Showing 6001 words to 9000 words out of 175796 words
Chapter 3 - AMIR DA AMIRA Complete by Maman Nusaiba.txt
karama ce dukafa 12 years gareta saidai tayi school acen kafin tagama tayi hankali
Daddy yace nima haka na yanke shawara nan ya kira mommy yafada mata itama ta nuna farin cikin ta dan tana son ameera nan sukayi sallama
Da dare bayan sallar isha'i ameera tayi d'amara a kugunta taci kwalliya kamar wata aljana tafito tace inna zanje dandali bazan jima ba
Inna ta dubaita tace a a hadda kwalliya haka
Ameera tace eh
Inna tace adawo lfy nan ta fita abinta tana wakar karo taci da ameer taja da baya tana dafe kirji tace sannu ban ganka bane yaya
shikuwa ameer k'uri yamata da ido dan yaga ta caba uwar kwalliya kamar aljana yace ina zakije
Cuno baki gaba tayi tace dandali
Ameer yace daukan magana dai ?
Sake turo baki tayi
Yace idan kika sake turomin baki saina cire miki shi
Da sauri ta mayar tana dariya tace to shikenan matsa na wuce
yace karfa ki jima
tace bazan jima ba
Yabata hanya tafice
Tana fitowa saiga khadija itama tasha kwalliyar irin na ameera taci damara a kugunta nan suka tafi dandali
wajan yan mata ne da samari wasu na hira wasu na wake wasu na kallon su.
...Kafin su ameera su iso wajan wani saurayi ya tare ta yace a a su ameera kune sai yanzu
Kallon tara saura kwata tayi mishi tace eh mune ya akayi , yace dama jiranki nakeyi gashi kuma kinzo
Khadija tace buba kabamu waje mu fice
Wanda aka kira da buba Yace ke dallah cen danma kunga ana kulaku waye baisan halinku ba hatsabibai yana aikawa harar
Ameera tace khadija kyaleshi ai yaya yacemin kar nayi fada bata idarba ya buge mata baki aikuwa taji zafi
khadija tace aikuwa sai mun rama yana hararar su yace mugani mana, ameera ta jumke kasa a hannun ta tace inka isa juyo yana juyowa ta watsa mishi kasar a idonsa
Ihu ya saki ka yana dafin kin makauta ni, sukuwa dariya suke Dan su ganima sukayi kadan suka mishi sai gobe zasuje gidansu da dare sumishi balle balle da reza nan suka wuce
Yau dai basuyi fada sosai ba suka dawo gida ameera tafara shiga gida tukun khadija
Washe gari
Misalin karfe 3:pm bayan sallar jumma'a aka daura auren 𝙖𝙢𝙚𝙚𝙧 𝙙𝙖 𝙖𝙢𝙚𝙚𝙧𝙖 akan sadaki raina dubu hamsin bayan angama su daddy suka iso gida ameer sai washe baki yakeyi
Ameera da aka fada mata an daura mata aure da ameer dinta aikuwa tahau tsalle tana taka rawa ita ala dole tayi aure kuma da ameer dinta duk wanda tagani sai tace anyimin aure tana dariya baruwan ta da damuwa ita ko ajikinta
Babu bata lokaci aka soma shirya musu kayansu na tafiya kano daga kauyen karkara
Inna na kuka tace ameera shikenan zan dena ganin ki , Ameera na dariya tace to kekuwa inna meye na kuka idan naje birni zanzo ina ganin ki kinji innata
Kowa na wajan dariya yayi dan ita batasan mai ake nufi da aure ba nan aka rakasu bakin kofa
Ameera ta soma gada musu hannu tana fadin sai wata rana umma da abbana natafi kano wajan mommy nake kwalliyar yan gayu ina kashe dauri ina hawa lilo tana ta surutun ta aka ja mota
Daddy ne ke jan su kuma suna baya shida ameera suna hirar su
MUHADU A GOBE INSHA ALLAH KUYI COMMENTS DA SHARE DIN NOVEL YAWAN COMMENTS DINKU SHINE KARFAFA MANA GWIWA NGD
[23/10, 23:12] MRS. MU'UTASIM: 🌟𝐀𝐌𝐄𝐄𝐑 𝐀𝐌𝐄𝐄𝐑𝐀🌟
𝙎𝙏𝙤𝙧𝙮 𝙖𝙣𝙙 𝙬𝙧𝙞𝙩𝙞𝙣𝙜 𝙗𝙮
𝐌𝐀𝐌𝐀𝐍 𝐍𝐔𝐒𝐀𝐈𝐁𝐀 𝐂𝐄✍🏻
4
Tin kafin suyi nisa ameera ta fara bacci nan ameer ya gyara mata kwanciya sukaci gaba da tafiya basu Jima ba suka kawo kano ta dabo tumbin giwa anguwar nasarawa J R A wani gida mai kyau daidai misali naga sun nufa nan aka bude musu suka shiga gidan ameer ne yasoma tashin ameera bude idonta tayi akanshi yace my ameera munzo kano
Ameera tace da gaske?
