Showing 63001 words to 66000 words out of 84412 words

Chapter 22 - YARDA Book Complete by Maman khady.pdf

Advertisement

12 Jul 2025

2674

Wata dariyar nishadi yasaki kamin ya gyaramin kwanciyata"To shikenan yi hakuri nafasa kinji
ko? Laifinkine Jidda har yanzu kinkasa sakin jikinki dani munfa riga munzama daya babu komai
tsakaninmu yanzu sai YARDA da Aminci bazan cutar dakeba zanyi iyabakin kokarina wajan
farantamiki insha Allah danhaka ki saki jikinki dani kinji? Ko wannan zafi-zafin da kikeji nasan
tsoron da kikasama kankine Amma inda zakidaina jin tsorona tabbas zakidaina jin zafi saidai
dadi ai kinaso ko?

Boye fuskata nai cikin jikinshi ina dariya,Kai daddy ko!!!


Da kanshi yaimin wanka kuma ya shiryani bunu-bunu yaimin sannu saikace wadda tasha
aiki.
"Yanzu ki saka wannan doguwar rigar saimufita ko zakiga abinda kikeso ko?

Da murna na mike dan sosai naji dadin jin cewar zamufita.

Muna tsakiyar falo hannuna cikin nashi mukaji kwankwasa kofar falo.
Sakin hannunayayi tare da cewa jirani nan inzo.

Kallo daya yaimata yaji wani irin mummunar faduwar gaba ta sameshi.
[5/9, 9:07 PM] Maman Dije: 55




Wani irin masifaffen dadi taji musamman data lura da yanda yasha jinin jikinshi.
Hannunta ta mikamishi tare da furta khairat Usman by name"

Dakyar yasamu ya daure be bata hannunba dan wani irin kwarjini yaga taimishi,Murmushi ya
sakarmata,Batare da yayi maganaba.

Ganin bazai bata hanya ta wucebane yasata furta"Dama inason yin magana dakaine idan
babu damuwa"

Samun kanshi yayi dabinta kamar yadda ta buk'ata bayan yajawo kofar falon.


""""


"Nasan zuwa yanzu ka manta dani,To kamar yadda nagayamaka sunana khairat Usman
muntaba yin aiki dakai shekaru biyu DA rabi dasuka wuce cikin asbtnku,So tun lokacin nakamu
da kaunarka kuma nai kokarin nunamaka awancan lokacin saidai Sam baka aminceba,To gani
nazo akaro na biyu inafatan zaka amince min awannan lokacin?

Wani irin miyau ya hadiye Wanda besan kona meneba Amma saiya nuna babu komai
azahiri,Domin wani murmushi yasakima,Tare da furta" Karki wani damu insha Allah babu
matsala,Saidai inada iyalifa ba kamar Sanin da Kikaimin bayaba.


"Babu komai karkawani damu ai nasan komai akanka dan Wannan matar takaba ai bata
wuce rainoba itaba Dan haka zanhada nakula dasu duka kamin tazama mace.

Murmushi yasaki,To shikenan nagode muje in ajeki sai inga gida kilama zuwa dare ki ganni
inafatan babu matsala ko?

"Laaa babu komai wallahi muje,Nida nakeson hakan!!




****

Gajiya da tsayuwar jiranshi nayi nakoma na zauna tunanin inda yashige nakeyi daga Bari
inzo.

Wani takaici ya danne zuciyata ganin har anyi magriba gida nikadai saikace mayya.
Sai kusan sallar isha'i Saiga ya usi ya maidosu su Sadiq,Sannan nadan sami sukuni Amma
duk DA haka hankalina bekwantaba dan tunanin inda daddy yashige yananan like cikin raina.

Tun Muna hira har Mimi tafara tambayar Ina daddy,Sannan suma sauran,Daurewa kawai
nayi na furta yaje yadawo.

Bashine yashigo gidanba saiwajan Tara dawani Abu nadare.

Duk yanda naso muhada ido dashi Sam kiyai dan sosai ta bangarenshi yakejin Sam babu
dadi Sannan kamar be kyautaba abundayayi.

