Showing 75001 words to 78000 words out of 84412 words
Chapter 26 - YARDA Book Complete by Maman khady.pdf
Yana dagoni nafara yunkurin amai Dan haka da saurinshi yaisama dani zuwa toilet din,
Saida nai aman duk wani Abu danaci cikin daren sannan nasami nutsuwa,Yayinda shikuma
duk ya rude sabida yasan hadda wahalar danasha ta tilastamin wannan aman.
Ina kwance ina sauke numfashin wahala shikuma yana gefena zaune yama kasa kwanciyar
saiwani jijjigani yakeyi yana matsamin jikina,Har saida yaga barci yai gabadani sannan shima
ya kwanta.
[5/24, 4:23 PM] Maman Dije: 68
Alhamdulillah Lafiya lau mukai sallama da daddy,Sai bayan yatafine nafara ramuwar barci Dan
sosai yabarni da ciwon jiki,Yaudai zahra babu bakin magana domin itama tunda ya usi
yakawota Dan yima daddy din rakiya taketa bin kujera duk inda tasamu kwanciya takeyi da
Alama itama irin lalurar data dameni takeyi.
Taso ta zauna gidanmu Amma ya usi ya matsa lallai su wuce tunda batajin dadin
jikinta,Nidai da idanu nabisu dannima ta kaina nakeyi.
"""***"""
Bayan wata daya: Kwance nake saman gadon daddy wata irin masifaffar kewarshi ke damuna
abinda bantaba tunaniba balle inkawoma raina,Duk inda na juya kamshinya nake shakowa
gashidai ya kwana biyu bashi cikin dakin dan hatta zanin gado na canza Amma k'amshin
turarenshi na kewaye da dakin. Kuma juyawa nayi tare da shafar dan Matashin cikina dake lahe cikin marata,Shi kanshi cikin
yai kewar dadynshi kwana biyu beji an tabashiba.
Inajin wayata tana ring amma wata kasala ta hanani ko motsin kirki balle in dauko wayar,
Saida aka kuma kira akaro na biyu sannan na dauka batare dana duba wake kirabama.
"Hello"
"Hey babyna kunyini Lafiya ya little babyna?
Wani siririn kukan shagwaba na sakarmishi,Wanda na tabbata saiya kassara kuzarin
jikinshi.
"Subhanillahi sorry babyna waye ya tabamin ke haka? Uhum gayamin waye?
"Daddy nagaji Dan Allah kadawo wallahi kewarka ta isheni,Ko dadin barci banaji kullun
bakanan!!!
Cikin wani irin farinciki ya kwashe takardun dake gabanshi tare da mikar da kafafunshi
yandazaiji dadin sosai ,Dan wata irin kasala yaji ta saukarmishi lokaci guda ga uwa uba kuma
shima kewar data addabeshi.
Ba k'aramin Dadi yajiba musamman dayaji wai Jidda na kewarshi ashedai hasashenya
yazama gaskiya cewa matarshi tafara kaunarshi Ashe dai hakanne.
"Alhamdulillah ya furta cikin zuciyarshi kamin yace"Kinga kwantar da hankalinki kinji,Kinga
yanzu har nayi wata daya da tafiya hadda kwanakima insha Allah kamar yaune zaki ganni
gabanki na dawo Amma bansan injiki cikin damuwa ko kinaso inkasayin aikin daya kawoni?
"Uhum uhum" shine abinda na furta cikin narkewar murya.
"Ok to ki kwantar da hankalinki zandawo kinji? Ya cikinmu yafara girma kuwa?
Dan shafar cikin nayi kamin ince"Kadanne daddy.
Murmushi yasaki Wanda harsaida naji sautinshiKamin yace to Alhamdulillah aidama ahankali
ahankali yake girma kinga lokacinda zandawo nasan ya girma sosai,Zantaho da kayan baby
masu kyau insha Allah,Ashe itama zahra cikin ta samu?
Kuma marairaicewa nayi,Eh fa daddy Amma ita batayin amai saidai zazzabi Amma ni kullun
sainayi.
