Showing 36001 words to 39000 words out of 84412 words

Chapter 13 - YARDA Book Complete by Maman khady.pdf

12 Jul 2025

2606

k'awa ta gari kuwa tuni inaga tazama 'yar hannu dankuwa daga wannan lokacin lif
kakeji nidai ko alamar wani tashin hankali daga gareta bankumajiba saima wani gogewa da
takeyi tana kuma cika.


Zaune muke cikin gidanta dagani sai ita,Sai kwasar hira mukeyi bakajin komai sai sautin
dararrakinmu dan lokacin labarin harka,ake bani akan yanda take wana ya Usman dan sosai
yake beda hakuri akan harkar tunda yasan dadinta.

Niko farinciki yagama cikani ganin yanda suke zamansu Lafiya lau.

"Aini ko zahra maganinki kenan wallahi dama nasan tsaf zaki shiga taitayinki matukar ya usi ya
cafkeki amma ya kikeyi da zafin wajan koya daina?

Madara da zumar data hada ta mikomin a kofi anshinan kisha,Gara indinga yima dadyna
tanaji kamin yadawo yacika aiki, Kina maganar zafi ai yanzu nazama tsohon hannu madam
wallahi yanzu babu zafi sosai idan ya likeminne saina dingajin wajan Nata zafi ammadai yace
ahankali zandainaji.
Cire tagumin nayi ina kallonta"Oh ni zahra yanzu lafiya lau kukeyi babu wata matsala?

"Yo eh mana wallahi yanzu Lafiya lau, sai shegen dadi.

Harararta nayi Ina mamakin ta tuni harta Saba kenan,Kamar yadda dady yace datasaba

zakiji shiru.

Lumshe idanuna nayi Ina lasar lebunana sabida dadin zumar da nakesha.

Sallamar ya usi tasamu nutsuwa,Abun mamaki sainaga zahra da gudu ta mak'aleshi tana
dariya,Shidinma rungumeta yai jikinshi tare da sumbatar bakinta.

Kunya tasani sadda kaina k'asa Ina mamakin iskancinsu ko kunyata basuji.

Saida sukagama lashe-lashensu Sannan ya karaso inda nake muka gaisa,Yana tambayar
Ina yaran suke?
Banwani kalleshiba sabida kunya nace"Suna. Wajan hajiya kaka anjima idan direban ya
daukosu zaibiyo ya daukeni saimu wuce gida,Ya usi kacemin zahra zatazo naji shiru har
yanzu!!!.

Murmushi yayi yana amsar ruwan da zahra din kebashi,"Kekam auta kincika Neman fitina to
zatazo amma sai dady yadawo saimuzo muyi mishi sannu da zuwa,Ainaji gobe zai dawo KO?

Hannuwana na Dora akirji tare da zare idanuna dan sosai zuciyata ta razana dajin
maganar"Kai ya usi ba gobe bane!

"A a aiko gobe zai dawo dan munyi waya dashi Dazu yakecemin gobe zai dawo dan yagama
abinda yakeyi yanzuma Hutawa ya tsaya yi da yau zai dawo.

Wani irin miyau na hadiye Ina maida numfashi shikenan nashiga uku dan wallahi ban
shiryama dawowarshiba koda yake aiyace ni yarinyace rainona zaiyi.

Zaman da bancigaba dayiba kenan na hada inawa inawa ya usi ya kaini gidan hajiya
kaka,Ko gidan Nata kasa hakuri nayi musamman danaga saiwani nan-nan takeyi Dani duk da
dama tana kula dani sosai Amma yau dayake atsarge nake saima naga kamar da biyu takemin
wani abun.
Bayan sallar magriba Ina zaune kan kujera dayake ina fashin sallah hajiyace gefena tanamin
bayanin wasu magungunan"Dan Allah ki kula Jidda kinga wannan kinganshi da kamshinya to
tsugunno zaki dingayi dakinyi wanka kuma koda yaushe.
Wannan kuma shakiji me dadine dabino ne zallah sai aya da madara kullun zakidingasha so
biyu ko uku arana, Zama ki iya zubamishi tafasasshen ruwa kisha kamar tea,Wannan kuma
turarene kadan zaki dinga shafawa amma sai zaki kwanta kinji KO?

