Showing 168001 words to 171000 words out of 175796 words

Chapter 57 - AMIR DA AMIRA Complete by Maman Nusaiba.txt

07 Aug 2025

3350

da akanta kizo ki karbi haihuwar

Doctor aisha tace ok ganinan zuwa ta kashe wayar

Ameer yace to yanzu zatazo kilama tana kusa

Ameera da har tasoma kuka tace to yaya kace tayi sauri please

Kallon ta yayi yace karki damu wife tana hanya

Zama sukayi jugum jugum suna zaman jiran doctor aisha

Da sauri tashigo ,Ameer ya mike yana fadin muje ga dakin cen

Doctor aisha tace yarinya ta jeki wajan ameera zan fito , Ikram kuka tasa da kyer ammi ta riketa sukayi gaba

Ameera ta bankawa ikram harara tace ke yimana shuru uwar yan rigima ana jimami ke kinawa mutane kuka

Ammi tace ba ruwanki da ita aiba ke aka bawa ita ba


Suna shiga ameer yafito ya nufi office dinsa ya kasa aikin sai tunanin yadda yaga jamila yakeyi sosai tabashi tausayi , ajiyar zuciya yasauke yace Allah yasaukeki lfy

Sunfi awa biyu tukun aka bude kofar wata nosee tafito da baby a hannun ta

Da sauri ameera ta amshe babyn tana fadin Alhamdulillah , mai muka samu ,murmishi doctor din tayi tace ansamu baby boy

Mikawa bilal babyn ameera tayi ,nan suka cika da farin ciki

Bilal yayiwa babyn k'uri da ido yana ganin yadda jaririn yake kama dashi

Ameera takira mommy tafada musu ,bilal ma anass ya kira yafada mishi

Ameera tace nosee ya jikin uwar ,Nosee tace tana cikin koshin lfy anjima zaku iya tafiya ,Ameera tace to Alhamdulillah

Doctor aisha tafito daga dakin tana murmishi ammi tace mungode sosai doctor aisha Allah yasaka da alkhairi

Murmishi ta kumayi tace ba komai ina yarinya ta kunsamu sabo kun manta min da yarinya


Yar dariya bilal yayi yace doctor kinganta nan fa zaune sai yaren yarabawa takeyi ni banma san mai take fadaba

Doctor aisha tace dama taya zaku sani yar mommy zomu tafi gida ,da murna ikram ta tashi tana rungume kafafun doctor aisha , daukarta tayi

Ameer ne yafito yace to har tafiya ce ,Doctor aisha tace eh zamu wuce sai munzo barka


Godiya sosai suka mata tukun ta tafi

Ameer ya rubuta mata sallama suka tafo gida cike da farin cikin samun k'aruwa , Ameera ta kira ikram tafada mata jamila ta haihu bazata zoba ,,da murna sosai ikram tace magana

Tace kai haba dan Allah baby kenan ta haihu to ganinan zuwa gidan nan ta kashe wayar


Kafin wani lokacin gidan jamila yacika da danginta da dana bilal dasu anty karima kowa ka ganshi sai murna sukeyi


Mai jego tana samun kulawa sosai tako wani bangare mommy tace ita zata mata wanka , sosai maman jamila taji dadin karamcin mommy , itama ammi dadi taji

Haka akaci gaba da kulawa da baby da mamanshi


Yau jamila kwanan ta shida da haihuwa hobe suna ,su umma yan kauye sunkoma gida , Ameera tace bayan sunan jamila zatazo kauye

Mato ce tashigo gidan su ameera bude kofar akayi fitowa yayi fuskar shi dauke da murmishi yasha shidda blue tasha zubin zare dinkin ya amshi jikinsa sai zuba kamshi yakeyi , wayarshi ya ciro a aljihu ya danna kiran bilal yana dauka yace bilal kafito nazo


Hajara ce ta fito sai waige waige takeyi kamar mai neman wani abu

Yana ganinta yace drama Queen iyayen rigima

Kuyowa tayi tana kallon shi wani sanyi taji zuciyar ta tayi dama tun dazun take ta tunanin shi sosai wankanshi yatafi da imaninta sai murmishi take


