Showing 66001 words to 69000 words out of 84412 words
hajiyar taki fahimtar hakan acewarshi,Balle dayaga yaran kamar
ma gudunshi sukeyi wai hadda Mimi uwar 'yan kulafuci,Amma yanzu shareshi takeyi saima
nanike jiddan da sukeyi, Gashi konan dacan hajiyar taki bashi damar zuwa.
****
Kai gaskiya bazata sabuba wallahi,Nawa nakashe akaimin wannan aikin Amma gashi komai na
nema ya lalace tun kamin aje ko ina.,To aiko wallahi bazai sabuba.
Itakadai ke sababinta sabida tun safe take kiran wayar daddyn Amma har la'asar babu wani
bayani daga karshema saitaga ashe kashe wayar yayima.
TO DAMA AI HAKA RAYUWAR TAKE MAGANAR BOKA KILA WA KALACE INKA YADDA
KA BACE SANNAN BA LALLAI KASAMI ABUNDA KAKESO DAN SUMA MASU NEMANE.
Bayan Sallar magriba;
Ganin irin kallon da daddy kebina dashi kamar tsohon maye yasani kasa zama falon
danhaka na lallaba nashige bedroom din hajiyar nai kwanciyata,Dantace mungama zama
wancan gidan harsai megidan yadawo hayyacinshi tukunna.
Tashin Danai Sam beji dadinshiba duk da cewa yafarasamun nutsuwa adan yinin dayayi
yau dinnan,Gashi yana kallo hajiya saita tofe kome da addua indai bashi zatai,Tanayi tana
sababi.
Bayan sallar isha'I Saiga alhaji yusuf dawani malami Wanda takanas hajiyar tasa azomata
dashi,Bansan da zuwanshiba Saida hajiyar taje ta kirani wai nima a kwankwasheni ko abin
yashafeni,Saidai ni qalau nake daddyn nedai me matsala.
"Ai hajiya kamar dai yadda Allah ya bayyanamin to gaskiya sihirine kuma Allah ya takaita dan
gabadaya da niyyar juya kanshi akayishi to Amma komai yazo da sauki danhaka saimudage da
addua Allah yasa iyakar wahalar kenan Allah kuma ya kiyaye gaba,Yanzu abinda yakamata
anan shine ga wannan rubutun nan ayoyine na karya sihiri da akai tofinsu cikin zamzam
danhaka zaidinga shane yana shafawa Cikin hukunci na lillahi komai zai warware cikin kankanin
lokaci indai yayi yanda yadace.
Godiya sukaimishi sosai tare ddabashi sadaka Sannan suka rakashi,Sai falon ya kasance
dagani Sai daddy dake zaune yai shiru da alama wani tunanin yafada.
Kauda kaina nayi ga barin kallonshi ganin zai kallo inda nake.
"Jiddana" Sautin muryar daddy ta bugi kunnena yana kiran sunana,Acikin zuciyata na amsa
kiran haka ko kallon inda yake banyiba,Amma kobabu komai nasami nutsuwar zuciyata tunda
naji inda matsalar take.
Nasan haka kawai bazaimin abinda yaiminba,Ga tausayin zahra dake zuciyata Dan tunda
taji labarin komai take kuka tare da furta inyi hakuri itace tajamin.
Jin yakuma kirana yasani mikewa tsam na barmishi falon,Lokacin Hajiya kaka tashigo falon
daga rakiyar malam din.
"Kaga ai bazama zakaiba auta tashi zakai kayi sallar isha'i Saikasha wannan rubutun ka
shafa inkuma baka iyawa saina shafamaka.
Da sauri ya dago kanshi yana kallonta jin wait m zata shafamai.
Harara ta wurgamishi kaini daina kallona da wa innan manyan idanun naka,Kana
mamakine kocemaka akai bazan iyaba? To ko daya dan lokacinda na tubeka naimaka zirr na
shafeka me nawama beganiba danhaka tashi maza ai ba zama zamuyiba dannatabbata zuwa
gobe ahaidaniyar zatafara wani sabon aikin tunda yaudai batasami yanda takesoba.
