Showing 3001 words to 6000 words out of 84412 words
kaina yayinda idanuna suke
lumshe harwani sauke numfashi nakeyi,Dan wani irin barci ke neman yin awon gabadani duk da
nasan ba lallai tabarni inyiba tunda yamma tayi.
"Inason kalar gashinki dan irin na mamanki ne lokuta da dama abbanki kan hanata yin kittso
wai yafison gashin ahaka'Cewar hajiya.
Kuma muskutawa nayi ina murmushi,Dan ba k'aramin dadi nakejiba aduk lokacinda take
bani labarin mahaifana.
"Uhumm ashedai Abbana dan soyayya ne shima inasonsu DA yawa hajiya nayi kewarsu.
Shafa kaina tayi tana hadiye wani kululu daya sakkomata kadda ki damu suna cikin
kwanciyar hankali da farinciki kedai ki dage dayimusu addua kinji KO?.
"To hajiya.
*** *** ***
"Zahra ki tsefe kanki ai kitso yau kinji ko?
Turo bakinta tayi kamin tace dady tun jiya nakecema zamuyi magana amma ka shareni
kumafa nasan kanasane.
"Zahra kemafa kin iya rikici hadda na banza gayamin meya faru?
Kuma matsawa tayi jikinshi yayinda kirjinta kewani irin matsanancin bugu,Dady dama akan
maganar da mukayi dakaine Dan Allah kadda kace a a dady kadda ka juya baya hakanshine
farincikinmu.
K'ureta yai da manyan idanunshi yana kallonta yayinda zuciyarshi tai wani irin
bugawa,Shifa ganewa kowa beyiba Amma wallahi tsoron matan yakeji duk da yanacikin
matsanancin buk'atar macen.
"Uhumm ina jinki 'yar gidan waye? Kuma Ina kikasanta da har kikai mata YARDAr da zata
iya shigowa cikin rayuwarmu?
Wani irin numfashi ta sauke tana sadda kanta k'asa Dan sai lokacinne taji wani mugun
shakka da zullumin yimai maganar,Dady, Dady jiddace wadda mukeso ta maye gurbin
mamarma idan ka amince da hakan.
Shiru falon ya dauka nawani lokaci yayinda idanunshi ke kanta yana karantar duk wani
motsinta.
"Uhumm zahra jidda da yawa cikin garinnan kimin bayaninta da inda take idan naga dacewar
hakan sai inyi yanda kikeso ko
"Dady Jidda k'awata wadda muke karatu tare nasan ka santa ai?
Wata irin zazzafar dariya yasaki wadda tasa gabadaya yaran maido hankalinsu kanshi sunamai
kallon mamaki domin dariya ba d'abi'arshi baceba komai zai faru bewuce murmushi. Yatsanshi
yasa yana nuna zahran yana dariya saida yayi me isarshi sannan ya sarara,"Nagode zahra KO
babu komai yau kinsani nishadi Wanda narasashi tun kamin rasuwar mamanku,Amma inaso
kima daina wannan tunanin dama nasan da wuya idan ba shirme zakiyiminba inba hakaba
daganace nabaki zabi zahra saikimin maganar wannan danyar yarinyar wadda ko zata girmeki
da kadanne? To bama hakaba ni kodacan danake saurayi bantaba sha'awar auran k'aramar
yarinyaba mamanki ahekararta sha Tara na aureta lokacin inada ashirin da biyu koda kike
ganina haka zahra inada shekaru bawai yaro bane ni, Dan hakamudaina wannan maganar
kedai kawai kitayani da addua idan inada rabon kumayin auren to Allah yabani ta gari wacce
zatayi daidai da tsarina,Amma ke yanzuma ai abin aimuku dariyane ace mahaifinku ya auri
k'ank'anuwar yarinya kamar wannan ko? Ya idasa maganar har lokacin yana dariya mara sauti.
Bakinta ta tunzura tare da tashi tabashi waje tuni idanunta sunfara zubar da hawaye Dan
takaici.
Da kallo yabita fuskarshi cike da murmushi shi abunma mamaki da dariya yabashi kamarshi
da auran sa'an diyanshi ai abun aimishi dariyane ma.
