Showing 30001 words to 33000 words out of 84412 words

Chapter 11 - YARDA Book Complete by Maman khady.pdf

Advertisement

12 Jul 2025

2651

nasan abun yaimiki nauyi da yawa amma Allah zai temaka
miki komai yai daidai kamin na dawo kinji ko? Duk abinda ya shigemiki ki nemeni idan
bakisaman ba ga hajiyata nan kusa dake kinji ko? Kings zahra ma barinki zatayi dan Allah ki
kula sosai nagode.

Shiru nai ina zare idanuna amma cikin zuciyata duk sainaji babu dadima wallahi.


Kwanciya yayi tare da dorani samanshi yana shafar bayana ahankali ya tube hijab din
jikina Wanda harwata ajiyar zuciya naji ya sauke,Rigar irin me laushinnan ce gata tabi jikina
sosai.
.

"Madam zaki bani hakkina yau ko?

Batare da wata damuwaba na dagamishi kaina alamar amincewa.

Wani murmushi yasaki kamin yakuma matseni cikin jikinshi,Yasan bansan komaiba
shiyasa nai saurin amincewa,Ammadai zaiyi kokarin ganin ya rage abinda ke dankare
amararshi kamin yabar garin.

Danhaka cikin wani irin salo na wayayyu wa inda sukasan me sukeyi yafara aikamin da

wasu sakuna masu matukar tasiri cikin gangar jiki danhaka bansan lokacinda nakuma bajewa
cikin jikinshiba babu abinda zuciyata ke gayamin sai ashema haka auren yake da shegen dadi.


YARDA.
Labarin YARDA na kudine idan kina buk'atar siye zakibi wannan tsarin domin samu,Naira Dari
biyune kacal,200

Acct no.
0005074141,Aisha sabiu ja'iz bank.

Kokuma katin waya ta wannan layin,
08142643253.

Atura shaidar biya ta wannan layin👆🏻.



29-30.



Irin murzar da yakemin yasa hakurina k'arewa nasaka kuka,Tuni kirjina da lebunana sun isheni
da azabar zafi.

Sosai yakejin wani irin farinciki da nishadi duk da komai be wakanaba ammafa yaji dadi kuma
ko ahankan yasami nutsuwa fiyema da tunaninshi.
Inajin lokacin daya rungumeni yana fadin"Sorry autar Mata nagama ai Allah yaimiki albarka
yabarmu tare,Kecefa kika amince Amma kuma gashi kina kuka!!Shikenan yi hakuri bazan
kumaba.
Jijjigani yakeyi yana shafar gashina zuwa gadon bayana harwani huramin iska akunne
yakeyi,Niko ai tuni nai barci zuciyata cike da farincikin nabawa mijina hakkinshi yau😃.


Yajima kwance cikin yanayi na farinciki da k'arin kuzari sannan ya lallaba ya mike gudan
kadda yatashi amaryar tashi,Wayarshi yasa ya haske fuskar wadda take duk busassun hawaye
saikuma Lura da yayi da libs din kamar yadan tashi sabida rashin sabon shan da akaimusu.
Murmushi yakuma Saki yana tuno zakin da yaji alokacinda yai hakan saidai ba k'aramar
godiya yaima Allah ba dayasa ya rike kanshi be aikata komaiba ayau.

Wanka yashiga ya gyara jikinshi,Sannan ya dosa nafila kamar yadda yakanyi lokaci zuwa
lokaci.

""""""


Wayewar gari,Tashi yai irin beyi komaiba dinnan dan ko alama,Danhaka dole nima na yakice
kunyar data addabeni nacigaba da harkokina.

Da misalin takwas na safe duk muna zaune falo yana kumayi mana nasiha da fada
musamman zahra da yasan bazasu haduba kuma yanzu sai ta kwana biyu da aure, Sosai
jikinmu yai sanyi sosai,Nidai banyi kukaba amma tuni zahra tafara sharar kwallah.
Wata sabuwar Waya yabani tare da cewa inbarma zahra waccan kome nake buk'ata
ingayamishi zai turo akawomana,Sannan yakuma tsawatama su Sadiq duk da cewa yaran basu
da wata matsala,Sannan yaimana sallama.
Kuka zahra takeyi amma tanaganin ya nufi d'akinshi ta taboni"Dallah kije kukumayin
sallama kedai kinada matsala Allah.

Bakina atunzure na nufi d'akin shikuma yana niyyar fitowa danhaka yana ganina saiya koma
ciki tare da ajiye jakar dake hannunshi.
Wata runguma yaimin tare da sauke ajiyar zuciya,"Zanyi kewarki da yawa jiddana idan ban
iya jurewaba tabbas zakiganni nadawo koda lokacin dawowar beyiba kicigaba da kulamin da
kanki sannan kiyimin kyakykyawan tanaji musamman bangaren hakkina na aure,Nikuma Zan
baki mamaki jidda Zan shayar dake da zumar kauna jidda,Zankula dake Zan kasance farincikin
ki jidda fatana ki YARDA Dani!!!!.

