Showing 57001 words to 60000 words out of 84412 words

Chapter 20 - YARDA Book Complete by Maman khady.pdf

Advertisement

12 Jul 2025

2672

Ina kallonshi yanata kaida kawo daga falo zuwa kitchen,Nidai iyakata ido domin ina sane
dashi.

Dayagaji shigowa yayi tare da tallabar k'uguna ya shigardani jikinshi tare da sunsunar
wuyana.
Makalewa nayi ina harararshi shikuma ya Saki dariya dan dama tsokanar maganar yakeyi.

"Bansan ganin fishi afuskar matata kuma farincikina danhaka tayi hakuri taimin afuwa na
amshi laifina kuma inabada hakuri Zan kiyaye gaba insha Allah.

Ajiyar zuciya kawai na sauke, Amma banyi maganaba.

"Yauwa Autar mata kin hakura ko?

Kaina na dagamishi alamar amsawa.

"To Alhamdulillah nagode,Allah yaimiki albarka.


Note.
HAKAN YAKAMATA MU DINGAYI MU MATA KADA MU KASANCE MASU RIKON
MAZAJENMU CIKIN ZUKATANMU DAGA LOKACINDA MUKA SAMI SABANI DASU DASUN

BAMU HAKURI KAWAI MU HAKURI DOMI N RIKO BEDA DADI,SANNAN MAZA DA YAWA
SUNA SAURIN TSANAR MACE ME RIKO DA NACIN MAGANA.



"Shanake bazaki iya girkinba ai,Amma dai jikinki lafiya lau ko?

Cikin yanayi na shagwaba nace daddy duk fa laifinkane Sabida Allah haka akeyi saikaji na
daina motsi sannan ka hakura idan ka kasheni ai ka huta.

Mirmushi yayi tare da matseni cikin jikinshi,"Kiyi hakuri kuma kiyima habibi uzuri,Matarshi
Jidda ta kasance me matukar debe kewar mijinta,Tare da farantamishi shiyasa aduk lokacinda
ya kasance tare da ita yake mantawa da komai da kowa.

Kauda kaina nayi Ina murmushi kai daddy ko Sam bejin nauyina idan yatashi maganarshi.

"To muje intayaki wanka tunda kin kammala ko?
Da sauri na kalleshi kai daddy wane irin wanka kuma?

"To tunda bakiso shikenan muje ni kimin dan gaskiya nagaji da yima kaina wankan sannan
kuma dama hannuna bekaiwa bayana kinga saiki cudankawai
Hannuwana na dauraye ina mamakin daddy wani lokacin saiya dingayin Abu saikace
k'aramin yaro, Wanda dama inaji anacewa samun kulawa ta gasken gasken to ka auri Wanda
yafara dibar shekaru bakuma Wanda zaka dinga kaima buta bayiba kawai😅.

"Wai mene nufinki bazaki kulaniba zo mana ina zaki?

Toni dady ka cika Neman magana dan Allah ya za ai na iya yimaka wanka,Nimafa nan
Neman meyimin nakeyi.

"Yauwa shikenan faduwa tazo daidai da zama muje inyimiki nasan ba k'aramar lada
zansamuba.

Dariya kawai na Saki na fice Lallai dady shima ya iya daru kenan.





""""

Duk irin maganar da mukayi da zahra akan indinga daurewa da sannu Zan Saba da Neman da
dadyn yakemin Amma ina tsoro ya dabaibayeni dan gaskiya ba karamar murza nakesha ba

matukar ya rikeni kaini jinakefa yayimin girma wlh.
Koda nagama shirina kwanciyata nayi cikin D'akina nai bakan dannasan dole saiyazo komi
dare,Ina sane nakicin abinda hajiya kaka ta aikomin dashin dan ban shirya mutuwa cikin
kwanakinnan.

Banwani jima da kwanciyaba,Saigashi ya shigo,Hade girar sama data k'asa nayi dan karma
yaga fuska.