Koda yashiga yin wanka be fitoba saidai yai zamanshi,Shiyasama yau hirar batai armashiba
tuni yaran sukai min sallama sukai kwanciyarsu,Nima ganin zaman ba alheribane gareni yasani
wucewa dakina nai kwanciyata Dan tuni zuciyata tagama hasala da abinda dadyn yayi yau.


Bak'aramin tsoro da mamaki nayiba lokacinda asuba tayi na tabbatar cikin dakina nakwana
domin nasan duk wuya bekwana shikadai yanzu KO nayi barci saiya daukeni ya maidani
d'akinshi Amma yau jiya beyi hakanba Anya lafiya kuwa?



****


Bayan sati daya;.Abu kamar wasa saigashi yazama gaske,Cikin kwanakinnan munshiga tashin
hankali musamman nida Sadiq domin shine babba kuma me wayau shine yasan meyake
faruwa cikin gidan yanzu.Sam daddy beda ookacinmu yanzu besan zama gida idanma
munsamu ya zauna to yana cikin d'akin shi yana waya abinda yaimatukar tasarmin DA hankali
lokacinda na fahimci eh dafa mace yake waya, ko makwanci yanzu mundaina hadawa,Sabida
be nemeniba nikuma banje gareshiba.
Tuni nafara figewa ga wani shegen zazzabin dare dayatasoni ga damuwa gashi yau Saura

kwana hudu mukoma makaranta,Tunanina anan wazan gayamawa wannan damuwar?


"Aunty wai kinaganin haka zamu zubama daddy ido?

"Uhumm To Sadiq ya zamuyi mishi tunda ba yarobane balle muce zamununamishi hanyar
data dace nikam gaskiya abunnashi yafara bani tsoro kana kallo yanzu ko gidannan beshigowa
saimunyi barci to yazamuyi mishi?


"To aunty ki kira yaya zahra saiki gayamata sannan agayama hajiya kaka kinga baki da
lafiya,Wallahi bakiga yanda kika komaba kumafa shekaranjiya da aka aiko kiranshi wallahi ina
lekawa wata mace nagani yanafita sukashige mota.

Shawarar Sadiq nabi nakira zahra saikuma akai sa'a tace taje wankin kai Amma gatanan
zuwa.
Shiru nida Sadiq kowa da tunanin dayakeyi,Yayinda faruk DA Mimi keta wasansu cikin falon.




""**""

Innalillahi munbani aunty yaushe daddy yakoma haka? Wane irin abun kunya yakenema
yajamana yanzu kuma?

Tsaki yasaki kamin yace kemadai kinfadi wallahi Saima kinga shegiyar matar dake zuwa
wajanshi haushi zai kasheki,Ga aunty bata da lafiya Amma babu ruwanshi,Cewar Sadiq yana
huci.


Matsowa tayi kusa dani,Dan girman Allah aunty kiyi hakuri nasan duk nice najamiki wannan
damuwar Amma inshaAllah komai zai wuce bantaba tunanin daddy zaiyi hakaba kai anyama
kanshi daya kuwa?Bama wannan mezaijamishi kula wata mace yanzu alhalin yana zaune
dake? Dan Allah kiyi hakuri kutashi muje gidan hajiya kaka Dan gaskiya abun yayi yawa,Kai
Sadiq jekacema isiya ya fiddo mota zamu fita.




***

Subhanillahi kai kutsaya bansan shirme duk yaushe hakan tafaru baku gayaminba?

"Hajiya kaka nimafa yau naji labarinnan wallahi.



"Tab to wallahi bazata sabuba ni kaina naga sauyi akan habibu Amma dana tambayeshi
saiyacemin ai sabida yanayin aikine To Amma akwai matsala dan wallahi ni binta ban haifarma
wata diya mace Dan dazata juyaba Allah kagani banshiga tsakanin surukata DA dantaba
sannan bantaba sama matan yarana idoba, To aikuwa babu tsinanniyar da zata juyamin kan
yaro.

