Showing 6001 words to 9000 words out of 84412 words
kamin ya
kalleta"Sorry kije gida zakuyi waya anjima.
Tana nan tsaye har saida muka bulle Dan Ina hangen lokacinda hajiya kaka tafito tashiga da
ita gida.
Ajiyar zuciya na sauke me karfi tare da lumshe idanuna,Allah yasani inason zahra sabida
inajinta cikin jikina sosai da sosai na YARDA da ita tokuma damme zatace inwani auri
dadynta,Duk da ba tsoho bane amma ai yaimin girma,Kumama nasan hajiya bazataimin aure
yanzuba. Lamo nai cikin motar idanuna arufe tuni tunani yagama dabaibayemin zuciya,Shidai ya usi
tukinshi kawai yakeyi amma na Lura hankalinshi na kaina.
***** *****
Lamo yayi Saman makeken gadonshi tsabar tunani sai mutun ya zata barci yakeyi Amma
Ina,Damuwace kawai ta saukarmishi da wata muguwar kasala da ciwon kai.
Wayarshi dage ring ya jawo idanunshi arufe ya Kara wayar akunnenshi,"Shigo ciki kawai
sulaiman Ina ciki,Abinda yace kenan ya ajiye wayar.
"Kai man yana ganka kwance nan jikin ko garin? Abokin ya idasa maganarshi tare da zama
gefen gadon.
"Uhumm kaidai bari kawai sulaiman zahra ke Neman samin hawan jini wallahi.
Idanunshi waje yake kallonshi"Kamin yace banganeba kamar yaya?
"Ta matsa sainayi aure sulaiman data isheni sainai tunanin inyimata dibara kawai,Sainace
nabata zabi ta zabomin wadda ta YARDA da ita,Wai kawai saigata da maganar wata yarinya
kuma wai abin haushi hajiya tahau kan maganar ta zauna.
"Hummm harkabani tsoro wallahi to inaga wannan aiba abun damuwa bane Habib kana cikin
buk'atar aure koba komai kaima zaka sauke abinda ke damunka sannan kaga akwai shakuwa
tsakaninsu insha Allah bazasusha wahalar zama da itaba,Akan na nemo wadda zata
tagayyarasu inace kaima abinda kakejima tsoro kenan KO?
"Baka ganeba sulaima yarinyarnan fa muguwar kwailace sa'an ita zahra dincefa sabida Allah
idan ba shiriritaba mezan gani cikinsu babu me hankalin kirki,Sannan wannan yarinyar KO rabin
larurata bazata iya daukaba balle Dan yarinyace sosai.
"Kajika da wata magana Dan Allah kaidai kawai ka kwantar da ha kalinka kayi addua amma
wannan duk bawata damuwabace indai takai zahra zata iya daukarka tunda Ina tuna zatakai irin
15-16 haka kuma kaga kamin Ku sabama takuma wayau,Sannan kadda ka manta auran
k'aramar yarinya wallahi shine kwanciyar hankalinka domin babu yanda za ayi ka dauko mace
me budadden ido me shekaru kace wai zata kulamaka da yara,Kaima kasani KO?
Kasa motsin kirki yayi saidai yabi abokin da idanunshi gabadaya kanshi ya kulle,Tsabar
tunanin ko rakiya besami sukunin yima abokin nashiba danshi sauri yakeyi zai dauko matarshi
daga gidan kunshi.
*** **** ***
"Ki kwantar da hankalinki zahra insha Allah zata amince aikinga tanada tausayi nasan zata
amince abunne yanzu zatajishi Asama,Yanzu saimu dage da addua muzubama sarautar Allah
ido, Danshima wannan rigimammen uban naku sai anyi da gaske indai anaso yayi yanda
akeso,Gobe idan Allah ya kaimu saimuje gidan nasu,Da kaina zanyima ita hajiyar bayani nasan
zata fahimta kinji ko?bansan wannan kukan naki kalli yanda duk kikasa kannenki cikin
damuwa!!!Cewar hajiya kaka datagama lallashin zahra
YARDA.
Na maman Khadija.
