Showing 3001 words to 6000 words out of 175796 words

Chapter 2 - AMIR DA AMIRA Complete by Maman Nusaiba.txt

07 Aug 2025

4536

kizoba saboda wannan shedaniyar jikar taki ta kakkarya mana jiki gata kamar kara amma sai shegen karfi kamar na doki

Inna ta hade kirar sama data kasa tace wllh a shirdinka karka kuma cewa jikata shedaniya dan ba karamin aiki na bane nayi tsukiya muci dambe awajan nan tana aika masa da harara

Mai gari yace dama ai nasan da haka ke kike daure mata gindi take fitsararta son ranta

Nan inna ta rufesu da ruwan masifa tace ba'a isa ya aibata mata jika ba

Su ameera kuwa suna gefe ita da kawar ta suna kwasar dariya harda rike ciki , Ameera tace Inna tace bazata bari a dakeni ba a
kofar mai gari

khadija tace aikuwa naga alama yanxu dai da dare zakije dandalin ne
ameera tace zanje mana

Ankawo mai gyara mai gari yace inna tabiya kudin gyara ko kuwa ayima su ameera bulala ashirin

Inna tace wllh baka isaba kace zaku zanemin yarinya , ta fiddo kudi dubu biyar ta watsa ma mai gari tace gashi nan anbiya to ko harara kamata saina sakata ta rama tace musu muje gida kunji suka kama hanya


Wata mota ce take shigowa layin sainaga tayi gidan su ameera ina lekawa naga wani mutum da bazai wuce shekara 47 yana dravin sai wani saurayi kyakyawan gaske wanda yake kamar sa da baban sa fari ne tas bazai wuce shekara 25 sai wani shan kamshi yake ameer kennan suna isa gidan yaran gidan suka fito suna ga baba na birni cikin fara'a baba na birni yafito yana dariya suka ce sannu da zuwa yace yauwa yarana nasameku lfy suka amsa a tare da lfy lau

Ameer ne ya fito daga motar ganin yaran yasa yasaki fuska nan sukayo kanshi suna yaya ameer sannu dazuwa yace yauwa kanne na nan sukayi sashen inna lokacin bata jima da dawowa daga kofar mai gari ba tana ta fada

ganin su ameer yasa ta washe baki tana lale barhabin mutanen birni suka shigo da sallama ta amsa musu ameera ce tafito da gudu tana cewa oyoyo baba taje rungume shi yana dariya yace a a kaga yar inna an girma

cuno baki gaba tayi tana shagwabe fuska tace Allah baba ban girma ba ni

yace to shikenan naji

Tana juyawa wa zata gani ameer aikuwa da sauri tayo wajan sa ya tsaya yana kallon ta yarinya har tayi saurin girma yana zancen zuciya yaji ta a jikinsa suka sauke ajiyar zuciya a tare

ta dago kanta ta marairaice fuska tace yaya ameer shine ka wani daure fuska ko bason zuwa garinmu kake ba

Sai lokacin yasaki fuska yace waya ce miki ai ina son zuwa sosai naga granny tsohuwa da ke dasu abba da umma

Ameera tace to na yadda yaya

Inna tace mai gida na ni manta ni kayi ne kodan kaga ameera ne,

Yace a wane ni hajiya inna mai duniya taya zan manta ki, dariya inna tayi tace to zo ga abinci da ruwa sadiya tayi girki irin naku yan birni

dariya yayi yace to suka zauna ameera na manne da ameer tana ta zuba mishi surutu shikuwa sai murmushi yake yi dan baya gajiya da surutun ta

Ameera tace daddy yau saida aka kaimu kara wajan mai gari

daddy yace kara kuma ?

