Showing 1 words to 3000 words out of 175796 words

Chapter 1 - AMIR DA AMIRA Complete by Maman Nusaiba.txt

07 Aug 2025

3330

[22/10, 22:31] MRS. MU'UTASIM: *🌟AMEER DA AMEERA*🌟





*Assalam alaikum barkanmu da wannan lokacin yan uwa ina fatan kuna lfy*




𝙨𝙩𝙤𝙧𝙮 𝙖𝙣𝙙 𝙬𝙧𝙞𝙩𝙞𝙣𝙜 𝙗𝙮



𝑴𝑨𝑴𝑨𝑵 𝑵𝑼𝑺𝑨𝑰𝑩𝑨 𝑪𝑬✍🏻




*1*


Gida ne babba wanda yake dauke da bangare uku ga yara nan suna wasa wata yarinya nagani an bigeta tana kuka yaran kowa yasoma guduwa suna shiga cikin gidan wanda ba yan gidan ba sun fita sunkoma gidan su

dayan yarinya ce ta tsaya akan mai kukan tana cewa yarinya kadan ma kika gani indai nice dama nace miki duk uban daya hadani da yaya Safiyan ya dakeni saina rama kanshi ko ance miki namanta ne to ina sani nace dama sai munfito wasa na rama

yarinyar na kuka tace saina hadaki da mama na
wata mata ce ta fito daga dayan bangaren tana fadin ke rashida wani dan iska ne ya tabaki agidan nan mu fidda reni nida uwarshi

wadda aka kira da rashida tana ganin mamanta tayo wajan ta tana cewa mama ba ameera bace ta ke dukana wai dan jiya munje gonar mlm bukar mun ciro mango shine yabiyomu kuma itace tace muje mu ciro idan bamu ciroba zata mana wankan qaiqayi duk wanda baije ba

mama ta banka wa ameera harara wadda ita kuwa ko ajikin ta mama tace yanzu ameera bazaki dena halin azzalumai ba na daukar maganar da kuke dauko mana kullin ana kawo mana karar ku musamman ma ke mai kunnen kashi

Ameera tace eh din baza adena ba kuma ai hadda diyarki muke zuwa wllh ko gobe tayimin gami da yaya safiyan saina jibgi banza ehee tana jijjiga jiki ita ala dole wai an bata mata rai sai masifa takeyi kamar ba gobe

Mama kuwa kama hannu Rashida tayi sukayi sashen mama ameer tana cigaba da masifa

Ameer kuwa nasashen innar ta ta nufa tana zuwa tayi sallama

sai wata tsohuwa ta amsa tana cewa ke kuwa kedawa naji kina daga murya tace nida rashida da mamanta" Inna tace to mai kika musu
ameera tace inna wallahi saina ci aban rashida wai jiyane munje gonar bukar shesuka shiga suna cire mango shine daya biyomu sukace wai ni na sakasu kuma ni ko gonar ma banshiga ba tana matso kwallar karya tace shine suka hadani da yaya safiyan yayi min duka da safe naje wajan umma gaisheta kawai yake dukana

Inna ta saka salati tana cewa shi dan banzan yaron nan shine ya dakeki to wllh bai bigi banza ba saina rama miki dan iska mugu, ita kuwa ameera tana murmushi tace kuma bakiga yadda yake dukana ba kamar wata yarshi

Inna tace zaizo yasameni anan badai ke ya dakaba zonaga wajan ta matsa kusan inna tana cewa wllh jikina ciwo yake yi tana kukan karya, Inna kuwa sai zuba masifa takeyi kamar ta aro baki. (nace ashedai su ameera gado akayo)


mama na shiga gida da isa wajan wata mata tace sadiya kiduba kiga yadda ameera ta yiwa Rashida gaskiya abin nan ya isheni haka dan tafi karfinta saitake zaneta kullin


wadda aka kira da sadiya ta dago kai ta dubesu tace kiyi hakuri nana wllh kinsan ameera inna ce ke daure mata gindi agidan ko abbansu idan yayi magana inna ke rufeshi da fada nima kaina abun damuna yakeyi kullin addu'a nake mata Allah yashirye ta yarinya bata tsoron kowa kisan da cewa mutum daya take tsoro safiyan shima wani lokacin saita mishi mugunta