8
Wani irin sukuku haka na idasa yammacina yayinda hajiya tai tambayar duniyar nan amma nai
biris da ita dole ta zubamin ido tanajiran ingama kuncin sannan Ingayamata abinda ya faru.
Abangaren ya usi shima duk saiyaji babu dadi musamman dayana tsaye awaje lokacin da
dady yafita kuma da alama afusace yake shima,Fatan alkhairi kawai yabimu dashi kamin yace
idan tayi wari ai dole muji.
Washe gari haka na shirya na nufi makaranta tuni na washe saikace banice na kwanta da
mugun kunciba,To gaskiya dama ni haka nake yanzu zaka batamin arai amma kamin wani
lokaci na huce,Allah beyoni da rikoba.
Kasancewar narigasu zahra zuwa sainaji duk babu dadi sabida bafa k'aramin sabone
tsakaninmuba.
Sai lokacinda zamu shiga aji sannan suka iso shaf na manta da wata magana datashiga
tskaninmu jiya danhaka da sauri na nufesu Ina murmushi.
Manyan idanunshi ya bude gaba daya ya zubaminsu wani irin kallone yake bina dashi daga
sama har k'asa tunanin abinda zai diba yakeyi cikin jikina kawai yakeyi yayinda yakemin
wannan kallon,Ajiyar zuciya ya sauke jin Mimi ta sakarmishi Sumba ta sallama.
Zahra ya kalla amma tuni ita ta isa wajena,Matsowa nayi jikin motar Ina riko hannun Mimi
daketa mikomin hannunta in sakkota daga motar,Nace dady Ina kwana?
Yatsanshi yasa ya shafi girarshi kamin yace Lafiya lau ya hajiya?
Tare mukashige aji,Saidai jikina yai sanyi ganin yanda zahra bata da walwala sosai,KO
magana dakyar takeyinta.
Bayan anyimana break ne na tsareta da tambayar meyafaru ko bata da Lafiya ne?
"Amma kin rainani jidda ingayamiki matsalata da damuwata kinada halin temakamin kiyi
biris Dani shine yanzu har kinada damar tambayata KO banda Lafiya?Wallahi kinbani mamaki
bantaba tunanin zakimin hakaba, Nai tunanin Acikin YARDAR da mukaima juna nidake babu
wani Abu dazan nema gareki ki kasamin shi sai wannnan Wanda ni aganina bawani abun
damuwabane kumafa nima Zan ramamiki tunda ya Usman na sona sai kawai in aureshi kinga
dai muna tare KO?
"Dan murmushi nayi kamin ince eh fa hakane to na amince Amma zahra kina ganin dady
bemin girmaba?
Dariyar farinciki ta saki kamin ta riko hannuwana,"Dallah bemiki girmaba ainasan rainonki
zaiyi bawai maganar wani abuba,Nidai fatana ace dadyna yanada aure,Sannan yasami
nutsuwar da ake buk'ata kinga nima da mun idasa makaranta kamin muwuce gaba sai kawai
Adauramana aure daya usi ko?
Murmushi kawai nayi dan wani irin sanyi naji jikina yayi.
***
*****
Saida kowa ya natsa sannan alhaji musa yai bayani kamar yadda masu buk'atar neman aure
kanyi.
Hannuwan hajiya akirji take binsu da kallo kamin tace"Ku dakata dan Allah wai wace jiddan
ce ta turoku inace dai makuwa kukayi bawai jidda tawaba?
Alhaji shehu k'anin mahaifinsu dadyne ya muskuta tare da gyara zama kamin yace" Hajiya
jidda taki dai muke nufi domin babu yanda za ayi muzo alhalin bamusamu kwarin guiwaba.
"Baba aminu Wanda tsoron Allah yasashi tagumin dole,Sai bin mutanen falon da kallo
kawai yakeyi shine ya kalli, Ya Usman kai jeka makarantarsu jidda ka daukomin ita, kutaho
yanzu dan Allah kaga anbar mutane zaune.
Cigaba da tattaunawa sukayi Akan maganar cike da mamaki bayan barinshi falon
musamman hajiya wadda tsoro yagama kamata,Ganin yanda masu Neman auren suka jajirce.