Inna tayi caraf tace wllh kuwa Muhammadu wai ameera tabi wajan da gudu ta taka mai gari shine fa akace kona bada kudin gyara ko ayi mata bulala ashirin

Daddy yace ashirin fa,


Ameera tace eh

Ameer yace yanzu kun biya kudin

Inna tace nabada ai bazan bari a tabamin naman jikin ameera ba

...Ameer yace to shikenan nan suka ci gaba da cin abincin su suna hira cikin nishadi


12:30PM abba yadawo daga kasuwa yana shigowa yaga mota agidan yace a ashe Muhammad sunzo ya wuce sashensu yashiga su Ibrahim suka tarosa da oyoyo ya rungume su yayi


Suna dariya hajara tace abba daddy yazo

Abba yace ai naga motarsa a tsakar gida

Umma tayi masa sannu da zuwa ta cedasu su tafi dakinsu abba zaiyi wanka idan yagama shesuci abinci suka tashe da gudu suna murna .Umma tace muje abbansu kayi wanka kaci abinci kafin muhammad yashigo

Abba yace to yau kuma kodan oyoyo dinma babu, Umma tayi murmushi tace akwai mana amma sai anjima , abba yace to shikenan , matata yafice yana murmushin shima


Abban su Rashida ne yashigo shima gidan yaga mota yayi murmushi yace yau munyi baki ashe yayi sashensa yashiga da sallama yaran nasa suka tareshi suna abbu sannu da zuwa yace yauwa


Mama nana ce ta fito tasha waka ta kashe dauri ta iso wajan su tana yiwa abbu sannu da zuwa


Abbu yace yauwa yana kallon ta yace wannan duk ni aka yiwa ,

Mama nana tayi farr da ido tace sosai makuwa , yayi dariya yace aikuwa kinyi kyau sosai


tace ngd mai gidana nan suka shiga ciki

Ameer tinda yagama cin abinci yaja ameera kauye suka dasa hira yana kwasar dariya tana bashi labarin damben dasukeyi idan mutum yakawo mata reni tana ta zuba kamar kanyar data nuna

Ameera tace kaga yaya akwai wani da yake tareni idan zanje makaranta wai sai yake cewa yana sona ta shagwabe fuska

Ameer ya b'ata fuska yace ke kuma mai kika ce mishi


Ameera tace ai ni bana sonshi sbd k'azami ne ranar a makaranta koroshi akayi sbd kazantarshi baya wanka ga kafar da kaushi kamar bayan bishiya


Murmushi ameer yayi sai kallon ta yake yana ta sak'a da warwara da zuciyar shi

taci gaba da cewa kasan yaya wllh adamu dan iska ne tana dariya

Ameer yace kamar yaya ?

tace wani lokacine naganshi a dandali yana taba nan din budurwar sa ta nuna mishi kirjinta


Ameer ya zare ido


kwashe da dariya ameera tayi tace shine nida khadija mukayi sanda muka karyo bulala biyu muka shafa gawayi a fuskar mu muka saka mayafin inna da dare mukaje gidansu har dakinsa yana bacci,

Na tsula mishi bulala da sauri yatashi yana kallon mu yana cewa dan Allah kuyi hakuri ku kuke ganinmu bamu muke ganinku ba

khadija tace wato kaine dan iska mai taba jikin mata ko toyau zamu tafi barzagu da kai


.yana kerma yace waiyo Allah na shiga uku wllh bazan sake ba


ameera tace shiiii bamason kana daga sauti idan wani yajika to mutuwa zakayi

Adamu na zare ido baki na rawa yace nadena wllh bazan sake kama hannun wata ba inba matar dana aura ba


khadija tace ai kasan idan anje barzagu walakiri zaiyita jibgar ka,
Adamu saboda tsoro baisan lokacin daya saki fitsari ba

sarai ameera tagani tana dariya kasa kasa..Ameera tace yanzu abinda zakayi mu kyaleka shine kayi tsallen kwado guda dari saimu barka da ranka


ya fitoda ido waje yace dari kuma


Ameera ta hade rai tace eh haka nace idan kuma ba haka ba saimu tafi dakai

Cikin kaduwa da tashin hankali yace zanyi kuyi hakuri mutanen boye zanyi

khadija tace to soma yanayi harya gaji kuma suna zuba mishi bulala ga sunce idan yayi ihu mutanen gidan su suka fito shima yasan gabar ya rufe bakinsa da hannun sa saida suka miki dukan tsiya tukun sukace miki rufe idon tinda kayi biyayya zamu barka

Haka adamu jin ance za'a barshi sai ya ji dadi yace na rufe

Ameera tace idan kasake ka bude da wuri to zaka ganka a k'ungunmin daji mai kuraye