Godiya naimata batare Dana kalletaba,Dan yanzu nasan komai ba kamar farkon
aurenba,Dan ko satima ba aiba aunty nafeesa takawomin wasu suma daga gani zasuyi
kyau,Gakuma hajiyata dake aikomin da farfesu duk dare.

""""""


Cikin dare Ina kwance nai lamo tsabar tunani tun inajin tumutmusar da Mimi kemin harta gaji
tai barci,Sannan na sauke ajiyar zuciya.

Wayata dake ring na jawo tare da d'agawa da sallama.
Amsawa yayi tare da lumshe idanunshi"Amarya bakya laifi kokin FASA bakin angon.

Dariya nasaki wadda banyi niyyaba,Kamin ince kai dady!!

"Eh mana Jidda ai kome amarya zatayi daidaine, Ya kuke ya gidan?

"Lafiya lau muke dady"

"To Alhamdulillah hakan nakeson ji ai,Amma mezaki shiryamin kinsan gobene fa?

"Uhumm daddy Zan shiryamaka abinci me dadi insha Allah,Amma da wuri zaka dawo KO sai
yamma KO dare?

"Ah bar fadi dare amarya ai inatunanin insha Allah zuwa azahar na sauka danhaka kadda
kije KO Ina kedai kawai ki shiryamin kanki dan shinafi buk'ata akan komai.

"Uhum to ai bansan wadda zata gyaramin kaina dinba saidai in wankeshi da kaina"

"Dariya yasaki kamin yace Kai Jidda Allah kincika wauta to sonakeyi ki shirya gabadayanki
kiyi gayu Wanda zangani inji dadi bawai gyaran Kai nake nufiba,yanzu kin gane KO?

Akunyace na sadda kaina k'asa Ina sakin murmushi,Sallama yaimin ya ajiye wayar Niko na
gyara kwanciyata nasandai duk tsiya be isa yaimin wani abuba tunda Ina fashin sallah danhaka
hankalina kwance na mimmke.



Tun asuba nahana yaran sakat da aiki dankuwa sosai muke gyaran gidan,Saida naga komai
yaimin yanda nakeso sannan naimana abinda zamu karya dashi,Shima muna gama karyawa
mukai kwanciyarmu sai wajan shadaya nasafe sannan mukaci gaba da aikin yanda yadace.
Lafiyayyen tuwon shinkafa nayi da miyar agushi wadda ta wadatu da nama saikuma
farfesun kan rago tunda nasan abincinshine dama.
Sai lemuna Dana hada.

Mimi ta Hana kowa sakat da tsallen murna dadynta zai dawo kuma zai siyomata sabuwar baby
me gashi.
Yayinda faruk yasami abokiyar tsokana.

Nidai dariya kawai nakeyi dan sosai suke sani nishadi idan suna diramarsu,Akai-akai zahra ke
kirana akan dawowar dadyn nikuma inaimata bayani dan so takeyi tazo daya dawo tunda ya
Usman kulle yakemata sosai kullun bata wuce makaranta.

Saida naga na kammala komai sannan nasasu yin wanka,Itakuma Mimi naimata tareda
yimata gayu cikin wata 'yar kanti me matukar kyau da tsada gashinta atsakiyar Kai tai kyau
sosai sai sakin murmushi take dan mimi akwai son gayu.

Direba ne ya leko lokacin Ina niyyar shiga wanka, yace agayamin saura minti talatin da
biyarfa jirginsu ya sauka.