Duk idanu muka zubamata musamman damukaga harwani huci takeyi kamin wani lokaci
tatashi hankalin yaranta da waya akan azo atahomata da habibu duk inda yake.

"Kiyi hakuri jidda kuma ki kwantar da hankalinki mijinki ya hadu da Shu'umar mace
Amma ki kwantar da hankalinki komai zai warware da iznin Allah,Kuma irin wannan ma Jidda ai
da wuri ake fadin irin wannan matsalar Dan Allah kadda kikumayin Shiru kalli yanda kikarame
kik karefa?

56




Nidai tunda hajiya kaka tagama sababinta saina wuce dakinta na haye gadonta danfa sosai
nakejin jikina ya canzamin gakuma cinkushewar zuciya data addabeni da zafi itama.

Wasu hawaye masu dumi naji sun sakkomin tunanin irin halin danashiga Ashe dama haka
mutun yake fuskantar qalubale kala kala Idan yai aure? Dama wannan dalilin kesawa duk
wanda zaimaka fada saidai yace kai hakuri,Kai hakuri,Kowadai kai hakuri?
Tunanin ya usi ya fadomin danhaka da sauri na lalubi wayata na dannamishi kira.

Bawan Allah kamar dama jiran kiran yakeyi Dan da sauri naji ya d'auki wayar"K'anwata kin
yini Lafiya ko?

Kuka nasakamishi hadda sheshsheka.

Innalillahi,Meyafaru menene na kuka kuma jikinne ya dameki?

"Yayana kazo ka d'aukeni ka maidani gida bansan daddy yanzu bazan iya zama dashiba
kaji?

Tashi zaune yayi daga kwanciyar da yake tuni hankalinshi yakuma tashi,Dama babu dadewa
ya kira wayar zahra yaji muryarta da alamun tasha kuka"Kinga Saurara muyi magana Jidda
kina gidanwa yanzu?

"Ina gidan hajiya kaka nidasu zahra.

"Ok to jirani inzo yanzu Amma kidaina wannan kukan kinga baki da lafiya kadda damuwa taimiki
illa yanzu zanzo saiki gayamin komai kinji ko?



Banwani jimaba saiga wayarshi,Wai yana harabar gidan hajiyar.

Hijab dina nasagala na fice duk da su hajiyar na falo Dan haryanzu bata daina fadaba
tahana kanta sakat.


Tuni zuciyata takuma karyewa musamman danaga yayannawa cikin damuwa,Dannikaina
shaidace akan irin son da yakemin be hada soyayyata data kowaba.

Shigewa nayi jikinshi inawani kukame matukar ban tausayi.

Rungumeni yayi jikinshi yanajin wani irin danasanin auran da akaimin tun yanzu,Dan
yasandai matsalar bazata wuce akan auranba.

Saida ya lallasheni Sannan nagayamishi dukkan abinda ke faruwa,Hankalinshi yatashi
amma tunani nafarko dayazomishi shine anya dadyn qalau yake kuwa?

"Jidda kodai kinyimishi wani babban laifine yake hukuntaki ta hakan?

Ya usi banyimishi komaiba har yaran yanzu babu ruwanshi dasu,Wannan macen ce
kebiyoshi har gida ta janyeshi.


Munanan zaune ya usi nakuma lallashina saiga yayan daddy dakuma shi kanshi daddy din
da alama tasoshi yayi.


Wani irin mummunan tashin hankali yaji lokacinda ya hangeni jikin wani rungume,Tsabar
kishi,Saida yamatso sannan yagane ya Usman ne Amma duk da haka zuciyarshi bata
sassautamishiba musamman dayaga yandanakekuma likewa jikinshi.

Ya Usman na kokarin gaidashi,Shikuma ya na kokarin rikoni,Aiko na makemishi hannu tare
da harararshi danwani irin mugun haushinya nakeji.

