Showing 21001 words to 24000 words out of 84412 words
gidannan yaimana yawa wallahi dukda naji dama yanacewa zaiisamo
me aiki.
Kuma yamutsa fuska nayi kamin ince yaufa nan Zan kwana gaskiya tunda bawani aiki
nakeyimishiba da Daren.
Da mamaki take kallona kamin ta matso kusa dani" Aunty dan Allah ki gayamin ko dai akwai
wani Abu da mukaimikine Wanda bemiki dadiba ina Lura duk yau haka kikayini baki da walwala
dan girman Allah kadda kisa aimin dariya da zaben da naima mahaifina,Wallahi YARDA dake
yasa naima dady sha'awar auranki bakisan akwai Mata da yawa wa inda ke buk'atar samun
damar da kika samu ba? Kigayamin cikinmu akwai Wanda yabata ranki ne?
Ganin yanda hankalinta yatashine yasa naji tabani tausayi tabbas zahra na sona nasani saidai
bansan cewa haka auren yakeba lallai da banyi gaggawar amincewa da aurenba, Kinga zahra
babu Wanda yaimin wani Abu wallahi amma gaskiya ina buk'atar fashin baki akan duk abinda
yashafi aure kullun ganin abubuwa nakeyi sabbi inaso insan yanda akeyin komai da komai.
"Idan kina buk'atar haka basaikin shiga damuwaba zamu sami mafita,Nidai fatanadan Allah ki
kula da dady yasami nutsuwar daya rasa shekarun da suka wuce.
Mikewa nayi ina tube kayan jikina,Shikenan karki damu insha Allah zanyi iya bakin kokarina
amma kema yakamata kifara kula ya usi ku fahimci juna kadda zuwa gaba kice bashi
kikesoba,Wanka nashige yayinda itakuma tasaki dariya fadin "Kai ina ba wannan maganar nida
ya usi mutu ka raba wallahi danma dady bazai yaddaba ai danima yanzu nashiga daga ciki dan
inbaku waje kuma ku wataya,Yanxufa nagama waya dashi yana jaddadamin kaunarshi gareni
niko ai tuni dama shine mabudin zuciyata.
Nidai murmushi nayi kawai nafara samajikina sabulu zahra akwai surutun tsiya.
Bakinshi ahangame ya wuce d'akinshi bayan duk yagama sauraron hirarmu,Mamaki yakeyi
na yanda ita zahran tafi jidda wayewa anan bangaren,Wani tunanine ya fadomishi danhaka
saiya sakimurmushi lallai wato yarjejeniya sukai tsakaninsu sabida shirme to aiko indai hakane
zai dauki mataki da kanshi. Gyara kwanciyarshi yayi yana nanata da kaina zankaima nafeesa ita domin su hada
kawance danta fahimtar da ita wasu abubuwan.
Nafeesa matar babban Abokinshine Dr.kamal sannan k'awar marigayiyace yasan bata da
matsala shiyasama tunaninshi ya tsaya akanta.
*****
Tsaye nai bakin k'ofar ina zare idanu saikace an girgiza bera cikin buta,Wani irin tsoranshine
naji cikin raina Wanda ya hanani k'arasaawa gareshi musaamman Dana Lura kamar ba barci
yakeba.
Shiko tun tsayuwata bakin kofar ya bude idanushi yana karemin kallo duk da cewa akwai
duhu cikin d'akin amma hakan behanashi kallonaba tunda akwai hasken daya shishshigo ta
windor.
Ganin bani da niyyar k'arasowane yasashi fitarda numfashi alamun irin barcin mutun yai nisa
dinnan.
Ahankali na lallabo tare da ajiye zanina gefe nad'an lek'a fuskarshi kadan naga barci yake
sannan nahaye gadon na kwanta gamidayin addua idanuna arufe.
Murmushi yaketa saki ganin dibarar danayi to kodai hartafara jin tsoronane abinda yake
tunani kenan cikin ranshi,Kamin yakai hannunshi ya rungumoni jikinshi.
