Showing 12001 words to 15000 words out of 84412 words

Chapter 5 - YARDA Book Complete by Maman khady.pdf

Advertisement

12 Jul 2025

2675

Dora hannuwa tayi akirji alamun tashin hankali kamin tace"Innalilllahi naga ta kaina ni binta
ke kuwa Jidda kina haukane da auren naki zakibar mijinki ki kwana dawasu shikenan Ashe jiya
kinsha tsinuwar Allah data mala'iku yo Ashe shiyasa naga fuskarki tafara duhu.

Tsalle daya nai saigani kusa da ita Dan na masifar tsorata wallahi,Tuni idanuna sunfara tsiyayar
da kwallah Ashe shikenan nagama yawo tunda Allah ya tsinemin,Kuka nasaka ina riko
hannuwanta.

"Dadine taji yakamata Amma saita fuske,"Kinga kwantar da hankalinki ai Allah zai yafemiki
ainasan baki saniba ko?

Kaina na dagamata ina share hawayen idanuna.

"To bari Ingayamiki gaskiya Danni bazanso wani Abu ya samekiba tunda ina sonki danhaka ki
nutsu inyimiki bayani kinji ko?

Hawayena na share ina kallonta.

"Yauwa to kingadai anriga an dauramiki aure yanzu dole zaki kiyaye wasu abubuwa sabida
kisamu ki sami tsira wajan ubangiji,Nafarko dole zaki dinga kula da mijinki duk abinda yakeso
shi zaki dinga yimishi zai kuma sonki sannan ga lada da Allah zaitabaki,Kinga yimishi sannu da
zuwa darakashi idan zaifita yimishi addua da kuma hadamishi ruwan wanka da temakamishi ya
shirya sannan inkinga ya gaji saiki dinga temakamishi da tausar jikinshi,Sannan dole ki dinga
kwana dashi.

Hannuwana na Dora aka zansaka kuka,Tai gaggawar jawoni jikinta tare da rufemin
baki"Shikenan tunda bakiso agayamiki gaskiya tashi kutafi.

Shiru nai amma har lokacin kirjina bekoma daidaiba yo ai abinne yazomin asama.

Ahankali ta dinga nunamin yanda zanyi cikin nutsuwa da kwantar dakai tun ina zare zaren ido
harna koma ina dagakai alamar dai na fahimta sannan tace tashi kiyi sallar isha'i saiku wuce
ammafa lallai yau kadda ki kwana d'akinki kibi mijinki inba hakaba aure zansa yakumayi wacce
zata kula dashi. Bakina na turo gaba kamin in mike"Nikuma wallahi yana auran wata zanyi tafiyata gida
wajan hajiya.


Kamin mu wacema saida hajiyar takuma jama zahra kunne akan kadda ta kuma yarda
mukwana tare inba hakaba babu wata shakuwa dazata shiga tsakanina da dadyn,Aiko nan da
nan tai na am da hakan Dan itakanta tunanin yanda zata hada tsakaninmu takeyi.



****


Ko cikin mota lamo nayi ko hirar nakasa sabida tunanin yau Zan kwana da dady,Shidai bekawo
komai arashiba hasalima tunaninshi ya tsayane akan kila kewar gidane ke nukurkusata.

Itako zahra ai tsara yanda za ai kawai takeyi.

YARDA.
Littafin maman khadija,Kamar yadda kukasani maman khadija tasaba kawo muku labarin
littatafai domin nishadanwarwa agareku,To wannan karonma gata DA wani sabon salo cikin

labarin YARDA.
Ina Mata masu gudun soyayya DA babban mutun? To kuzo zakuji yanda manyan mutane ke
baje kolin soyayyarsu me matukar birgewa da tsayawa arai.

Duka wannan labari zaizo muku akan naira Dari biyu kacal game buk'ata,200.

Account number.
0005074141 Aisha sabiu ja'iz bank.

Kokuma number waya.
08142643253
Maman khadija.

Duka zaku turo shaidar biyanku ta wannan layi👆🏻Nagode sainajiku.


Maman khadija.
Haske writer's asso.



