Showing 9001 words to 12000 words out of 84412 words
bansan komai akantaba na kalar abinda takeso danhaka saiki
duba ko?
"Eh hakan yayidady Allah ya Karo budi.
. Irin tsaruwar da wajan yayi shine yasakata tsallen dadi lallai zasu wataya cikin gidannan,Wani
Dan madaidaicin falone Wanda aka shiryashi da wasu musulman kujeru masu numfashi sai
kayan kallo da frij agefe Sam babu komatsai balle hayaniya cikin falon daga can gefene akai
kofar kitchen dakuma wajan Dani daga gefe. Kai komaifa yaji sai kofar bedroom guda biyu ko wanne anzubamishi kayan gado masu
matukar kyau da daukar hankali gawani mayen k'amshi daya kewaye wajan gwanin dadi,Wani
irin numfashi taja tare da fesarwa Kamin tace kai gaskiya nima auran zanyi,Saurin waigawa tayi
taga babu kowa sannan ta rufe bakinta tana dariya.
Fitowa tayi tare da jawo kofar hasaso soyayyar Jidda da dadyn kawai take tana dariya wai
gwarama kenan,ammadai batajin dadyn dantasan 'Dan soyayyane shi.
Da misalin k'arfe uku saura aka daura aurena da Dr.habeeb yanda wasu suka sanshi kokuma
alhaji habibu duk sunanshine domin babban likitane saidai tuni kasuwanci ya danne likitancin
Dan inba yaga buk'atarshi takai dinba Sam ko asbt be yadda ya lek'a.
Tunda ya usi yashigo yana shaidama mutanen gidan an d'aura sai kawai naji hankalina yai
wani irin muguntashi musamman danaga kowa yasha manyan kaya anata washe baki.
Kuka nasaka tare da k'amkame hajiya Ina nanata banso ni bansan auran.
Itama kukan tasaka tanafadin"Wannan yaro baka kyautaminba da zaka rabanida takwara
lokacinda banyi zatoba Dan Allah Ku kirashi ya janye aurannan harta k'ara wayau.
Nanfa hankula ya tashi ganin hajiya na kuka ga gida cike da surukai da jikoki ga 'ya'ya.
Dole aka Kira yaranta maza manya sukazo sukaita aikin lallashi amma da ta tubure saidai
akirashi yazo ya keni ita tafasa bashi auran.
Bayan sallar i'sha,I zuwa lokacin harna Fara fita hayyacina sabida tsabar kuka,Haka aka
shiryani Dan tuni motocin daukar amarya sun hallara abun mamaki waini Jidda akaima
aure!!!Abune na mamaki ai,Saidai komai rubutaccene sannan kowane bawa be isa ya gujewa
k'addarar da take akanshiba.
****"""""****
Su ukune zaune saman mota lokacin gidan ya sarara da mutane Dan tuni aka maida wasu
gida,Hajiya kaka da Hajiyane suka fito daga gidan fuskokinsu awashe Dan tuni k'awance yaci
uban nada,Kai tsaye wajansu suka nufa,Shiko da sauri ya diro daga kan motar yataho wajan
hannunshi rungume da babbar rigarshi wadda zafi ya tilastamishi cireta,Kuma durkusawa yayi
ya gaidasu kamin hajiyarshi ta kuma rattafo zance kamar yanda suka shirya ita da hajiyan"To
gadai Jidda nan ankawomaka habibu Dan Allah banda wauta da garaje kabita asannu tasaki jiki
da kowa kaji ko? Duk abinda kagani Wanda bemakaba ka tuntubeni ko hajiyarta kagadai yanda
Allah ya tsara komai babukuma yanda muka iya kaji ko?
Kanshi ak'asa sabida kunyar fadan hajiyar tashi ya amsa da "insha Allah hajiya.
"Yauwa to Allah yayi albarka,Hajiya ko akwai abinda zakice?
Gyalenta ta gyara sannan ta washe baki"Allah yabaku zaman Lafiya habibu Amma Dan
Allah kadda kaima yarinyarnan ciki tun yanzu kagadai yanda take,Daurewa zakayi kaimata irin
'yan dabarunku na likitoci kaji ko?