Ganin yaran natakallonshi har lokacin yasashi watsamusu hannu tare da d'agemusu gira.
Duk maida hankulansu sukai akan kallon da sukeyi amma bunu-bunu sun waigo su kalleshi
dole yasashi tattare kayan da yake aiki dasu yatashi,Kuma har lokacin murmushin be gushe
daga fuskarshiba.
K'okarin shigewa bedroom dinshi yakeyi saiga zahra tafito janye da akwati tana kuka.
Kirjinshi yaji yai wani irin bugawa Ashe da gaske take,Watsar da takardun hannunshi ya
nufeta yana kwace akwatin hannunta,"Ke bansan hauka da rashin hankali gidan ubanwa zakije
nifa bansan rashin hankali da Neman fitina Ina zaki?
YARDA.
5
Wani irin kuka tasaki me matukar k'arfi Wanda yakuma rudashi balle da sauran yaran suka
nufosu ko wanne fuska akwabe alamar kukan zasu taya yayarsu.
Rungumeta yayi ajikinshi yanadan buga bayanta alamun lallashi zuciyarshi ta raunana Dan
beyi tunanin da gaske takeba.
"Kinga ku koma d'aki kidaina wannan kukan zanyi shawara da hajiya kome kenan saimuyi
magana amma ni bansan wannan damuwar haba mana fatimana ko so kikeyi duk ki sakamu
cikin damuwa?
"Girgiza kanta tayi tana kuma sharbe hawaye,Ammafa cikin zuciyarta cike take da farinciki
tunda dai magana zataje wajan hajiya to kuma dama sungama tsara komai.
Tun shigarshi cikin d'akin zagaye kawai yakeyi tsabar damuwa da tashin hankalin dayake
ciki,Yanason farin cikin yaranshi domin beda kamarsu saidai bejin zai iya biyemusu Dan
wannan dalilin idan har auran sukeso tayi to gara ya nemi babbar mace ya aura hakan
zaifimishi sauki akan auran wannan kwailar yarinyar me shagwabar tsiya. Kayanshi ya canza tare da daukar key din motarshi yabar gidan dole ya sanarma hajiya da
maganar nan tunkamin abun yai nisa har rayuka su baci, gara idan fada zaikai zahra din aimata
to da sauki akan hakan.
***
Zaune muke muna hira nida hajiya sa ya Usman Wanda lokuta da dama nake kiranshi da ya
usi,Hankalina kwance NA kalleshi jiya kanacan yawonka zahra tazo da kakarsu hajiya kuma
sunjima wlh.
"Mirmushi yayi yana shafar suman kanshi tare da kallon hajiya,Aiko bansan zasuzoba Dana
tsaya mun gaisa inafatan kinadan shigar dani wajanta Dan gaskiya nida gaske nake indai
sunshirya.
Hajiya dake rike da haba takama dariya"Lallai yau naga yayan banza kai bazaka iya kai
kankaba sai k'anwarka zata tura aiko indai hakane inaga baka da rabo cikin jikinta.
"Kai hajiya"Kai hajiya Dan Allah yanzu idan bakinki beda kyau ai shikenan kin kasheni
kinyimin baki haba mana,Wallahi Ina sonta da gaske,Kinga auta tashi ki shirya mukai musu
ziyara ma.
Da gudu na shige dakina na shirya cikin atanfa Riga da siket bawata kwalliya nayiba amma
fuskata fes take Dan sosai nakeda baiwar kyau.
Wani irin k'amshi nakeyi me kwantar da hankali Dan nifa akwaini dason k'amshi koda yake
gadanayi wajan hajiya nima
Gefenshi na zauna Ina cewa to yanzu gidansu zamuje ko gidan hajiyarsu sabida ba lallai
ataddasu waje dayaba balle yau asabar.
"Haba ai kamata yayi ace ko k'ananun waya akwai ahannunku domin ganin
junankuma,amma muje gidan kakarsu din kawai idanma basunan saita kiramanasu amma
zuwanmu gidansu akwai matsala tunda basu da mahaifiya.