yayi murmushi yace tashi kigani
tashi tayi akan shi taga dai ashe dai da gaske yake yi sunzo cikin murna ta rungume shi tace yanzu zan ga mommy ko
Ameer yace sosai makuwa keda zaki zauna tare da mu
Ameera tace to amma zan ke lilo irin na gida ko
Yace zanke kaiki wajan wasa nan suka fita
Fauziya ce ta fito daga wata kofa ita da fatima suka yo inda ameer yake suna oyoyo yaya nan suka rungume sa suna murna
Fati ta juya gefen ta kawai sai taga ameera tana cika sai hura hanci sama take ta rike k'ugu ita wai an share ta taga basu ganta ba
Fatima tace la anty ameera fuskar ta dauke da farin cikin ganin ameera
fauziya ta juya itama nan suka rungume ta suna cewa dama dake za'a zo mommy bata fada mana ba
Sai alokacin ta saki fuska tace eh ai tare daku zan zauna tana yar dariya
Fatima tace aikuwa munji dadi
Ameer yace to iyayen surutu sai kuzo mu shiga daga ciki ko yayi gaba suna binshi abaya wata kofa naga sunbi wadda zata sadasu da falon gidan da sallama suka shiga mommy ta mike tana musu oyoyo yarana
Da gudu ameera taje ta rungume mommy tana dariya tace mommy na munzo
Murmishi mommy tayi tace to sannunku da zuwa ya kauye yasu inna da umman ki da sauran yan gidan
Ameera na dariya tace ai in gaya miki mommy harfa kofar gida suka rakomu , kinga kuwa yadda inna take sharce hawaye kamar fa ance mata bazan dawoba kuma ma kin me mommy
Yar dariya mommy tayi tace a a saikin fada
Ameera tace nifa banyi kuka ba yayana yacemin zaike kaini wajan lilo shiyasa banyi kuka ba
Mommy tace to masha Allah mu zauna ko , zama suka mommy tayima su ameer barka da hanya
gidan yana da part uku
daya a sama
biyu a kasa
na saman shine na ameer
kasa kuma daya nasu mommy daya na Fauziya da fatima
Mommy ce ke jera abinci akan danner da
Suna zauna a falo fatima na bakale da ameera sbd itama indai surutu ne ba'a bayaba
Tace anty ameera a dakin mu zaki zauna ko
Ameera tace eh
Ameer ne ya harari Fatima yace kedai yarinyar nan kin cika magana
dariya fatima tayi tace yaya ai zamuke hira idan mun shiga daki
Ameer yace to naji
...Mommy tace "idan kungama surutun kikai ameera tayi wanka sai kuzo muci abinci
Da murnanr ta tace to mommy
Fauziya ta rakata da kayan ta a jaka nan ta nuna mata yadda zata yi wanka da ruwan dumi tace "idan kin gama ina jiranki
Ameera tace to nan dai ta soma kalle kalle tace tab wllh wannan bayin na aljanune ko kuwa a aljanna ake ganin irin wannan bayin ahaka dai ta fidda kayan jikin ta wanka ta soma duk abinda ake anfani dashi fuziya ta nuna mata
Kuma tagane haka take dan akwai ta da saurin fashimta saida ta gama wankan tazo wanja alwala aikuwa taganta ta zama biyu idan ta taba fuskar ta sai taga wadda take gabanta ma ta taba idan ta zare ido itama saita zare ido tsoro ya kamata tana ja da baya itama ta jikin bangon tana ja da baya
Aikuwa ta saki uban ihu a guje fauziya da fatima da ameer wanda zamansa kenan yaji karan ameera aikuwa da sauri fauziya da bude toilet din taga ameera sai kerma take bakin ta na rawa
Fauziya tace lafiya dai kike wannan uhi !haka
Ameera tace wllh anty fauziya aljana ce nagani mai kama dani tana kallo na duk abinda nayi itama sai tayi
fauziya tace ina take aljanar
Ameera tace gata cen jikin bango tana nuna mata da hannu