Kallo daya yaimin ya Saki dariya me sauti dan har Mimi saida ta motsa.

Harararshi nayi tare da juyamishi baya"Yi hakuri matar zokiji bake nakema dariyaba kawaidai
inayine sabida tsaro kiyi kiyi hakuri taso muje yau babu abinda zanyi miki insha Allah iyakata
rungumarki ainima inada imani Jidda ,Nai miki wannan aikin jiya mezaisani damunki yau?
Zomuje mu kwanta Allah bazanyimiki komaiba.
Murmushin dake kan fuskarshi yasani kasa gasgatashi danhaka marairaicewa nayi,Dady
kace wallahi!!!

Wani murmushin ya Saki lallai yau gashi matarshi nasashi rantsuwa,Cike da nishadi ya
furta"Ammadai ko wa innan tagwayen abari intaba ko?

Bakina na turo gaba,To Allah banzuwa ni nan zankwana.

"To naji har nan dinma nafasa tabawa tashi muje.

Duk da haka bakina adane nabishi shiko sai sakin mirmushi yakeyi.


Dan girman Allah dady karkamin komai wlh nagaji har yanzu jikina bedaina ciwoba kaji?


"Karki damu Jidda babu abinda zanyimiki kinji? Yi kwanciyarki.

Sauke ajiyar Zuciya nayi na gyara kwanciyata cikin jikinshi ina shak'ar kamshin da yakeyi.


Shima inajin yanda yakekuma shigewa jikina.




****

"Haulat inbaki shawara zakiji?

Saida taiwani das das da cingam din dake bakinta kamin tace inajinki.

"Kinga dai tun farko dama Dr. Habib betaba cewa yana sonkiba balle kince yanzu dayai aure
ya yaudareki,Hasalima saidaga bayannan sannan yasan kina sonshi,Kuma tunda kika
gayamishi yabaki hakuri harma da shawarar kisami miji daga masu nemanki kingadai ai be
cucekiba,Amma yanzu idanunki sun rufe kina Neman cutar da yarinyar dabatajiba
bataganiba,To inbaki saniba ki sani matar da ya aura marainiyace gaba da baya danbata da
uwa balle uku,Wallahi kika tabata Allah bazai barkiba,Sannan nasan koda aikin da zai aureki
akayimiki zai aurekin Amma wallahi bazaki taba samun kwanciyar hankaliba dan ba sonki
yakeba,Danhaka dan Allah ki hakura tun kamin lokaci ya kure miki,Nikinga tafiyata.

Dawani kallon banza tabita bayan barinta dakin,Amma Sam maganganunta ko daya babu
Wanda yai tasiri akanta.


50.




Cikin rashin kuzari ta tura kofar tashiga ranta amatukar bace domin duk abinda suka tattauna
kusan akunnenta akayishi bata taba tunanin rashin hankalin diyar tata yakai hakaba.

Kallo daya haulat din taimamahaifiyarta taji hankalinta ya tashi domin mace ce Wadda Allah
yayota tsayayya musamman akan yaranta.

"Tashi zaune dan ubanki kimin bayani dalla-dalla yanda Zan gane kamin in miki shegen bugu
yanzu kamin wani cikin yayunki ya shigo insa ya karairayaminke wallahi ,Gara inyi jinyarki da
masifar da kike Neman jamana gayamin waye Habib?

Tuni tafara hawaye yayinda cikin zuciyarta taketa tsinema aminiyar tata dan itace tajamata
komai.

"Umma dan girman Allahkiyi hakuri wallahi na daina.

"Abunda na tambayeki kenan dama?

"A a Umma shine wannan likitan da muke aiki k'arkashinshi wanda yataba duba hajiyar Abba
lokacinda tai ciwo,Wallahi babu komai tsakaninmu.