YARDA. 13



Duk dacewa cikin kowa acike yake amma saida ya biya damu yaimana siyayyar kayan kwadayi.

Har wannan lokaci jikina asanyaye yake nifa mamakin yanda Zan kwana DA dady
nakeyi,Afakaice nad'an waiga kadan na kalli girman jikinshi musamman kirjinshi,Ai sainaji wani
kwattt na hadiye wani miyau batare Dana shiryaba.

Kamin mu k'arasa Mimi tai barci,Dayake dama nida itane gaban motar.
Dan kallona yai kad'an kamin yace"Jidda ko baki da lafiyane?

Bakina na turo gaba tare DA kauda kaina ga barin kallon inda yake kuma banyi maganaba
saima Mimi Dana gyarama kwanciyarta ajikina sabida barcin nata yai nisa.
Murmushi kawai yayi tare da 'dan buga sitiyarin motar,Fadan da yasha wajan hajiyarshi
kemai yawo cikin zuciya,Shiko taya zai shawo kan wannan rigimammar.


Kasa motsawa nayi koda motar ta tsaya saida duk suka gama ficewa sannan ya zagayo
wajena ya sabi Mimi akan kafadarshi"Idan kin kintsa ki kawomin tea d'akina.

Bayanshi na harara kamin in fito cikin motar,Ina gyara hijab dina.

Ruwa kawai na watsa sabida zafi-zafin da akeyi,Ina k'okarin saka kayane zahra ta
shigo."aunty dady na kiranki fa kadda ki manta ki kwanta"

Zahra nifa bansan wulakanci gaskiya nace ki daina cemin aunty ko?

"Kema fada kikeyi amma kinsan dolene mu kiraki da aunty daddy kike aure fa! Bama wannan
ba ai ki godema Allah da ba mum muke kiranki dashiba,Hayewa gado tayi tana
murmushi,Yayinda nabita da harara kamin ince dan Allah kikaimishi tea din Allah kaina ciwo
yakeyi.
"Hahhhha aiko banzuwa wlh aiyasan danidin amma yace saike danhaka kije kawai amma
yakamata kidan k'ara turare yanda zai gigice gaba daya.

Baki na hangame Ina kallonta"Ah lallai zahra Ashe tuni kikazama 'yar iska dady nefa?

Lumshe idanunta tayi kamin tace wayyo soyayya dadi Allah hadani da mai sona zanbashi
tsantsar soyayya,To dallah dazakice dady nefa,Cemiki akai shi dadyn be iya soyayyaba KO
beson soyayya?Ai zakiban labari waataran Amma wallahi dady k'arshene wajan iya love.


Hijab Dina nasaka nabarmata dakin dannaga yau wani tashen iskanci takeji,Saida safe aunty,
Cewar zahra ganin zanbar dakin.

Bantashi jin wani mugun tsoroba saida nai sallama cikin D'akin babu wani haske sosai amma
Ina hangen dadyn zaune gefen gado da babbar wayarshi ahanunshi,Dakin saiwani mayen
k'amshi ketashi musamman yanda ac din tagama sanyaya d'akin.
Fararen idanunshi ya zube akaina kamin ya Saki murmushi sabida ganin yanda bakina yake
ad'ane da alama rigimar na kusa.

Niyyar cokana yayi danha saiya maida wayarshi ya ajiye gefe"Amarya shigo mana keda d'akin
mijinki"

Tuni idanuna sun kawo ruwa jin abinda yace,Kuma ban motsaba saidai kaina Dana sadda
k'asa.

Sam banji motsin tasowarshiba saidai naganshi gabana yana niyyar amsar tea din Dana
hadomishi.
Saurin sakarmishi nayi Ina niyyar juyawa,Danhaka da sauri ya riko hannuna daya yana fadin
"Ah to kuma inazaki inace yaran duk sunyi barci ko?

Cikin murya wadda take cike da shagwaba nace to ai nima barcin zanyi ko.

Zaunar Dani yayi bakin gado yacigaba dashan tea dinshi saidai lokaci zuwa lokaci inajin
idanunshi akaina.
Saida ya wanko bakinshi sannan yadawo kusa Dani ya zauna har guiwarshi nadan tabo jikina
tuni nakuma takurewa saidai shi yaiwani irin basarwa dinnan kamar ma besan abinda yayiba.