Maman rashida tace to shikenan amma kija mata kunne gaskiya tace to insha Allah, suka juya suka fita

Umma tayi tagumi tana tunani rashi ji irin na ameera yarinya kamar aljana babu wanda take ragamawa ita batasan ya zatayi da yarinya nan ba kodayake ai lefin inna ne ita ce bata ganin lefinta
Tana nan abba yashigo da sallama amma yaji shuru ya sake wata nan ma shuru kawai saiya sayo kai ciki umma yagani zaune tayi tagumi da alama ta nisa cikin dogon tunani yazo yazauna akusa da ita duk batasan yazoba saida ya shafo fuskarta


Ta zabura da sauri yayi saurin riketa yana cewa haba sadiya menene yasaka kike wannan tunani ? Umma taja numfashi tace abban safiyan wllh lamarin yarinyar nan ne yayi yawa kaduba kaga yadda take dauko mana magana a garin nan amma inna bata gani duk wanda ma yazo sai dai suyita fada dashi


Abba yace kiyi hakuri umman yara mucigaba da mata addu'a insha Allah wata rana zata dena umma tace amin nan ta dauko mishi ruwa da abinci takawo mishi tace na hada maka ruwan wanka yana bayi

Abba yace to matata farin ciki na yana murmushi, Umma dinma murmushin tayi yazo ya rungumeta yamata kissing a kumatu tayi dariya tace oga ruwan fa zai huce

Ya saketa yana dariya yace ki fiddo min kayan dazan saka tace ai tuni na fiddo maka yana kan gado

Ya fice bayi ita kuma ta zauna tana jiransa,

Safiyan ne yashigo gidan bangaren inna ya nufa yana shiga banka mishi harara tayi dariya yayi zuciyar sa yace to inna gidan masifa kennan yau kuma komai nayi ake min wannan harara haka yana maganar zuci, yaji inna tace wato azzalumi ko uban me ameera tayimaka ka daketa inata magana ka wani ziramin ido kamar na uwarka da hanci kamar karass


dariya yayi dan ya saba da wannan ba'ar ta inna yace hajiya inna ikon Allah kaka ta ni kadai , Ameera na kan cinyarta tace tab wllh bazan yadda ba ta soma tirje tirje a kasa tana cewa itafa kakar tace ita kadai bada kowa ba

Inna tace butar uwaka safiyanu nace tashi kabar min gida ai nan ba gidan ahmadu bane da sadiya to tafiyar ka nace kazo kasaka min yarinya kuka


Safiyan ya kama baki yace Allah yabaki hakuri masifatu, Inna kuwa ta dauko wani filo akusanta ta jefa miki tace fice tin kafin na karya maka kafa

yace kai kaji karfin hali irin na inna ni har zaki iya karyani sabon jini ne nifa kekuwa duk kin tsufa

Inna tace uwarka sadiya ce ta tsufa baniba
Ameera tace inna kyaleshi ai yasan kinfi karfinshi, harara yamata ta koma bayan inna tana boyewa fita yayi daga gidan yayi bangaren umma yashiga da sallama

Suka amsa ya karaso yana cewa umma abba sunun ku da gida atare suka amma da yauwa ,, Umma tace har kadawo daga makarantar yace eh umma na amma Hajara fa da Ibrahim

Umma tace basu zoba tukun nan daiko mai suka tsaya yi ne, Abba yace ai zasu dawo

aikuwa basu rufe bakiba sai gasu sun shigo Ibrahim ne agaba yana kuka hajara na rike da jakar makarantar su umma tace a a lafiya kukashigo Ibrahim yana kuka


hajara tace umma wllh kamal ne da Hanifa suka dakemu wai mufadama ubanda zai rama mana