"Ayya!! Sorry kema zaki daina kullun inayimiki addua gakuma lada da kikesamu ko? Kedai
kita hhakuri har indawo saina dinga tayaki,Kinadai dansamu kici wani abun ko?
"Eh daddy inaci Amma ba sosaiba.
"To shikenan Ammadai bawata matsala ko?
A a akwai daddy Mimi ke fama da mura Amma naba Sadiq kudi yasiyo Mata maganin mura
nan gidan babu maganin mura.
"Ok to hakan yayi Allah yaimiki albarka,Zankiraki kamin ku kwanta saimu gaisa da yaran.
Cikin shagwaba na furta Dan Allah daddy inkasami lokaci kadawo inganka wallahi nagaji DA
rashinka komai yadaina min dadi.
Wani murmushin jin dadi yasaki kamin ya shafi sajenshi"Karki damu autar mata insha
Allah,Nasan nafiki jin kewarnan musamman Idan na tuno da daddadan kamshinki da laushin
fatar jikinki sai inji Ina neman zaucewa balle idan na tuno da lafiyayyar ni'imar jikinki baby Allah
nayi kewarki irin sosai dinnan,Amma gayamin idan nadawo mezaki tarbeni dashi?
"Allah daddy duk abinda kakeso shizan baka indai zaka dawo din.
"Ok to shikenan kin yarda babu korafi kuma babu kuka ko?
Cusa kaina nayi cikin filo kamin nace kai daddy!!!
"Eh mana kadda danadawo adinga kuka aka kiran wayyo hajiya daddy zai kasheni.
Kashe wayar nayi Ina dariya dan sosai yabani kunya ashedama yanajin duk ihun
danakemishi Amma saiyaiwani biris dani yakoma kamar kurma.
""""
Ahaka mukacigaba da rayuwa cikin jin Dadi da farinciki hhankalina kwance haka na 'yan uwana
sabida bantaba zuwa nace gawata matsalaba,Duk da sunaganin kamar basu kyautaminba na
auramin babban mutun amatsayina na yarinya me k'ananun shekaru,Saigashi hakan ya
kasance alkhairi ga rayuwata,Kusan yanzu Sadiq shine ke komai na gidan sabida yanayin jikina
Amma kullun nikeyin girki,Sam yaran basu dawata matsala.
Shiyasa nakesonsu kamar kamar me,Kuma suma haka suke kaunata,Dan idan har
sukaganni kwance to suma kamar marasa lafiyar haka suke komawa inko inayin amai ai har
rige rigen zuwa yimin sannu sukeyi.
Alhamdulillahi bangaren makaranta banda matsala dan yanzu kullun inazuwa koda inajin
ciwon ina kokarin daurewa balle hajiyata kullun k'ara wayarmin dakai takeyi akan dukkan abinda
yashafi harkar cikin hakama hajiya kaka duk asabar da lahadi nan takeyini tare damu.
***
Zaune muke Muna hira sai kwasar dariya mukeyi,yayinda faruk da Mimi ke tausamin kafafuna
dasuka dameni da ciwo yau tunda mukadawo makaranta.
"Kunga gobe tunda babu islamiyya dawuri zamudawo makaranta to mu wuce gidan zahra
Kawai muganota kunga yauma bataje makarantaba.
Faruk ne yaimin sigina yana kallon Mimi Dan daddy yahanamu fita kwata-kwata to shine
damunfita itake gayamishi.
Riko kunnuwanta nayi tare da zaromata manyan idanuna"Kinsan Allah Mimi idan kikagayama
daddy munfita sainasa yaya Sadiq ya mikama karnuka ke kuma bazamu kuma fitadakeba
saidai ki zauna gida keda megadi.
Bakinta ta turogaba kamintace nabari aunty bazan kumaba kumama AI daddynne ke tambayata
Ina mukaje
Harararta nayi kamin ince nadaigayamiki Allah kuwa.
[5/24, 4:23 PM] Maman Dije: 69
Tun asuba yau ban komaba sabida samakaina zuwa gidan zahra danayi, Saida mukagama
aikin komai sannan na hadamana tea kawai mukasha muka fice,Bantsaya yin girkin ranaba
sabida nasan bazamu dawo gidan da wuriba.