Janyeshi Alhajin yayi suka wuce yanamai fadan"Damme zakace zaka janyeta ita da
yayanta,Tunda kai kasata bakinciki aidole shi dan uwanta yasata farinciki kuma ya lallasheta
tunda yanasonta.

Bakinshi ya tsuke kamin yace"Kuma kawai danyana yayanta saiyakamata ya wani
kwakube,Kuma ainima iinason abata ko!!



"Kinga wuce gida nasan hajiya kaka zata dauki mataki akanshi kome akeciki saiki
gayamin Amma kidaina kuka,Zandawo anjima daukar zahra saimuyi magana kinji ko?

Kaina nadagamishi tare da barin jikinshi na nufi falon hajiyar.




***

Mugun kallon data wurgamishi yasa yaji har hanjinshi saida suka motsa,Danhaka da sauri ya
sadda kanshi k'asa yana zullumin abinda ka biyo baya.

Saida tagama karemishi kallo kamin tace" Ah lallai jin dadin duniya wato kai habibu wulakantani
kakeso kayi a idon duniya ko?
To wallahi bakaji da kyauba danninan DA kakeji da gani nafi karfin wannan,Kai bama
wannanba wace shegiyace kake bibiya yanzu dahar tasa kake wulakanta iyalinka iyi?


Kanshi akasa yake tauna maganar da zaifadi danyasan bawai jin dadibane zai biyo baya ba
tsakaninshi da hajiyar," Uhum hajiya dama watace nake nema kuma auranta zanyi!!!!


Wani irin jirine naji yana neman kayar dani dan sosai maganar tai matukar bugarmin zuciya.

Baki bude hajiyar da Alhajin ke kallonshi jin yanda maganar tazomusu amatukar bazata.

Kamar kazar da kwai ya fashemawa aciki haka na idasa shiga falon harwani ganin biyu biyu
nakeyi bantaba tunanin haka nakeson daddyba sai yau.

Duk maido hankalinsu kaina sukayi amma bankalli kowaba cikinsu na wuce, Dan sonake in

dauko wayata da jakata inwuce gidanmu nagama zama da daddy koda sonshi zai kasheni
kuwa.


Kayana ahannu nafito saiwani ganin uku hudu nakeyi,Kallo daya sukaimin duk suka mike
tsaye sauri nakesonyi dan infice batare dawani yaimin maganaba,Saidai kashh wani jirine ya
watsar dani batare danayi tunanin hakanba.



[5/9, 10:12 PM] Maman Dije: 57




Wani irin tsalle yayi saigashi gabana,Saidai hakan besa yasamu damar tabaniba kamar yadda
yai niyya Dan tuni hajiyakaka taimishi wata ingiza saida ya hantsala Dan beyi zaton samun
hakan daga garetaba.

Ruwa suka fara shafamin afuska saida nafara numfashi sannan takamani zuwa tsakiyar
falon.

Kwanciya nayi tare da rufe idanuna Dan wani irin barci naji yana lullube idanuna.

Tsayuwar yagaji da ita Dan haka ya lallaba yakoma gefe ya Zauna Amma hankalinshi nakan
kirjina yana kallon yanda numfashina ke hawa da sauka,Tausayina ya mamaye zuciyarshi
musamman dayaga fuskata takuma komawa k'arama saidai akwai wani sihirtaccen kyau
danakara ga cika da kirjina yayi,Yasan albarkacin tayin dake maratane. Samun kanshi yayi dason jin dumina Amma yasan hakan bame yiwuwa bane,Sannan shi
kanshi sai yanzu yakejin haushin kanshi da abinda ya aikata Sam zuciyarshi bata
kyautamishiba.