Agurguje na shige wanka bayan nagama fesama Sadiq da faruk turare,Wa inda sukai gayu
cikin wani danyen boyel yellow hadda babbar Riga kowanne kanshi da hula da fararen glas
gaskiya koni sun burgeni.

Anatse nai wankana sannan nagyara jikina yanda nasan harmu dawo bazan baciba,Sannan
na shirya cikin wata Riga da siket na wata koriyar atanfa me ratsin ja,Bawai k'aramin kyau
kwalliyar taiminba saina Dora farin gyale da farin takalmi Kai gaskiya gayu yayi.



""""""

Kusan duk Wanda zai gitta cikin filin jirgin saiya kalle sabida yanda mukabada Kala sosai
mukai kyau.

Dukanmu munzuba idanunmu jira kawai mukeyi mutanen dake ciki sugama fitowa muga ta
inda dadyn zai fito.

Zuciyarshi cike da farinciki yake zare manyan idanunshi yana hangen ta inda zai hango
iyalin nashi.

Wani k'ayataccen murmushi yakuma saki lokacinda ya hangi Mimi da babbar takarda
ahannunta An rubuta WELCOME HOME DADDY.
Wayarshi ya zaro cikin dibara yaimana hoto sannan ya k'araso yana sakin murmushi,Tuni
Direba ya kwashe kayanshi ya nufi mota dasu.

Cikin wani irin farinciki daya lullubeshi ya dinga d'aga mimi sama duk muna dariya yayinda
muka dauki hankulan mutane dayawa,Sannan babu wanda zai ganni yai tunanin wai

matarshice Saidai KO k'anwa,Danshima gayun dayasha bazakai tunanin wannan bataliyar
tashiba.
Ajiye Mimi yayi ya d'aga faruk tare da sumbatar goshinya yana amsa gaisuwarshi sai Sadiq
nice ta k'arshe da yaima kyakykyawar runguma cikin kunnena ya furta,Inda nasan haka zakiyi
gayu danace bandake jidda,Mazamuje mota sai kallonki akeyi.



YARDA.
Labarin yarda na siyarwane idan kina bukatar siye zakibi wannan tsarin kibiya naira Dari biyu
domin samu.

Acct no.
0005074141.Aisha sabiu ja'iz bank.

Kokuma atura katin waya ta wannan layin.
08142643253.

Sa atura shaidar biya ta wannan layin👆🏻.




35



Wani irin kallo yakebina dashi kasa-kasa cikin motar domin dani dashi da Mimi mune abaya sai
Direba da faruk da Sadiq agaba.
Rungume mimi yai jikinshi ta yanda bazataga me yakeyiba,Sannan ya kamo hannuna ya
matse cikin nashi yana lumshe ido,Wata irin nutsuwa yakeji nabin jinin jikinshi,Cikin zuciyarshi
yafara shima zahra albarka data kasance mishi sila ta mallakar Jidda.

Tundaga harabar gidan yasan cewa lallai anba kai wahala dan bazaka taba cewa da
tsintsiya aka gyara wajan ba,KO Ina tas gilasan winduna kuma sai kashe ido suke suna
walwali,Shi kanshi wani lokacin har mamakin irin tsaftar Jidda yake.

Sassanyan kamshin daya shak'ane lokacinda yasaka kafarshi cikin falon ya tilastamishi
lumshe idanunshi.
Zama yai ak'asa kan kafet ya bubbuda Sannan muka gaidashi bayan megadi yazo ya gayar
dashi.
Idanunshi na kaina yana murmushi"Madam nasameku Lafiya babu wata matsala KO?

Alhamdulillah daddy ya hanya munafatan ka iso lafiya?

Murmushi kawai yasaki idanunshi nakan 'yan madaidaitan libs Dina wa inda sukasha
jambaki.
Maida kallonshi yayi akan yaran nashi yagansu fes dasu sunma kuma girma sannan har
nutsuwa sunkumayi sai Mimi uwar 'yan zakwadi dan tuni tafara addabarshi da akwance tsaraba
kuma abata sabuwar babyn.

