Showing 123001 words to 126000 words out of 175796 words

Chapter 42 - AMIR DA AMIRA Complete by Maman Nusaiba.txt

07 Aug 2025

3341

nakeji,,


Tashi tayi akanshi,,tace to mutafi ,,yaya so nake muje naga inna " dariya yayi yace to nidai ba ruwana bacci zanyi idan naje, , hajara tace to shikenan


Harsun,, dan wuce wajan yan matan,, nan wata tace
Hello ameera

Cak suka tsaya " Hajara tajuyo tana kallon ta,,

Mikewa budurwar tayi,, tace kai ameera wannan kallon fa kamar baki taba ganina ba,, nice yar ajinku "dana taba cewa inason ameer ,, kika cemin mijinki ne,, nabaki hakuri,, kin tunani ko,, tana kama hannun hajara


Hawaye ,, hajara ta share tace,, niba ameera bace

Da sauri ta kalle ta tace haba ameera,, dan kinga nazo gaban ameer dinki " shine kike cewa bake bace,

Hajara tace, da gaske nake bani bace,, Ameera nan tabata " labari batan ameera yanzu shekara biyu da rabi kenan,, da batan ameera


Kuka take sosai,, tana fadin innalillahi wa inna ilaihin raju'un waiyo Allah ameera,, gaskiya natayaka jimami " yaya ameer ,, Allah yabayyana ,, mana ita


A tare sukace,, ameen

Tace ni sunana ,Rabi'atu ni friend din ameera ce,, Allah yabayyana ta " ban taba jin labarin batan ameera ba sai,, yanzu


Nan suka yi sallama ,

Kawar ,, Rabi'atu tace, wai dama kinsan sune

Rabi'atu tace nasan yayan ta ashe wai ta jima da bata matar wannan doctor dince ,, kuma wllh inkika ganta kamar an tsaga kara da ameera da ameer da wannan kanwar tasu,, Allah ya bayyana tadai ,, tace ameen nan suka tafi ,,



Su mama sunkasa tsaye sunkasa, zaune, ' har sukafi awa biyu ,, awajan baa bude,, kofar dakin da aka saka ameera,, har muhammed yazo shima duk a kidime yake


Bawan minti kamar arba'in aka bude kofar, doctor aisha ce tafito,, tana share gumin dake goshinta,,

Da sauri suka yo wajan ta muhammed yace mommy,, ya jikin ameera ",
Kallon shi tayi tace Alhamdulillah mun tsaida jinin,, insha Allah zata samu lfy ,,a tare suka " sauke ajiyar zuciya nan suka zauna

Doctor aisha ta matso kusan su ikram,, tace baby da murna ikram tayo wajan doctor aisha daukar ta tayi tana mata wasa,, shikuwa muhammed yana bakale jikin abubakar,, ,, ko kallon inda su ikram suke bayiba yayi kwanciyar shi

Umar yace zai koma gida ya dauko , kayan abinci da,, dana sawar ameera nan ya tafi



Fatima ce zaune ,, tana rusar kuka " hadda jan majina takeyi da sauri anass nazo,, yana fadin lfy sweetheart

Kallon shi tayi kawai sai taji,, wata masifar fada nacinta "

A masifamce,, ta mike tana banka mishi harara,, kamar idonta zai fadi kasa tace,, to ruwanka dani dama kake tambaya " ta konace kazo inda nake mutum sai naci ,, wllh kafita idona,, kona shuka maka rashin mutumci,,, a gidan nan har zakake kallona kace min wai lfy to meye naka aciki " iyee nace meye naka " da kake tambaya ta,, kamar wani ,, minkarin da walakiri " ko a kabari nake da zakake tambaya ta " nifa banason damuwa kafita idona na rufe wllh kuma kazo ka kaini gidan mama kona tafi da kafata,, eehee


Baki da ido,, yabude yana kallon fatima namishi masifa " da kashe shi da mamaki ,, wai shi takewa fada to danya,, tambayi dalilin kukan nata, shine " take wannan fadan " kodai akwai wanda yataba ne kafin yazo