"""""
Sanye da farar jallabiya yafito me gajeran hannu sai tashin k'amshi yakeyi,Zama yai tare da
shafar kanshi"Nagama shafawa hajiyata.
"To Allah yaimuku albarka yakuma bamu dacewa Dan Allah kadage kaji?
"To Hajiya ins ha Allah zanyi yanda kikace,Amma ni Ina mzankwana?
"Yo inafa zaka kwana KOnan falo ai saikai kwanciyarka inkuma bakason nan din baga
dakuna nan da yawaba saika zabi inda kakeso.
"Amma hajiya nida zahra ko?
"Taimaka ubanmi halan yarinyar dake fama da kanta, Kumama yanzu kasan da ita?
"Dan Allah kiyi hakuri Allah sonakeyi inbata hakuri.
"To indai hakane kajira zuwa safe saikabata.
Yamutsa fuska yayi tare dayin kalar tausayi tabbas akwai damuwa wlh Indai yau beji dumin
matarshiba.
[5/9, 10:12 PM] Maman Dije: 59
Saida ya tabbatar da kowa na gidan yai barci Sannan ya lallaba cikin d'akinda nake kwance
domin wata irin masifaffar sha'awa ke damunshi saikace yai shekara rabonshi da mace.
Sakin labulen tayi bayan taga shigarshi cikin d'akin dama tana sane tace jiddan ta kwana
ita kadai, murmushi tasaki kamin tace habibu kenan Allah ya warware damuwarku cikin
gaggawa ya tsarekai da sauran 'yan uwanka,Cikin wannan zamani me matukar ban tsoro.
Hajiya kaka kenan mace jajurtatta akan iyalinta.
Ajiyar zuciya ya sauke lokacinda ya rufe kofar bayan yashige dakin,Lallabawa yayi zuwa
gadon kallo daya yaimin yaji yana kikarin idasa rudewa Dan wata farar rigar barcine jikina da
hajiyar tabani kuma kwance nake cikin haske abuna, Dan bansan lokacinda barci ya daukeniba.
Rigarshi ya tube tare da lallabawa gefena ya kwanta,Harwani bugu zuciyarshi keyi Sabida
tunanin yanda Zan karbeshi cikin wannan dare,Yo dama yaya lafiyar kura.
Ahankali naji saukar hannunshi cikin jikina bansan lokacinda na sauke ajiyar
zuciyaba,Sabida akwai wani irin Sanyi a hannunshi,Afusace nai niyyar tashi Amma ya Hana
hakan dan da karfinshi ya maidani cikin jikinshi yana sunsunar wuyana tare da birkitani da
zazzafan soyayyarshi.
Tun ina mutsu mutsun tureshi tare dason kwatar kaina harna gaji na daina Dan sosai ya
shiryama hakan dama.
Kadan ya hanani inyi dariya jin yanda yake sakin sambatu da nishe nishe irin arude yake
dinnan.
Yi yai kamar bazai barniba Dan saida nafara kuka Sannan ya sararamin.
Bayan komai ya kammala ina rungume ajikinshi Ina aikin kuka,Yayinda shikuma yai shiru
yana saurarena tunanin ta inda zaifara lallashina yakeyi.
Saida yaga lallaidai ba shiru zanyiba tsawon lokaci Sannan yafara jijjigani da furta"Dan
Allah kiyi hakuri kiyi shiru Jidda nagamafa kuma bazan k'araba shikenan ai ko banso kanki yayi
ciwo kinji ko?
"Kan nawa yai ciwon ina ruwanka dani,Kuma sainagayama hajiya ince fyade kaimin.
Manyan idanunshi ya fiddo waje gabadaya daya kamin yace yi hakuri dan Allah na tuba
matata bazan kumaba ki rufamin asiri ko so kikeyi hajiyan ta bugeni?
