Showing 69001 words to 72000 words out of 84412 words
balle wwai zata canzamishi kamanni.
***
Hankalinshi na kaina duk da tukin mota yakeyi,Nikuwa nai lamo cikin kujerar hankalinama ba
kanshi yakeba.
"Jidda ko zamu biya asbt ne akuma dubaki?
.
Manyan idanuna na lumshe "a a karka damu inajin sauki tashin zuciyarne ke damuna.
"Sorry zaki warware insha Allah bari mubi ta cikin gari ko zakiga abinda kikeso Amma Dan
Allah kisaki jikinki kinji?
Nidai kwantar da kaina kawai nayi Dan Sam wani lokacin ko magana banso wlh.
***
Malam kamar yadda naimaka bayani sonakeyi ya aureni kuma idan ya aurenin to in mallakeshi
sai abinda nace ko mahaifiyarshi sainace Sannan yaimata.
"Subhanillahi baiwar Allah meyai zafi haka duk meyakawo wannan zancen amatsayinki na
musulma? To maganar gaskiya ni ba kalar wa innan bokayen bane dake fakewa da malunta
suna aikata fasadi akan kasaba,Kuma kullun adduata anan shine Allah yakareni daga fadawa
wannan halakar!!!Maganar gaskiya lokuta da dama ku Mata kuna aikata kuskure musamman
idan maganar soyayya tashigo ciki, Duk abinda baka da rabo akanshi to tabbas bazai zama
nakaba idankuma ka kwaceshi da tsiya to tabbas saiya kufcemaka danhaka tunfarko gara ka
nemi zabin Allah yabaka mafi alkhairi,Wannan maganar wautace ba k'aramaba amatsayinki na
musulma wadda ta yadda da k'addara me kyau ko akasinta tabbas akwai matsala da damuwa
akan abinda kakeso ka rasashi ko baka sameshiba Amma sai Inga babu wata mafita datawuce
hakuri DA Addua idan Ayau jikai asiri Wanda kika aureshi to kisanifa dole saiya sakeki domin
abun zai iya sakinshi koda yaushe kuma saiyaji babu dadin zama dake,Danhaka garama Kiyi
addua idan da Alkhairi Allah ya daidaitaku inkuma babu Allah ya kawomiki daidaike kuma mafi
alkhairi Dan haka kudaina wannan kuskuren na siyen masifa da kudinku tunkamin lokaci ya
kuremuku.
Kuma har kinada bakin da zakice ashiga tsakaninshi da mahaifiyarshi? Ke kuwa kinsan
wacece mahaifiya? Ke yanzu Idan akaimiki haka zakiji dadi? Kokuma ayima mahaifiyarki haka
zakiji dadi? Yaya zakiji idan kikai dakon cikin yaronki watanni Tara sannan kisha nakuda ki
haifeshi kuma kidasa raino har ya girma yazama mutun lokacinda kike tunanin zakifarajin
dadinshi kawai kuma saiwata mace Asama ta rabaki dashi yaya zakiji? Ina kuma matar zatakai
hakki irin wannan?
Danhaka ki kula duk abinda bazakaso aimakaba to ko cikin zuciyarka kadda kai tunanin
yimawani,Waima Ina maganar manzan Allah (s.a.w) inda yake gayamana cewa imanin
dayanmu baya cika harsai munsoma 'yan uwanmu abinda mukesoma kammu kenan yanzu duk
munada k'arancin imanin kenan ko?
Kuka takeyi sosai jikinta yayi Sanyi lallai tayi kuskure Amma ta tuba kuma bazata kuma
aikata kuskure irin wannan ba.
Godiya taimishi me tarinyawa Sannan tabarshi.
To dama haka rayuwa take ai.
Yanda ka dauketa haka take zuwamaka domin Allah da kanshi yagayama baya dorama wata
rai face sai abinda zata iya, Dan haka idan har kakai kanka mahakala to kaddama kace wai
Allah ne ya jarabeka a a kada ka zargi kowa sai kanka.
[5/24, 4:23 PM] Maman Dije: 62
Bayan kwana biyu.