"Gobe zakuje school ko?
Akunyace na dan kuma muskutawa sannan na dagamishi kaina batare danayi maganaba.

To tube hijab din saiki kwanta ko?

Manyan idanuna na fiddo waje kamin ince Ina Zan kwanta dady?

Kauda kanshi yai gefe yana dariya cikin zuciyarshi lallai yarinyar nan da wayanta kenan.

"Kinga Jidda ki tube hijabin ki kwanta gobe zakuje makaranta nikuma zanshiga abuja idan
Allah ya kaimu so kinga zamu iya makara ni sai inkwana falo hakan yayi miki?

Kusan Adan tsorace na d'aga kaina,Sannan na raba gejenshi na kwanta batare danacire
hijab dinba ammadai araina naji dadi tunda yau mala'iku bazasu tsineminba tunda nazo kwana
dakin dady.

Saita ya tabbata barcina yai nisa sosai sannan ya lallaba ya janye hijabin jikina idanunshi
nakan kyakykyawar fuskata domin betaba tunanin haka nakeba hasalima betaba zama ya
k'aremin kalloba duk ganin da yakemin idan yaje makaranta wajansu zahra.
Saurin kauda kanshi yayi lokacinda idanunshi suka sauka akan 'yan madaidaitan kirjina wa
inda bawai gama tasowa sukaiba hasalima yanzune suke tashensu.

Daki-Daki haka yadinga bin surar jikina da kallo Wanda har saida yaji idanunsu sun wadatu
da hakan dan Kansu sannan ya lallaba ya kwanta kusa Dani,Kamar mejin tsoron wani Abu ya
cutar dashi haka ya rungumoni jikinshi.
Wata irin ajiyar zuciya me k'arfi ya sauke,Musamman dayaji nakuma shigewa
jikinshi,Hancinshi ya kuma mannawa wajan wuyana danjin wani sanyayyan k'amshi me matukar
kwantar da hankali.


Motsawar farko da yayi saijiyai Ana sallar asuba,Ahanzarce yaso tashi saidai jin yanda aka
nannade jikinshi yasa ya tuna bashi kadai ya kwanaba,Rabon da ya rasa sallah tun kamin
mariganya ta rasu domin alokacinne da cikinta ya tsufa sosai to basucika samun barciba sabida
ciwo. Da kyar ya yakiceni jikinshi sannan yatashi,Niko ai duk tunanina hajiyace na makale.
Saida duk yatashi yaran sannan yadawo dakin yafara tashina,Dan lokacin tuni angama sallah
ma.

Addua nayi sannan na bude idanuna aiko sai akan dady Wanda ya zubamin ido yana
kallona cikin hasken daya kunna.

Akunyace natashi nai saurin maida hijab Dina kayi hakuri dady yau na makara.

Murmushi ya saki kamin yace"Aidole tunda kinji dadin jiki ba irin na hajiyaba ko?

Kusan da gudu nabar dakin Ina murmushi.

Zahra na tadda ta idar da salla,Da sauri nima nayo alwalar nazo na kabbara sallar.
Ban tsaya biyema zahraba wadda keta tsokanata wai kamshin turaren dady nakeyi,Na wuce
bedroom dinshi domin gyarawa.
Saida na gaidashi sannan nawuce na wanke toilet bayan na daurayemishi wandunanshi
safuna danaga yajik'a.
Yana zaune akan doguwar kujera harsaida na gyara ko Ina nasa turare sannan na kalleshi
"dady yanzu zakai wanka ne?

"A a jeki abinki ki huta amarya Ashe haka kike da zafin nama? Allah yaimiki albarka anjima
saikizo kimin wankan.

Da gudu na fice kai dady Anya ba d'an iska bane kuwa,To yanzu saiya dinga min maganganu
irin haka,Dan Allah aga naimishi wanka ai sai acemana 'yan iska.