Yar dariya yayi yace drama Queen zo mana , wurga mishi harara tayi tace anki din

Murmishi yayi yace haba please kizo kinji , karasowa hajara tayi tace gani tana murguda baki

Dariya yayi yace yakike yasu umma

Dan sakin fuskar ta tayi tace lfy lau ina ikram karama bakuzo tareba ne, Muhammed yace no tana wajan mommy ta yau wayo na mata na gudo

Hajara tace ayya ,gyara murya yayi yace yauwa kanwata dama inason muyi magana dake Allah yasa zaki karbi maganar tawa hannu biyu

Murmishi hajara tayi tana addu'ar Allah yasa dai yacemata i love you , tace ina jinka

Yace kanwata tun ranar dana fara yin arba dake na kamu da tsananin kuanarki nakasa fadamiki sai yau Allah yasa dai wani bai rigani ba


Rufe fuska hajara tayi tana dariya zatayi magana ameer yashigo

Wajan su yayo ,yana fadin a a aboki yadai naga kasa kanwata jin kunya ,ai da sauri hajara ta rungume ameer tana dariya

Dagota yayi yace to maiyasa faru afadamin , Hajara na dariya tace yaya wai cewa yayi yana sona ni kuma kunya nakeji ,dariya ameer yayi yace to ke yakika gani kina sonshi ko

Sake rufe fuskar ta tayi tace eh yaya nima ina sonshi tana sakin ameer da nufi ciki da gudu

Ameer ya kalli Muhammed yace kai amma naji dadin wannan lamarin Allah yakaimu lokacin bikin insha Allah


Muhammed yace ameen nagode sosai ai bazanyi wasa ba ina zuwa zan fadawa mommy azo tambaya
Ameera yace hakan yayi gaskiya nan suka ahiga sashen su ameera dakin baki ameer yakaishi yayi waya aka kawo babyn


Addu'a sosai muhammed yawa yaron kafin yatafi gida



Yau take ranar suna tinda akayi sallar asuba ameera da tashi suka daura shinkafa da miya da kuma mai wake wasu suka daura tuwa da miyar kubewa , kafin karfe 8:00 am tayi sun gama komai


Gidan suka gyara aka saka turaren wuta nan da nan gidan yadau kamshi sosai ,Ameera ta koma sashenta doyin wanka


Jamila taci ado kamar sabuwar amarya tayi kyau sosai baby ma am mishi wanka da kaya masu kyau ajikinsa yana bacci


Ameera tace suma fans din 𝙖𝙢𝙚𝙚𝙧 𝙙𝙖 𝙖𝙢𝙚𝙚𝙧𝙖 baza'a barsu abaya ba ta dinka musu anko riga da sket wasu doguwar riga wasu riga da zani ,ko wacce tasha adonta


Ni kuma 𝙢𝙖𝙢𝙖𝙣 𝙣𝙪𝙨𝙮 baa min ba😔 sai dikin salla na nasaka abina na koma kauye na rakube saboda banida anko



Gidan suna yacika da yan uwa da abokan arziki ansha shagali sosai yarinya taci sunan ammi fa'iza bilal yace kar aboye mata suna a kirata da fa'iza ta


Haka akayi taro aka tashi lfy mommy tace jamila gidanta zataje babu muso iyayen jamila suka amince , nan aka hada musu kaya suka tafi gidan mommy

Haka akaci gaba da kula dasu jamila sosai kuma take jin dadin zamanta agidan


BAYAN KWANA BAKWAI


Yaune aka daure auren fauziya da yaya safiyan , akan sadaki naira dubu dari biyu abbu ne yabada sadakin ,Abba yace baza'a ayi wani shagali ba diner da walima kawai zaayi ,


Hakan kuwa akayi ba'ayi shagali sosai ba aka kaita gidanta dake unguwar kofar mazugal ,gidan ya tsaru sosai abba ne ya siyawa yaya safiyan gidan , sosai umma taji dadin wannan hadin kowa namusu fatan alkhairi agaresu , amarya fauziya Allah Allah yabda zaman lfy