Tsakanina da Allah nadagamishi kaina Alamar eh dan har lokacin bandainajin haushin
abinda yaiminba Amma dayake beda ta ido yanzu yawani lallabo ya tausheni"Nikatashi kabani
waje tunda ka daina sona gobema gidanmu zanje kuma bazankumadawowaba bazan zauna
dakaiba.
"Dan Allah yi hakuri Jidda bazan kumaba,Wallahi inasonki kema kinsani kece cikon
farincikina Lallai idan babuke farincikina bazaitaba cikaba,Sannan bansan abinda yahau
kainaba har hakan ta faru kinga yaranama duk fushi sukeyi dani kiyi hakuri kuma kitayani
shawo kansu,Nasan ma indai kika hakura suma zasu hakura bazan kumaba kinji. Kuma shigar da hancinshi yayi cikin jikina yana furta"Nai kewarki sosai Jidda duk dare bana
iya barci,Jikinki yakuma canzawa indan k'ara kadan? Ahankali zanyi kinji matar albarka!!!
K'okarin kwace jikina nakeyi amma ya rikeni kam yana murmushi,Ganin danayi da gaske
yake yasani furta " to kaje kayo tsarki"
Dariya yasaki ahankali yanakuma shigewa jikina,"Karki damu yau basainayiba idan
nagama zanyi tsarkin gabadaya.
Duk tirje-tirjena be hanashi kumayiba sosai jikina yai ligif sabida wahala.
Ina rungume jikinshi har Saida barci ya kwasheni Sannan ya lallaba yatashi fuskarshi cike da
walwala,Wata irin nutsuwa dayarasa cikin kwanakinnan yajita yanzu tana sauka jikinshi,
Alhamdulillah yake nanatawa cikin zuciyarshi da fili.
Gudun fitinar da zan iya gwadamishi yasashi barina nai barcin sosai inyaso idan ya farka
sai ya tasheni na gyara jikina.
""""
Da ciwon jiki natashi ga tashin zuciya kamar ankarominshi haka kawaima yunkurin aman
nakeyi.
Adaddafe nai sallar asuba bayan yadawo Dani daga wankan da kusan shine yaimin shima.
Ki daure inkawomiki ko tea ne inaga kamar hadda yunwa Jidda bakison cin abinci.
" Bawani nan bakaine jiya kakusa kasheniba kumama ai banso kaimin dole ko!!!
Bakinshi yadafe kamin yace"Naji autar Mata laifinane naimiki dole Amma kuma ai kin
temakeni kuma nagode sosai tunjiya nake shimiki albarka nasan kinsami lada me tarin
yawa,Inje inkawo miki tea din?
[5/24, 4:23 PM] Maman Dije: 60
Idanuna kamar zasu fado haka nake harararshi Amma bawan Allah ko ajikinshi hasalima
saikuma lallashina yakeyi.
Da kanshi ya shiga kitchen,Dan har hajiyar ta tambayar"Kai waye nan?
Kanshi AK'asa ya furta nine hajiya tea Zan hadama jidda.
Wuceshi tai tana murmushi"Shakiyyin wofi yanaso yana kaiwa kasuwa.
Kusan da daru yasamu nasha tea din kuma saigashi naji dadin jikina Dan dama hadda
yunwar.
Sai nan nan yakeyi dani nikuma saiwani basar dashi nakeyi Dan tuni na huce tunda ba
laifinshi bane Allah ne ya jarabcemu ta hakan,Sannan koba komai namiji beson mace me riko
sunfison dasun baki hakuri to ki hakura.
Ina kwance da safe shikuma yanacan gefe zaune,Yaran sukai sallama suka shigo duk
gaidani sukai tare da min sannu da jiki,Sai suka kama kallon uban batare da sunyimishi
maganaba.
Ina cikin bargon na kalli Sadiq "Kai Sadiq bakuga daddy bane kuma haddakai babba?
Duk gaidashi sukai tare da ficewa suna turo baki musamman Sadiq Dan shine babba kuma
yafisu hankali.