Kuma shigewa nai jikinshi inajin wani irin dadi da farinciki shiyasama daya lalubi bakina
yafara sha Sam banyi yunkurin hanashiba.
Asama mukaji Mimi na fadin"Dady nima.

Sakina yai yana dariya tare da d'aukarta"Kema mene Mimi?
Bakinta ta nunamishi tare da d'agamishi gira.

Dariya mukasaki kamin ya manna Mata kiss akunci da goshi yana fadin"Ke saidai wannan
Amma wancan na aunty ne ita kadai.


Saida mukaga tafiyarshi daga harabar gidan sannan muka koma cikin gida babu Wanda
yawani damu Cikin yaran da alama dama sunsaba da tafiye tafiyenshi tunda dama akwai
lokacinda zahra kecemin idan dadyn yai tafiya saidai su koma gidan hajiya kamin yadawo.

Sai gidan najishi duk wani daban tunda gaskiya dady yaimin kokari sosai wajan Jana
jikinshi,Shiyasa sabo yafara shiga tsakaninmu.

""""*****"""""


Saida dady yai kwanaki biyar daidai sannan mukasami wayarshi lokacin tuni anata
shirye-shiryen bikin zahra dan tuni muka kwasa mukakoma gidan hajiya da zama balle da
bamuyi waya da dadyn bama balle ya hana.

Zaune nake cikin d'akin hajiya kaka ina ninkemata kayanta sabida hidimar bikin,Shigowa tai
rike da wayarta ahann"Hauwa'u amshi nan ki gaisa da mijinki sai yau Allah yasa ya tuna damu.

Amsar wayar nayi akunyace ina murmushi, Shima dariyar yakeyi jin abinda hajiyar ke fadi.

Saida tabar d'akin sannan nafara gaisheshi cike da girmamawa saikace yana gabana.
"Madam jidda kin manta dani kwana biyu ko?

"Cikin shagwaba nace kai dady yazakace haka alhalin munata jiran kiranka amma shiru
wama yasani ko Kaine ka manta da mudin!!!

Kwanciyarshi ya gyara yana sakin murmushi,Jiyake wani nishadi nakuma dabaibayeshi jin
muryarta kawai.

"Uhumm ni nasan bazan manta da iyalinaba kuma farincikina danhaka kimabar wannan
maganar ya kuke? Komai Lafiya ko? Tunda nazo ban zaunaba sai yau inafatan duk kuna cikin
k'oshin lafiya?

"Alhamdulillah dady ya aikin naka?

"Komai qalau madam jidda saidai kewarki ta hanani sukuni inafatan kema hakanne daga
gareki?

. murmushi nasaki batae Dana tankaba dan sosai nakejin farinciki yau danajishi.


"To shikenan nasandai anyi kewata shikenan zahra zata gudu ta barki ko?

"Eh hakane dady amma ai bamu rabuba tunda zamu dinga haduwa kullun a school.

"Hakane my jidda Allah yasanya alkhairi yanzu Zan dinga kiranki duk lokacinda nasami
lokaci,danhaka kidinga barin wayarki kusa dake musamman da dare,Sannan daga angama biki
lallai Ku koma gida kinji ko?

To dady insha Allah.

"To shikenan nagode Allah yaimuku albarka Bari na barki sai anjima.

Ajiye wayar nayi ina sakin murmushi,Saida naji gyaran murya sannan na waiga,"Kai zahra
gaskiya Allah ya rabaki da gulma wato labe kikaimin ko?

Dariya tasaki tare da zama kusa Dani"Lallai su dady manya duk soyayyarce haka!
Gaskiyane aini bance komaiba ammadai gaskiya yakamata adinga sakarmishi zafafan kissing
yanda zaisami kwanciyar hankali kinsan nifa banhada son dadyna dana kowaba.

Tsaki nai ina harararta Allah dai yasa ya usi ya gyaramin bakinki wallahi,Kin ishi kowa ke
kodan irin girgizar nan da amare keyi Sam bakiyi saima wani kuma gogewa da kikeyi saikace
wadda bata da matsala.

"Idanu ta fiddo kamin tace"Haba aunty fatan matsala kikemin dan Allah? Nagadai masoyina
Zan aura ba auren doleba sannan nasan bazai tauyeniba balle ya cuceni ko,Ke nifa nan jinake
kamar ma inkai kaina Allah,Sannan irin gyaran da nake samu yasani harwani yanayi nake shiga
sabida tsabar shauki da ishki.



******


Ranar asabar kamar yadda kowa yasani aka daura auran fatima zahra da Yayana Usman
,Daurin auren da yatara manyan mutane kamar nawa sai kace dady na gari.