Da sauri yace bazan bude da wuri ba


nan suka fita da sond'a suna fita suka kama dariya,

khadija tace wllh ameera ke muguwa ce kinfini dukansa Ameera tace ai yabani haushi ne yadda yake tare yan mata yake taba musu kirji ko wani kalar iskan ci ne wannan oho?

khadija tayi dariya tace ai ya fitini kowa a garin nan yaudai munyi maganin dan banza

Suna tafiya a hanya wasu mutanen sun taho suna hira ameera tace khadija bari mu baiwa wadancen mutunen tsoro tace to

suka rakube a jikin wata bishiya suka saida mutanen suka tunkaro kawai suka fito fuska bak'i k'irin jiki kuma fari kamar fatalwa

Mutanen sukayi baya ameera ta makale murya ta juye hannu tace idan kuka kuskura kuka gudu to zaku mutu

Ai da sauri suka dunk'ule a waje daya suna mazurai suna kerma


......Ameera tace daga ina kuke ? wani acikinsu yace daga dandali muke shine muka taho gida

ameera tace kune marassa kunya har kuka tsaya har wannan lokacin baku dawo gidaba ko

nan suka soma cewa dan Allah kuyi hakuri bazamu sake zama dare ya mana ba awaje


khadija tayo kansu tana wani gurnani kamar wata aljanar gaske tace daga yau idan kuka sake bari dare yamuku to zamu tafi daku duniyar aljannu


Cikin tsoro sukace baza musake ba amana afuwa nan dai basuyi muguntar ba suka barsu suka tafi....


khadija tace bacci nakeji mutafi gida .....

Ameera ta dawo daga labarin da take baima, Yaya ameer shikuwa sai dariya yakeyi harda rike ciki yana jin mugunta irin tasu

ameera ita ma dariyar tayi tace amma yau zaka bini muje dandali ko yace sosai makuwa dan naga adamu

Dariya tayi tace zan nuna maka shi


*SHIN SU WANENE AMEER DA AMEERA*



Mlm shareef shine asalin baban su abba auren gidan aka musu shida matarsa maryam wato inna

Ahmed shine dansu na farko wato abba. Bayan shekara uku maryam tasake haihuwar namiji muhammad wato daddy na birni bayan shekara biyu tasake haihuwar wani namijin Abubakar wato abbu sai autar su Mufeeda ..Abba shi yafara gama makarantar sa yasoma kasuwanci yana da shekara 27 years suka hadu da sadiya wato umma nan suka saba da juna basu wani jima ba suka yi aure

Bayan aurensu da shekara uku muhammed yagama karatun sa yace shi birni zaikoma yaci gaba da karatu nan aka bashi dama mlm shareef yanada abokin a cen kano nan ya mishi waya yace mishi ga muhammad nan wato daddy na birni

yana karatun nan yar gidan wadda ake kira da fadila suka kulla soyayya aikuwa babanta yaji dadi nan da nan akayi auren su


sai Abubakar wato abbu shima yagama karatunsa ya kama kasuwanci Allah yadashi da nana yar cikin garin katsina suna fara soyayya babu bata lokaci aka musu aure



Abba yana yara hudu
safiyan
ameera
hajara
Ibrahim

Sai daddy na birni yana da yara uku

Ameer
Fauziya
Fatima autarsu


abbu kuwa yana da yara biyar

Rashida
Usman
Abdul rashid
Nasser
sai kausar auta


.....yanzu mlm shareef shekarar sa goma da rasuwa lokacin ameera tana yar shekara 2years ya rasu

*wannan kennan*



CIGABAN LABARI

Abbane da abbu da daddy na birni suka shigo sashen inna nan suka gaishe da inna ta amsa


Abbu yace inna dama munzo ta wata magana ne

Inna ta gyara zama tace to ina jinku

Sai abbu yace ameera da ameer ku je wajan umman ku na kiranku

nan suka mike suna fita abbu yajuyo kan inna yace,Inna munaso za'a daura auren 𝙖𝙢𝙚𝙚𝙧 𝙙𝙖 𝙖𝙢𝙚𝙚𝙧𝙖

Gobe saboda ta koma birni taci gaba da karatun ta acen

inna ta dago tana bankawa abbu harara tace....