"Dady zaka Fara wankane ko inkawo abinci?

Sauke mimi yayi daga jikinshi kamin yabata wayarshi tai game,Ya kalleni muje ki hadamin
ruwan infara wanka kila naji jikina yasaki nagaji.

Ina gaba yana bayana,Tasbihi kawai yakema ubangiji hasaso yanda zankoma idan
nakuma girma yakeyi lallai Allah shine abin godiya.

Wajan fitowata daga toilet dinne ya matse ajikinshi yana sauke numfashi"Ke madam haka
ake tarar oga babu wani zazzafan kiss ko I nkoma ne?

Kokarin kwace bakina nakeyi dan inyi magana amma ina da zafi yake sumbatata abinda
yakumatsoratani,Tuni idanuna sunciko da hawaye saikace ba dadyn danasaniba.

Saida yagaji dan kanshi sannan yasakeni yana maida nuumfashi"Sorry Jidda ttukuicin
wannan kwalliyar na bayar fa amma harkin Fara hawaye!!

Nidai lallabawa nayi nabar wajan ina shafar bakina oh ni duk yagama lashemin baki,Nagama
shanye miyanshi.

Kaya marasa nauyi na ajiye mishi kamin na koma falo dan shiryaabincin dannasan yafison
yaci abinci A k'asa.

Murmushi yasaki lokcin yasaka kayan dama yasan ba lallai in zauna falonba musamman
yanda yaga na tsorata sosai.

Kiran hajiyarshi keta shigowa wayarshi nasandai sannu da zuwa zataimishi,Danhaka saina
anshi wayar daga hannun mimi na mik'amishi"Gashinan hajiya keta kiranka"

Yanke kiran yayi sannan ya kirata suka gaisa taimishi sannu,Sannan ya Kira hajiyata itama
suka gaisa dan saidama muka gaisa da ita Sannan ya ajiye wayar idanunshi nakan kirjina
sabida alokacin duk'e nake gabanshi ina zubamishi abincin.

Huuuuu!!!! Ya saki wani numfashi yayinda yakejin tsigar jikinshi nawani mikewa ahankali

ahankali.

Sakin jikinshi yayi sosai ya narki abincinshi yayinda yaran suka addabeshi da labari
kowa labarin abinda yafaru yakebashi da benan.
Nidai ina gefe dan tuni jikina yagama sanyi bankosan in kalli inda yake sabida Dana kalleshi
saimun had'a ido dashi,Na Lura yanzu ko kunyar kureni da ido beyi.

Kirjina yaiwani mummunan bugawa lokacinda naga ya ware wata Leda yana gayama
Sadiq yaje Direba yakaisu sukaima hajiya,Idan anyi magriba zaizo gidan saisu dawo tare.

Rau-rau nayi da idanuna tare da kallonshi dady nifa?

Girgizamin kai kawai yayi yayinda yaran sukabar gidan suna murna dan idan sukakaima
hajiya tsaraba to kassafinsu da banne dama.

Ajiyar zuciya ya sauke bayan jin fitar motar daga gidan sannan ya jawoni jikinshi yana sakin
murmushi"Amaryata meyasa ke baki gajiya da yawo ne? Inace KO jiya kinje wajan hajiyar
yanzukuma mijinki ya dawo ai kinbashi lokacinki ya huta ko?


Bakina na turo ina hararar gefenshi cike da shagwaba.

Maidani yayi saman cinyarshi tare da zame kallabin kaina yana sunusnar wuyana tuni nafara
motsin kwacewa,Aiko rikeni yai kam yana sakarmin nishi cikin kunne.
"Wayyo dady Zan mutu"

Dariya me sauti yasaki kamin yace" Haba Jidda wane irin mutuwa kuma daga jin dadi,Kinga
tashi muke kiyi aikin lada barci nakesonyi kinga idan kika tausamin jikina da wannan lallausan
hannun naki nasan da wuri zanyi barcina ko? KO zaki shayar Dani da jikinki?