Jiyai harwata hajijiya ke Neman kadashi tsabar kunya kamar ya nitse awajan,Shiru yai yana
zare idanunshi,Ganin halin dayashigane yasa hajiyarshi sakin dariya tana fadin kashiga ciki ka
lallashi yarinyar mutane Dan yau yini tayi kuka.
Da sauri yabar wajan bayan yabada umarnin akai su hajiyar gida.
Nan sukai sallama da sauran abokanshi ya shige cikin gidan.
Yayi tunanin zai shiga ya taddata tanata kukan kamar yadda akace saidai tunkamin ya
k'arasa yakeji dariya da hira, Danhaka ahankali ya lek'a ta yanda nacikin dakin bazaisan wani
ya lekoba aiko Saiya hangesu sun baje kajin daya siyo da sunan amarci sunaci suna korawa da
lemo Jidda ko kallabi babu kanta tsabar dadin naman ne kona hirar ne oho. Idanunshi ya kuma fiddowa cike da mamaki lokacinda yaga harwani kashewa akeyi tsakani.
TIRK'AShi lallai yarannan basu da hankali,Lallabawa yayi yabar wajan yana sakin ajiyar
zuciya.
Allah ya hadashi da aiki.
YARDA.
Na maman khadija.
11
Da ASUBA,Kasancewar bamu kwanta da wuriba sai kawai muka makara Dani da zahra da
muka kwana gado Mimi akan wani k'araminkafet dakecan wajan Miro dina sai su Sadiq da sukai
kwanciyarsu kan kafet din dake malale tsakar dakin sabida Sam kin yadda sukoma wajansu
sukayi.
"Gajiya da kiran sunan zahra yayi saiya bude kofar aiko nan yaga yanda ko wanne yake sharar
barcinshi irin barcinnan Wanda zakasamu meyinshi Sam beda wata damuwa ko matsala.
Mamaki yagama cikashi Dan beyi tunanin duk anan suka kwanaba,Mazan yatasa Dan zuwa
masallaci sannan ya tashi zahra itakuma ta tasheni.
Saida yaga duk muntashi sannan yabar dakin,Sai jinini yakeyi cikin Zuciyarshi lallai kuwa
yayi aure ko anhadashi da wani rainon banda Wanda yake fama dashi.
Munayin sallah na kalli zahra wadda keta hamma da alama barcin be iahetaba,Harararta
nayi kamin ince"Kinga tunda bamu kaiga tsara komaiba tashi kawai mugyara d'akunan da gidan
yanda zamu huta anjima.
Da kallon mamaki tabini kamin tace" Haba aunty tun yanzu?
Tsaki naja kamin ince ji shirme aidama da duku duku akeyin dukkan aiki idan gari yawaye ai
Sam mutun bazai iyaba tashi nidai ki gyaranan inje falo ,Idan nagama sai in doramana abin
kari,Haka mukeyi da hajiya kinga zuwa anjima ai saidai muyita hira muna hutawa ko?
Itadai bahaka tasoba tunda bata sababa amma saita mike,Nikuma ina kuma jaddadamata
tafara wanke bayi.
Lokacinda garin Allah ya idasa wayewa ai sai abun yaba mutun mamaki,Dan har wanka
munyi kowa ya shirya zaune kawai muke munajiran dady yatashi barci mu karya.
Sanye nake cikin Riga da siket na wani yadi me laushi dinkin yaimin das ajikina sai kamshi
nakeyi,Kunsandai amarya aduk inda take sai yanayinta ya nuna,Nidai bazance akwai wani canji
danasamu saina muhalli danhaka babu ruwana da wata maganar aure Dan tunima na manta
dashi.
Fitowarshi kenan daga wanka yana gyara jikinshi Mimi tai sallama dakin,Kwalliyar da
akaimata yau kawai yasan ansami cigaba cikin gidanshi,Gawani k'amshi dayaketa shakowa
tunda yatashi barci.
K'afafunshi ta rike tana lilo "dady kalla aunty taimin wanka da kwalliya kuma tayi girki me
dadi amma ta hanani wai saika tashi barci.
