Showing 69001 words to 72000 words out of 175796 words
Chapter 24 - AMIR DA AMIRA Complete by Maman Nusaiba.txt
jin hayani
Ikram tace lafiya kuke daga murya haka, bata " lura dasu ameera ba " tana karaso wa kusan su nan ameera ta fada jikin ikram tasaki kuka
Da mamaki ikram ke kallon ameera,, tace baby wani mai " tsautsayin ne ya taba min ke yar lelen ameer da momsy ta,, tana bubuga bayan ta,
Fatima da jamila suka karaso wajan su,, nan ikram tace kai amma ina da amare agidan nan "
Ameera ta dago tana turo baki gaba kamar zata sake , fashewa da kuka tace momsy ba waccen bace ta zageni wai zan zanje " room dinki
Ikram kallon inda take nuna mata "" tayi kanwar ta sumayya tagani, tace ke sumayya " waye yace ki zageta " kinsan ko su waye su,, kinsan wani matsayi garesu a wajena " amma har kike zaginta to kishiga,, hankalin ki " duk wanda yakeson zaman lfy to karya tabamin baby
Baki asake sumayya take, kallon antyn ,, nata tace to ai ni bansan itace " babyn da kike fada ba
Banza ikram tayi mata,, ta jasu suka zauna " nan suka gaisa tana tambayar " ina mazajen nasu
Fatima tace ai momsy suna waje " sunce sunason gaisawa " dake
Ikram tace to bari na kira ameer ,, nace suje dakin baki " zan tarar dasu
Mutanen falon kuwa sai kallon su ameera sukeyi " suna cewa wai a ina, ikram tasamu kyakkyawan yara " haka
Ikram tace mama " ga baby wadda nake baki labarin ta "
Wadda aka kira da mama ta washe, baki tace kuzo nan dukan ku,,
Kusan ta suka matsa nan suka gaisheta ,, tukun suka koma,, inda suka tashi nan aka kawo musu baby's din
Mace da namiji ne, ameera ji tayi kamar ta hadiyesu, saboda sosai sun shiga ranta
Fatima ma rumgume namijin tayi,, tana murmishi
Macen ameera tabawa,, jamila kallon babyn jamila ,, tayi tana cewa muma wataran " mune muka haifi namu "
Ikram taje sun gaisa dasu,, Ameer kuma taji dadi harda su bilal
Sai bayan isha"i tukun su ameera akazo daukarsu
Kullin Haka suke zuwa su yini, gidan ikram har lokacin suna yayi nan sukayo siyayya tagani tafada su ukun, hadda mazajen su
Ranar suna yara,, sukaci sunan
*AMEER DA AMEERA*
aikuwa lokacin,, su ameera kamar ,, tayi ihu dan dadi ansaka " sunan ta dana mijinta kai amma momsy tabiya su
Haka shima ameer,, yayi farin ciki marar musaltuwa, jin ansaka,, sunan shi dana wife dinshi
Haka akasha suna,, kamar aure ne ake gidan yacika dam
Su anty haleema anzo suna tana ganin ameera nan da nan ta rude,, ita a tunanin ta ameera aljana ce ba mutum,, ba saida, taga dai mutum ce tukun tasaki jikinta,, amma bataso suhada ido da ameera
Su ameera kirjin biki,, ansha kwalliya ita da Fatima da jamila ,, ga kayan da suka kawo,,Ikram kamar ta goyasu saboda murna
Haka akayi suna taro yatashi lfy,, aka bar mai jego da jariran ta
*BAYAN SATI BIYU*
Yau ne ummi mufeeda zata,, koma dubai su ameera sunzo rakiya " suna zaune a falo hajara tafito,
Da mamaki ameera tace hajara dama,, kina nan dariya tayi tace "tace ina, nan ai Dubai zamu tafi,, nida ummi mufeeda
Ameera tace, wai ummi da gaske zaku " tafi dubai da hajara