Jikifa kullun kuma laushi yakeyi kusan adaddafe nakezuwa makaranta sainayi kamar ma kar
inje hakanan nake daurewa gudun matsala Dan gaskiya inason karatuna sosai.
Gashi abinci be ciwuwa ko ruwa nasha saiya dawo shiyasa sai inkicin komai shikuma yaita
naci tokuma danacin saiya dawo, Nan da nan na fige na lalace fuska sai uban hanci da
idanu,Gawani irin fari danayi kirjina ya ciko haka 'kuguna Amma daga basuba babu abinda keda
auki ajikina.
Kuka nakeyi sosai hadda sheshsheka dan ciwon yajemin ko ina Neman mafita kawai
nakeyi Toma wani irin ciwone wannan?
Inajin yaran cirko-cirko akaina amma Sam batasu nakeba nidai fatana insami saukin jikina.
Shigowar motar daddy yasasu nufarshi ko wanne da damuwa fuskarshi.
"Lafiya naganku haka sadiq?
"Daddy aunty ce keta kuka bata da lafiya kuma tunda muka dawo makaranta ko ruwa
batasha ba yau.
Da sassarfa ya nufo dakina danhaka ahalin kukan ya taddani,Allah yasa Sadiq yai hankalin
tsaresu falo,Dankuwa gabadaya arude ya rungumoni jikinshi ya na lallashi.
"Sorry Jidda yi hakuri nasan da wahala Amma daurewa zakiyi inshaAllah zakisami sauki me
kikeso in siyomiki?
Banza nai dashi Ina kukana,saida naga ya gigice da tambaya Sannan na tsagaita da
kukan"Daddy nagaji DA wannan ciwon Dan Allah kakaini asbt agwadani wallahi bantaba ciwo
irin wannan ba ko mutuwa zanyi?
Maidani yayi cikin jikinshi yanajin babu dadi"Daina fadin haka Jidda babu abinda zai sameki
sai Alkhairi babynmune ke wahal dake Amma zai daina kinji?
Kallonshi nayi ido cikin ido kamin ince baby daddy.
Dan shafa sajenshi yayi numfashinya na canzawa"Eh Jidda akwai ciki jikinki kuma duk muna
buk'atarshi Dan haka kiyi hakuri ki haihu Dan Allah.
Ga mamakinshi saiyaga nakuma shigewa jikinshi Ina sauke ajiyar zuciyar kukan
danasha,Sam beyi tunanin hakanba yai tunanin wata sabuwar rigimar ce,Tokuma gani yayi
boyewar bata dawani amfani musamman dayake ganin irin wahalar danakeyi.
Shafar bayana yaitayi cikin wani yanayi danfa dama amatukar takure yake baby yahanashi
rawar gaban hantsi.
Tun Ina tunanin shafar iyaka ta lallashice saigashi ya zarce Dan tuni yafara sakin layi.
Dakyar na kwaci kaina daddy cikin dakina mukefa yaran zasu iya shigowa kuma jikina babu
Dadi!!!
"Yi hakuri Jidda nagaji wallahi amatukar takure nake Dan Allah kiyi hakuri ko kadanne Dan
mitsima ya isheni.
Hannuna yakama zuwa d'akinshi duk da irin tirjewar da nakeyi, Dannasan muna shiga zai
sauke gajiyarshi akaina duk da wannan rashin lafiyar tawa.
Saina tuna wata hira danaji Matan kannen Abbana sunayi.
Wai daga zarar shekarun namiji sunfara mikawa shikenan sai kuzarinshi ya ragu wanima
bazai iya kula da buk'atar matarshiba,Amma abinda nakasa ganewa akan daddy shine duk
lokacin zamu kwanta dashi sainaji jiki anya maganar gaskece kuwa? Kokuwadai Ana magana
ne akan maza wa inda basu kula da kansu? Irin wa inda Rana da zafi ga basir suka cinye,Dan
gaskiya ban tunanin daddy yanada wata matsala.Tokuma kodai danni yarinyace awajanshi
sosai?