Ita kuwa, Fatima ganin yana kallon ta kamar yasamu tv yasa ta karasa,, inda yake tana dafe cikinta daya mata kyau sosai , tace magana fa nake kawani,, saki baki kana kallo na kamar wata tv


Dawowa,, yayi daga tunanin sa, yace muje

Nan tasaka,, hijab din ta tayi gaba abinta ko kallon shi batayi ba

Anass kuwa,, har yanzu mamaki ne akan ,, fuskar shi " yana tunanin anya fatima batada aljanu nan yafita yashiga motar suka tafi gidan mama




Su hajara na " isa gida inna suka samu a falo ita kadai, tayi ture kaga tsiya,, tana taunar " goron ta


Da sallama suka shiga amsa musu " Inna tayi dacewa Amin wa'alaikum salam badan halinku,, ba futsararru " kundawo, kenan

Dariya hajara tayi tana sakin hannun ameer " tace eh mundawo hajiya inna mai duniya


Harara ta,, aikawa hajara tace a kinga mararsa kunya kunzo yanzu zaki soma ko to wllh karrr nake ganinki " kamar,, takarda,, ja'ira ,, kawai


Murmishi sukayi kowa yabar mata falon ganin inna ta soma fada,, suka barta ' anan tana zaginsu


Ameer na shiga dakinsa ,, ya zauna " yana rike kanshi wanda take miki ciwo sosai ,, ruwa mai sanyi ya dauko daga yar kawamar,, frijj, dinsa ,, ya kafa abaki " saida ya shanye tass kafin ya ajiye gorar ruwan,,


Kwanciya yayi yana tunanin ameera yanzu ko wani hali take,, koya labarin cikin sa dake jikinta,, kota haifa , kome ta haifa mace ko namiji, , mirginawa " yayi yace Allah sarki wife na, na kina kusa dani bazan zama maraya ba marar gata,, nasan duk daren dadewa " insha Allah zaki dawo gareni ina jin hakan a jikina, , ganin bamai bashi amsa yasa ya hakura a haka bacci yayi gaba dashi




Su fatima,, na isa gidan mama,, ko baking bai,, gabayi ba tabude motar tafito,, tana hura hanci

Anass ko yana ga ikon Allah yaudai ga fatima sa yakasa gane kanta ,, shima ciki yanufa


Da sallama,, tashiga kafin mama ta amsa tarusa kuka, tana karasowa,, wajan mama


Mama tamike tana fadin lfy fatima kedawa , rungume ta mama tayi tana rarrashin ta,,saiga anass yashigo " duk fuskar tanuna damuwa

Zama yayi ya kallesu ,, yace mama barka da gida


Amsa mishi tayi tace mekamata,, tashigo tana kuka, son


Cike da damuwa yake kallon mama yace wllh babu " abin namata,, dawowa ta kenan daga aiki na ganta tana kuka sosai ,, shinefa na tambayeta lfy,, kawai ta rufeni da masifa, kamar zata sakeni,, hakan bai mata ba " tace saina kawo gidanki ko tazo da kafar ta ,,,bakiga ko uniform ban cireba,, tasakanii agaba saida mukazo


Ran fatima ne yakara baci,, ta dago tace to, ina ruwanka dani hadda tambaya ta,, ni dan wake nakeso mama zanci yunwa nakeji


Yar dariya mama tayi tace ,, yanzu kuwa zan miki,, yarinya maza kije dakin son ki kwanta " kinji


Mikewa tayi tabi ta kusan anass saida ta mika hannu ta mintsine shi a wuya har sau uku,,


Anass yana jin ta,, yayi shuru kuma , yaji zafi sosai a wuyansa


Mama na kallon sai dariya take kasa kasa ta danne dan kar su gani


Ficewa fatima tayi hallau saita waiwayo,, aikuwa akaci sa'a anass na, kallon ta, harara ta banka mishi , ta soma kuka tace waiyo Allah mama,, kin yana min gwalo ko " wllh anjima zan rama,,


Mama tace yi tafiyarki daughter kyaleshi ni zan rama miki,,, nan fatima ta tafi


Anass ko kallon mama, yakeyi sai dariya take mishi ,, mama tace amma mai gidan nawa sai,, saka min yarinya fada yakeyi,,