Murmushi yayi sannan ya d'agata sama ya sumbaci bakinta "inye gayun ba to zauna nan
ingama shiryawa sai muje ayi break fast ko?Tunda sun Hana Mimi Dina abinci gashi kuma
tanajin yunwa ko?
Anatse ya shirya yana ayyano kalar kwamacalar da zai tadda Dan dama ko zahra shike
kokarin koyamata wasu abubuwa tundashi ya iya,Tunaninshi Jidda babu abinda ta
iya,Musamman idan yai la'akari da irin gidan data fito,Uwa uba kuma gatan da takeciki,Beson
mu'amala da masu aiki amma yasan yanzu dole ya cigito kodan ta dinga ayyukan gidan.
Babu kowa babban falon ammafa daga gani yasha gyara dan gashinan sai walwali ko Ina keyi
da tashin k'amshi,Mamaki ya kamashi to waye yai wannan aikin haka?
"Mimi Ina abincin yake to?
"Dady duk suna wajan aunty A can zamuyi anjima saimu dawo nan da rana.
"Hummm" Shine kawai abinda yasamu ya furta Sannan yabita zugui zugui yana mamakin ganin
ko Ina kal saikace bajiya yaga gidan yafita hayyacinshiba sabida taro,Betashi Kara tsinkewaba
saida yasaka kafafunshi cikin sabon falon,Ya hangi yanda akaima wajan cin abincin wani irin
gyara yanda duk tsiya sai wajan ya birgeka,Gawani mayen k'amshi dayacika falon,Ya kalli 'yan
samarinshi yagansu tsaf yau babu fama akan suyi wanka ko wanne yasha gayunshi saiya
maida idanunshi akan zahra da kwailar matarshi ,Can k'asan zuciyarshi ya furta Alhamdulilah.
Kusan tare duk muka mike munayimishi Sannu tare da gaidashi,Itadai Mimi na jaye da
hannunshi saida taga ya zauna gaban kulolin abincin sannan takoma gefenshi itama ta zauna
tanafadin aci dady.
Da kaina na zubama kowa inayi Ina doka murmushi Dan gaskiya abun ba k'aramin kayatar
Dani yayiba wai ina zubama babba abinci da wasu kuma yau da kaina nai komai babu korafin
hajiya,Dan haka mukeyi da ita gashidai zanyi komai yanda tace harma ta yaba amma hakan
bazai hanata tanaci tana korafi ba. Be tambayi inda akasami garin kunuba ammayai mamakin ganin kunu da kosai,Gakuma
lafiyayyen tea idan akwai me bukata saikuma farfesun naman kaji Wanda zahra ta debo can
bangarensu,Na sarrafasu.
Dagajin kamshin da gurin yakeyi kasan komai dake wajan zaiyi dadi.
Abazata yaji wani irin farinciki da nishadi ya lullubeshi,Aiko ganin batashi nakeyiba yasa
shima yasaki jiki cikin yaranshi ya narki abinci Dan rabonshi da walwala irin wannan tunkamin
matarshi ta rasu.
Yanayi yana satar kallona niko bammasan yanayiba Dan babu tunanin aurenshi akaina,
Yanda su zahra kedan tsokanarshi nima haddani Dan matsayi daya nake ganinmu akai.
Alhamdulillahi yaketa nanatawa fili da boye bayan mun kammala, Sadiq nasa ya kwashe
kayan yakai kitchen shikuma faruk ya goge wajan,Sannan na kalli zahra "muje mu wanke zahra.
Ajiyar zuciya ya sauke me karfi bayan munshige,Ah lallai da Alama Allah ne yaimishi wani
gata na musamman Dan gaskiya abun ya k'ayatar dashi fiye da tunani,Shafa cikinshi yayi jin
yanda ya cikashi sosai.
Kallo ya hada duk suka komatsakiyar falon suka zauna kafet sunayi yanadan jansu da hira
sama sama ya kosa su fito kuma yaga menene aiki na gaba da za akirkiro.
Muna tafe muna hirarrakinmu da dariya muka dawo falon,Nidai ban zaunaba saida na dauko
wani littafi Wanda yanzu nakeso mutsara ayyukanmu yanda komai zai dingazuwa mana da
sauki sannan kosu yaran kowa zaisan aikinshi.
