Showing 81001 words to 84000 words out of 84412 words
kamar yaro wallahi.
Hira suka dasa da hajiyar kuma har lokacin yaron na hannunshi,Mimi ma na like jikinshi
tanayima haidar din wasa.
Sai dare sosai Sannan yaimana Sallama zai wuce.
Hajiyace ta kalleni ki rakashi mana jidda.
Adan kunyace nabi bayanta bayan na ajemata haidar din,Be juyo ya kalleniba saida yashiga
cikin mota ya zauna,Sannan ya budemin bangaren ya na kallon cikin idanuna musamman da
hasken nefa ya gauraye harabar gidan.
Dan turo bakina gaba nayi kamin in shiga,Ko kaiga zama banyiba ya rungumeni jikinshi tare
da lalubar bakina, wani irin zazzafan kiss yakemin kamar zai cinyeni kamin wani lokaci ya ruda
kanshi ya rudani tuni jikina yafara kyarma kamar yadda nashi ke tsuma,Muryarshi taiwani irin
laushi ya furta"pls Jidda ko kadanne Dan Allah wallahi nagaji"
"Kayi hakuri daddy insha Allah jibine kawai kaga nan kodawane lokaci ya Usman zai Iya
shigowa tunda bezoyaimana saida safeba,Nasan bazaka Sami nutsuwar DA kake bukataba
kayi hakuri.
Matseni yayi jikinshi ya na sauke numfashi sosai yakejin wata irin masifaffar kewa, Bekuma
tabbatar DA cewa Jiddan na kokari wajan biyan bukatarshiba Sai yanzu data kwana biyu basu
tare duk dare dakyar yake runtsawa.
Anan mukai sallama yawuce nikuma nakoma cikin Gida tausayinshi duk yacika dabaibayeni.
Washegari;Hajiya da kanta ta rakani gidan me kitso da kunshi, Sai wajan azahar muka dawo
abinci kawai mukaci ta hadani da matar baba habu ta rakani zuwa gidan gyaran jiki.
Aranar dai gyare-gyare naitayi haka kayammu tuni an ga ma kintsamana komai.
DA darema hajiya zagewa tai wajan kuma nunamin yanda Zan gyara kaina taitayi da sauran
dubarun zaman aure tunda yanzu nadan kuma hankali ba kamar farkoba.
"""**"""
"Yauwa Sadiq zo ka idasa goge wajannan inje inyo aski indawo"Cewar daddy wa inda
ketafaman gyare gida duk sabida dawowarmu.
Dariya Sadiq din yasaki kamin yace to"Ai daddy kajira mu idasa saimutafi tare muma munaso
muyi askin ai yanda zata gammu fes.
Hararar wasa daddyn ya sakarmishi kamin yace "Wato sabida kaga ka kusa taddoni tsawo
shine kakeneman rainani ko? To karma kafara nikadai zanje Allah.
Yana niyyar fitane Saiga zahra da uban cikinta agaba kafafu duk sun kumbure,Kallon mamaki
daddy yabisu dashi musamman ya usi dake rike da Jakarta Ahannu.
"Kai bansan hauka daga Ina zuwa Ina haka?
Dan sosa kai ya usin yayi kamin yace"Daddy anwuni lafiya?
Harararshi dadyn yayi kamin yace bakaji tambayar danayiba kenan?
"Uhum daddy dama daga gida muke kuma iyakarta nan Sabida zata taryi jiddane kuma dama
asbt ance tadan dinga tattaki shine na rakota anjima sai indawo daukarta.
Haba dadyn yakama kamin yace,Ammadai yakamata kurage yawo kaga DA ga yanzu
zuwa kowane lokaci zata iya haihuwa Dan haka ku kiyaye indai ba so kukeyi ahaihu ahanya
ba,Ficewa yayi bedaina fadaba.
Saida ya temakamata Sannan ta zauna gidan ko Ina tas yashagyra ga kulolin abinci Wanda
hajiyakaka ta aiko dasu sabida tarar baki.
"Sadiq Ina daddy zashine naga kamar sauri yakeyi?