Kallona yayi tare da furta" Jidda kinga yanda yara sukai fishi dani ko? Abunda betaba shiga
tsakanina dasuba Dan Allah kisaki jikinki dani nasan suma zasu saki,Amma kina dauremin ko
nuna rashin walwala zasucigaba da zarginane akan Ina cutamiki.
Cusa kaina nayi cikin bargon batare dana kulashiba,Amma duk dahaka nai niyyar yima
yaran magana dankada abun yai nisa.
***
"Kinga aikin danaimiki ba kalar wanda nasaba yima kowabane shiyasa na amshi kudinki da
yawa, Amma dama ai saidanagayamiki Akwai Matsala fa to ai wannan shine matsalar
mahaifiyarshi tsaye take kyam akanshi yanzu haka idan kika matsa akumamishi wani abu to
duk abinda akai kanki zai dawo maganar gaskiya inkuma kinaganin ayi wani to? Bama wannan
ba mezaihana kije ki hada da 'yan dibarunku na mata ko hankalinshi zai karkato zuwa gareki
ko?
Kwallar data cikamata ido ta goge tare da kallonshi ka barshi kawai bari inje Amma Zan
dawo kome kenan saimuyi magana.
Wani k'aramin tsaki yaja bayan barinta bukkar tashi, wawuya kawai asararra,Mata halinku
saiku ko wacce mace sai shegen son kan tsiya Sam wasu basu da tunani mata da yawa na
mantawa da wannan kalmar ta k'addara tabbas duk Wanda yayi hakuri to hakika kaddararshi
zata sameshi walau me dadi ko akasin hakan.Idan namiji ya kasance akwai aure tsakaninku
tofa basaikin bi malami ko boka ba zakisame ba A a addua kawai zata jawoshi gareki,Amma Ina
amfani ajawo soyayya da tsiya sai ya aurekin sati daya yai yawa anfara fada daga karshe
yafara ganin bakinki sai maganar saki to dama badan Allah akayiba,Wani tsakin yakuma ja
kamin yace kodayake inda babu gafalallu kamarku aida bamusami kudi ba.
Note.
Dan Allah Mata mu kula da halin rayuwa nayau da kullun tabbas duk kusan kura-kurai na
duniya Mata ke aikatashi yau Allah ya kawomu wani zamani da babu wani aiki na laifi da Mata
basu aikatawa,Wai ina rauni da tausayi wanda Allah ya haliccemu dashi? Amsar itace babu
sabida munyi watsi daduk kusan damar DA Allah yabamu.
Mutuna ayau idan Allah yasa mijinki zai auri mace goma wallahi kuna tare zai aurosu kuma
duk Wuya kuna tare Amma idan mukai hakuri saimuga komai yazomana da sauki,Tabbas hakuri
nada wahala amma yinshi kawai shine mafita agaremu.
Allah kasa mugane ka shiryar damu hanya ta daidai.
""""""
"Am Jidda nace ba kidan tambayarmana hajiya mana mukoma gida wallahi nagaji dazama waje
dayannan nasan kema zakifi sakewa idan muna gidanmu,Naimiki Alkawari babu inda zanje
kinji?
Kallo daya naimishi na kauda kaina,Batare dana tankaba dan gaskiya inajin tsoron
mukomacan kuma yadasa daga inda ya tsaya,Dannasan sihiri becika warwarewaba
gabadayaba kuma lokaci daya,Nasandai dole sai anbi komai sannu.
Kwanciya yayi kusa dani tare dadan sunbatar goshina yai lamo ya na shakar kamshina
yayinda nima nakuma shigewa jikinshi dan sosai turareshi kekuma shigardani.
"Bazaki kulaniba jidda? Shikenan kidai k'ara hakuri bazan kumaba insha Allah.
***
"Wai zahra ni amatsayina na mahaifinki Amma ki shareni tsawon kwanakinnan kinaganin kin
kyauta kenan?
Turo bakinta gaba tayi kamin tace"To daddy aikaima batamu kakeba ko?