"Dama ainasan babu komai tsakaninku domin mutun me hankali kamarshi bazai tsaya
sauraran mahaukaciya Mara nutsuwa kamar kiba,Ke inbanda hauka wani shege yacemiki
Awannan zamanin mace na cewa tanason namiji? Kila kallo namiji ma kezuwa yace yana sonki
amma idan anyi auren ya ake k'arkewa balle kinkai kanki gareshi,Wai meyasa baki da nutsuwa
ne haulatu?
To wallahi dagayau zuwa Rana itayau ki fidda mutun daya cikin masu nacin nemanki,Inba
hakaba wallahi wallahi haulatu ina tausayamiki dan tabbas zanyima mahaifinki bayanin komai
yabaki duk wanda yaga dama nagayamiki sati daya tal nabaki,Yo banda sakarci irin naki ga
masu sonki wa inda basu damu da wulakancin da kikemusuba sudai fatansu kawai ki amince
amma sai Wanda bemasan kinayiba,Kuma kinsami k'awa ta arziki tana gayamiki gaskiya amma
kekina ganin bataimiki daidaiba!!! Yanzu Ke Saiki iya zuwa wajan wani katon banza yai miki
asirin da zaki auri wani?Angyamiki so haukene?

To kiyi gaggawar fidda miji tunkamin incanza shawara ma wlh.



"""""

"Jidda Tashi ga ruwan zafi can nafara doramiki wanda zakiyi amfani dashi wajan girki kinji! Ko
jikinne?

Manyan idanuna da sukadanyi surkin ja Sabida barcin da be isheniba na zube Saman
fuskarshi dan har wani baya yaja sabida yanda kallon ya bigeshi.
Cikin shagwaba na kalleshi,Wallahi dady ko ina ciwo yakemin kumafa lafiyata lau amma
jikina kamar ba nawaba.
Hannuwanshi ya daga sama"Sannu Ammadai ai ni babu ruwana ko? Tunda jiya barci
kawai mukayi banyimiki komaiba ko?

Wani kallo na sakarmishi kamin ince Ai tunna shekaranjiyane ko.

Dariya ya Saki kamin yace"Amaryar dady sarkin rikici to kiyi hakuri zo inrakaki ki wanke baki
saimuje inkamamiki girkin kinga yau juma'a nima zanshiga wajan aiki yau.

Hatta ruwan da Zan wanke bakin da kanshi ya zubamin shi,Duk motsina akan
idanunshi,Yayinda yaketa furta sannu Allah yaimiki albarka jidda,Allah ya jikan su mama.

Nikuma wannan adduar ke kuma farantamin rai wlh.
Lallai ko yanzu naga ribar auren babban mutun kuma me shekaru,Dan duk tsiya sai ansami
banbancin hankali da tunani tsakaninsu.

Bina yake kamar jela har saida na kammala komai naima Mimi wanka shikuma yaimata
shafa ya shiryata, Ah dady baka shiryaba Kai?

Langabar da kanshi gefe yayi"Ai kenake jira jidda bazan iya shiryawaba.

Hijab kawai nasaka akan tawul din dake jikina na fice zuwa d'akinshi,Yayinda shikuma ya tura
Mimi falo ya biyo bayana.

Numfashinya kawai naji saman fuskata,Har mamakin daddy nake wallahi.
Hijab din jikina ya zare yana kallon cikin idanuna niko bansan na lumshe idanunba sabida
yanda gabadaya ya kashemin jiki.
Manyan idanuna na fiddo waje lokacinda naga yana cire kayanshi,Nan da nan naji
hankalina yana nema yatashi,Amma saina daure ban nunaba,Humm wanka ko wasa,Haka
yagama jagulani sannan muka fito ko idanuna kasa budewa nayi sabida kunya shiko ko
ajikinshi,Saima mirmushi da yake saki duk lokacinda ya kalleni.
Ko wajan cin abinci kusan siriki haka ya zamemin dan wata irin masifafar kunyarshice ta
addabeni bantaba ganin babban mutun babu kaya jikinshi ba sai yau.




