau,Gaidasu nayi sannan nawuce daki yayinda sukabini da
albarka kamar yadda suka saba dan sosai suma suke nunamin kulawa.
YARDA.

Na maman khadija.

3


"Fatima bintu zahra 'yar gidan manzo,Me zaki gayaminne naga bakinki yanata motsi alamar
lallai akwai wani bayani dai,Cewar hajiya kaka wadda take mahaifiya ga dady.
Murmushi tasaki sannan ta riko hannuwan farar tsohuwar wadda itama idanunta nakan
zahra din domin tanason zahra sosai musamman da itama take takwara wajanta.

"Kaka alfarma nake nema wajanki dangirman Allah kadda kice bazaki iyaba domin dole kece
karfin guiwata kinji kaka?

"Karki damu zahra indai har inada dama basaikin hadani da Allah ba insha Allahu bakida
matsala Allah yasa alkhairice maganar.

Cikin yanayi nakuma marairaicewa domin aji tausayinta tafara magana"Kaka nasan kina iya
bakin k'okarinki wajan ganin dady yayi aure tunkamin Mimi ma tai wayau saigashi beda ma
alama har zuwa yanzu musamman Dana Lura ko maganar ma beso, Rannan naji abokinshi
nayimishi fada akan zai halaka kanshi indai beyi aureba amma sainaji yana gayamishi shifa
bazai yadda ya auro wacce zata watsamishi gidaba kinga kenan sabida mu yaki auren,Saidai
awashegari naita fushi da damuwa har saida ya tsareni da tambaya shine nace aure mukeso
yayi sabida muna buk'atar makwafin uwa sannan yara da yawa kamar yadda kowayasan
burinshi kenan Tara yara da yawa,To shinefa yace yabani zabi inje in zabomishi duk wacce
nake ganin tadace dashi sannan bazata cutar damuba,To Alfarmar da nake nemadai wajanki
itace sonake ki shirya yanzu muje gidan wannan k'awartawa ki ganta idan har tayimiki saimu
dawo mufara shirya yanda abubuwan zasu kasance duk da nasan cewa dakyar idan hajiyar
zata yadda da shirinmu.

Fuskarta cike da farinciki take furta Alhmdulillah amma naji dadi sosai Allah ubangiji ya
shigemana gaba insha Allah komai zaizo da sauki indai kin amince da ita Sannan kin YARDA
da ita babu matsala saimudage da addua yanzu tashi muje mudawo anshi wayata kiramin
babanki tahir ya kaimu dan inaga shine kawai beyin nisa ranar juma'a.

**** ****

Wando da rigane jikina na fakistan masu laushi tuni sunbi jikina saidan siririn kllabinta
Wanda na daure gashinadashi.
Wainar fulawa nakeyi hankalina kwance inayi Ina karanto suratul Maryam kamar yadda
d'abi'ata take nayin karatu musamman idan aiki nakeyi.
Sallamar zahra nadingaji sama-sama saidai banyi tunanin itan bace musamman dayake
dazu muka rabu kuma tace kila sai asabar zata shigo wajena tabani labari.

Wani uban tsalle na buga lokacinda na tabbatar itace,Nan muka rungume juna muna
murna yayinda hajiya batabi ta kanmuba sai sannu da zuwa da takeyima kaka.
Cikin mutunci suka gaisa sannan nakawoma kaka lemo da ruwa itadai sai kallona takeyi
suna hira da hajiya muko ai cikin dakina muka shige mukafara hira saikace ba Dazu muka rabu
ba.

"Dallah dazufa da ciwon Mara nashigo gida wallahi damma saida ya usi ya siyomin magani.
Dariya tai kamin tace ah kice abun yazo niko wallahi idan zanyi banjin komai saidai kawai inji
yanayina ya sauya kuma danaduba sai inganshi.

Saida mukasha hirarmu sannan muka koma falo lokacin tuni su hajiya anzama k'awaye duk
da dama sunsan juna amma hirar tasu tayau tafi armashi.
Jikin hajiya na shige tare da lafewa Ina leken kaka wadda keta dan kallona irin asace
dinnan.

Shatara ta arziki hajiya ta hadamusu mukai sallama cikin jin dadi bayan hajiya tagama
jaddadama kaka cewa itamafa tana nan zuwa.



*****


Hummm Ammma gaskiya harkinsa jikina yai sanyi zahra banda abinki yaya dadynku zaiyi da
wannan yarinyar danya jagal da ita inagama ai da kadan ta girmeki yo ai duk shiririta gidan
naku zai zama KO?

"Haba hajiya ya zakice haka dan Allah wallahi jidda babu abinda bata iyaba,Bama wannan
ba ku lokacinda akemuku auran ai ko kaimu girma bakuyi,Nidai yanzu kawai temakon da
zakimin guda dayane Shine idan nagayama dady zabindanaimishi kawai ki jajirce sai anyi
hakan nikuma insha Allah Zan shawo kan ita jidda din.
"Uhumm to shikenan Allah yashigemana gaba insha Allah Zan kokarta.


Alhamdulillah,Cewar zahra tana lumshe manyan idanunta.

YARDA.

Na maman khadija.

4



Ranar asabar kwance nake saman cinyar hajiya tana tsefemin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login