Saida yai dariya Sannan yace ba sauri yakeba wallahi aski zashi tun jiya yake kalkale kalkale
saikace mace inaga duk gyaran tarar aunty ne.
Bugu ya usin yakaimishi duk suna dariya,Saida yahuta Sannan yabar gidan da niyyar insha
Allah zaizo ya maidata gida dawuri basaidare yayiba.
***
Alhamdulillah yaudai gashi nadawo gidan mijina kuma Nagode Allah domin nasami tarba ta
musamman daga matan yayun daddy dakuma Hajiya kaka gakuma aminiya zahra da k'aton
cikintaí ½í¸….
Sai daf DA magriba Sannan akawatse gidan yakoma daga mu Saimu,Dabhaka nabawa Mimi
haidar mukafara gyaran gidan yaudai hadda daddy aikin.
74-5
Komai da walwala da farinciki mukeyinshi Dan gaskiya munyi missing din juna, Saida haidar
yafara kuka Sannan daddy ya karbeshi mukuma mukaci gaba da aikin,Saiwajan goma saura
Sannan muka kintsa ko'ina tuni faruk da Mimi sunyi barci tunda angaji.
Saida na shiryar haidar haryai barci Sannan nima nashiga wanka lokacin daddy yai wani
dai-dai akan gado da alama jirana yakeyi.
Humrata me matukar kamshi nashafa jikina tare da saka rigar barci'yar Mara nauyj tunda
naji garin akwai zafi babu laifi.
Saida nagama kalkalena Sannan na raba gefenshi na kwanta.
Rungumeni yayi cikin jikinshi yana Sauke ajiyar zuciya Dan wata irin nutsuwa yakejin tana
sakkowa cikin jikinshi.
Cikin wata sassanyar murya ya furta"Nai kewarki sosai Jidda'Ina matukar bukatar kasancewa
dake saidai naga kingaji dayawa yau.
Kuma shigewa nai jikinshi inajin yanda tausayinshi kekuma dannemin zuciya"Karka damu
daddynmu Zan iya ai dannima nai kewarka irin sosai dinnan.
Dan murmushi yasaki kamin yafara gwadamin zazzafar kaunarshi Dan daddy akwai zafin
hannu.
Basainace ga yanda akaiba Amma nasan kowa zai hasaso wannan dare,Alhamdulillah Lafiya
qalau natashi sai gajiya data rafkeni to ko daddyn saida jikinshi yai laushi balle kuma ni.
Allah ya temakeni haidar bed a yawan fitina shiyasa nai kwanciyata bayan Sallar asuba.
Saidai me daddy nadawo masallaci yafara neman k'ari.
Manyan idanuna na zubemishi yayinda cikin zuciyata nake mamakin wai duk irin yin da yayi
jiya Amma yanzuma k'arawa zaiyi toma abinda suke fitarwa be k'arewa ne.
"Dan marairaicewa nayi Ina kallonshi danyaji tausayina Dan sosai nasha wahala jiya Dan ba
k'aramin gyara nashaba wajan Hajiya,Shima marairaicewar yayi hadda langabe kanshi gefe
guda kamin yace"Pls jiddana ko kadanne kinji!!
Kusan saida gari ya idasa wayewa Sannan ya barni lokacin ko hannuna sainayi da gaske
nake motsashi Sabida gajiya,Shi kanshi uban gayyar tunda ya kwanta yake maida numfashi
Amma banji yai motsin kirkiba,Bayan rungumata dayai.
Allah ya rufamin asiri yau lahadi nasan da anji babu dadi.
Haidar ne ya tashi, Danhaka na lallaba nawuce toilet dan gyara jikina,Shikuma daddy ya
dauki yaron yana jijjigashi.
Yaudai bamu karya da wuriba tunda an makara,Amma yaran babu wanda yasamu
musamman da ganin haidar ya daukemusu hankali Sai wasa sukemishi.