Haka rayuwar su yacigaba da tafiya cikin kwanciyar hankali a ko wani gida , anje tambayar auren hajara da muhammed daddy yaji dadin sosai yace gaskiya ina farin ciki da wannan lamarin
Allah yabar zuminci


Amsawa sukayi sa ameen an saka ranar bikin wata biyu masu zuwa dangin muhammed suka koma gida suna yaba halin kirki irin na daddy




Wani dogon mutum ne ke tafiya a bakin hanya ,duk fuskar shi tacika da k'asunba ganin mutane na kallon shi yasaka shiramin kanshi ya rufe fuskar shi

Ameer ya fito daga wani shago yana sauri yaji an kira sunanshi waigawa yayi da sauri , zare ido yayi ganin wanda yake kiranshi yace......✍🏻




To kowaye wannan wanda ameer yagani ?


Idan kin karanta kidaure kiyi comments
[30/10, 19:29] MRS. MU'UTASIM: *🌟𝗔𝗠𝗘𝗘𝗥 𝗗𝗔 𝗔𝗠𝗘𝗘𝗥𝗔🌟*




*𝘴𝘵𝘰𝘳𝘺 𝘢𝘯𝘥 𝘸𝘳𝘪𝘵𝘪𝘯𝘨 𝘣𝘺*


*𝙈𝙖𝙢𝙖𝙣 𝙣𝙪𝙨𝙖𝙞𝙗𝙖 𝙘𝙚✍🏻*

💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️*


https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl

_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_

*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*

Wannan fagen na sadaukar ga k'ungiyarmu *JARUMAI WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️*


Bazan manta dakuba jarumai masu aiki da jarumta yan amana ta 💃🏼 ina yimkun sosai


Ummu shukhura

Umma amsad

Ummu julaibibi

Miss hajo

Fanan A.A.


Maryam Yusuf (ummu juwairiyah)

Mujaheedah

Lovely momma

Zarah tukur

Antyn muhsin

Zee sardoner

Kyauta daga Allah

Princess sayyada

Amina sulaiman

*Dadai sauran wanda ban ambata ba*





*THE END*


Da sauri ameer ya kalli inda aka kirashi zaro ido yayi yace kaine yana nunashi da hannu. Mutumin yace eh nine wllh sai yanzu Allah yayi na nasamu y'anci a duniya. Ameer yace wai bakai bane yaron aliyu na ganeka kaine wanda ameera tabani labarin ka taimaketa alokacin da aka saceta

Mutumin yace eh nine wllh ai nima agidan yari nake nataka sawun barawo,Ameer yace kamar yaya fa ?

Mutum yace lokacin da aka gama shari'arku nadawo gida natuba ina zaune abakin kofar gidana kawai naga jaka a gefena ban ankara a itaba saida naji anrufeni da duka ana cemin mugu azzalimi dan mafiya nace bansan komai ba amma basu yadda daniba in takaicema labari dai karata sukayi akace nine nake sace yara saboda jakar kan mutum ne aciki ,banida mafita dan babu wanda ya yadda dani sai matata hakan tasa aka yankemin hukuncin daurin rai da rai agidan yari ,dayake Allah maji rokone ya karbi addu'a ta yaji tausayina sai gashi anwanke ni daga zargin da akemin ankama mai lefin shine aka fiddoni nida aliyu shiya tafi gidansu ni kuma natafo gida na biyo nan ne danna siyo kaya nasaka shine na ganka nace bari namaka magana kozaka ganeni


Kallon ameer yakeyi cike da tausayin halin daya shiga yace ayya Allah sarki dan uwa gaskiya na tausaya maka Allah ya tsare gaba.Yace ameen

Laluma aljihunsa yayi yaciro bandir din kudi yabashi yace kaje kasiyi kayan kayi cefane saika aske gashi nan katafi gida Allah yakiyaye gaba

Murna sosai mutumin yayi yace nagode sosai dan uwa ameer gaskiya kai mutumin kirki ne ni sunana sulaiman ne

Murmishi ameer yayi yace eh na tuna yanzu ameera ta taba fadamin sunanka to sai anjima ,nan sukayi sallama kowa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login