*** ***
Zaune yake gabanta k'afafunshi atankwashe yana faman jiranta bayan yagama koramata
bayanin duk abinda ke faruwa.
"Hummmm To ai Ni abinne ya dauremin Kai wallahi kuma wannan abun duk laifinkane babu
yanda banyi dakaiba akan kanemi matar aure idan ma ba kaiba kodan yaranka amma alokacin
sabida bakason maganar saima ka dauke k'afa da zuwa gidannan saida na nemeka nariga
nagamaka yaranka na buk'tar matar da zata zama uwa agaresu tunda kai biris da maganar
aigashinan yanzu diyarka taimaka zabi ko?
"Umma Dan Allah kice wani Abu nidai kiyi hakuri sabida Allah Ina zankai sa'ar diyata? Bama
wannanba wayasan kalar haukan da zasu dingayi cikin gidan bannan Dan wallahi wannan
yarinyar tafisu rikici Dan gata yaimata yawa.
"Uhumm yanzudai kasa direbanka ya kawomin su zahra din kaikuma ka kiramin yayanku
yazo kawai aje gidansu ayi tambaya danni hakan yayimin daidai dama duk Wanda beji bariba ai
saiyaji woho.
"Kuma marairaicewa yayi yanajin yanakuma shiga wani mugun tashin hankali,Idanunshi ya
zubama hajiyar yanajin kamar ya Dora hannu aka yaita sakin ihu kozaisami sukuni.
Wayarshi yasa yakira habu Direba sannan ya kira yayanshi din kamar yadda hajiyar ta
buk'ata sannan yakoma gefe ya makure saikace almajirin daya rasa abinci.
Suna nan zaune zaman shiru lokaci zuwa lokaci hajiyar NA kallon yaron nata tausayinshi
takeji sosai,Saidai tanaso yasami nutsuwa shima kamar sauran magidanta tunda yasami shaida
kudi basu rudeshiba yafara harkar banza dukda yanada damar hakan saidai gara adauki mataki
tunkamin abun yazo yafi karfinshi,Dan sha'awa mugun abuce.
Sallamar Alhaji musa tasa dadyn kuma tunzuro baki kamar k'aramin yaro danshima dadyn
autane Amma ahaka har yakema wani sherin shagwaba.
Dariya Alhajin yayi kamin yace"hajiya meya farune naga autanki nata kumburi kamar fanke
yaji yis
Dariya tayi sosai kamin tace kaimadai ka fadi waifa ahaka wata yakema sharrin tacika
shagwaba alhalin gatashinan alike yana fama da ita,Diyarshice ta nemomishi matar aure shine
yazonan zaimin rikicinshi.
Gama bayaninta ga Alhaji musa saiga su zahra sun dira gidan,Nanfa Falon ya dauki wani
shiru na musamman.
Sallamar mu cikin falon takusa dauke numfashin dady Wanda dama yake cike da fargaba
musamman ganin har lokacin zahra bata da walwala.
YARDA.
NA maman khadija.
6
D"aure fuskarshi yayi tamau irin karma arainashi dinnan,Ammafa saiya samu kanshi da kasa
dauke idanunshi daga gareni so yake yaga wata alama dazatasa aga dacewar aurena dashi.
Tsallen zahra da ihun su faruk yasaka hankalin kowa komawa kanmu rungumeni sukayi
muna murna,Akunyace ya usi ya gaidasu sannan nima na gaidasu muka wuce cikin bedroom
din hajiya kaka.
Tsam yatashi kamin yace hajiya bari injirata waje kamin sugama gaisawa dama wucewa
zamuyi nace bari inbiyo mu gaisa ashema su zahran na nan?
"Eh fa amma aidakayi zamanka usmanu ai anriga anzama daya ko?
"Babu komai hajiya bari injirata waje.
Ajiyar zuciya dadyn ya sauke me k'arfi tare da maida hankalinshi kan hajiyar ya kafeta da
idanunshi jiyake duk ya muzanta.
"Dariya tayi kamin tace"dady me amarya lallai zakasha amarci.