Yankewa tunanina yayi lokacinda najini saman gadonshi.
Azabure na mike shikuma yakuma damkeni yanawani marairaicewa"Habamana Jidda wai sai
yaushe za afara yin abinnan cikin dadin raine? Ki tausayaminba kumafa lallabaki nakeyi duk
lokacinda Zan nemeki Amma saikin nuna bakiso kinaso incutune? Tunda ina ganinki kullun
kuma inaso ke halaliyatace idan banzo garekiba Ina kikeso inje,Yanzu yaushe rabona dake
Jidda tunfa agidan Hajiya kumacan dimma so daya kacal nayifa!!!
Cikin shagwaba nace"Toni daddy akwai zafi fa!
"A a jidda wallahi babu zafi saidai wahala da gajiya zakice amma ai yanzu babu zafi tunda
inashiga jikinki Lafiya lau.
Turo bakina gaba nayi alamar dai baniso.
Jawoni cikin jikinshi yayi cikin sigar lallashi "To shikenan yi hakuri inyi d'an mitsi kuma
ahankali idan naimiki mugunta zanbari ki Rama kinji?
Da wayau DA lallashi amatsayinshi na babba ya kwantar dani tare da rufeni da zazzafar
soyayyarshi,Tuni nabada kai bori yahau.
Munaji ana kwankwasa kofar amma tsakanina dashi akarasa Wanda zai motsa balle abude
kofar, Kuma tunda akanace kwankwasawa to abune me muhimmanci.
Muryarshi ashake kamar Wanda aka tada barci ya furta waye?
"Daddy nine baba kamal ne yace inkawomaka wayar"
Shaf ya manta da sunyi zaizo gidan yaduba Jidda idan yadawo aiki.
"Je ka budemishi get Sadiq kace yashigo na manta megadi benan.
" Jidda tashi muje in wankemiki jikinki ga kamal nan zai dubaki.
Yamutse fuska nayi batare Dana kalleshiba danni nagaji.
Wucewa yayi ya gyara jikinshi Sannan yazo yaigaba dani dan ko magana beminba,Saidai
najini cikin ruwa.
Da kanshi yaimin wanka Sannan ya nadoni soyai in shirya da kaina amma ganin ina niyyar
kwanciya yasashi sakin dariya Lallai aiki yasami manyan mata,Allah hadda yunwa ke damunki
Jidda shiyasa jikinki Sam babu karfi, Dago hannun insakamiki rigar nan muje kamal ya dubaki
inma asbt zamukoma sai mukoma din nafiso inji jikinki da kwari.
Saida ya kwantar dani falo Sannan yafice waje Dan kamal din kin shigowa yayi yanajiran
iso tukunna.
***
"Kai mutumin inanan tsaye ina jira nace badai Mara lafiyar ka tausheba inata kiran wayarka
saidai yarona ya dauka"
Hannu ya mikamishi suka cabe kamin ya dora"To sarkin sharri nibabu abinda nayi.
"Karya kakeyi wallahi wannan lemar ruwan na uban maye kace kawai kaine ke kuma kwantar
musu da yarinya.
"Dan Allah kabar fadi muje ka dubata ko jiya saida nasamata ruwa Sam batason cin abinci
[5/24, 4:23 PM] Maman Dije: 63.
Idanuna alumshe suka shigo dakyar na samu natashi zaune tare da gaidashi.
Amsawa yayi asake yanayimin Sannu.
Kallon daddy yayi, Inaga saitasha ruwa da yawafa Dan asami kwarin jikin kuma dole saika
kula da abinda zata iyaci kaga saikaita kokarin samomata yunwace kawai taima jikinta
illa,Kaban mamaki Allah saikace ba likitaba!!
"Bazaka ganeba kamal Allah ina dubata jikinne Sai inga kamar kullun kuma saki yakeyi ma
shiyasa nace bari inyimaka magana.
"Babu komai yanzu kasamo wa innan afara saimuga abinda za ai dagabaya,Yai maganar
yanacigaba da rubutun da yakeyi,Mikamishi takardar yai"Gashi yi sauri Dan Allah hajiyarmu ke
jirana wlh.