Yiyai kamar bamu yake kalloba ammafa gabadaya hankalinshi yana wajanmu.
"Yauwa zahra ke zaki dinga gyara ko ina daga yau amma wancan babban bangaren dakuma
d'akunan yara nikuma Zan gyara nan dakuma dakin dady,Kaikuma Sadiq Kaine babba zaka
dinga share harabar gida kullun dakundawo sallar asuba, kaikuma faruk zaka dinga
kwashewa,Dakun gama sai wanka idan kukabari muka rigaku to zamutai makaranta mu barku.
Ihun Mimi yasa mukai shiru muna kallonta,Dirza kafa tafara wai ita menene aikinta,Duk
dariya mukayi kamin ince ke zaki dinga d'auko kayan da zamudinga cin abinci Amma duk ranar
da kikafasa wani Abu daya to Zan canzaki.
"Banji kinyi maganar girkiba"cewar zahra.
"A a ai nice zandingayin girki safe da Rana dakuma dare amma daidai cikinmu Zan dingayi
kadda mubarshi ranar da ake makaranta kuma zamuyi break me kyau yanda bazamuyi saurin
jin yunwaba harmu dawo,Amma idan kingama aikinki da wuri zaki iya kamamin girkin tunda
kince ke baki iyaba sosai.
Mamaki da tsoron yarinyar yaji yana neman kamashi sannan yanaso yai magana sabida ai
alissafin da akayi aikinta yafi na kowa yawa kadda taita wahala kuma,Saidai beso yasamusu
baki tunda basusa dashiba.
""""*****"""""
Shinkafa da miya naimana da Rana wadda na wadata miyar da namansa sai kayan lambu.
Ina gama sallar azahar nasaka kuka sabida kewar hajiya.
Duk kewayeni sukai yayinda sukai dako dako kamar zasu saka kukan suma, Mimi ce ta
zanzare ta Kira dady Wanda gama wayarshi da hajiyarshi kenan tana tambayarshi badai
matsala gidan nashi ko!!!.
Da mamaki ya biyo bayanta sabida yaga Lafiya lau akagama cin abinci gwanin ban sha'awa.
Tasasu zahra tayi sukabar dakin ganin shigowarshi,Jiyai wani nauyima ya dabaibayeshi,Amma
saiya sami kanshi da rashin jin dadin kukan Nata musamman yanda tsakanin jiya da yau
gidannashi yake cikin farinciki kuma yasan itace sila.
Matsowa yayi kusa dani tare da riko hannuwana Niko uwar 'yanson jiki ai gabadaya na
rukunkumeshi ina kuma bare bakina.
Rungumeni yayi ajikinshi yanajin wata irin nutsuwa dayajima beji irintaba,Besan lokacinda
yafara shafar gadon bayanaba yanadan jijjigani alamar lallashi,Saida yaji na daina kukan sai
ajiyar zuciya sannan ya Fara magana cikin sanyin murya"Jidda meyafaru kike kuka?uhum
gayamin me kikeso? Bakina na turo gaba kamin ince ni gida zani.
Damm kirjinshi ya buga kamin wani tsoro yanemi rufeshi,Kaddai ace hartagaji damu,"Sorry
Hajiya kikeson gani?
"Kaina na dagamishi inakuma lafewa cikin krjinshi danjinai yanawani mayen kamshi gwanin
dadi.
"To daina kuka kinji ko!duk lokacinda kikeson ganin hajiya ki gayamin kawai zankaiki
basaikinyi kukaba kinji ko?Tashi maza ki shirya saina kaiku anjima saina koma na daukoku
hakan yayimiki ko?
Jiyai hankalinshi yatashi da amsar da zanbashi danhaka inadaga kaina alamar na amince
harwata ajiyar zuciya ya sauke.
Dan Allah kuyi hakuri banda caji ne
YARDA.
Na maman khadija.
12
Kasancewar dama nai wanka yasani jawo hijab Dina Ina kallonshi alamar na shirya.
Dariya yayi kamin yace"Haba hajiya Jidda ki d'an watso ruwamana sannan kiyi kwalliya har
gidanmu zamuje fa!!
Yana barin d'akin na lek'a falo wajansu zahra"Banza kuyi sauri Ku shirya unguwa zamuje.