Bak'aramar faduwar gaba najiba lokacinda malamin mu ke kirana saikuma danafito naga ya
usi,Zahra ce ta rikemin hannu idanunta cike da kwallah"Kimin alk'awarin bazaki canza daga
maganar da mukayiba jidda!
"Karki damu zahra nariga na amince bazaki sami matsalaba tunda kema zaki auri Yayana
danhaka ki kwantar da hankalinki.
Murmushi tasaki kamin face saikin dawo amma dan Allah kadda kik'i dawowa.
Hannun ya usi na rike bayan munshiga cikin motar,Kasa hakuri yayi har saida yaimin
magana,"jidda meke faruwane tsakaninki da zahra nifa nakasa fahimtar komai!!!
"ALLAH babu komai Yayana,Menene hajiya ke nemana?
"Watsa hannuwanshi yayi kamin yace nima bansaniba kila unguwa zakuje.
Jikin hajiya na rabe lokacinda naga idanun kowa akaina dakyar nasamu na iya gaidasu Sabida
zullumi.
"Hajiya kijeda ita ki tambayeta,Cewar baba yusuf shima yayan mahaifinane.
Hannuna ta rik'a tai ciki dani yayinda falon yaiwani shiru na musamman,Kowa da abinda
yake kissimawa cikin ranshi.
""Ke jidda dan gidanku gayamin su waye wa incan?
Turo bakina gaba nayi Zan sakamata kuka dan nima bansansuba"Kai hajiya ba yanzu na
gansuba zaki tambayeni nima bansansuba to.
Rikeni tai cikin lallashi tace" Jidda kadda muyi haka dake ki gayamin meke faruwa wa incan
zuwa sukai Neman aurenki fa.
Kauda kaina nayi daga kallonta kamin ince eh dadyn zahra Zan aura sabida itama zata auri ya
usi kawai ki amince Zan dinga zuwa nan gidanki kokuma kikoma gidansu zahra din kema.
"Tirk'ashi lallai kuruci dangin hauka, Ke ubanwaye yabaki wannan shawarar lallai na yadda
baki da hankali to badaniba wallahi danhaka Bari naje naci uwarsu tukunna tunda suma naga
alamar Neman saitin kwakwalwa suke nema.
Fuuuu tatashi tabar falon batare data kuma kallonaba Niko ai KO ajikina dan bani da damuwa
akan masifarta dannasan Ina matsawa na nace dole itama ta amince.
YARDA.
Na maman khadija.
9
Wani birki taja tana sauke numfashi dan hajiya akwaita da zafi wani lokacin musamman idan
taboni akayi.
"Kunga kadda muyi haka daku dukanmu nan munsan cewa Jidda bata da hankali balle
wayau danhaka kutashi kutafi bakinku alekum Dan nidai banga haukan da zaisani amincewa
inbada auran Jidda ayanzu ba,Danhaka kuyi hakuri ya nemi wata Dan Allah.
Malam Nura Wanda duk yafisu tsufa shine yafara magana cikin kwantar da Kai musamman
daya Lura itafa hajiyar atsaye take"Kinga zauna hajiya ai maganar duk me saukice insha Allah
babu wata matsala Dan alkhairine ya kawomu,Yarinya dai ta amince domin itacema ta bashi
iznin turowa ga iyayenta sannan bafa tauyeta zaiyiba zatacigaba da karatunta har zuwa
lokacinda zatace tagaji Dan kanta sannan shima bazai matsamata da amsarshi amatsayin
mijiba zai jira har zuwa lokacinda zatakuma girma shidai fatanshi damu baki daya Ku amince
ayi hidimar nan kodan YARDAr dake tsakanin yarannan domin dama YARDAr ce ta kasance
sila.
Kasa magana tayi ayanzu sabida takaicin sunki fahimtar ta danhaka saitai shiru saidai
tabisu da kallo.
Baba Ibrahim Wanda shine babba cikin yaran hajiyar shine yafara magana cikin
nutsuwa"Munji buk'atarku amma munaso kubamu lokaci muyi shawara sannan saimu tuntubeku
insha Allah ba matsala.