"Zan bata rankifa zahra kome nayi kuma saiku biyemin bazaku tayani da addua ba ko cemiki
akai dole kullun mutun saiya kasance akan daidai? Kumama ai ba halina bane yakamata
kuyimin uzuri ita wadda naima laifinma ta hakura Amma ku kunkasa mantawa inace yanzu
nadawo lafiya ko? Yanzu idan aure nace zan k'ara wannan wulakancin zakuyimin?
Da sauri ta kalleshi"Aure kuma daddy?
"Eh mana ko cewa akai dole da ita kadai Zan zauna?
"Tab Allah daddy saidai ka saketa nima asakoni indawo gida Amma babu matar da zata
zauna gidannan ta cutarmin da k'anne,Wai kamasan irin YARDAR dake tsakanina da aunty din
dahar na yarda ta zamo makwafin mahaifiyarmu? To wallahi ko iyayenta bazasu yardaba haka
yayanta surukin naka na tabbata duk irin son da yakemin saiya sakoni domin basu hada sonta
da komaiba,Kasanko wannan abun dayafaru ko barcin kirki dainawa yayi? Kai meyasa bazakaji
tausayintaba amatsayinta na marainiyaba gaba da baya?
Ajiyar zuciya ya sauke "Lallai yarannan sun dauramana wani ta kumkumi da Allah,To shidai
dama beda ra'ayin rike Mata biyu tunda yake,Sannan bazaiyi fatan wani Abu Mara dadi yashiga
tsakaninsuba danhaka dole ya kiyaye komai da iznin Allah.
Ganin ya zubamata ido Amma yai nisa cikin tunani yasata mikewa tabar d'akin.
"Aunty har yanzu jikin yaki dadi ko?
"Wallahi kuwa zahra narasa abinda ke damuna gashi gobe zamu koma makaranta ni
bammasan yanda zanyiba jiyama da dare saida daddy yasamin drip.
"Allah ya sawake Amma gaskiya kinyi saurin yima daddy hakuri yakamata ace kin nunamishi
bacin ranki sosai danya kiyaye gaba Amma sainaga saiwani kulashi kikeyi namiji ne fa?
[5/24, 4:23 PM] Maman Dije: 61
Haba zahra yakamata fa ki tuna daddy ne babbane shi kuma yasan abinda yakeyi yakamata
mudinga yimishi uzuri shi ma beji dadin abinda yayiba,Babu komai awajena ya wuce Kawai
saidai mutari gaba kuma.
"Humm wani lokacin haushi kikebani wallahi, Daddy mahaifinane bazanso abinda zai
sakashi cikin damuwaba Amma abinda yayi yakamata ace kin tauna tsakuwa Dan aya taji
tsoro,Amma kinwani biyemishi kilama har kanki saida kikabashi ko?
Murmushi kawai nayi tare da kauda Kai na "humm zahra kenan nima ai na dauki mataki
yanzudai ba wannan ba Dan Allah kiyimin tuwo yanzu ko kadanne wallahi haka kawai nake
sha'awarshi.
Ajiye hijab dinta tayi tare da mikewa to shikenan bari inje Amma Dan Allah kidaina
sakarmishi fuska har sai yagane kurenshi nasan lokacinne zai San kinada Rana wajanshi nifa
raina yabaci sosai wallahi.
"""
Duk zaune muke afalon Hajiya kaka yau kwananmu uku agidan sai yau taga damar barinmu
mukoma namu gidan,Fada da sababi gami da mita babu kalar Wanda batayimishiba daga
karshe dai saida taga lallai yashiga taitayinshi Sannan tace kutashi kuje amma duk abinda kaga
tana bukata to ka kira ayimata nan Saura idan ankwana biyu ka dinga barci babu addua kajika
zakaga yanda Zan sauyamaka kamanni.
Sadiq ne ya guntse bakinshi sabida dariya,Yo ai abinne yanzu yaya Hajiya zatayi da daddy
koda akwance yake