Aiko yauba batazo makarantarba saidai waya da mukayi tace da sauki Sosai.
Wani bata fuska isiya Direba yayi lokacinda nace ga inda zai kaimu.
Banza nai dashi Dan karma yaga fuskar tambayata nasandai daddyne yagama yimishi
kashedi akan kaimu wani waje.
"Isiya ko muhau napep ne?
Sosa kanshi yayi A a hajiya muje Ammadai bazaku jimaba ko?
Sadiq ne yadan harareshi,Kamin yace Sannu daddy"
Duk dariya mukasaki sabida yanda Sadiq din yai maganar,To dama kowa yagaji da zaman
gidan,Balle kuma su maza musamman shi Sadiq din dayafara girma ko kwallo dadyn ya
hanashi fita kuma ga yara nayi irinta cikin unguwa haka.
""**""
Kai gaskiya ciki manyane,Duk karadinnan na zahra babu shi tai laushi sosai gashi sai aikin Tara
miyau takeyi abaki.
Dariya nasaki sosai hadda kwanciya ganin yanda taiwani dai-dai Saman kujera daga ita sai
bes idanu duk sunfada.
"Hahhha wayyo dadi kasheni,Zahra kintuna iskancin da kikrmin akan wai Dan naga daddy
na lallashina shiyasa nakekuma lauyewa to yau gakinan ba baka sai kunne.
Hararata tayi ta mike taje ta zubar da miyan bakinta,Saigata dawani danyen lemon tsami
waishi take lasa, kutt Ammadai cikinnan ya kwareki da yawa wlh.
Zama tai tare da yamutsa fuska,"Dan Allah kidaina dariya aunty wallahi gabadaya banjin
dadin rayuwata yanzu nifa cikinma harnaji bansanshi wlh.
Murmushi nayi kamin ince Wallahi zahra garake kinacin abinda kikeso kuma ya zauna tunda
bakiyin amai Amma nikumafa? Ko ruwa nasha wani lokacin sainayi amanshi,Kuma rabon da
inci wani abinci mesunan abinci harna manta saidai yame yame suma bakowanne ke
zamaba,Kinga ko ai gara ke.
"Eh hakane gaskiya gara ni inaga so biyu kawai natabayin amai wlh Amma yanzu haka
jinake duk nagaji dashi, gaskiya Allah ya sakama iyayenmu da mafificin Alkhairi.
"Ameen kedai bari kawai wani lokacin bansanin ina hawaye sainaji zubar ruwa sosai cikinnan
ke gwalani wai yanzuma kinsan abunda ke damuna kuwa?
"A a inafa zansani saikin gayamin.
"Wallahi zahra wata irin kewar daddy ke damuna, Sosai nakejin damuwa aduk lokacinda
natuna yaimin nisan da zaijima bai dawoba,Gashi indare yayi ko barcin kirki ban iyawa sosai
sabida tunaninshi.
"Hahhhhha wayyo dadin duniya,Allah dai ya biya daddynmu,Alhamdulillah,wallahi naji dadi
sosai ashedai daddy beshiga zuciyarki da wasaba!!! To hakan yayi Amma yakamata ki
gayamishi danyai kokarin shigowa tunkamin kewar ta tabamana baby tunda kince baki barci
sosai,Ah Lallai Abu yayi kyau.
Jingina nayi da kujera tare da lumshe idanuna,Tunanin tattausan Lib's dinshi ya fadomin da
irin zazzafan kiss dinshi, jinai gabadaya tsigar jikina tatashi,Bude idanuna nayi na saukesu akan
zahra dake aikin kallona tana sakin murmushi.
Dan tsaki naja tare da kauda kaina ga barin kallonta danna lura shakiyanci cikin jininta yake,
dangashi bata da Lafiya Amma ta na nema naimini hakan.
"""""""
Akace kwanci tashi asarar merai,To lallai kam dangashi kamar yaune daddy yai shirin tafiya
saigashi yanzu da watanni uku hadda sati dayama.