****"""""****

Bakwai saura duk muna zaune afalo Mimi Nata kwaso kayan buk'ata kowannenmu da kayan
makaranta jikinshi yayinda dady ke zaune saman kujera yana waya amma wani Abu Dana
fahimta shine duk idan nadanyi satar kallonshi sai inga idanunshi na kaina shiyasa sainaji duk
kunya ta kamani.
Yayinda shikuma mamakin halayena yakeyi saikace wata babbar mace,To kuma dama haka
abin yake indai iyaye zasu Fara nunama yaransu yanayin ayyukan gida Dana zamantakewa
musamman ta aure to lallai komai kankantarsu babu abinda zai gagari yarinya,To matsalar da
akesamu yanzu wasu itayenma sai bikin yarinya ya Fara matsowa sannan za ace za
akoyamata ayyukan gida girki da kula da Mijin wannan ko ai kowa yasan ba lallai idan wani ya
shigaba wani ya shiga.

Saida mukaci muka koshi sannan muka maida sauran akulla Wanda zamu wuce dashi
makaranta dan yau sai yamma sabida islamiyya.

Idanunshi akaina yake fadin Baku da wata matsala ko?Zan wuce abuja amma kila zuwa

dare indawo inkuma kunji shiru to Zan turo sulaiman ya tayaku kwana wancan room din
danhaka saiku kula bansan yawo kunji ko?

Da to duk muka amsa mishi tare damai fatan dawowa Lafiya.

Dallah kije ki rakashi ke wallahi kamar wata bakauyiya!!!Cewar zahra.

Bakina atunzure nabi bayanshi aiko yanajin takuna ya juyo da sauri,Dan jiyai kirjinshi
yawani buga musamman daya tuno yanda kayan makarantar suka fiddo surar jikina kuma
yasan da wuya idan nasako hijab din,Ilai kuwa yana juyowa muka hada ido,Ganin yaran babu
Wanda yafito yasashi jawoni jikinshi,Abinda ban zataba haka zalika bankawoma rainaba. Ajiyar zuciya ya sauke yanawani saukemin numfashi akunne Wanda yasani jin wani fitsari
zai kuccemin.

"Kiji tausayina kidaina sa turare idan zaki fita sannan kidaina fitowa harabar gida babu mayafi
kinga gamegadi sannan ga Direba zasu kallemin iyali kinji?

Neman kwace kaina nakeyi daga gareshi kawai sainaji wata zazzafar Sumba saman goshina
Abazata.

Wani taga-taga nai zanfadi lokacin lokcinda yasakeni,Shiko ficewa yayi yana murmushi
yayinda yakejin wata nutsuwa na ratsa jikinshi.

Saida zahra tazo tajani sannan muka koma cikin falon dan tuni jikina yagama
mutuwa,Gaskiya hajiya Zan gayamawa dan da alama dady lalatani zaiyi.



TUSHEN LABARI.
Yanzu Kai tsaye zamu farkon labarin shin wai wayema Dr.Habib?


YARDA.
Labarin yarda na kudine idan kina buk'ata zakibi wannan tsarin domin samu.

Acct no.
0005074141 Aisha sabiu,Ja'iz bank.

Kokuma katin waya ta wannan layi,08142643253.
Maman khadija.
Tura shaidar biya ta wannan number👆.

14

Alhaji ishaka inkiya Alhaji nabature,Babban mutunne sosai cikin garin Kaduna haifaffen garin ne
domin anan ne duk tushensu yake,Alhaji nabature me arzikine sosai dan D'an kasuwane na
nunawa cikin jaridu.
Yanada matarshi guda d'aya hajiya binta wadda sukai aure tun saurayi da budurwa kuma
Allah besa yaimata abokiyar zamaba harta Allah ta kasance akanshi.
Hajiya binta itama 'yar nan cikin garin Kaduna ce kusan kowa Nata anan yake shiyasa duk
inzaka bada tarihinsu to lallai zakace sudin 'yan kadunane gaba da baya.