Ban fahimci meyake fadiba danhaka bamma kula da zancen nashiba.
Hannuna ya rike muka nufi d'akinshi yana bani labarin irin kewata da yayi fadi
yake"musamman k'amshinki Jidda na sosai nake kewar wannan k'amshin naki,Shiyasa nakosa
indawo gareki,Yanzu zuwa dare ki shirya zanzo hira wajanki dammu fahimci juna ko?

Dariya nasaki inajin dadi nima zaizo hira wajena kamar yadda saurayi da budurwa kanyi
kamin auransu.

Ganin yanda nake farinciki yasashi kuma gasgata abinda kamal ya gayamishi na hanyoyi
mafi sauki da zaibi danganin ya shawo kaina cikin sauki.

Jallabiyarshi ya cire tare da hayewa gadon gaba daya yana shafar gefen kirjinshi.
Da sauri na kauda kaina gefe ina turo baki,Murmushi yasaki tare da jawoni zuwa
jikinshi"Barci nakeji Jidda ,Idan natashi zamuyi magana inji wannan k'araminbakin da aketa
tsukewa duk me ya jawo.

Nidai ba barci nakejiba amma irin rikon da yaimin ya tilastani tayashi barcin batare danayi
niyyaba.




"""""""""


Shidai bansan lokacinda yatashiba amma nikam koda natashi biyar na yamma tayi,Karadin
zahra ma yaasheni.

Ihunta nakeji bakin kofa"Waike dallah ki fito tun dazufa nake ihun tashinki barci amma
sabida Allah barci saikace na mutuwa.

Nasan bazata shigo dakin dady ba shiyasa natashi jikina duk yayi nauyi dan gaskiya
nibansaba kwanciya barcin ranaba.

Riko hannuna tayi muka nufi dakina tana rufe bakinta alamar dariya takesonyi.
"Kekuma baiwar Allah daga tayamiji barci saiki wani zake harshi yatashi yabarki?

Hararaeta nayi tare da wucewa toilet saida nai wanka nagyara jikina sannan nafito inajin
yanda marata take juyawa amma ba irin sosai dinnanba.

Zama nai gefenta ina yamutsa fuska,Hannuna ta rike kamin tace"Sai kawai naji dady ya
dawo wallahi dama nakosa infito ina tsarabata.

"Kedai wallahi kinbani da surutun tsiya ko gajiya bakiyi to nima babu wata tsaraba
danagani.

Tare muka shirya Abincin dare da ita,Sai bayan isha'i saiga dady da ya usi saisu Mimi,
Rugawa nayi na shige jikin ya usi.

Da sauri dady ya kauda kanshi dan haka kawai saiya sami kanshi dajin babu dadi
musamman da idanunshi suka kai daidai kirjina inda yake hade da damtsen hannun ya usi din.
Akunyace shima ya yakiceni daga jikinshi yana fadin"Zaki kayardani Jidda Bari in zauna.

Hirarsu suka dasa shida dadyn,Tare suka ci abinci duk da cewa shi ya Usman din yana

Nuna danjin kunyar dadyn,Ammashi da alama babu ruwanshi.

Hirar da mukeyi ta daukemana hankali saida dadyn yashigo da mimi akafadarshi tai
barci,Tunanin yanda za adinga kwanciyar yakeyi beso mimi ta dinga kwana dasu Sadiq sannan
beson kwananta ita ita kadai,Sannan yasan bazai yiwu yakwana da itaba tunda ga jidda.

Shimfideta yayi saman gadon yana fadin "Ke zahra tashi Ku wuce dare yayi.

Sallama taimin ta fice,Sannan ya maido hankalinshi kaina tare da zama gefen
gadon,"Bansan inda mimi zata dinga kwanaba tunda yanzu babu Zahra, Ya kikeganin za

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login