"Wallahi habibu kafita cikin idanuna in rufe,Karka yadda musaka kafar wando daya dakai
indai kanason zaman lafiya,Kodayake wannan ba abin damuwabane dannasan bawai cikin
hayyacinka kakeba Amma duk da haka ubanwaye yaja?Gakuma kullun aikina kenan akan
tunamuku riko da Addua musamman na tsarinjiki wa inda Annabinmu yabamu sabida irin wa
innan masifun Amma bakuyi sabida kuga 'yan karshen zamani wai addua wannan tagagari
bawa sabida Allah? Sai masifa ta afku aita tsalle-tsalle alhalin sakacin duk namune!!! Adduar
fita gida ta gagari mutun? Inzaka kwanta shima ta gagara adduar maraice da safiya duk mutun
yagaza yinsu Saiku dinga rayuwa haka kawai Kara zube,Ni shikenan bazakubar zuciyata ta
hutaba habibu? Alhaji yatafi yabarni cikin duniyarnan me cike da rudani da tashin hakali.

Duk matsowa sukai gareta ganin tana kuka abinda basu saba ganiba,Sannan karshen
musifa shine kasanya iyayenka zubarda hawaye matukar bana farinciki bane.

Hakuri sukaita bata har saida tafara sauke ajiyar zuciya Sannan Alhaji Yusuf din yace zaije
yadawo.

Shima daddyn mikewa yayi da niyyar ficewa.
Saidai tuni ta katsamishi tsawa"Zonan zauna Dan ubanka gidan uwarwa zakaje kamike
tsalau tsalau dakai kamar zakara yasha ruwa,Wallahi ka kiyayeni,Bama wannanba kaga habibu
ina tausayamaka idan wani Abu yasami yarinyar mutane wallahi babu ruwana,Kuma ka zauna
nan babu gidan ubanda zaka kuma zuwa sainagama daukar mataki daganan inga Mara kunyar
da zatazo harnan tajaka, Kuma ka zauna karka dage da addua tunda kaima kazama talasuru.

Dolenshi yakoma ya zauna yana zare idanu,Dan hajiya kaka badai masifaba ga bakar mita
saita yini maganar Abu misamman idan yabatamata rai.



***


"Kindaisan bancika son kukaba zahra so kikeyi kita tadamin hankaline da wanne kikeso inji?
Jidda na cikin damuwa har yanzu zuciyata bata daina zafiba sabida yanda naganta kekuma
yanzu kinzo kin tasani da kuka na tambayeki kinki magana kasheni zakuyi ne?

Kuma lafewa jikinshi tayi tana sauke ajiyar zuciya tunanin ta inda zatafaramishi bayani
takeyi, Itadai daddy be kyauta mataba wallahi.

"Kayi hakuri daddyne duk ya jagula komai bansan zaiyima Jidda hakaba gashi bata DA lafiya
Amma hajiya kaka zata dauki mataki.

"Karki damu kanki zahra,Tsakanin mata da miji sai Allah babu me iya shiga tsakaninsu kina
nan kina kuka kilama sun daidaita kansu babu gidan auren da babu sabani cikinshi danhaka
kima daina damuwa,Daddy nason Jidda haka itama tanasonshi kosun sami matsala zasu
daidaita kansu tunda shidin ba yarobane balle ya biyemata,Damuwar da kika ganni cikima
tunanin ramar danaga tayi nakeyi ga laulayi bazanso hajiya ta ganta ahakaba.

Kwanciya tayi jikinshi kawai ta gamsu da maganarshi Amma har lokacin tanajin zafin
daddyn cikin zuciyarta.

"""
Yauwa sannu Jidda tashi ki Salla saikici wani Abu kila kinji dama dama saikisha magani Allah
yabaki Lafiya yarabaki da abinda ke damunki lafiya.


Tashi nai zaune Sai idanuna suka sauka akan daddy dake zaune akan sallaya da alama
sallar ma batabari yafita yayitaba,Harara na wurgamishi hadda murguda baki, Saidai yai
murmushi kawai yacigaba da tasbihin da yakeyi.
[5/9, 10:12 PM] Maman Dije: 58




Yauwa ga wannan kisamu kisama cikinci ko Allah yasa adace ya zauna Amma kidaina damuwa
dan Allah, Cewar hajiya kaka wadda ke lallashina bayan nagama salla.

Juyawa tai ta wurgamishi harara ganin yanda yake kallonmu.


Yana cikin samuwa Amma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login