Dariya alhaji musa yayi shima kamin yace"To kai Habib menene na damuwa akan wannan
lamari tunda sunaso kawai zamutayaka da addua amemakon kaje ka dauko babbar mace
wadda zata wahal dakai da yaranka ko?
"Uhumm nima abinda nake nunamishi kenan to Amma kasan habibu da shegiyar kafiyar
tsiya.
"Yanzudai kaje ka kwantar da hankalinka saimusan abinda za ayi kaga tunda har
makarantarsu dayama ai abun zaizo da sauki kaima zakasami nutsuwa tunda yarinyace amma
auran babba bazaimakaba ayanzu,cewar Alhaji musa.
"Fuuuu yatashi yabar gidan yana sauke numfashi Dan sosai yaji ranshi yabaci musamman
dayakejin sautin su zahra din sunata shewa jiyake kamar ma dashi suke.
Da kallo suka bishi lokacin dayabar gidan,Kamin hajiya ta dora da cewa"Uhum kyale sakarai
nan gaba kadan zakaga yafara jin dadi harma fatarshi ta canza tunani yakeyi sai babbar
macece zata iya kulawa dashi sabida shirme,Yanzu kaje ku shigemai gaba komeyakamata kuyi
kuyishi Dan Allah inafatan Allah ya doramu akansu su amince mana da auran ayanzu domin ba
lallaibane su yardaba indai ba itace ta nuna tanasan hakanba.
*** ***
"Kai kuje falo zamuyi magana idan mukagama saiku dawo,Cewar zahra tana harararsu Mimi da
suka cika dakin da hayaniya kowa k'okarin bawa jidda labariyakeyi.
"Harararta nayi nace saikimin bayanin abinda yasa kika korarmin k'anne.
Dariya tayi kamin tafara magana cikin yanayi aji tausayinka,Jidda kinsan Ina sonki Ina kaunar
zama tare dake sannan na YARDA dake Dan Allah ki temakamin kamar yadda Allah yabaki ikon
iya temakon Dan Allah ki amincemin da wannan bukatar tawa kinji?
Haka kawai naji jikina yai sanyi tare dajin faduwar gaba,Amma hakan be hanani riko
hannuwantaba"Karki damu zahra munriga munzama daya kawai ki gayamin meyafaru?
"Uhumm ba fadinba jidda Alkawari nakeso kimin.
"Murmushi nayi kamin ince karki damu naimiki Alkawari insha Allah duk abinda kikeso indai
har inada dama babu abinda zai gagara.
"Hannuwana takuma matsewa cikin nata kamin tace nagode jidda Allah yasakamiki da
alkhairi,Dama Alfarmar danake nema wajanki shine inaso ki amince ki auri dadynmu kidawo
gidanmu da zama.
"Atsorace na fisge hannuwana daga cikin nata tare da zubamata manyan idanuna,Kirjina
kamar zai fashe tsabar fargaba da tashin hankali"Dakyar nacemata Anya kinada hankali kuwa
zahra nice Zan auri dadyn?
"Temakamana zakiyi jidda dan Allah ki tausaymana bamusan kalar wacce zai daukoba Dan
Allah.
YARDA.
NA maman khadija.
7
Wani kallon banza nabita dashi kamin in mike tsaye,Bazan iyaba zahra bazan iya auran dady
ba keni babuma tsarin aure ayanzu cikin rayuwata duka nawa nake? Sannan saikice in auri
dady? Shi kanshi yace ya Auri wa?
To bama wannan ba idan har kikai tunanin sabida inasonki ne kuma na YARDA dake zakimin
wannan abun to kisani ni bazan iya wannan cin amanarba baban k'awata wadda NA amince da
ita na YARDA da itane Zan aura? Kai Ina badaniba wallahi danhaka kinga tafiyata,Dama ya usi
ne ya matsamin in rakoshi tunda kinsan sonki yake amma wallahi indanasan wannan maganar
Zan tadda da baki ganniba zahra.