""""

Bayan wata daya, Kwance nake saman doguwar kujera idanuna arufe barci nakeyi amma irin
barcinnan Mara dadi.

Sadiq ne wajan kafafuna yanata matsaminsu,Sunyi dako dako dasu domin da zazzabi
nakwana bawani barcin kirki nayiba ga dadyn benan yai tafiya akan kasuwancinshi.

Wayata daketa ring Sadiq ya dauka tare da gaida mahaifinshi dan dama shine yaketa Kira
akai akai.

"Sadiq yaya jikin auntyn naku da sauki ko? Zahra din tazo kuwa?

Eh tazo daddy gatacan tana girki amma auntyn bata daina zazzabinba yaushe zaka dawo
ne?

Jiyai hankalinshi yakuma tashi fiye da farko"Kaga Sadiq bani ita muyi magana tukunna
kaji!!!!

"Daddy ai barci takeyi.

Kanshi ya dafe yana kallon Kamal dake gefenshi.

"Ka kwantar da hankalinka dan Allah baga hajiya can ka turaba insha Allah zata warware
damma Allah yasa cikin hutu suke,Gobe idan Allah ya kaimu saika wuce,Nikuma idan ankuma
kwana biyu na kammala ayyukan nan saina biyoka,Amma Anya ba cikine da itaba Dr.?

Wani zazzafan huci ya fitar kamin yace ina tunanin shine kamal ni wallahi tsoron fadan
hajiya nakema kasan tace duk dibarar da zanyi inyi kadda inyima yarinyar mutane tun yanzu
aita fama gara zuwa gaba,Nikuma inason haihuwa da ita bama hakaba wani lokacin sai Inga
kamar zata iya barina Amma kaga idanmuka Tara zuri'ah da ita,Rabuwarmu zata iyayin wahala.
"Eh hakane kam,Ai kawai share maganar hajiya zakayi tunda da lafiyarka itama da lafiyarta
arasa samun cikine Habib ai kawai fuska zakayi,Allah dai yasa tasami laulayi me sauki.

"To amin ya Allah danma yarinyar Nada kokari wallahi har mamakinta nakeyi wani lokacin.

"Eh haka naji nafeesa na fadi,Allah yakawo masu albarka dai.




**""""**


"Aunty dan Allah kitashi kiduba abinda nadafa ko zaki iyaci tunfa safe nazo gidannan amma har
yanzu ko ruwa banga kinsama bakinkiba wannan yunwar mafa wani ciwonne,Cewar zahra.

Dakyar natashi zaune,Zazzabin ya sauka amma Sam banjin dadin jikina hasalima jinake
kamar inta ihu konaji dadi,Zahra banjin dadi wallahi jikina kamar ba nawaba bakinama daci
yakeyi.

Cikin tashin hankali ta koma gefe tare da dannama dadyn kira, Dama har lokacin zaune
kawai yake danhaka da sauri ya yanke kiran ya kirata.
"Zahra ya akai?

Daddy takicin komai wallahi kuma jikinta ko kwari babu,Dazu har kuka tayi.

Jin yanda muryar zahran ke rawa yasasu sakin murmushi dan yasan indai kukane to suduka
sukayishi.
"Bata wayar Bari inyimata magana.

Duk da nayi kewarshi amma jinai kamar infasa wayar dannifa jinake komai babu dadi.

"Babyn habibu ya jikin naki?

Cikin sanyin murya nace da Sauki.

Zamanshi ya gyara kamin yace"Sannu Allah yabaki Lafiya gobe insha Allah zanzo sai indubaki
ko muje asbt,Amma yanzu ki taimakamin kici wani Abu kinji? Inkuma akwai wani Abu da kike
buk'ata nadaban gayamin sai insa akawomiki kinji ko!!!!


Yamutse fuskata nayi kamin ince to.