Bakina yai gaggawar rufewa jin Zan saki ihu,"Ke ninefa kike niyyar sakarmin ihu.
Bakina na turo gaba kamin nace "Kai dady to bakai barciba Ashe Kai wani lamo.
Dariya yasaki kamin yace lallaima yarinya ai idona biyu yaushe zanyi barci alhalin matata
batazo nabata hakkintaba!!!
Akunyace na sadda kaina k'asa dan koni sai yanzu maganar kebani kunya amma kuma ai ba
laifina bane laifina bane laifin hajiyane datasani aikata hakan alhalin tasan bansan abinda ake
nufiba.
Hannuwana ya laluba ya dumtse cikin nashi kamin yakumayin k'asa da murya,"Nasandai ba
hakanan kika yarda da aurenaba madam gayamin itakuma zahra dame zata biyaki ladan auran
mahaifinta da kikayi?
Najima banyi maganaba sannan nace" A a babu komai barci nakeji.
"Aiko bazakiyi barciba tunda mijinki betashi yinshiba danhaka juyo ki bani hakkina tunda ke
kince kin yafe ko?
Sunne kaina nayi akirjinshi Kai dady kunya yakebani wallahi,Maganarshi ta katsemin
tunanina"Hajiya nifa ban ganeba kina niyyar juyamin baya keda zaki lallasheni inyi barci"
Dariya nasaki sabida yanda maganarshi tabani dariya,Wannan damar yai amfani da ita wajan
shigewa cikin jikina yanadan tabe-tabe ajikina Wanda hankalina bekai kan hakanba saida
nagama dariyar lokacin hannunshi har yakai saman shafeffen cikina yatsanshi cikin ramin
cibiyata.
Haunnunshi na rike ina fadin"uhum 'uhumm nikabari barci zanyi fa Zan makara da safe.
Muryarshi ashake yace" Karki damu Zan tasheki da kaina ammadai yanzu kibari indan sami
nutsuwa dake mana ko kinaso Allah yai fishi dake sabida kin juyamin baya?Ai me aiki zansamo
mukima gara kidinga girki kawai da kula Dani itakuma ta dinga ayyukan gidan ko?
Nidai lamo kawai nayi ajikinshi ina sauke numfashi amma na daiga kokarin kwacewa daga
jikinshi.
"Weekend insha Allah zankaiki gidan matar abokina ku gaisa kinji ko?
Kaina kawai nadagamishi dan wani irin waiwayi nakeji yanamin agefen kunne.
Cikin wani irin salo yadinga bin jikina da shafa kamar Wanda yake shafar jariri,Saida yaga
yana Neman wuce gona da iri sannan ya rungumeni jikinshi yana sauke numfashi,
Shikenan su jidda an zama 'yan is
YARDA.
Labarin YARDA na kudine idan kina buk'ata zakibi wannan tsarin domin samu.Naira Dari
biyune kacal 200.
Acct no
0005074141. Aisha sabiu ja'iz bank.
Kokuma katin waya ta wannan layin.08142643253.
Tura shaidar biya ta wannan layií ½í±†í ¼í¿».
20.
"Dady dady". Nai kiranshi cikin wata murya me sanyi dan jikina dayagama mutuwa.
"Uhumm shine abinda ya furta kamin yakuma gyaramin kwanciyata jikinshi.
"Dady" nakuma kiranshi ina yamutse fuska zansaka kuka.
Tashi yai zaune yana lalubar wayarshi.
Lumshe idanuna nayi ganin yanda ya haskemin fuska "Jidda meyafaru?
Dan kauda fuskata nayi gefe kamin nace dady jini ne yake zubarmin yanzu.
"To subhanillahi tashi to ki gyara jikinki Amma nabani kina ciwon maraba kumama ai baki jima
dayiba tunda naji kwanaki zahra tace bakijin dadi ko? Tashi muje in hadamiki ruwan dumi saiki
wanke jikinki.
Ahankali natashi gudun kadda in bata jikina sosai,Saida najira ya fito sannan nashiga ina
ganin yana gyara shimfidar kamin ya zauna jiran figari ta dan yasan dole infita dauko abinda
zansa.