Duk mikewa sukai suna dariya yayinda shikuma ya idasa ficewa yana murmushi,"Ji Dan Allah
saikace ba itace yanzu tagama bare baki ba tana kuka.
Nida Mimi agaban motar kusa dashi su zahra suna baya,Tsabar hirarmu gabadaya babu me
sauraren kowa,Yayinda yakejin kamar ya saka ihu sabida shifa Sam ba ma'abocin son hayaniya
bane shiyasama ake kiranshi da miskili wani lokacin,Amma ya lura zuwan Jidda gidan kowa
bakinshi ya bude.
Da ya usi mukafara cin Karo mamaki ya kamashi lokcinda yaji na makalkale jikinshi Ina
dariya,Lallai aiki gameyinka,Abinda yake nanatawa kenan cikin zuciyarshi.
K'arasawa yayi wajan motar yana gaida dady,Yayinda su zahra suka gaidashi lokacin duk sun
fimijinki, motar.
Cikin girmamawa ya usi yace to kashigo mana.
"A a kuje ciki kawai anjima idan nadawo d'aukarsu sainashigo mu gaisa ku gaishe da hajiyar.
Baki ahangame take kallonmu kamin tace"Nashiga uku ni Hauwa wane mahaukacin yace ku
fito yau?Ke Jidda hardake Dan gidanku akaiki jiya yau kidawo ubanme zakiyi anan din?
Bakina na turo gaba Ina harararta Kai hajiya nifa nayi kewarki ne shine nai kuka sai daddy
yace in shirya ya kawomu.
"Oh inkana duniya zakasha kallo ammadai na yadda shi kanshi dadyn naku bawai hankaline
dashiba,Tunda zai iya biyema shirmenki kajifa Usman!!!
'Dakina muka shige nida zahra mukabar hajiya nan tana sababi Number hajiya kaka take nema
ta turomata ta dady ta wankeshi yanzu yanzu Dan abun ai hadda shirme akai amarya jiya
amma yau ta dawo ganin gida?
****
"Kai dago idanunka nan ka kalle nima in kalleka Danni nan da kakegani bawai kanwar lasa
bace,Ashe kaima sakaraine habibu?Sabida Allah haka zaka dinga biyemata tana shirme
kenan? Dama ai kasan dole sai ahankali zata Saba da rashina ko! Amma shine dagayin kuka
zakawani kwasota ka kawo gida ubanme zanyimata tunda ita tace tanason auren iye To bari kaji
idan kakuma debo wa innan dogayen kwaurin naka ka kawomin ita gidannan saina cinyeku
d'anyu daga kai har ita, Danhaka idanma zaka koyi yanda ake lallashi saika fara.
Shidai yana zaune yana jinta hasalima masifar tata dariya takebashi.
Saida ta rakamu har wajan mota sannan ta kalleshi"To dady aita hakuri Dan Allah Ana
kwabawa ba komai ake biyewaba Ku gaida gida Allah ya tsare,Jidda idan kika kuma zuwamin
gida bakiyi wata dayaba to kitabbata sainasa usmanu ya karye miki wa innan siraran kakafun
naki. Jan motar yayi yana dariya kai hajiya akwai mita da fada tai lallashi tai fada ita da hajiyarshi
besan wacce tafi wataba.
""""*****"""""
Itamadai hajiya kaka saida tai fadan fitowar ammadai ba kamar hajiya ba.
Ina zaune d'akin hajiya kaka bayan na idar da sallar magriba sukuma su zahra duk suna
falonta sabida zahra abun yazo Mata wajan la'asar babu halin yin sallah.
Zamatai gefena tana mirmushi "ah Jidda anyima miji addua ko?
Murmushi nayi ina rufe idona sabida kunya.itama dariyar tayi kamin tace" badai kunyata
kikejiba nida nazo muyi hira kuma!
Kaina na girgiza ina kallonta amma ba yi maganaba.
"Washe baki tayi kamin tace gayamin jiya tare da dadyn kuka kwana ko?
Manyan idanuna na fiddo gabadaya ina kallonta,Kai hajiya mezai kaini dakin dady
kuma,Nidasu zahra muka kwana fa!!!!