Saurin ajiye wayar nayima dan kadda yakuma yimin wata maganar daban.


Kallona na maida akan zahra da tayi wata kalar tausayi da ita,Abincin ta kawomin shinkafa
da miya wadda ta wadatu da nama saidai kallo daya naima abincin naji kyamarshi ta
kamani,Danhaka da sauri na dauke kaina,Dan Allah zahra fitar da abincin nan wallahi ko
ganinshi bansan yi. Da sauri ta mike hartana kokarin faduwa"nashiga ukuna ni fatima zahra wai meke damunki
dan Allah me kk so yanzu?

"Banidai lemo insha kawai idan bakina ya warware naci abincin amma banjin dadin bakina
Sam wlh,Inaga zazzabin da nayine kawai.

Muna cikin wannan artabun da zahra saiga sallamar hajiya kaka da kuma hajiyata da alama
dayane ya biyama daya.

51




Dukansu da alamar damuwa suka k'araso ko wacce namin Sannu niko gwana saiwani bata
fuska nakeyi,Dama yaya lafiyar kura.

"To ke takwara haka ake rayuwar duniya sabida Allah Dan naga da Alama kwanan nan zaki
zama mama"

"Kai hajiya kibarmin diya ta wala gaskiya,Ai duk laifin na wannan shakiyyinne,Tunda har fada
naimishi akan lallai yayi 'yan hikimominsu na likitoci kadda yai gaggawar yimata abunnan amma
yai biris gashinan tun ba aje ko inaba za afara zarya asbt.

Kinjiki dawata magana komai ai na Allah ne ke zahra kiramin usmanu yazo ya mik'amu asbt
aduba kamin megidan ya dawo.

Bakina na turo gaba daya ,Allah banzuwa ni babu inda zanje bama wani wuri kemin ciwoba
yunwa kawai nakeji.

"Humm aifa abin nema yasamu ke zahra samo Mata wani Abu taci,Cewar hajiyata.


Nidai lemo kawai nasha nasamu na kwanta yayinda suka dasa hirarsu saikace ba Mara
Lafiya sukazo ganiba.



Sai yamma liss nasami sukunin farkawa,su hajiya kaka nanan har lokacin gabadaya
sunhana gidan sakat DA hirarsu.

Wanka nayi tare dayin Sallah sannan zahra ta kawomin dambu Wanda hajiya kaka tasa
ayomata.
Nadanci amma bada yawaba Dan har lokacin banjin dadin bakina.


Bayan sallar magriba ya usi yazo ya kwashesu gaba daya zasu biya su ajiye hajiya kaka
saiyakai hajiya gida Sannan su wuce bayan yaimin alkawarin gobema zai kawo zahra din ta
yini.

Adaddafe nai sallar isha'i Mimi na gefena gabadaya yaran basu DA walwala sabida ganina
kwance DA sukayi.

Faruk ne ya mikomin wayata, DA kyar na amsa idanuna alumshe nasan dai bazai wuce
daddy ba tunda dama kullun saimunyi waya kamin mu kwanta.

"Autar mata ya kike ya jikin naki?

Alhamdulillah naji sauki sosai ya aikin?


"Komai qalau baby gobe da wuri zan shigo insha Allah saimuga yanayin jikin,Ammadai kinci
wani abun yanzu ko?

"Daddy banjin yunwa bakina babu dadi ni wallahi komai ya canzamin daddy.

"Ayya!! Yi hakuri zakiji sauki insha Allah bari harna dawo yanzu kisa Sadiq ya rufo kofar falon
saiku kwanta kinji ko?

""""***"""""


Da wani irin kasala DA nauyin jiki natashi wanda yafi na jiyama,Abinda yai matukar
tsoratani,Sadiq ya hadamana tea tsurarshi mukasha danshi ko kwai be iya soyawaba tea dinma
ni na dinga gayamishi yanda zaiyi.
Gyaran gida da d'aki kuwa basu da matsala

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login