Idan kaga zahra bazakace wai itace amaryaba narasa meke damunta Sam bata da matsala
dan tafini walwala ma da alama ita ko ajikinta,Har mamaki nakeyi idan naji irin hirar da
sukeyi,Balle yanzu daya kirata yanagayamata anfa daura har saida yasa taimishi kiss cikin
wayar sannan ya hakura oh Ashe shima ya usi din dan air ne ban saniba, Tashi nai nabar
Mata falon ina fadin Mara kunya kawai.

Dariya da gwalo tasaki tana fadin"Eh din nasan kishi kikeyi kinji muna bada kala cikin love.


Matar yayan dady mesuna hasana itace ta shigo falon hajiyar fuskarta asake,Gaisawa
mukai kamin ta tambayi hajiya ina amryar take?

Kira daya saiga zahra saikace dama irin jirannan takeyi.

Kular ce cike da wani irin dahuwar nama Wanda daga gani ansan yaji magani domin tuni
yatashi daga ferfesu yakoma magani zallah,"Amshinan sai ku cinye keda auntyn taki yanzu aka
kawoshi daga gidan matar wlh."cewar hasanar tana kuma gyara zaman kular.

Godiya hajiyar taimata kamin tace "Ai jiyama uwarta Safiyya ta kawomata wani,Kuma yanda
kikasan kura duk abinda akabata haram haram ta cinye,Gadai wadda nakeso agyaramin nan
cikin sati nasama danhaka kibani number matar saimu daidaita da ita Amma saidai ta dinga
zuwa nan dan habibu be yarda taje ko inaba inba makarantaba.
"To hajiya insha Allah zanyimata magana idan tazo saiku daidaita.

Nama ne lafiyayan nama saidai tuni magungunan dayasha yasa yakoma kamar magani
danhaka duk kwadayin zahra haka ta dinga yanga wajan cinshi balle kuma ni da sai hajiya tayi
magana sannan nakeci.


Zuwa dare masu zuwa d'aukar amarya sukazo,Sai lokacin idanun zahra suka raina fata kai
tsaye tace tafasa auren kuma bata zuwa ko ina.
Kai rigimafa sosai dan tun Ana d'aukar abin wasa hardai aka tabbata gaskene dan kuka take
hadda birgima duk kwalliyar da akaimata tagama lalatata.

Saida yayar dady taimata Jan ido Sannan tayarda akaje shiga mota,Inata kokarin shigewa
mota hannuna rike da Mimi kiran wayar dady yashigo wayata.
Agaggauce na gaidashi,Saidai abinda ya fadimin yasani saka kuka ban shiryaba.
"Jidda an dauki zahra dinne?

"Eh dady yanzu aketa tafiya.

"To maza ki wuce wajan hajiya ban yarda kije ko inaba cikin darennan kindaisan usman yarone
nasan abokanshima duk haka suke danhaka ban yarda aimin wasa da iyaliba ni inacan wata
duniya kinji ko?

Jin kukana yana Neman karyamishi zuciya yasashi kashe wayar,Sadiq da faruk da Mimi
daketa jira mushiga mota sukaga na tsaya ina kuka duk sai suma sukafara dama gashi anwuce
da zahra nata ihu.

"Ku wuce kuje Sadiq ni dady ya hanani zuwa.

Duk biyoni sukayi batare da sunjeba dan sosai yaran ke sona gami da yimin biyayya.
Kuka naitayi cikin falon hajiya kaka yaran natayani,Ita kuma tana aikin lallashi dan itama ya
kirata yace be yadda tabarni inje ko inaba.

Ranar dai haka na kwana cikin jin haushin dady dan so uku yana kiran wayata amma saidai
in harareta.




Washe gari.


YARDA.
Labarin YARDA na kudine idan kina buk'atar siya zakibi wannan tsarin domin samunshi A naira
Dari biyu tal.200

Acct no.
0005074141,Aisha sabiu Ja'iz bank.

Kokuma ta katin Waya akan wannan number, 08142643253.

Haske writer's asso.



31




Da Asuba ma da kiranshi na farka,Kuma nakuma shareta sai nai sallah natashi yaran sannan
na zauna gefen gadon tare da d'aukar wayar dan har lokacin be daina kiraba.

Wata irin ajiyar zuciya ya sauke kamin yace"Haba jidda Ashe kema fishi gareki ban saniba?
Sabida na hanaki fita sai kawai ki tashi hankalina ki k'i d'aukar wayata ko?

Bakina na turo gaba kamar yana gabana kamin ince "Dady ina kwana?
"Ni banga wani kwanaba ina tuhumarki kina canza hanya,Kinaso kisani damuwa ne?

Kaina na girgiza kamin ince kayi hakuri bazan kumaba ,Amma dai yau zamuje gidanta kamin
mu koma can ko?