""""
Cikin barcin dayafara dibana naji shigar allura sonai in zabura amma naji nakasa Ashe rikeni
yayi sosai tunda yasan bawani son allura nakeba.
Lamo nayi ajikinshi har aka gama samin sannan ya kwantar Dani yatafi rakashi.
Sannu aunty gaskiya babyn nan nabaki wahala wallahi harna farajin haushin babyn,Cewar
Sadiq cikin damuwa.
Dan murmushi nayi tare da shafar cikina Wanda yake alafe kamar ma babu hanji cikinshi
tsabar yanda yake lafe.
"Yaya Sadiq Ina babyn take? Cewar Mimi.
"Auntyce zata haifomana idan tasami sauki kimata addua ta warware kinji!
.
***
"Baban zahra yakamata kafa dagamata k'afa har tasami nutsuwa gaskiya kagadai jikinnata
yanda yake ko?
"Wallahi bawani takurata nakeba,Yauma kasa hakuri nayi dan rabona da ita anfi sati biyu
sabida wannan matsalar da mukasamu sai gidan Hajiya shima dakyar ta yarda to yaukuma naji
nagaji ainayi kokari.
"Eh hakane kam danni ko kwana biyu ban iyawa ko fashin sallah take saitamin 'yan
dubaru,Bari inje samatashi kawai zakaitayi daganan har zuwa dare nasan idan sunshige jikinta
zataji dama dama Allah yabata lafiya ya kawomana wannan baby Lafiya.
Barci nakeso inyi amma sunkacame hirar baby,Saida yashigo Sannan suka fice, Faruq na
fadin yanzu gidan duk babu dadi sabida rashin lafiyarki aunty Dan Allah kiyi ki warke.
Da kallo yabi bayansu yana sakin ajiyar zuciya,Kamin ya raba gefena ya kwanta, Sai tunanin
mahaifiyarsu ya fadomishi arai gaf da zata rasu kusan kullun saisunyi rikici da ita sabida
matsamishi da takeyi akan yakamata yai aure Dan yaran su saba da wata badole sai itakadai
mahaifiyarsuba,Shikuma alokacin abinda kebashi haushi kenan takawo maganar mutuwa Ashe
Ashe lokacintane take hangowa.
"Haba Abban zahra nifa sai Inga kamar ma yanzu ka daina sona shikenan kai daga magana
saika kama fada kumadai ai maganata gaskiyace kowa zai mutu bawai ni kadaiba kuma kasani
danhaka dole ingayamaka gaskiya ni mutuwa zanyi nan kusa inma zaka shirya shirya,Maganar
marigayiyar keyimishi kuwwa adaidai wannan lokacin. Matsawa yayi jikina yanajin yanda zuciyarshi ke tsananta bugawa,Kamar alokacin takemishi
maganar.
Rungumeni yayi jikinshi cikin Sanyin murya ya furta"Kadda ki barni Jidda Dan Allah mu
kasance tare inafatan Allah ya dawwamar damu cikin farinciki nagode da kikasance cikon
farincikina Allah yabani ikon farantamiki yarabaki da abinda ke cikinki lafiya.
Ahankali na Dora hannuna saman fuskarshi"Ameen daddynmu Allah yabarmu tare.
Matseni yayi jikinshi cikin farincikin jin amsar dayasamu,Wani Dan karamin Kara nasaki jin
yanda ya matseni jikinshi,Da sauri ya sassauta rikon da yaimin tare da furta"Sorry, Kina bukatar
wani abune inkawomiki?
Cikin shagwaba na girgizamishi kaina,Idanuna arufe dan barci nakeji.
""**""
"Zee na hakura da Dr.Habib wlh Dan saura kadan infada cikin halakar datafi wacce nakeciki,Ke
wannan malamin fa cewa yayi sainakawo wasu abubuwa na jikin shi Dr.din naga Ina
zansamesu dole na hakura waikuma naje wajan wani wai saiya aljanu sun kwanta dani sau
bakwai kumafa karya sukeyi sune ke kwanciya da mutun saisu fake da wai aljanu haka kawai
inje a sakamin cutar kanjamau Ina zaman zamana.