Babu jini babu alamunshi saidai wani Abu dangani Wanda bansaniba shiyasa sainai wuri-wuri
da ido ina tunanin ya zanyi.
Ganin shiru naki fitowa yasashi matsowa wajan kofar yana fadin"Jidda zaman me kikeyi
cikin bayi da dare fito mana"
Sumi-sumi haka nafito batare Dana kalli inda yake tsayeba"Ah to ya baki tube kayanba ko
basu baciba?
Zamanai gefen gadon kamin ince ai ba jini bane wani abune daban.
Dariya yasaki med'an sauti yana nunani da yatsanshi kamin yadawo gefena ya
zauna"Wallahi kincika wauta jidda ke komai sai an fahimtar dakene To ba wani abubane daban
n'imar jikinkice ta motsa sabida tabawar danaimiki, Inye dady dan gatan jiddan ba Ashe zansha
dadi. Ya idasa maganar yana kuma sakin dariya gamida rungumoni, "To kinyi tsarki ko?
Rabawa nayi gefenshi na kwanta ina rufe ido ashema ni banzace bansaniba meyasa ban
fahimci meneba saida dady ya gayamin gashinan naja yanamin dariya.
Cike da farinciki ya rungumeni jikinshi yana sakin murmushin dadi Ashe matar tashi
lafiyayyace kenan tunda gashi daga tabata jikinta ya amsa Alhamdulillah yake nanata fili da
bayyane har saida barci yai awon gaba damu.
Asuba ta gari sabbin kauna.
*****""""""*****
Ban yarda na kalleshiba har mukagama shirin makaranta saima naji har zahran kunyarta
nakeji musamman danaji ta nace fadin"Wallahi dady yafara sonki jidda kinga irin kallon da
yakemiki kuwa lallai nan gaba za abuga love gidannan.
Yau bashine ya ajemuba dan dawuri ya fice yau.
Kinga aunty bari inkaima zee wayarnan tasamu cikin grp grp nasan zamu k'aru da wasu
abubuwan Amma dan Allah kadda mubari dady yagani kinji?
"To"Ammadai duk da haka kadda asamu inda bedaceba dan wallahi zai iya duba wayar
wataran to babu ruwana.
Ficewa tayi daga ajin nikuma na maida hankalina akan littafin faruk daya kawo inyimishi
wani zane.
""""""""
"Katasani kanata kallo Habib akwai damuwane? Jiya nakecema nafeesa ta shirya muje
wajanka saikuma nai tunanin ai duk Baku zama.
"Humm Kamal bawata matsala wallahi domin nayi matukar mamakin ganin abunda ban zataba
daga yarinyar,Bantaba tunanin tanada wayauba wallahi kula takedani yanda kasan wata babbar
mace gashi ta iya girki kamar wata tsohuwar hannu ga tsafta ga nutsuwa su Kansu yaran yanzu
harsun Fara canzawa wallahi,Ammadai akwai matsala daya!!!
"Muskutawa kamal din yayi kamin yace Alhamdulillahi ai abinda ake fata da buri kenan
dama to hakan yayi menene matsalar yanzu?
"Dan shafar suman kanshi yayi yana sakin wani murmushi, Balle dayaga yanda shi kamal
din ya kureshi da ido yana kallonshi,Da alama jiranshi kawai yakeyi.
"Uhumm ina jinka sai murmushi kakeyi Dr.
"Uhumm dama akan maganar bangaren aurenne gaskiya batasan komaiba akai dan
hargarama zahra akanta So inaso ta fahimci wasu abubuwa kamin inje gareta gaba daya.