Bayan sati daya; Cikin kwanakinnan ba karamar jigatuwa nakeba hannun daddy Sam babu
sauki duk inda naso zanzarewa yananan like ko damuwa da yaranshi zasugane meyakeyi
beyi,Yayinda na canza idanuna sundan fada Ammafa nai kyau jikina yakuma murjewa daka
ganni kasan Ina cikin nutsuwa da kwanciyar hankali. Amma bangaren daddy ai sai Sam barka Dan tuni yai kiba ya canza koda yaushe cikin frinciki
yake da walwala.
***
Yaudai gabadayanmu gidan zahra muka nufa yau, Daddy ya ajemu bayan yagama jiddadamin
da anyi la'asar mukoma gida koda bezoba.
Cikin farinciki zahra ta tarbemu duk dacewa zaune take sabida yanda cikin yaimata wani
girma gabadayama ta kumbure cikin kanshi zaune yake akan cinyiyinta"Ikon Allah wai zahra
haka cikinnan Ya maidaki Sannu inagadai biyune gaskiya.
Dan hararata tayi kamin tace" A a kin manta uku ne.
Banwani zaunaba sabida yanda gidan Nata yake babu kintsi nasan nauyin DA tayine yasata
kasa gyaran,Shiko dama gyaran namiji ba lallai yai kamar na maceba.
Har girki Saida naimana domin ya usi na shigowa yai farinciki daganina kamin yace"Yauwa
yau munhuta da shan tea da rana do min dahuwar tea kawai ya iya hadawa saikuma farar
shinkafa.
Hira mukeyi cikin farinciki da walwala"Nagode Jidda nagode sosai Allah ya sakamiki da
alkhairi Allah ya jikan iyayenmu.
Tare muka amsa da amin kamin inbita da kallon dalilin godiyar.
"Dole naimiki godiya jidda kin kawo farinciki me tarin yawa cikin gidanmu,Daddy ya canza
canjin da kowa ke magana kuma kalli wa innan yaran ma basu taba kawomin wani korafi akan
kiba,Hakika YARDAr danaimiki bata tashi abanzaba,Shiyasa nakekumajin alfahari dake Jidda
nagode sosai, Wallahi ko yanzu Allah ya dauki rayuwata nasan banda damuwa akan kannena
domin alhamdulillah daddy yayi dace da mata'Mata irin ta nunawa sa'a fatana Allah yasa ki dore
ahakan nagode.
Jikina naji yaiwani irin Sanyi nan da nan idanuna suka ciko DA kwalla dan tunanin mutuwane
kawai ya darsu cikin raina.
Hannuwanta na rike Ina kallon cikin idanunta,Zahra kindaisan ba'ason meciki da shiga
damuwa ko? To Dan Allah ki kwantar da hankalinki Lafiya lau zaki haihu mu rayu tare zakiga
abinda zaki Haifa kamar yadda nakeganin nawa, kuma zamu kasance tare insha Allah.
Hannuwana ta matse cikin nata tana murmushi"To shikenan nagode sosai,Yakamata kitashi
kuje gidafa kinga har yamma tayi kadda daddy yai fada nima gobe zamu koma ganin likita
dama sati daya sukabada idan ban haihuba to kinga shiru kuma ga ciwo inaji.
"Eh gara ku komadin Allah ya raba lafiya,Kai Sadiq jeka taromana me napep muwace kadda
musha fada.
Nidai koda mukabaro gidan hankalina dukba kwanceba,Sabida gaskiya kallo daya zakaima
zahran kasan tanashan wahalar cikin.
Cikin dare.
Kuma shigewa nai jikin daddy Wanda yaketa sauke numfashin samun nutsuwa Dan yanzu
yagama cakudani.
Mannamin kiss yayi saman goshina kamin yace"Nagode jiddana me kikeso naga kina ta
motsi ko in tausamiki jikinki ne?
"A a daddy kawaidai hankalina yaki kwanciya zahra batajin dadin jikinta wlh kuma duk ta
canza dazuma duk ta kumbure.
Kaina yake shafa ahankali cikin nutsuwa kamin yace "Karki damu dama lalurar ciki yawane
da ita,Amma insha Allah zata haihu Lafiya saidai mutayata da addua,Tashi muje ki gyara jikinki.