Nan sukaita godiya kamin suyi sallama subar gidan cike da fatan nasara akan hidimar.
Wani irin shiru falon ya dauka bayan dawowarsu daga rakiyar bakin.
"Uhumm hajiya kinyi shiru bakice komaiba,Cewar Alhaji Yusuf k'anin mahaifina.
"Uhumm toni yanzu mezancemuku wallahi abun ya dauremin Kai,itafa da gaske takeyi auren
takeso,Kumama sabida Allah duka jiddan nawa take? Da zata fadama wannan babban kusan
sa'an babanta iye?
Danhaka kai Usman kiratanan tazo kila idan taga idanun iyayenta maza ta janye.
Makurewa nayi cikin kujera Ina zare ido musamman danaga gabadayansu ni suke kallo
balle ya usi harwani kalar tausayi yakoma damuka hada ido.
Baba Ibrahim ne ya yafitoni da hannunshi tare da cewa "Zonan me sunan manya dawo kusa
dani in tambayeki kinji KO?
Matsowa nayi jikinshi batare Dana kalli idanunshiba sabida tsoron ko fada
zaimin,Hannuwana ya Kama ya rike sannan yace"Wai kece kika turo wa incan mutanen Neman
auranki?
Hannuna daya rike naketa mutsu-mutsun kwacewa amma ya rikeshi kam,Dole na daga
kaina ahaka,Alamar amsawa.
"Tirkashi,Cewar hajiya tana rike da baki.
Kuma sassauta murya yayi alamun lallashi"Mesunan hajiya auren kikeso yanzu kodai abasu
hakuri saikin kuma girma?
Sabodayi"danhaka bansan lokacinda na turo bakina gaba ba Ina fadin nidai a a baba yanzu
nakeso,Zan zauna dasu zahra zamuje school tare hadda islamiyya kumama ai itama zata auri
ya usi.
Baki hajiya ta bude zatai magana amma Baban ya hanata ta hanyar yimata alama datai
shiru,"To shikenan Kai Usman tashi ka maidata makaranta.
Gaba daya hajiyar suka tausa akan tai hakuri kawai ayi abun,Aiko ranta besoba tuni tafara
durama dady zagi akan zai rabata dani hadda hawayenta tsabar bahaka tasoba,Saidai tana
tunanin kadda taje tahana kuma ni inshiga damuwa.
Danhaka anan suka tsaida magana nan da kwanaki biyu zasu nemi iyayen dady domin suzo
atsaida magana saidai sunyi shawarar za a daura aurene kawai in tare sauran shagulgulan biki
idan Allah yasa nayi candy Lafiya sai ahada gabadaya ayi.
***,,, ***,,,
"Kasan wani Abu habibu Bari inyimaka yanda zaka gane dannaga kana Neman ka maisheni
sakarya,Wallahi wallahi saika auri yarinyar nan kajima na rantse indai kaga ba'ayiba to ka
tabbata iyayentane suka haka danhaka idanma zaka kwantar da hankalinka ayi komai cikin
nutsuwa to inkuma shirme zakaitayi gaban yaranka to wannan damuwarkace ba tawaba
nagayamaka,Fiiiiiiiii tatashi tabar mishi falon bayan tagama zabgamishi harara kamar idanunta
zasu fado k'asa.
Tashi yai yakoma saman kujera ya kwanta tare da lumshe idanunshi,Tariyo dukkan yanayin
Jidda yakeyi,Saidai haryagama tunaninshi be hango wata makusa ajikintaba sai kuruciya da
shagwaba to ahakan Ina zaikai wannan mitsitsiyar yarinyar Dan Allah?
Yana nan kwance besan lokacinda barci yai awon gaba dashiba.
**""""****""""
Ranar laraba,Abu kamar wasa saiga k'aramar magana tazama babba dankuwa iyayen dady
basuyi k'asa aguiwaba aranar labara suka kuma dawowa inda iyayena suka amincemusu akan
sun amince da wannan aure danhaka idan sun shirya ranar juma'a sai adaura aure intare
ammafa akwai shagalin biki idan mungama makaranta. Sunyi farinciki da murna inda tun anan suka zube komai na buk'ata sannan suka wuce,To
dama abune na ansan juna ansan tushen juna balle atsaya wani kalkale kalkale.