Kwace jikina nayi NA raba ta gefenta Zan wuce saidai hakan ya gagara dankuwa hajiya kaka
na tsaye ta tare kofar da Alama tajima wajan tsaye.
Kukan zahra ya cika d'akin wani irin kuka takeyi me matukar taba zuciya da sauti me k'arfi
Wanda hakan yajawo hankalin kannenta dake falo shigowa kamin wani lokaci suncika d'akin da
kuka.
Nima gefe na durkushe tare da fashewa da kuka yo ai abinne daban mamaki tare da
rikirtawa yo yaushema hajiyata zata yadda da wannan maganar.
Saida sautin kukan kowa yafara k'asa sannan hajiya kaka tafara magana cikin hali na alhini
dakuma Tausayi"Inaso ku saurareni kuji abinda zance domin wannan koke-koken babu abinda
zai harfar muku sai k'arin damuwa danhaka ku kwantar sa hankalinku duk ku saurareni.
"Ke Jidda dake Zan fara da farko inaso inbaki hakuri akan wannan maganar sannan kuma
inaso ki fahimci inda wannan maganar ta dosa dangirman Allah Ina rokinki Dan soyayyar da
kikeyima iyayenki kiyimusu wannan alfarmar jidda,Kinsan dai yanda wannan zamanin yake
acakude kuma ahargitse Wanda mutane da yawa babu abinda sukasagaba sai hassada da
bakinciki sannan uwa uba mugunta kusan kowa kanshi yasani ko dukiyace da mutun yafison
yacita dagashi sai yaranshi,Mata sunason me kudi komai mugun halinshi yayinda maza keson
Mata kyawawa koda basu da tarbiyya,Kinga kenan kotawane bangare akwai matsala KO?
"To hakanne yake kasancewa ga maza wa inda suka rasa matansu,Daga lokacinda namiji ya
rasa matarshi tafarko ma'ana uwar 'ya'yanshi shikenan saiya kasance cikin zullumi da tashin
hankali sabida tunanin yanzu da wacce zai zauna sannan zata soshi tsakani da Allah kuma ta
kula da wa innan yara nashi? Tabbas wannan abun damuwane da tashin hankali to wannan k'addararce ta fada akan
habibu yanason matarshi Jidda so irin na kwantance saidai lokacinda sukafara Tara iyali kawai
sai Allah ya dauke rayuwarta,Shikenanfa saiyashiga cikin garari damuwa da tashin
hankali,Wannan daliinne yasa babu kalar matsawar da bamuyimishiba akan yai aure tun Mimi
na jaririya amma ya kiya sabida beyarda da kowaba akan yaranshi gani yake kowa zai iya
cutarsu,Dan Allah kinga laifinshi jidda?
Yana bukatar kulawa amatsayinshi ta cikakken me gida amma yarasa kuma sabida
farincikin yaranshi ya hakura,Wanda ahalin yanzu Allah ne yasakama diyarshi hankali da
nutsuwar tunanin yakamata yai auren data matsamishi shine yace yabata zabi,Itakuma taga
babu wacce ta dace da wannan matsayin kamar ke,Dan Allah jidda ki amince da hakan kizama
cikin family Dina hakan zaisani farinciki,Bazai hanaki karatunkiba kinga gaki ga k'awarki kuje
makaranta tare kuyi girki tare Ku gyara gida tare sannan Ku kula da kannenku,Idanma bazaku
iya aikinba Zan nemi dattijuwa wadda zata dinga yimuku sauran ayyuka kinji?
Tsawon lokaci d'akin yai shiru sai sheshshekar kukana Dana zahra dake tashi lokaci zuwa
lokaci.
"Mikewa nayi tare da rabawa ta gefensu na fice daga gidan yayinda zahra tabini da sauri
saidai tuni nakusa shigewa mota ma.
Batadamu da kayan dake jikintaba ta dawo gabana tana kuka"Dan Allah jidda ki amince
kinji kadda kitafi bakice komaiba!!!
Idanu ya zaubamana yana mamakin meyakawo wannan tashin hankalin haka alhalin yaga
yanda muka cika da farincikin ganin juna da farko? Rungumeni yayi jikinshi