Kallon inda ameera ta nuna fauziya tayi mirror din jikin bangon ta kalla anan ne taganta ajiki
Fatima ta kwashe da dariya tace amma anty ameera kedai kauyencin ki ya miki yawa madubi ne fa
Ameera ta turo baki gaba tace to ai mu a garinmu ba'a saka madubi a bayi
Fauziya tace to mu muna sakawa
Ameer ne ya karaso toilet din yaga ameera bako pant a jikinta yayi murmushi yace rigimanma yanzu saboda wannan ne kika saka mu gudu
fuskar tausayi ameera tayi tace to ai dai tsoro naji
nan suka fito daga toilet din fatima namata dariya
itama fitowa tayi bayan ta shirya suka fita falo suka tarar daddy da mommy a zaune suna jiran su
Daddy yace yar gidan inna ihun mai kike yi
Tace daddy wai madubi ne suka saka a bayi ni kuma da farko ban ganshi ba saida nagama na nazama biyu shine naji tsoro ko aljanu gareku agidan
Dariya daddy yayi yace to kidena jin tsoro
tace to nan suka fara cin abinci bayan sun gama
daddy yafita shida ameer ana neman sa a kasuwa
Ameer yanzu yagama karatun sa yana koyar wa a wata makaranta kuma nan yake so yakai ameera saboda ya kula da ita sosai dan ta nutsu tayi karatu
Da dare bayan an gaba cin abincin ne aka soma hira inda ameera keta basu labari irin barnar da sukayi a kauye ita da khadija kawar ta
Sai dariya suke ba kamar Fatima ma harda rike ciki takeyi
Ameera ta juya wajan mommy tace mommy kinsan harna tuna lokacin da muka yima malamin mu na school wankan kaikayi
Mommy tace kaikayi kuma ameera
,Dariya tayi tace sosai makuwa lokacin muna cikin aji sai malamin namu ya riga mu shiga shine fa da mukazo sai yace mu tsuguna a gabansa yayi ta zanemu da bulala ranar har ruwan zafi inna tayimin kuma tace sai taga waye ubansa da har zai ke zaneni haka nida khadija mukace zamu rama inna tace tana bayanmu mu rama tinda bamu yafe masa ba
Washe gari , muka je gonar mlm bukar muka cire mana mango sai gashi ya biyo mu zai zane mu muka boye a wani bayan bishiya yana isowa muka zuba masa kaikayi acikin rigar sa khadija ce ta hau sama ta zubo masa aikuwa ya soma zazzaga rigarsa baiga komai ba kuma jikin sa yana mishi kaikayi kafin wani lokacin tuni yacire rigar sa da wandon sa saina
Mukayi ta masa dariya ganin abin na karuwa ya yabar gonar yana zaginmu
Bayan yatafi muka fito nida khadija ta sauko daga sama nina fito daga inda nabuya , sai muka rankaya school din mu
Muna zuwa mukaga mlm kamar da gaske gaisheshi mukaje sallama muka mishi ya amsa gaishe shi mukayi nanma ya amsa da fara'arsa
Yace mana su khadijatullah ne da ameeratullah kijifa mommy dan shegen iyayi hadda mana karin suna
Khadija tazo tabayanshi ta zuba mishi kaikayin mukabar wajan
Ko minti goma ba'ayi ba akaji tana ihu asosa mishi
Shima yayi irin na mlm bukar yacire kayanshi ganin zai haukace aka kaishi gidanshi mu kuwa muna mishi dariya
Mommy na dariya tace kai ameera bakida da dama
Fatima tace ashedai kedin indon kauye ce
Ameera tace ba ruwanki yarinya
Hira akaci gaba dayi
10:00 PM ameera tasoma bacci mommy tace kowa yaje ya kwanta nan suka nufi daki akayi saida safe
𝙗𝙖𝙮𝙖𝙣 𝙨𝙖𝙩𝙞 𝙙𝙖𝙮𝙖
Aka nemawa ameera school a inda ameer yake koyawa aka kaita
Yaune zata fara zuwa sai murna takeyi saboda farin ciki ko baccin kirki batayi ba
