Showing 132001 words to 135000 words out of 175796 words

Chapter 45 - AMIR DA AMIRA Complete by Maman Nusaiba.txt

07 Aug 2025

3357

taji shigowarsu


Da sauri tasa hijab ta fita tana tsaye har suka fito

Baya suka bude nan suka fito da karima da mamaki take kallon su


Wajan ta sukayo ameera tace please momma ba lokaci muje ki duba mana ita


Bunsu tayi ciki kamar rakumi da akala , a falo suka shimfide ta ,


Ruwa yasoma diga daga jikin alamar kankarar tasoma narkewa , Muhammed ya kalle ta yace mommy ki dubata mugani tana da rai


Kayan aikin ta ta dauko tashiga auna karima tajima tana aunawa , kafin ta dago tace tana da rai zuciyar ta na mugawa ,,amma tana mugatar " karin numfashi saboda nata yamata kadan , kuma dole sai an ringa gasa mata jikinta da ruwa mai zafi sosai saboda kankarar jikinta, ta fita kozata samu damar motsawa da kanta

Muhammed yace to ,mommy muje hospital din , karmuyi jinkiri , kayanta ta hada , umar yadauki karima nan suka shiga mota sai hospital din mommy


Suna karasawa , doctor aisha tashiga office dinta,, ta saka kayan aiki tukun tafito ,, nosee nabinta abaya

Karin numfashi aka sakawa karima shima da kyer aka samu aka saka mata saboda duk ilahirin jikinta yayi tauri ,


Umar ko yama rasa mai zaiyi shida , ameera ,, kuka ameera tayi rusa kamar ance karima ta rasu ,, Umar na bata baki akan tayi shuru amma kamar kara mata karfin kukan yake,, haka ya hakura yazuba mata ido

Cen kuma saiya kira mama , ringing daya ta dauka , dama tana kokarin kiransa ne saigashi ya kirata dan taleka dakinsa sai, Abubakar tagani na ameera kuma sai muhammed , yana bacci nida mufeeda



Mama tace hello umar wai ina kuka tafine na leka banga ameera ba kaima banganka , ba sai yara suna bacci


Ajiyar zuciya yasauke yace mama ki kira , maman karima dukkanku , kuzo hospital din doctor aisha , idan kukazo zakuji komai



Cike da tashin hankali ,Mama tace na shiga uku hallau wani abunne yasamu ameera din

Umar yace no ba ita bace kudaizo nan ya kashe wayar yana kallon ameera da har yanzu take kuka abinta



Ameera ko kukan farin ciki ne takeyi, saboda tacikawa karima burinta gashi kuma sun fiddo ta daga cikin inda aka boyeta ,, shiyasa take kukan farin ciki saboda ,, takusa komawa wajan mijinta da danginta , duk wani nauyin da zuciyar ta kemata kullin yau tana kukan , yana fita , tana haka su mama sukazo


Doctor Aisha ce tafito kallon muhammed tayi tace son , kaje gida ka wanki ikram saikuzo idan kunyi break , , ya amsa da to nan yatafi baima ,, tsaya sun gaisa da su mama ba , ta tafi


Doctor aisha tace, zaku iya ganin ta kafin asoma shirye shiyen mata aikin nan da sati biyu ,


Ameera na ganin mama da sauri ta fada jikin ta tana kuka ,, Mama tace wai lfy kike kuma shi kuma sai murmishi yake " ku fada mana


Dagowa ameera tayi tace mama mun samo anty karima ,

Kallon mama tayi da sauri tace ke ameera bana son wasa " kinsan me mike cewa kuwa


Cikin kuka ameera tace , eh mama kuzo muje kugani , nan suka nufi dakin da aka kai karima,


Cike da mamaki suke kallon karima da take kamar gawa a kwance , maman ta ta karasa wajan da take tana kallon ta tace tabbas wannan karima ce " wannan kayan dashi ajikinta , akace ta mutu kowa

Umar ne yamusu bayanin komai da dakota da abinda doctor aisha tafada

Mama tace Alhamdulillah Allah mungode maka ,sai ta kalli ameera wanda take share hawaye , tace lalle ameera ke haske ce agaremu,, alkairan ki yana dayawa " agaremu Allah yasaka miki da alkhairi yadda kikayi sanadiyar, fitar damu daga duhu Allah yarabaki da duhun kabari, Allah yamiki albarka


Ameera tace ameen mama , nima ai yarki ce , yanzu dai mubari , muga tashin antyna



Nazeer ma kukan yake share hawayen sa yayi yana murmishi ,, yace kaji masu anty to sannu ko


Harara ameera ta banka mishi tace ,eh anji din tuzuru kawai


Dariya sukayi , Nazeer yace oho dai yarinya ai nima zanyi auren na huta da gorin dakike min ,,, nan suka fita daga dakin



Yau ne ake bikin ,sunan babyn fatima , sosai aka cika gidan maman anass da dangin mommy hadda yan kauye sunzo

Umma tacewa khadija tabiyosu , amma tace bazata zoba tin babu ameera , haka ta hakura ta kyaleta



Yarinya taci sunan mommy fadila za ana kiranta da ,Iman , masha Allah anyi suna abin burgewa, anyi taro lfy , (*cen* *nagano* *fans din ameer da ameera* *musamman* *ma* *mrs*. *Sadeeq *wato kawas 💃🏻da ,Queen farida su asna maman sudes ,dadai sauran fans kowa na cashewa*)



Haka akayi taro lfy kowa yatafi gidanshi , aka bar mai jego da baby iman ,mama tacewa anass fatima gida zataje wanka