"Humm ai shiyasa kikaga naja baya wallahi, Ni wa innan karerayinne banso na malaman
tsubbun nan Amma sai kukeganin kamar nacika son kudi, Wallahi duk mayaudarane yanzu
kiduba kiga yanda naso Nasir kamar Zan mutu Amma ya dinga wulakantani yana tozartani
saigashi danai hakuri kuma na tattarashi na watsar bagashiba yanzu shine me bina kamar zai
haukaba,Insha Allah karshen watannan ma zankai maganarshi gida muyi aurenmu lokacin
nagama jamishi rai,Danhaka wallahi tun wuri ki Kama kanki ga mazanan da yawa ciki bazaki
rasa na aureba tundadai yanzu auren kk so.
Dama haka rayuwar duniya take me cike da qalubale Saidai kai fatan tazomaka da sauki.
[5/24, 4:23 PM] Maman Dije: 64
Bayan sati daya.
Shigowarmu kenan daga makaranta wanka kawai mukayi,Nafito Dan Dora girki sukuma
yaran gyaran Gida duk da haka hira mukeyi tsakaninmu duk da cewa kowa da abinda yake.
Naji saukin jikina Sosai tsaknin jiya da yau, shiyasa harnasami sukunin danyin walwala.
Daddy ne ya maidomu gida, Do min yanzu tunda nasami cikinnan shike kaimu kuma shike
maidomu,Amma yau ko shigowa gidan beyiba yana diremu ya koma da alama aiki gareshi.
Tuwon shinkafa naimana miyar ganye wadda ta wadatu da naman sa tuni gidan yagama
budewa da kamshi,Yaushe rabon danayi girki dole na daddy mukeci,Dan ya hana a amso
nawani gidan.
Saida nahada lemon kwakwa Wanda yake mahadin tuwon Sannan nashiga wanka lokacin har
anfara kiran sallar magriba.
Wanka mekyau nayi sabida inji dadin jikina Dan rabona dako wankan kirki nakwana
biyu,Amma yau jikin da sauki sosai Dan babu inda keyimin ciwo.
Saida nai Sallar magriba sannan nakoma gefen gado na zauna ina shafa,Shafarma kanta
yau ta dabance,Kai inama haka zanta samun sauki kullun aidanaji dadi.
Tare dasu Sadiq daddy yashigo sabida sunfita sallar isha'i.
Sannu da zuwa naimishi kamin nacigaba da jera abincin,Wani irin kallon sha'awa yabini
dashi,Dan yaushe rabon da ya ganni cikin Lafiya haka,Ga wani irin kyau da jikina yayi,Danshi
aganinma saiyaga kamar yanzu nafara girma.
Inata magana ganin bejiba yai nisa cikin tunani,Yasani dan zungurinshi kadan.
Lumshe idanunshi yayi kamin ya budesu akaina.
"Cewa nai ga ruwan wankan can"
"Ok to Jidda bari nadankuma hutawa kadan nagaji da yawa ne yau gakuma yunwa
inaji,Rabona da wani Abu tun tea din safe.
"Subhanillahi to ko abincin zanfara kawomaka?
Riko hannuna yayi ya zaunar dani gefenshi Saiwani mayen kallo yakebina dashi"Share
kawai jiddana zanfara hutawa tukunna daganan sai kimin wanka Saikuma inhuta saimuci
abincin inafatan hakan yayi ko?
Kauda kaina nayi inadan murmushi ganin yanda yai maganar k'asa-k'asa duk da cewa
yaran kallo sukeyi Amma haka yake yana matukar yin takatsantsan wajan ganin basuga wani
Abu na ashsha daga gareshiba.
"Kinyi kyau jiddana yaushe rabon danaganki cikin walwala haka? Inafatan zaki bani
hakkina yau ko?
Dan ja baya nai kadan kamin ince"Kai daddy Dan Allah daga samun saukina? Inkuma
kakuma jawo ciwon fa?