Umma tace to kuyi hakuri kunji wata rana sai labari, Abba yace kuje kucire kayan naku kizo kukai wa inna abincin su tace to
umma

sukashige cikin daki suna fitowa saiga ameera tashigo da sallama tana cewa abba sannu dazuwa


yace yauwa yar inna ya innar take tace lfy lau abinci mu nazo karba tana fada


Su ibrahim suka fito daga dakin nan yawo wajan ta yana cewa anty ameera yau aka dakemu nida hajara

Ameera ta janyo shi jikinta tana bubbuga bayansa tace wai wani dan iska ne ya tabamin kune wllh ko waye babansa saina yi masa b'alle b'alle

Ibrahim yace kamal ne da haneefa

Ameera tace kai kai kai aikuwa basu daki banza ba dani suke zancen

Umma da abba da yaya safiyan sukayi kuri da ido suna kallon yadda ameera take masifa

Abba yace haba yar inna kiyi musu hakuri kila suma tsokanar su sukayi shiyasa suka dakesu

Ameera tace haba abba ya za'ayi a dakesu kuma kace wai na hakura gaskiya bazai yiyuba saina rama musu

Umma tabige mata baki tace kiyima mutane shuru uwar neman rigima to karna ganki a hanyar gidansu ma


aikuwa ta saki kuka tana ihu waiyo Allah bakina inna umma ta kasheni

Abba yayi dariya yace kai wannan yarinya da neman rigima kike. yace mamana kiyi shuru mana ki dauki abincin ki tafi

Ai kafin ya karasa inna tashigo tana cewa iyee lalle sadiya ai dama nasan kece zaki daketa ba kowa ba to Allah idan kika sake dukanta yanzu zanyi tsukiya muci danbe nidake dan baki isaba kike dukarmin yarinya tafada tana huci


ita kuwa ameera tana ganin inna aikuwa ta kara sakin kuka tana rungume inna tace inna babu abinda na mata wai dan nace zan ramawa su Ibrahim dukansu da akayi shine ta dakeni


Inna tace wai sadiya nace uwarki ta haifeta ne kokuwa a kasuwa aka siyota ne da kullin saikin daketa to bari kiji duka dai saita rama musu dan basu isa ba suci bulus ta kama hannun ta suka fita


Washe gari tinda sassafe ameera ke shirin makaranta dan yau zata daukama kannanta fansar dukan da aka musu

Inna tace ameera fito mana ameera tace ganinan inna dan kwali dan daura ta fito

Inna ta kama hab'a tace a a kinga kuwa yadda kikayi kyau

Aikuwa ameera ta washe hakora tana dariya taji an yabeta tace inna ta to na tafi


Inna tace nadawo lfy tana fitowa bangaren umma ta nufa nan suma su Ibrahim anshiryasu ta gaishe da umma da abba da yaya safiyan nan suma suka gaishe da ita, ta kama hannu su suka fita

Sauran yaran bangaren suma suka fito da shirin makaranta nan suka fita daga gidan yaran suka isa makarantar su

tukun Rashida da ameera da nafeesa suka isa nan malaminsu yazo suka gaishe shi nan aka fara koyarwa


Ameera ce taga wani yaro yana kallon ta yana dariya dankuwa tasha kwalliya kamar aljana kuma kowa yasan halinta dan idan aka kama fada da ita bata barin bashi


aikuwa ta aika mishi harara mai nuni da zamu hadu anjima


Ana tashi ameera da kawarta khadija suna tafe suna hira


Ameera tace kawata ki rakani yau mu casa wasu yara

Khadija tace yauwa dama kwana biyu ban yi fada ba hannu na har kaikayi yakeyi mutafi amma suwaye


Ameera tace kamal da haneefa mana jiya suka kama min kannan suka zanesu nikuwa nace saina rama musu dan babu wanda ya isa ya dakar min yan uwa


Khadija tace aikuwa sun taba bala'i dan bazamu raga musu ba

can suka hangosu ita da kaninta sun tafiya aikuwa da sanda su ameera ke tafiya har suka zo wajan su