Yaran hajiya binta bakwai maza biyar sai Mata biyu,Habib shine k'arami dan shine
autanta,Cikinsu babu Wanda beda rufin asirinshi har matan domin ko wacce tana aikinta
sannan duk sukan hada da kasuwanci kamar yadda mahaifinsu ya shawarcesu tunkamin k'asa
ta rufe idanunshi. Hajiya Aisha na aure kano sai hajiya Rukayya dake aure hadejia ko wacce tatara iyalinta.
Sauran mazan kuma ko wanne da muhallinshi babu wanda yai sha'awar zama da ita koda
yake itace batason zama da surukai.
Allah ya temaketa wajan ganin hade kan dukkan iyalanta dan gaskiya akwaisu da hadin kai
da son juna sosai sukeson junansu.

Ayanzu hajiya tana tare da jikanta tahirr kamin yatashi dan yanzu haka da ranar aka,To
hakafa hajiya binta take Sam bataso ta zauna ita kadai amma kuma bata yadda ta zauna da
surukaba shiyasa takema jikokinta haka idan ta zauna da wannan dayai aure saita kuma daukar
wannan komace ko namiji. Saidai duk da haka lokaci zuwa lokaci kakan sami gidan Nata cike da jikoki dan Sam bata da
matsala,Wasuma sukanje Mata weekend.

Dr.Habib me kimanin shekaru akalla 41 yanzu shine yaron hajiya na karshe yayi karatunshi
na likitanci a kasar China Wanda saida yazama cikakken likita sannan yadawo najeria afarkon
samartakarshi,Habib irin miskilan mutananne saidai yanada duk wasu halaye na kwarai da ake
burin samunsu akan mutumin arziki.
Dawowarshi yafara aiki awata babbar asbt cikin kwarewa da sanin makamar aiki ga kulawar
dangi tako Ina domin awannan datsin ne Allah yaima mahaifinsu rasuwa,To saikowa yake bashi
kulawa duk da cewa alokacin yakusa shekaru 30 Saidai ganin shine k'arami yasa ake
nunamishi hakan.
LALURARTA ce sanadi;Tazo ganin likita sabida azababbane ciwon ciki Wanda takanyishi
duk wata aiko ranar Allah ya dorota akan sa'a sabida alokacin shi ganinshi ma saikayi sa'a.

K'amshinfa shine Abu na farko daya fara yimishi sallama dalili na farko dayasashi sanin eh

budurwace wadda zaigani yanzu.

Saida yayarta ta temaka Mata tadan zauna sannan suka gaisheshi,Amsawa yayi batare daya
kallesuba saidai tuni zuciyarshi ta azalzaleshi akan ya kalli fuskar Mara lafiyar.

Danhaka dole ya kureta da kallo Wanda besan lokacinda yai hakanba har saida kukanta ya
fargar dashi.

Magunguna ya rubuta mata da allura bayan yarubata wasu gwaje gwaje da za aimata,Saidai
alokacinne yasamu kanshi da bata umarnin ta dawo bayan kwanaki uku,Alhalin shi kanshi
alokacin besan dalilin dayasashi Neman hakanba.

Awannan lokacin bata isa tace ga kalarshiba dan ciwo be barta ta kalli ko fuskarahiba.


Wannan shine silar haduwarshi da Maryam wato mahaifiyarsu zahra.

Kunsandai miskilin mutun be iya son abuba danhaka irin kulawar dayabawa matarshi abar
ayi koyi da itane.
Haduwarsu da watanni bakwai akaimusu aure,Dan itama haifaffar kadunace aiki mahaifinta
keyi zaria shine sukan bishi wani lokacin,Wani lokacin kuma suyi zamansu nan kd din.
So bawani wahalar bincike bangarorin zasu samuba.

Idan kashiga gidansu to lallai zaka fito da kunya domin Maryam wayayyace musamman data
Lura da abinda mijinta ke buk'ata kenan kulawa,Shiyasa bata hada kulawa dashi da komaiba
hasalima bata da wani lokaci Nata matukar yana gidan.



*****"""""*****

Haihuwarsu ta farko suka sami me sunan hajiya wato fatima saidai suna kiranta da Zahra,Duka
shekarar zahra uku da haihuwa ta haifi Abubakar Sadiq taso kwarai alokacin ta tsaida haihuwa
amma yai biris da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login