Dariya yasaki me sauti kamin yace"shege mutumina ah lallai zaka huta da wannan kwailar
taka, To ai inaga wannan bawata matsala bace indai zaka dinga janta jikinka sama sama
sannan Sannan zuwa nan gaba saika dauke zahra daga gidan inba hakaba kanaji kanagani
wani abun zai gagareka musamman tunda yarane kaga ita madam dole saika maida kanka yaro
kamarta kozaka sami yanda kakeso to kaga bekamata ita zahra ta dinga ganin
hakanba,Sannan zanyima nafeesa magana duk lokacinda tasami time saitaje wajanta kaima
idan kana free saika kawota nan ta yini to nasan ahaka zata dauki wasu abubuwan insha
Allah,Amma shanake rainonta zakayi wallahi.
Wata harara ya wurgamishi kamin yace"a a ciki Zan maidata in fiddota ba rainoba bazan
iyaba wallahi,Abun da bedamu yanzu damuna yakeyi,Itakuma na Lura da ita shegen tsorone da
ita dan Allah ma yasa bata da gardama Aida nasami matsala,Yanzu yaushe zaku shigo to?
"Insha Allah juma'a da yamma zamuzo kaga saikai k'okarin tura su zahra gidan hajiya dan
susami sakewa sosai ko?
"To shikenan hakan yayi Allah ya nuna mana juma'ar Lafiya.
"Ameen ya Allah,Ango ango lallai mutumina kwanan nan za aga kafara aje tumbi da kumatu
danni sainagama kamar har haske ka k'ara,Cewar kamal din yana maganar yana sakin dariya.
Tsaki yasaki kamin yatashi yafara tattara kayanshi,Banza ka girma Amma har yanzu baka da
hankali ni tashi kabani waje in wuce gida.
Dariya yake sosai kamin yace wato iskanci zakamin nagama baka shawara ko? To nafeesan
tafasa zuwa naga Wanda zai nunamata yanda zata karbeka,Kuma ka taushe musu yarinya ta
koma gida ba.
Yasan iskancin kamal ya wuce nan ma indai tsokanace shiyasa saiya saki murmushi kawai
bekuma kulashiba dan yasan yanzu zai iya kunnashi da iskancinshi.
Ko ina fes gidan tsabar kulawar da yake samu shi kanshi megadin gidan yasan cewa ba
k'aramin cigaba aka samuba cikin wannan gida yanzu dan komai ya fita yanda yakamata ga
uwa uba lafiyayyan abinci da akeci koda yaushe yanzu,Bazaka taba cewa ba manyan Mata
bane cikin gidan sabida yanda akeyin komai akan tsari.
GAREMU IYAYE YAKAMATA MUDINGA NUNAMA YARANMU DUKKAN ABINDA YADACE
BAWAI SAI LOKACI YA KUREBA AYI AURE YARINYA BABU ABINDA TASANI DAGA
KWALLIYA SAI CHATING DA KAWAYE.
Wainar fulawa naimana yau damuka dawo makaranta ammafa me kyau dan taji kwai da
nikakken nama falon kamshi kawai yakeyi nace babu Wanda zaici sai dady ya dawo muci gaba
daya,Yayinda Mimi keta fitina itafa abata tafaraci.
Muna cikin wannan artabun yai sallama yashigo fuskarshi awashe sabida yanda yaga ko ina
fes sai tashin k'amshi take.
Mimi ta makaleshi tana fadin"dady aunty ta hanani waina"
Zama yai kan kujera yana sauke numfashi kamin yace "Sorry rabu da ita zanyimata bulala kuwa
tunda ake tabamin Mimi dina.
Sannu da zuwa duk mukai mushi,Ya amsa cikin farinciki da walwala afuskarshi lallai Allah
yaimishi gata.
"Aunty kije ki hadamishi ruwan wanka mana" cewar zahra tanamin rada cikin kunnena.
Saida nadan jima sannan na mike tsaye na nufi d'akinshi dan hadamishi ruwan yayinda
yabini da manyan idanunshi harsaida nashige.
YARDA.
Labarin YARDA na kudine idan kina buk'ata zakibi wannan tsarin domin samu naira Dari biyune
kacal.200
Acct no.
0005074141 Aisha sabiu ja'iz bank.
Kokuma katin waya ta wannan layi 08142643253.
Tura shaidar biya ta wannan layií ½í±†í ¼í¿».