Carab sukaji an rikesu haneefa tace uban waye ameera tace ubankine nan suka bude musu idon aikuwa sukayi arba da ameera

Haneefa da yake itama mafadaciya ce cikin fada tace lfy kuka taremu a hanya muna tafiyar. Ameera tace maiyasa kuka dukar min yan uwa


Haneefa tace su suka zagemu , aikuwa bata idar ba ameera ta bade mata ido da kasa nan suka kama dukan ta kamar Allah ya aikota tana ihu tana cewa kiyi hakuri wllh bazan sake dukansu ba


Aikuwa ameera tace batasan hakuri ba saida suka nada musu duka sosai dan har an fasama haneefa baki da hanci kamal kuwa marin da khadija ta wanke masa har hudu


Shine ya gigitasa ya rasa inda zai nufa ya rike yar uwarsa suka tafi suna kuka


wani dan saurayine ya karaso wajan su ameera yace to iyayen fada


Ameera tamai harara tace ina ruwanka sarkin iyayi

yace ke wllh yanzu zan zaneki , Ameera da khadija suka tafa suna dariya ameera tace kama isa saidai muzaneka wllh , khadija tace kai yanzu lado in banda abinka ina ruwanka damu banza jaki alade


Aikuwa lado ya shaka yace nine jakin ? tace eh din anfada jaki bata ida ba ya wanke ta da mari

Aikuwa ameera ta dauko wani dutse tasamu bayansa ta buga mishi yasaki kara ya juya kan ameera


Itama khadija ta dauki dutsen ta buga mishi a kugunsa aikuwa yaji zafi cikin fushi yace wllh saina karya ku yanzu nan yafada yana huci


Da gudu suka bar wajan yana binsu dayake dukkansu basuda jiki aikuwa sukamishi nisa


duk inda suka fuce suna ihu suna wai mahaukaci gashi nan zai kashemu taimako jama'a

aikuwa duk inda sukabi indai akwai mutane suma mutanen rufa musu baya sukeyi kafin kace me tuni sun yaye mutanen layin kowa gudu yake yi nan suka yako kofar gidan mai gari



mutane ne a zaune ana hira a kofar mai gari ameera ta fara zuwa mai gari ya dauko lomar tuwo ameera tayo sufa ta tsallakeshi ta taka bayanshi


Mai gari ya wanke fuskar shi da miyar kwanon tuwo ga akwai zafi tuwon


Mai gari yasaki ihu yana cewa annoba ce ta yo nan bai ida maganar ba khadija itama tazo a mugun gudu tabi takan kafarsa ji kake kass ta dira akan kafar ta kara karfin gudunta


mai gari yakara sakin kara yace man liman taimaka min ka kaini gida wannan wani iftila'i ne yashigo mana gari


Liman ya yunkura zai mike

kowa yayi zuru zuru yana kallon mai gari hallau shesu kalli hanya dasu ameera suka fice

Liman yakusa mikewa lado yace ya angizashi kan mlm bukar


Sukayi gwaran kawuna kan mlm bukar ne ya bugu da gini aikuwa wajan ya fashe sai jini


Mlm bukar rike wajan yana fadin innalilahi wa'inna ilaihin raju'un munshiga uku wannan wani irin masifa ce bai gama fadar sauran magana ba ya hango wasu mataliyar na maza sunyo kansu da mugun gudu

liman na ganinsu yace jama'a kutashi ga wasu bataliyar nan

Suna kokarin tashi suka iskesu aka ringa tabin kansu ana ficewa


Su ameera kuwa suna ta gudu a hanya wata mata tana tafiya ashe mahaifyar su kamal ce aikuwa suka bangajeta sukayi gaba kafin ta tashi lado ma yazo yabi da kanta


Da sauri tayi ta maza ta mike tana komawa bakin hanya


Su ameera suna gudu suka samu wanu lungu anan suka boye lado yazo ya fice aguje sauran ma suka fice da gudu saida sukaga sunyi nisa sosai tukun suka fito sukayo gida