Zuwa wannan lokacin gabadaya nafita hayyacina kumafa karkuyi zaton laulayin ya maidani
haka A'a ko kadan kawai tsabar kewar mijina ke wahal Dani kullun da tunaninshi nake kwanciya
kuma dashi zantashi duk da cewa koda yaushe muna waya dashi danwani lokacinma idan
yakira da dare tofa sainayi barci yake kashe wayarshi,Duk kuma aikin lallashina yakeyi Amma
duk da haka bangane komai nidai kawai bukatarshi nakeyi kusa dani.
Gashi sunkuma bashi sati biyu akan wata ukun da yayi.
Ranar dayagayamin cewa sunk'aramishi sati biyu saida naimishi wani k'aramin hauka sabida
tashin hankali da damuwa,Dan nasa rai sosai DA zuwanshi,Ranar nan Hajiyata da Hajiya kaka
suka yini suna lallashina Amma haka na yini kuka.
Iyakar tashin hankali ya shigeshi Sosai yaji aikinma ya ficemishi arai sabida halin danashiga.
Bayan kwana hudu; Kwance nake Ina barci kasancewar yau asabar tun safe nake kwance
sabida kwalemar da mukayi jiya saida mukaima gidan tas Sannan muka kwanta.
"Aunty,"Aunty daddy na kiran wayarki.
Yamutse fuska nayi kamin ince"Kai Sadiq nacefa kabar tashina idan ina barci ko kanaso
kaina ya isheni da ciwone?
"A 'a aunty yi hakuri naga daddyne ke kiran ko yanada muhimmanci kiran shiyasa na
tasheki,Kumama ai yakamata kitashi hakanan kici abinci.
Amsar wayar nayi Ina tambayar"Kai Ina Mimi karfa kabari tafita waje mubani kaga jiya
hakatai shi megadi yanacan yana gyangyadi zata fice ta barshi.
"Hello daddy,
Ajiyar zuciya ya sauke kamin yace"Uhum amaryar daddy ya kuke ya jikinki?
"Alhamdulillah daddy komai lafiya.
"Masha Allah Amma yanaji muryarki haka babu matsala ko?
Tashinai daga falon na nufi dakinshi,Saida na kwanta tare da rungume filo Cikin
jikina"Daddy Dan Allah kadawo hakanan wallahi nagaji nakusa komawa wajan hajiya tunda
bazaka dawoba.
"Ah subhanillahi kadda muyi haka dake Dan Allah ki rufamin asiri zandawo ko zuwa jibi ne
hakan yaimiki?
Cikin zumudi da murna nace DA gaske daddy?
"Insha Allah babyna indai hakan yaimiki ba matsala zanyi duk yanda zanyi danganin nazo
gareki,Amma yaya kikejin cikinmu yana motsi Lafiya lau ko?
Hannuna nakai na shafashi kamin nace yanayi daddy komai Lafiya lau,Amma dai DA wuri
zaka dawo ko?
Wani k'ayataccen murmushi yasaki Kamin yace kadda kidamu duk yanda kikeso autar mata.
Cikin farinciki yaudai mukai sallama kamin infice falo ina murmushi,Hannu na mikama Sadiq
muka kashe kamin ince yaro daddy jibi ya na nan tafe.
Tsalle yai ya dire saman kujera Ammadai naji dadi wallahi haba aigara yadawo Abu wata da
watanni.
"To yanzu Sadiq ta Ina zamu Fara gyaran gidannan?
Idanunshi kalar na daddy ya fiddo waje kamin yace Kai Aunty kibari Dan Allah yanzu kuma
me wannan gidan yayi? Inacewa Allah yabani Mata me tsafta kamarke Amma gaskiya yanzu na
canza gara wadda batakaikiba yo aunty ai taki tayi yawa wallahi,Dannasan wataran amatsayina
na megida haddani zantaya aikin.
Dariya nasaki me sauti"Kai Sadiq yanzu sabida Allah sharri zakamin ?
"Bawani sharri wallahi ai idanma daddy yaji kina wannan aikin DA cikinnan wallahi saiyayi
magana sabida Allah jiya inane bamu toneba cikin gidannan saikace injina haka kika maidamu
kuma yau kice ya za ai? Tab ai Allah sai ingudu gidan Hajiya kaka inyi zamana.