Mufeeda tace eh, ameera da ita zantafi,, bayan angama bikin ku, ne na samu " yaya ahmed da ,, zancen abani "" Hajara babu muso " yace yabani ita
Cike da farin ciki ameera "tace to yayi kyau,, gaskiya, naji dadi
Nan aka soma fiddo da, kayansu waje ana zubawa ", a mota
Hajara mike,, kamar wani abu zatayi tace ", tace to jama'a mu zamutafi,, kasar turai sai adarul samalu tana koma ta zauna
Dariya su mom sukayi,, sosai
Mom tace hajara kinsan ina ne kuwa darul samalu kike cewa, sai acen
Tace, ina nufin sai wani lokacin dan saina zama injiniyar computer,,
Ameera tace to lahira cedai darul salamu ba wani wajeba,, ko idan kika koma,, dubai din bazamu,, zake ganin kiba
Da sauri hajara, ta koma jikin,, ummi mufeeda tace " a a gaskiya inason na sake ganinku,, mana
Dariya suka mata,, nan suka " fita kowa yahau mota " suka nufi airport suna zuwa,, babu jimawa" jirginsu,, ya yazo nan aka soma kara " babu bata lokaci suka shiga saida su mom sukaga tashinsu " tukun suka dawo gida su ameera ,, sukayi gidan su
Suna zuwa tayi kitchen ta daura,, musu abinci " dawowa tayi falon taga ameer " yana nan kusa, dashi tadawo tace yaya gobe fa zamu koma school da islamiya,, hutun,, mu ya kare
Kallon ta yakeyi yace, yanzu kenan gobe sai, school da islamiya ko
Tace eh yaya insha Allah
Yace to Allah yakaimu goben insha Allah
Tace amen yaya bari naje magama girkin kar yunwa, takama min, kai
Ameer yace to bari na kwanta , kafin kigama tace to
Nan tamike tayi kitchen
Da dare,, suna " zaune bayan,, salla " isha"i saiga fatima tashigo da sallama amsa mata sukayi,, nan ta karaso,, zama tayi tana gaishe su suka amsa mata
Fatima tace, anty ameera momsy ta kira tace nahada, ku video call nan ta danna,, kiran
Babu jimawa", Ikram ta daga kiran tana cewa hello Fatima ina baby take,, tin dazun nake kiran ta bata dagawa
Saurin, matsowa " Ameera tayi tace waiyo Allah yau nayiwa,, momsy na lefi " wayar ce a room take na saka ta a caji ne, ni kuma ina falo " ga yaya
Murmishi ikram tayi,, tace ina yake,, wayar suka , gyara suka saka ,, Ameer a tsakiya " nan ya gaishe ta
Ameera tace , momsy ina takwara,, da mijina suke bangansu ba ko suna wajan uncle ne
Ikram tace ,, a a gasu nan ta rungumosu, tana gyara " musu kwanciya ajikinsu,, suna tsaye basuyi bacci ba
Ameer yace anty kinga wife tashi kyau, kalli har dariya takemin taga mijinta,,
Ameera ta harare shi ta kallo wayar, tace momsy wllh mijina yafi kyau kinganshi hadadden,,, gaye dashi saima yagirma,,
Fatima tace,, dukkansu,, suna da kyau " sosai
Dariya ikram tayi jin yadda suke muso ,, tace duka suna da kyau kamar ku, kunga fa sunan ku garesu,, saboda suyi kamanni "" kamar ku yasa nasaka musu,,, sunanku dan haka kubari,,, su girma tukun sai,, a tantance"
Ameera tace to shikenan momsy
Haka sukaci gaba da hira , har wajan taran dare,, tukun suka kashe kiran " fatima, ta koma sashenta
Washe gari duk sun, fito mazan,, zasuje wajan aiki matan kuma,, school " haka suka fita su dukansu,,
Suna tashi,, daga school din gida suka nufo,, bayan sallar la'asar sukayi shirin islamiya,, dan yau akwai , taron malamai a islamiyar, tasu kuma,, za ake daukar dalibi daya acikin,, aji yayi wa'azi ko wani jawabin mai kyau ko labari sahabbai ko na innabawa ,, da sauransu,