Acen kuwa kofar mai gari sai bayan sun tafi liman yayi karfin halin tashi ya tada mai gari da mlm bukar yana musu sannu duk da shima yaji ciwo a hannu


Amma raunine yayi

mlm bukar yace wllh ko tambaya ba'a yi wannan yarinyar ce data addabi mutane itace ta tabo wani suke wannan tseren


Mai gari kuwa sai share ido yakeyi yana jan numfashi yace wllh saina mata hukunci aje a kiramin inna tazo sai tabiya kudi an mana gyara


Dan aike aka tura kiran inna gidanta



Inna tana zaune saiga khadija da ameera sun shigo kamar wasu na Allah sukayi sallama inna ta amsa tana fara'a tace harkun dawo

Sukace eh inna suka shige daki dan sungaji sosai gudun dasukayi ba kadan bane a kan gadon inna suka zube


Ameera tace khadija kisan kuwa ameer ya kusan zuwa hutu nan kauyen ? Khadija tace da gaskiya , eh wllh ta bata amsa suna haka shesukaji ana sallama da inna ameera tace ke kin manta dazun muna gudu ta kan mai gari mukabi


khadija tace to sai me dan munbi ta kansa mu mukace yazauna a waje

Ameera tace shegiya kawata kina wuta suka tafa

Inna na fita waje akace mata ana kiranta a fadar mai gari , tace to uban shi mai garin zai banii da yake kurana ko wani akace yana bina bashi tana hararar dan aiken


Wanda aka aiko yace inna gaskiya ban saniba kawai kizo mutafi idankinje zakiji ko menene ma


Tace to jirani na fito

ya kalleta yace badai guduwa zakiyi ba yana kallon ta


Inna tace kai ya naga kana kallona da fuska kamar an kona jarka to ba guduwa zanyi ba tashiga ta cewa su ameera wai ana kiran ta a kofar mai gari

Ameera ta zaro ido tace inna mai kikayi

Inna tace babu abinda nayi yanzu zanje naji naga dan iskan dayakai karata ta fada tana fitowa tace dasu kufito mutafi , sukace to suka tafi zuwa gidan mai gari inna kuwa she surfa ruwan bala'i take ita ala dole an bata mata rai tana son taji wani yan banza ne yakaita kara wajan mai gari....


𝙖𝙣𝙖𝙣 𝙯𝙖𝙣 𝙙𝙖𝙠𝙖𝙩𝙖 ✍🏻
[23/10, 00:40] MRS. MU'UTASIM: *🌟AMEER DA AMEERA 🌟*



𝙨𝙩𝙤𝙧𝙮 𝙖𝙣𝙙 𝙬𝙧𝙞𝙩𝙞𝙣𝙜 𝙗𝙮



𝐌𝐀𝐌𝐀𝐍 𝐍𝐔𝐒𝐀𝐈𝐁𝐀 𝐂𝐄 ✍🏻






*2*

Suna tafiya a hanya inna tace to waima wani kaniya mai garin zaibani da yake kira sai wani sauri kakeyi kamar zakaje daurin auren ka,

wanda aka turo kiran inna yace idan munje dai zakiji


Ameera tace khadija anya kuwa ba gudan da muke bane sbd kinga munbi dakan mai gari , khadija tace hmmm kedai kibari idan muka je zamu gani ameera tace ni kinga inna tace jiya ameer dina zaizo daga birni kuma yau ne zaizo gashi an kira inna gidan mai gari ahaka dai suna hira suna tafiya


Lado kuwa gajiya yayi da gudun ga kuma bayansa da yake masa ciwo kamar zai tsage zagi da tsinuwa kuwa su ameera sun shashi kamar mai yayi alwashin duk ranar da taje wajan wasa dandali to saiya rama shi idan yatashi ma kafafuwa zai karya mata


Su inna na zuwa taga su mai gari yayi dai-dai akan tabarma yana zare ido kamar wani tsohon maye

Inna tace ranka ya dade gani naji ance kana kirana shine nazo naji ko lafiya tin kafin ta dasa aya

Mai gari yace ba dole

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login