Aikuwa takafe shi babu inda za'a kai mishi mata ta tsare gida yahana , ganin abun da anass yake gaske ne yasa mama hade rai


Tace anass ,, jin takira sunanshi ful yasan babu wasa , saiya zauna

Kallon shi tayi tace wannan tafiyar dole, Fatima taje gidansu wanka haihuwar fari haka akeyi tin asali,, kai dan kaine shugaban marassa kunya kace , bazata tafiba " naji kara fadin bazata tafiba saika hadu da fushina , haba yaran zamani sai shegen rashin kunya tana, rankwashin sa aka


Dafe kanshi yayi yace ,washh mama wllh akwai ciwo sosai ,, shikenan naji sutafi

Inna dake jinsu tin dazun tace,, ka anaru kake ko anu , to ka kiyaye wllh " in banda ma ku futsararru ne,, hadda cewa bazata jeba " ni yanzu saina hada maka jini da majina dan butar uwa kake wani sunne kai kamar tsohon munafiki,,, kai nifa baa kawomin reni ko rashin kunya yanzu saina saita maka hanya " dan kwal uba , uwar taka na maka magana , kana tankawa, yo inbanda ma karfina yadan ragu da tuni na dauki sandar nan " na mammake ka da , ai dakai da ameeru ,,duk tafiyarku daya,,, dogayen banza kawai masu hankalin,, rakuma duk wanda yake rashin kunya acikin ku , dukanku zan bubbuge ja'irai ,, tana kai karshen maganar tana , gyara daurin dan kwalinta ,, ta turoshi gaba


Mama na dariya tace yauwa inna , ai gyara ki mana maganin su wllh basuda kunya


Anass ma dariyar yake yace yi hakuri inna nadena ,, kutafi


Inna na aika mishi kallon tara saura kwata tace, kobaka fadaba tafiya zamuyi dan kan uba ,baki kamar tukunyar daddawa,


Dariya sukayi mama tace inna , kyaleshi muje muhada kayan , nan suka shiga dakin fatima,, aka hada kayan suka fito dan tuni direba yazo daukarsu

Fatima na kallon anass saidai ba damar tamishi magana ,, inna ta balbale ta da masifa yasa ta daga mai hannu fuskar ta cike da damuwa, na rashin barinta da inna takiyi tayi sallama da mijinta ,

Da hannu anass ke mata nuni zasuyi waya ta kula mishi da iman , nan sukatafi har mama




Yau su raju suka shigo cikin
Majami'ar , da farin ciki suka shiga nan suka yi dakin kasa wajan akwatin suka nufa,, budewa sukayi amma me???

Shesuka ga babu karima aciki da sauri raju yafito yana kiran masy tsaron dakin


Tambayar su yayi ina ajiyarsu ta cikin akwati ,, amma kowa yace bai gani ba , cike da tashin hankali suke zarya shugaba yace ,shikenan karyar mu takare , lalle bana tantama,, wannan yarinyar ce tagano inda take shiyasa tazo ta dauketa

Amma taya zata iya zuwa nan ,, babu mai basu amsa nan suka fita sai wajan bokansu dan yar mairo ta koresu


Yau saura kwana daya afara wa karima aiki,, amma matsalar tata tafi karfin doctor aisha ,,


Nan takira umar da muhammed ta fada musu , cewa bazata iya aikin nan ba yafi karfin ta , amma akwai wani doctor ,,kwararren likita ne ana kiranshi da doctor ameer , shi zata kira yanzu ta fada mishi ,, yazo suyi aikin tare,, Umar yace ba matsala kirashi muji, nan ta dauki wayar t......




*anan zan dakata dan Allah kukeyin comments fans*

*idan kinsan bazakiyi min comments ko sharhi ba karki karanta min littafi*
[30/10, 19:17] MRS. MU'UTASIM: *🌟AMEER DA AMEERA 🌟*



*STORY AND WRITER BY:*


*MAMAN NUSAIBA CE ✍️*






💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️*


https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl

_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_

*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*



*wannan shafin na sadaukar gareki my daughter na , miss hajo* ina yinki over Allah yayiwa rayuwar ki albarka

*77—78*


Doctor aisha , tasoma duba contact din wayarta , sai cen tukun taga nember din ameer , Kira ta danna , nan tasoma ringing


Lokacin ameer , yana tsokanar inna tana sauke mishi ruwan masifa , shi kuma sai dariya yake "jin ana kiran shi ya ciro wayar daga " aljihunsa da mamaki yake kallon mai ", yace ikon Allah doctor aisha kuma , bari nadaga nan tayi faking, yace assalam alaikum ,


Daga cen bangaren doctor aisha , taji ajiyar zuciya , tana abdallah da , yadauki kiran "tace amin wa'alaikum salam doctor ameer likitoci bokan turai , barka da warhaka


Murmishi ameer yayi yace , yau kuma " harda tsokana lfy lau yagida ya aikin yasu mai sunan daddy na


Doctor aisha tace kaga da yana nan a zaune , amma yanzu ya tashi ta kun gaisa ,, yau ameer dan Allah wani taimako ,konace alfarma nake nema , agareka " Allah yasa zaka amince


Ameer yace haba dai, kakata kodan mai sunan daddy , zan miki komai " barema kinfi karfin haka agareni ki fadi " bukatar ki insha Allah indai baifi karfina ba , zan miki shi komai " wahalar shi


Murmishin , jin dadi doctor , aisha tayi tace gaskiya jikallena " yauwa ameer dama inason , kazo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login