21-22
Yunkurawa yayi yana yakice Mimi daga jikinshi"Jirani inyo wanka mimina duk na gaji ko"
Wani maayen murmushi zahra tasaki ganin dadyn yashige cikin d'akin.
Ina niyyar juyowa dan barin bayin saigashi yashigo dagashi sai jallabiya Mara
nauyi,Akunyace nai kokarin kaucewa danyashigo sainaga yawani tokare kofar yanabina da
kallo.
Sadda kaina k'asa nayi inajin wata mashahuriyar kunyarshi.
K'aramar dariya yasaki yana fadi"Dady jini ke zubarmin"
Kuma cukuikuye fuskata nayi ina murmushi Kai dady ya iya tsokana wlh.
Wani murmushi yakuma Saki yana fadin muje ciki kimin wankan to ai duk cikin hakkinane
dake kanki.
Da gudu nabar dakin idanuna arufe Kai dady zai iskantani wlh.
Shima dariyar yakeyi sosai ahaka yai wankan yana cikin nishadi dajin dadi. Lallai auren
yarama farincikine wani lokacin indai kasami me hankali.
Isata falo ina sauke numfashi yasa zahra kallona gamida wani kashe ido alamar shakiyanci.
Harararta nayi tare da zama gefenta"Kedai kinbani wallahi to Zan gayaki da dady ince kinfara
samishi ido.
Dariya tasaki "To wallahi barin gidannan zanyi tunda sauran mutuncina dannaga Neman
soyewa akeyi agabana oh su dady manya.
Banza nai da ita ina murmushi lallai shima dady dan soyayyane kenan to niko ina Zan iya
yima wani babba wanka dan Allah saikace wani baby.
Muna nan zaune yashigo falon da farar jallabiya jikinshi fuskarshi fes sai k'amshi yakeyi,
Gefenmu ya zauna ak'asa yana fadin"Ina jiddan kawo abincin muci tunda kungama jama
yarinyata rai dan Anga tanaso ko?
Da dariya na mike' kai dady wallahi bawani Jan rai kawaidai ita tacika rigimane dantaga bata
da k'anne,Sam badawata manufa na fadiba shiyasama ina maganar ina tafiya dan kawo
abincin.
Yayinda yabini da kallo yana fadin "Zonan Mimi wai kinji aunty dan baki da k'anne kikeyin
rigima saitazo ta Samar miki da k'anne ko? Wa inda zasu dinga kiranki da aunty kema ko?
Abazata yaji sauran sun amsa cikin farinciki "ehfa dady muma munaso.
Kallonsu yayi yana murmushi,Kamin zahra ta Dora da fadin aikuwa kowa nason sabon babies
danhaka saimu taya aunty da addua kuwa.
Hahararta yayi yana murmushi amma bece komaiba dan sosai ya fahimci zahra tayi wayau
akan sanin abubuwan dake faruwa ba kamar jiddan ba.
Kallo yabi abincin da kallo kamin yace" Yaukuma mezamuci jidda?
Murmushi nasaki kamin nace wainar fulawacefa dady amma me dadi.
Duk da cewa dayawa nayi amma haka muka cinyeta tas sannan kowa ya hakura Sai kowa
ya gyara zama aka Dora da lemo me sanyi saikuma hira bayan nagyara wajan ita kuma zahra
ta dauraye kayan da muka bata.
Kusan hirar duk dady ne dasu faruk,Nida zahra mun duk'ufa akan waya sabida wani GRP na
magana akan yadda mace zata kula da mijinta,Nida zahra sai kallon juna mekeyi muna sakin
murmushi.
Shiko dady lokaci zuwa lokaci yakan kallemu duk da yanaso yaga me mukeyima kus-kus
haka.
Wayarshi aka Kira danhaka saiya tashi yabarmu nan falon, Jikina Mimi ta dawo kamin wani
lokaci tai barci Sadiq ma sai gyangyadi yakeyi sabida maganin mura dayasha faruk ne ke kallo.
Wow gaskiya nima