** ** **
Tun Ina sallar asuba ake kiran wayar daddy danhaka saida nagama Sallar sannan na dauki
wayar saidai tuni kiran ya yanke,Ina ajiye wayar Saigashi wani kiran yashigo ta wayata.
Wani irin mummunan faduwan gabane ya sameni kamin indauki wayar da sauri.
"Ya usi"
"Na'am jidda Ina daddy inata kiran wayarshi be daukaba Dan Allah kimishi magana.
Agaggauce nace masallaci yaje be dawoba tukunna lafiya?
Aika ko Mimi ne ta kirashi zahrace ta haihu yanzu yara biyu mace da namiji Amma kuma bata
motsi bazan iya kaita asbt ba kuma bansan Wanda Zan nemaba yanzu.
Hijab dina na yayiba tuni nafara kuka, Ahanya mukai Karo dashi,Arude yake tambaya lafiya?
Bayani naimishi inayi Ina kuka.
Shima nan hankalinshi yatashi Ya dauki mota ko haidar bamufita dashiba.
Saida mukabiya muka dauki wata abokiyar aikinshi mace Sannan muka isa gidan.
Tashin hankali,Ya usi zaune da yaran rungume sunata tsala ihu shima yana tayasu gakuma
zahra kwance babu numfashi jikinta.
End.
Basainace hankula suntashiba domin zai iyazama bata lokaci,Shi kanshi daddyn wani irin
zaman dirshan yayi yana sauke numfashi,Yayinda zuciyarshi tafara tunamishi da rashin da yayi
awancan lokacin.
Dr.hajara itace tai karfin halin fara duba zahra din aiko saita fahimci bawai mutuwa tayiba
tsabar wahala yasata doguwar suma.
"Dr.kuje asbt tanada rai bari in shirya yaran saimu biyoku daga baya nida madam.
Zumbur duk suka mike daddy da ya usin,shine ya dauketa suka fice kowa jiki na rawa.
Daddyne yai tukin danyafishi dan nutsuwa ba laifi.
Nidai iyakacina riko,Ina kallon matarnan ta gyare yaran tsaf,Sannan ta gyare wajan nikuma
yaran na hannuna Ina jijjiga Dan sosai suke ihun kuka da wutsul wutsul.
Saida komai yai daidai sannan muka fice gidan Allah yasa key din motar ya usi na kusa.
Alhamdulillah tunda sukaje komai Lafiya qalau domin anyimata duk temakon daya dace
lokacin gari ya waye ma.
Gabadayanmu zaune muke munyi jigun jigun Dan har lokacin bata farkoba,Ga yaran sai kuka
sukeyi,Ni Kai na nonona yaimin hake hake to haidar na gida.
Mikewa daddyn yayi ya kallemu"Bari inje Gida wajan yarannan bamusan halin da suke cikiba
Sannan nasan kila haidar nacan na kuka dan rabonshi da abincinshi tun dare.
Duk DA to muka amsa Sannan yafice danyasan alokacin kodayace ni inje gidan bawai zuwa
zanyiba,Kuma har lokacin bamuyi tunanin mugayama wasuba.
Yai mamaki lokacinda yashiga gidan ko Ina tsaf yanata tashin kamshi,Gakuma faruk DA
Mimi sunashan tea da kwai,Ga Sadiq tsaye yana jijjigar haidar Wanda keta korafi.
Ajiyar zuciya ya sauke kamin ya furta*Alhamdulillah abayyane yana karasowa Cikin falon.
Gaidashi sukai,Sannan ya amshi haidar din daketa rarume-rarumen nono DA alama yunwa
yakeji sosai.
Zamayai sannan yagayamusu abinda yafaru ya Dora dafadin rikeshi inwatso ruwa Sadiq sai
inzo inkainatashi Dan da alama ta manta dashi ma.
Bayan tafiyar daddy Zahra ta farko kuma Alhamdulillah qalau tatashi danhaka dagani har
ya Usi din baki har kunne.