Shiryawa tayi cikin uniform dinta blue and rid tayi kyau sosai tana fitowa falo ta zauna jira ameer bata jima da zama ba yafito cikin shirinsa
Murmishi tamishi tace good morning yaya
Shima murmishin yamata yace morning my wife kintashi lfy
Ameera tace Alhamdulillah , yace to muje mikewa tayi suka wuce
Suna zuwa school din yakaita ajin da za'a koya mata karatun tana shiga bata kula kowaba kowa yayi shuru jin malamin nasu tana tafowa
[24/10, 00:08] MRS. MU'UTASIM: https://chat.whatsapp.com/Gu2Mxr0SRlx8Da4tv0J2AR
🌟𝐀𝐌𝐄𝐄𝐑 𝐃𝐀 𝐀𝐌𝐄𝐄𝐑𝐀 🌟
𝙨𝙩𝙤𝙧𝙮 𝙖𝙣𝙙 𝙬𝙧𝙞𝙩𝙞𝙣𝙜 𝙗𝙮
𝐌𝐀𝐌𝐀𝐍 𝐍𝐔𝐒𝐀𝐈𝐁𝐀 𝐂𝐄✍🏻
5—6
Suna a haka Malamin "nasu ya shigo nan aka yasoma yimusu lecture,
Bayan antashi ameera ta fita domin zuwa wajan yayan nata tana karasawa wajan motar shima ya iso, tace yaya yunwa nakeji
Ameer yace to raguwa ai yanzu zamu tafi gida
ta turo baki gaba tace" nidai muyi sauri
yace to shikenan, nan suka fice gida
Suka zuwa gida ko dai-daita motar baiyi ba ta bude ta fita a mota
Ameer yace a wai Ameera duk yunwar ce ?
tace eh itace
yabi bayan ta suka shiga ciki
mommy suka tarar a falo fatima da fauziya ma sun dawo
Fatima tace sannunku yaya,
Yace yauwa
Mommy tace har kundawo ?
Sukace eh
mom tace to "idan kunyi wanka kuzo ga abinci angama suka amsa da to
Bayan sun gama ne kowa yafito sukaci abinci 'bayan sun gama cin abincin suka koma falo
Fatima tace anty Ameera wai da ni shekarar ki nawane?
Ameera ta mata kallon tara saura kwata tace ki tafi kauyen mu ki tambayi mana inna ko umma
Fauziya tayi dariya,tace kai kudai baku rabuwa da shirme
Ameera tace to ba ita bace ke nenani
mom kuwa na kallon su sai murmushi take dan ita yaran nata burgeta sukey
"Ameera tace to shekara ta 13 years na kusa cike 14 years tana kallon ta,
Fatima tace kai nifa nadauka kinkai kamar 15 years din nan,
Ameera tace to kuma sai kiyi ai
Ameer ne yasauko tin daga sama yake jin surutun su yana saukowa yace kai wannan yara Allah yashirya ku, ku kennan sai shegen surutun tsiya. Yakare magana yana zama
......Fatima tace nifa yaya tambayar ta nayi nawane shekarun ta wai duk ma a 13years take ,tana kallon sa
Ameer yace to da jikike shekarun ta nawa ?
tace kamar 15years haka
murmushi yayi yace to haka ma ai tafiki da shekara uku
turo baki gaba tayi tace, tab injiwa wannan har zata fini
ganin fuskar Ameer a hade yasa tayi shuru bata idar ba ya tashi zai fita
Ameera tace yaya zanje tare dakai
Ameer yace a a wajan abokina zanje
Ameera tace haka nan ma zanje
mom tace kutafi mana tare
Ameer yace to shikenan sako shijab dinkin mutafi,
Tayi daki da gudu dan karma yamata wayo ya gudu a mota ta tarar dashi nan suka fita a gidan
Suna tafiya suna hira har suka isa wani gida mai gadi yabude musu suka shiga,
Ameera tafito shima fitowa yayi sukayi kofar gidan suka shiga "da sallama suka saka kai cikin falon
wata dattijuwar mace magani zaune a falon tana ganin ameer tace a awanake gani kamar ameer koda idona ne keyimin gizo
Murmushi Ameer yayi yana rike da hannun Ameera suka karaso har kasa suka durkusa suna gaisheta tace, lfy lau alhamdulillah ya maman ka yace lfy suna gaisheki tace "ina amsawa tace wannan mai kama da kai din fa ko ita ce wadda aka daura muku auren,
Cikin jin kunya yace eh mama itace