Murmushi nayi to shikenan naji yanzu saimu canza zannuwan gado da labulaye Ammafa
sai gobe danni kaina har yanzu jikina ciwo yakemin.
"Ahaf aidama nasan dole kiji ciwon jiki yanzu Allah ya kaimu goben lafiya saimu canza abinda
kikace din,Amma me zamu dafa da darene yau?
"Kagane ko Sadiq kawai kabari idan kafita magriba ka siyomana tsire can tsallake,Wallahi
kasalar girkin nakeji.
"To shikenan Allah yakaimu aunty,Allah ya rabaki da cikinnan Lafiya muma muhuta da ganin
rashin lafiyarki.
Ranar litinin babu yanda Sadiq beyiba muje makaranta Amma nakiya nafison dai muyi
komai anatse balle inaso inyima daddy abinci nagani na fada,To idan naje makaranta karfe
nawa zandawo kuma harmuyi abinda yakamata.
Lokacinda Sallar azahar tayi ai tuni komai ya daidaita hatta wanka munyi jiran shigowarshi
kawai mukeyi,Musamman ni danakejin kamar inyi tsuntsuwa inganni cikin faffadan kirjinshi.
Mimi ce ta rabo jikina"aunty zai dawo kuwa?
"Zaidawo mana Mimi bakiji tun dazu yace sun saukaba nasan sunkusa karasowa
yanzu,Zaikuma dawo Lafiya insha Allah.
Hon..din motar daddy yasamu mikewa gabadaya muna rige rigen ficewa dan ban yarda su
rigani zuwa gareshiba kowa tashi ta fishsheshi.
Fitarmu harabar gidan da gudu yasa daddyn Saurin fitowa daga motar bakinshi hangame ya
na niyyar dora hannu aka,Be Bari mun karasa gareshiba ya iso da sauri ya hademu gabadaya
ya rungume yana dariya.
Jinai harwata hajijiyar nishadi ke neman kayar dani lokacinda najini cikin jikinshi.
Cikin kunnena ya radamin"Anya Jidda kinada hankali kuwa da wannan abun ajikinki kike
gudu salan kijamin asara ko?
Duk ficewa mukai daga jikinshi muna dariya kowa fuska awashe, Shikuma saiya dauki Mimi
akafadarshi yakama hannun faruk zuwa cikin gida.
Sadiq shine ya shige gaba danhaka shine zaifara aiwatar da shirinmu na farko dan tarar
daddyn.
WELCOME HOME DADDY.
SHIne Abu nafarko dayafaramishi Sannu da zuwa Dan jikin kofar shiga falo muka likashi.
Juyowa yai tare da kashemin ido daya ya na murmushi.
Wasu kankanan takardu suka fara zubowa masu kamshin gaske lokacinda ya zura kafarshi
cikin falon gawani mayen kamshi dakekuma gauraye ko Ina na falon Dan sosai kamshin keda
daukar hankali.
Lumshe idanunshi yayi gabadaya yanajin wani irin matsanancin farinciki dakekuma baibaye
zuciyarshi,Alhamdulillah ya Allah,Allah na godemaka da dukkan Alkhairinka gareni Allah Kaine
abun godiya.
Kuma rungumemu ya dingayi daya bayan daya tare DA mannama kowa Sumba agoshi.
Kan kafet ya zauna tare da mike kafafunshi yana kallon inda tsafta take,Saika rantse da
Allah sabon gidane ba a kaiga tarewaba tsabar yanda ko Ina yake tsaf ya na sheki.
Duk gaidashi mukayi ya amsa yanata murmushi yayinda yaketamin wani zazzafan kallo me
matukar ratsa jiki.
Be matsa konan da canba Sai bayan la'asar lokacin yaci ya koshi kuma munsha hira.
Sannan yace na hadamishi ruwan wanka Idan Zan iya dannaga kinyi nauyi ashe.
Dan murmushi nayi kamin na mike Ahankali,Haka ya bini DA kallo cannaji ya na tambayarsu
"auntynku nacin