Gaskiya zahra ta jigata,Munanan munata murna saiga daddy dakuma yaran
gabadaya,Wayyo sai lokacin naji tausayin yarona musamman daya cafki nonon har kwarewa
yakeyi.
Idanu daddy ya zubamin nasan korafi yakeso yayi, aiko muna hada ido na turo bakina gaba
Dan karma yace wani abu,Murmushi kawai yayi tare da kauda kanshi.
Su hajiyama kusan tare suka shigo,Daganan kuma kamin wani lokaci wajan yacika tuni ya
usi da daddy sukabar wajan duk DA akwai yiwuwar zuwa dare mukoma Gida.
***
Alhamdulillah komai yayi yanda akeso kuma ake bukata.
Yara sunci sunan mamanmu da abbanmu inda ake sakaya sunan da SULTAN DA SULTANA.
Yarane masu matukar kyau dashiga rai,Zahra ta warware Dan tuni tadawo hayyacinta
yanzukuma sai kula da yara.
""**""
Bayan shekara biyar:
Kwance nake ina kallon Mimi da kannenta har uku wasa sukeyi sai ihunsu kawai dayacika
gidan Dan kowanne beji indai wajan rashin jine.
Bayan haihuwar Haidar da wata shadaya nakuma samun ciki Wanda saida mukakai ruwa
rana da daddy akanshi Amma Allah yayi saida na haifeshi inda yaci sunan Ahmad,Naso kwarai
inyi planing alokacin Amma yaki yarda aiko saigashi Ahmad na shekara daya nakuma samun
wani cikin,Alokacin haukane kawai banyiba Amma har yaji saidanayi gidan hajiya Amma
abanza Dan saida na haifi Usman cikin ikon Allah kuma saigashi yanxu Ina hutawa duk dacewa
kusan atsorace nake Amma har yanzu bansami cikinba.
Abangaren zahra ko yaro daya takuma haihuwa bayan twins dinta inda yaron yaci sunan
daddy amma ana kiranshi da khalifa.
Bazancrmuku ga ranar datazo muka sami sabani da zahraba kuma kusan duk weekend
takanyi kokarin yinshi wajena,Kaunar da takemin nasan batakai wadda nakemataba duk da
cewa inajinta araina fiye da kowa yanzu.
Maganar makaranta kuwa tuni karatunmu ya mika domin dafarko daddy kin yadda yayi
Amma dagabaya ranakwatsam yace inshirya zamufita,Ban tambayeshiba kamar yadda nasaba
nasako hijab dina,To dama yanzu bawai fita da yaro nakeba tunkan haidar sabida ga 'yan
uwanshi gidan matukar basuje makarantaba. Daganan nakoma karatuna wanda gashi yanzu ina daf da zama ma'aikaciyar jinya.
Tsakanina da daddy sai Sam barka domin nidai har yanzu bazan iya bugun kirji infadi wani
kwakwkwaran laifinshiba kullun kokarin kyautatamun yakeyi haka yaranshi biyayyar da sukemin
koni na haifesu iyakarta kenan,Shiyasa gaskiya ni bazan boyeba auran babban mutun yaimin
Rana domin nasan da wuya insami hakan daga saurayi metashen samartakarshi,Waima
kunsan cewa duk inyana gida tare mukeyin komai dashi? Kuma yanzu haka duk lokacinda yake
gida wankana nashine haka shafa aikina kawai kwalliya itama danyace be iyaba.
Idan kukaji yanda muke hira ake arerewa dashi saikuyi mamaki.
Bazangaji da godema Allah ba akan wannan baiwa dayaiminba.
Gabadaya yanzu inada shekara aShirin da daya kusan Zan iyacewa sai yanzune nakekan
ganiyar girmana nai wani irin kyau da tsari,Shiyasa yanzune daddy yafi nuna kishinshi zallah
akaina be yarda inje konan dacan batare dashiba,Daidai da Media be yarda inyi hulda da
kowaba. Alhamdulillah kamar yadda bani da matsala hakama ta bangaren zahra,Lokuta da dama
mukan bawa junanmu shawarwarin dasuka dace batare