Anass yace mama kamar yaya,, nifa nakasa gane kan fatima kodai aljanu gareta,, ban saniba


Mama tace babu wani aljanu,, cikin jikin tane ke sakata,, yin wannan fadan


Da mamaki yake kallon mama yace,, to dama mama ciki nasaka wannan abun


Mama tace sosai makuwa,, ai halaye dayawa zakake gane awajan mace mai ciki "
Wata yasaka
Rashin magana

Wata fitana

Wata haka kawai sai kaga tana masifar fada

Wata kuma batason jin kamshin turaren mijinta


Wata kuma idan tasamu ciki sai yawan cin abinci kamar gara

Wata rashin cin abinci,


Wata bacci


Gasu nan dai dadai sauransu, ,, to ita fatima nata fada yasakata,, dan haka idan kaji tana wannan fada, bata hakuri ka rarrashe ta,, shikenan saiku daidaita


Ajiyar zuciya yasauke yace, tab lalle Allah yasaka muku iyaye da gidan aljana ,, tin daga ciki kukasha kahala,, damu har girmanmu,, har auren mu,

Ameen mama tace,, tana mikewa tace bari namata,, dan wanken inyaso " saiku tafi


Anass yace to nan yamike yanufi dakinshi,, yana zuwa yaganta tana bacci hankali kwance ,, murmishi yayi yace Allah yasaukeki lfy sweetheart dina,, nan shima ya hau gadon ya janyota jikinsa suka kwanta



Yau satin ameera biyu ,a asibiti sosai take samun kulawa " wajan doctor aisha ,, Alhamdulillah yanzu jiki yayi sauki dinkin da aka mata ya warke saidai rashin kwarin jiki " nan aka basu sallama,,


Mama ta kira " Umar yazo yakaisu gida an sallamesu

Da murna suka shigo asibitin


Su bubakar " suka tafi dakin da gudu, suna mommy mu ta warke, yeee zamu tafi gida yau

Murmishi ameera tayi ganin , sun shigo yaran su hudu,, kowa sai mommy yake cewa ,,,hannu tabude musu nan sukayo kanta,, suna rungume ta,,,,, beauty tace sannu mommy


Kallon ameera tayi shesuka bata tausayi yandda suka lafewa ajikin ta,, tace,, to kutashi muje gida kunji yaran albarka, ,, mikewa sukayi tasauko,, koya kama hannun ta, tana tsallen murna



Doctor aisha ce tashigo tace to ,she gidako " Allah yakiyaye gaba, ikram tasaki hannun ameera ta kama na doctor aisha,,

Murmishi tayi tace,, a a ikram ko mutafi gidana dake,, hannu ta daga, tana fadin umbo,, mommy, ,dariya tayi tace wai ameera wannan bagwariyar,, yar taki mai take cewa,


Kallon su ameera tayi, tace idan tace umbo,,, wato tana nufin ki dauketa, idan kuma tace aiya , to ku zauna take nufi,, idan tace, mamo kuma bacci take nufi kai wani yaren nata nima ,, kasa ganewa nakeyi idan tanayi ", saidai in tana nunamin da hannu zam gane abinci take nufi


Dariya sukayi su duka,, Umar yace ai akwai yaruka akan ikram wani abun intana jagalgwawa ,, sai ka kasa gane ina ta dosa ,

Doctor aisha tace,, gaskiya naga alama zo mutafi ,,gidana nan ta dauketa ", ita kuwa sai murna takeyi, antafi da ita,,,suma tafiya gida sukayi



Ikram ce zaune a falo,, yauma aikin tunanin ameera takeyi,, abu kamar wasa ameera har tayi shekara biyu da rabi ,, da bata yanzu a ina take


Su ameer da ameera ne suka shigo
Jikinta suka fada


firgigit tadawo daga,, tunanin tace harkun dawo,, ina daddyn ku yake


Ameer ne yace mom " daddy yace mushigo shiya koma ,wai meeting gareshi,


Tace to muje namuku wanka nan sukayi daki



Ameera ce,, kwance cikin dare sai juya kanta takeyi, tana yatsina fuska, kamar mai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login