Danhaka saimu hangi juma'a insha Allah.
YARDA.
Na maman khadija.
10
Ganin yanda taketa kallona yasani turo bakina gaba Ina harararta,Waike hajiya mene da zaki
tasani kita kallo hadda tagumi KO mutuwa zanyi ne?
"Uhum to wama yasani ko mutuwar zakiyi ammadai nasan indai har kika kuskura wannan
habibu yake da suna ko habibane oho dai matukar ya doramiki nauyinshi nasan saidai wata
amma ba keba.
Batare da wata damuwaba nace yo hajiya shi beda hankaline da zai doramin nauyinshi
inama zai ganni balle ya danneni ai muna tare dasu zahra koda yaushe ko?
"Mitsww taja tsaki kamin tace wawuyar banza Ana rabata da kiwon akuya tana kyalla ta
haihu,To danneki zaiyi ya amshi hakkinshi indai an daura auren.
"Hhhhhha Kai hajiya to meye idan ya amshi hakkin nima ai zai sauke nawa kinga zandingacin
kayan dadi kamar ina wajanki zaikuma dinga biyamin kudin makaranta kinga shikenan kunhuta
damin siye siye.
Tsamm tatashi tabar dakin tana sharar hawaye itafa duk Dan farincikina takeyin komai amma
Sam naki ganewa tasandai kewata kawai saita kusa kasheta yanda tasaba Dani bata Saba da
yaran data haifaba sannan tafi tausayina fiye da kowa da komai saigashi kwatsam Rana guda
wani k'aton gardi zai rabamu,Bari akwana biyu itama cangidan zata koma idan taji takasa
jurewa,Ragwas ta zauna akan kujera cikin falonta Wanda ke cike da 'yan biki wa inda suka
kasance surukanta da 'ya'yanta Mata tunda gobene daurin auren,Dole ayi wasu abubuwan
koda ba dukaba.
Tunanintane ya yanke lokacinda Gwaggo Uwani kecewa"Dan Allah hajiya ki cire wannan
damuwar aranki wallahi kuruciyace kawai ke damunta amma idan ankwanabiyu zata fahimci
abinda ake nufi da aure,Amma yanzu kinagani duk Wanda yaimata magana Neman yimishi
kukama takeyi Dan Allah ki kwantar da hankalinki.
""******""""
"Zahra kinga abinda kikajamin ko?Sabida Allah auran sa'arki!!!Gashinan kinsa hajiya tatashi
hankalina ko?Idan ita Jidda din batasona shikenan kin hadani da wani aikin banda Wanda
nakefama dashi ko?
"Kayi hakuri dady insha Allah zakaji dadin aurannan ni abinda yasa kaga na nace sai ita
Wallahi tanada hankali sosai ga ilimi na addini dana boko tanada tarbiyya gatanda akaimata be
lalatataba dady ita kadaice zata zauna damu tsakani da Allah ka duba su Mimi yanda suketa
murna jin zata dawo gidanmu insha Allah bazakai Dana saniba dady saima godiya da
zakamin,Kuma nasan Jidda zata soka aiba tsufa kayiba inbama Wanda yasaniba ai baza'ace
Kaine ka haifemuba Dan Allah kayi hakuri dady kabamu goyon baya pls dadyí ½í±í ¼í¿».
"Shikenan zahra Allah yaimuku albarka yasa hakan yazama alkhairi garemu baki daya.
"Yeeee yauwa dadynmu mungode Allah yasa haihuwar farko Jidda tabamu twins masu
Kama dakai dady.
Rungumeta yayi yana dariya shima saiyaji zuciyarshi tacika da farinciki musamman
kwanakinnan da yakejinshi sai ahankali,Lallai zahra kin rainani wlh.
"Kije ki duba wancan dakin masu gyaran sungama saikiga idan akwai abinda ake buk'ata
kinsan gobe zasu kawota tokuma