Tin kafin su kai islamiyar,, Nafeesa ta, kira ameera tace besty maza,, kizo nan da minti goma zaa fara program din ,, Ameera tace gani nan zamu shiga ciki nan ta kashe kiran suka fita,, a motar wajan program din suka nufa, suka zauna
Babu bata lokaci aka soma gabatar da program din , malaman suka fara jawabi ,, sai suka gama tukun aka soma kiran dalibai
Nafeesa,, aka kira,, aka ce tazo ta bada tarihin annabawa,, ko wata kissa
Nafeesa ta to ta amshi,, spikar tace assalam alaikum suka amsa mata da amin wa'alaikum salam ,,
Nafeesa tace yan uwana masu albarka da kuma,, iyayenmu laman mu ina mana barka da wannan lokacin da fatan,, duk kuna lfy Allah , yasa duk wanda yazo taron nan lfy yakaishi, gidan sa lfy,, suka amsa da ameen
Nafeesa tace wata rana, wani sahabi ya tambayi manzon,, Allah (S.A.W .) Yace wani aiki ne Allah yafi so acikin aiyukan, musulinci wannene yafi
Sai annabi Muhammad (S.A.W) yace (tud'u" imun d'a"ama) kaciyar ga mai jin yunwa ka taimakawa marar shi (watta q'ara"u salama ala man arabta waman lam"arifu) kuma kayi sallama, ga mutum koka sanshi ko baka sanshi ba ,,wannan hadisin ya koya mana mashimmancin, bayar da gudun mawa ta abinci
Ko kayi kunu ,, ko kayi tuwo ko kabada ruwa sanyi,, ko kayi kosai duk zaka iya basai kace,, sai abinci mai tsada ba ,, a a koda ruwan sanyi ne kabawa mai jin kishirwa, to ka taimakesa,, kuma zaka samu ladan sa
Dan haka yan uwa mu taimaka wa marayu,, masu bukatar taimako ko wanda suke kasan mu
Nagode nafeesa ta fada tana ajiye abin,, maganar
Mutanen wajan, sukace ce Allahu akbar
Nan malamin ya yace masha Allah nafeesa mungode da tunatarwa,, Allah yasa ka da alkhairi
Yanzu muna kiran ameera, tazo tadan bamu wata kissar, ko labarin sahabbai, nan ameera tamike " tazo ta amshi,, abin maganar
Tace assalam alaikum yan uwan mu da iyayen mu malaman mu " ina fatan kuna lfy ,, Allah yasa,, yadda kowa yazo wajan, nan lfy Allah yamaida" kowa gidan shi lfy
Amsa mata sallamar,, sukayi har da gaisuwar,
Tace wata rana antaba, tambayar mala"ikan mutuwa azara"ilu
Ka taba dariya
Na taba dariya sau daya
Kataba tausayi
yace na taba tausayi sau daya
Kataba mamaki
Yace na taba mamaki sai daya
To yaushe kayi dariya ya mala'ikan mutuwa azara'ilu
Yace wata rana nazo kabar ran wanii bawan Allah minti daya in karbi ranshi, shikuwa alokacin yabada dinki takalmin sa fadi yake kasamin fata wanda zai shekara goma ina anfani dashi bai lalaci ba , azara'ilu yace wannan maganar tasani dariya
Tausayin kuwa shine wata rana nazo daukar wata mata,, atsakiyar daji ga ciki tana cikin halin nakuda ga wurin babu kowa,, haka na zare ran baiwar Allah nan nabar jaririn yana kuka
Mamakin kuwa shine wata rana, nazo daukar ran wani bawan Allah sainaga kawashi tana shaske da kamshi ga wasu mala"ikun rahama zunzo tafiya da ranshi saboda tsabar,, aikin sa na alkhairi
sai aka fadamin cewa, jaririn nan ne ya girma yake aikin alkhairi
To kunga wannan yana muna nuni da mutuwa bata shawara,, dakowa idan lokacin ta yayi,, saidai kaga mala"iku a