"To jidda ya zanyi daku kuje din amma dan Allah akoma gida da wuri bansan inkuma Kira
inji Baku komaba kumama hajiya tacemin ansami wadda zata dinga miki aikin,Danhaka saiku
wuce tare banda surutu babu ruwanki da ita sainadawo naga kalarta tukunna kinji ko?

" To dady.

"Yauwa to sai anjima,Ki gaidamin yaran.


Ajiyar zuciya na sauke ina saikin murmushi,Kenan gaskene da zahra tace dady ya afka cikin
kaunata ji yanda ya rude dan Allah kamar yaro, Ashe nima zansami me sona kamar zahra to
Amma meyasa ni bemin hirar soyayya ,Koda yake yace zai dinga zuwa hira wajena idan
yadawo daga tafiyar.
Da wani farfesun zabbi na karya bayan nasha tea hajiya kaka ta tasani saida na cinye
kwano guda sannan nasha ruwa.
"Gara ki saki jikinki jidda ki gyara jikinki kamin mijinki ya dawo kinga zahra tafiki wayau
komai bata gardama take amsa,Danhaka kema yakamata kiyi koyi da ita wa innan abubuwan
na gyaran jikine tare da jawo soyayyar megida danhaka ki kula kinji ko?


"To hajiya insha Allah.



Saida mukai sallar azahar sannan nagama hada kayanmu tas nabawa Direba
yakaimana gida mukuma direban hajiya yakaimu gidan zahra.
Ihu taita saki tana tsalle lokacinda mukaje,Gidan babu kowa da alama kowa Yakama
gabanshi,kasancewar gidan yasha gyara babu abinda yake sai Kamshin sabunta ga kaya da
dady ya zubamata 'yan ubansun.
Naman kaza ta kawomana tare da drinks nanfa muka baje inabata labarin abinda ya hanani
zuwa jiya nida yaran.
Oh muna nan zaune Amma kiran ya Usman yakai bakwai duk yana tambayar yatake,Sainaji
sun birgeni sosai.

Bayan munyi sallar la'asar saina kamamata muka gyara gidan,Saiga sakon Abinci daga
matar baba habu gakuma na hajiyata.
"Inye zahra 'yar gayu haka ake gatantaki Ashe,Baridai mutashi mu wuce kadda dady ya Kira
yai fad'a.

"Kai dan Allah aunty kijira sweety ya shigo mana yanzu zai dawo Allah.
Bakina bude nake kallonta kamin ince ah lallai ya usmandinne sweety?

Dariya ta saki"Ah lallaima waida nufinki yanda kowa ke kiranshi haka nima Zan dinga
kiranshi? Kai ina bazai yiwuba danhaka share kawai.

Da sallamarshi ya shigo hannuwanshi dauke da ledoji,fuskarnan kamar me tallar hakora
tsabar washesu da yayi.

Sannu da zuwa duk mukai mishi kamin ta wuce da kayan hannunshi kitchen,Shikuma ya
nufo wajena bayan ya mannamata kiss agoshi babu ko kunya.

Hannuwana ya rike yana murmushi,Autar hajiya bata fuskar duk na mene inace nabaki
hakuri ko? Wallahi sabida zahra yasa banzuwa gidanki kinga inajin kunyar dady amma tunda
yanzu na aureta insha Allah zamu dinga zuwa wajanki akai akai kinji ko?

Kaina na d'aga mishi tare da lafewa ajikinshi Allah yasani inason Yayana sosai bani da sama
dashi ahalin yanzu,Shine komaiba duk da cewa Hajiya bata rageni da komaiba amma hajiya
kakatace Amma shi yayanane cikinmu daya dashi shine nake kallo amatsayin mahaifi agareni.

Shikanshi bansan tunanin daya lulaba yanadai rungume dani,Tausayina ke dawainiya dashi
sai yanzu yakejin kewar rashin iyaye da mukayi, Fatanshi Allah yasa dady ya jure duk wata
kuriciyata yakuma rikeni amana kamar yadda shima yai Alkawarin rike d'iyarshi Amana.

Zahrace ta kutso tsakaninmu tanafadin wallahi nima sai an rungumeni.
Dariya muka saki sannan ya rungumota itama hadda sumbatar goshinta,Sannan na yunkura
natashi daga jikinshi,Bari mukoma gida kadda dady ya kira.

Kayan ciye ciyen dayashigo dashi ya dibarmana sannan suka rakamu mota tana fadin
saimun hade school gobe kitaho da wuri dan Allah.

Da kaina na amsa Mata lokacinda nake Dora Mimi ajikina.




"""""""""

Wata irin kewa ce ta isheni babu hajiyata babu zahra sannan shima dadyn danadan Fara
sabawa dashi yanzu benan dagani sai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login