TO ANAN ZAN DASA AYA SAI MUN HADU DAKU A GOBE INSHA AND kuyi comments da share ko like ngd🥰
[23/10, 09:25] MRS. MU'UTASIM: 🌟𝑨𝑴𝑬𝑬𝑹 𝑫𝑨 𝑨𝑴𝑬𝑬𝑬𝑹𝑨🌟


𝙎𝙏𝙤𝙧𝙮 𝙖𝙣𝙙 𝙬𝙧𝙞𝙩𝙞𝙣𝙜 𝙗𝙮



𝑴𝑨𝑴𝑨𝑵 𝑵𝑼𝑺𝑨𝑰𝑩𝑨 𝑪𝑬 ✍🏻





3


Inna tace amma kai kuwa bukari kazama mahaukaci taya zakace ameera yarinya da ita kace wai ayi mata aure


....Abbu yace inna bawai tarewa zayi ba za a daura auren ne idan takoma birni sai taci gaba da karatu tinda kinga sai ta zama likita da kike fatan zaman ta


Inna tayi jum kafin tace to shikenan na yadda tinda dan uwanta ne shi nasan zai kulamin da ameera

.....Cikin jin dadi abbu yace mungode
Allah yakara girma


tayi murmushi tana kallon diyan nata tace ku fada ma Mufeeda dai suka ce to nan suka fita daga sashen inna


Ameera kuwa tinda taja ameer suka fita ta kaishi wajan umma suka gaisa tana tambayar sa maman sa


Kasa yayi da kai yace suna gaishe ta nan dai suka fito suka nufi sashen mama


suka shiga mama tace a a ga mutanen birni isowa sukayi ya durkusa ya gaisheta

Mama ta amsa da fara'ar ta tana tambayar sa yan gidan yace lfy lau suke sunce agaishe ta

Su rashida ne suka fito daga ciki suna ga yaya ameer

Murmishi ameer yayi yace yan k'annan na

zama sukayi suna bashi labarin school yana dariya sun jima tukun suka fito


Waje suka fita ameera tace yaya kasan kawata khadija kuwa ?

Ameer yace a a ban santa ba


Tace to muje ku gaisa

Da yake yana son zaga garin yace ok muje

suna tafe suna hira har kofar gidansu khadija duk inda suka bi sai mutane sunce la kalli wani saurayi mai kyau kamar balarabe kuma suna kama da ameera


Ita kuwa babu ruwanta sai zuba zancen ta takeyi

......A hanya ne sukayi arangama da lado

aikuwa yayi kanta dama shi kullin da makamin sa yake yawo sbd karma ya hadu da ameera ta gudu


ameera na ganin lado ta labe a bayan ameer

Jin ta rikeshi yace menene ?

ameera tace yaya gashi nan zai dakeni

Ameer yace wanene da hannu tayi mishi nuni da inda lado ke tunkaro su


Lado yace yarinya wana kama dama nace miki duk lokacin da muka hadu saina karya miki kafa

Ameera na zare ido tace please yaya karka bari ya dakeni

Shikuwa ameer so yake yaga bakin kokarin lado

yana matsowa kusan su ameera ta kara kamkame yayan nata

ameer yace kai dakata cikin tsawa

Da sauri lado yaja birki ya tsaya

Ameer yace lfy ?

lado yace wannan yar iskan yarinya jiya saida suka yimin targade ita da kawar ta khadija yana nuna ameera data cakume ameer


Ameer yace to kayi hakuri nawa ne kudin gyara

......Lado yaji kudi saiya saki ransa yace raina dari biyar ne

Ameer ya ciro kudin a jakar sa yabasa yace karka sake koda ka ganta a wani wajan ka daketa

Cikin jindadi lado yace ai ranka ya dade bazan ma ko kallon taba bare duka


Ameer yace to shikenan tashi kaje nan yabar wajan


Ameer yace wai maiyasa ke bakijin magana ne kullin kina fada kamar baki gajiya

turo baki gaba tayi tace to yaya bashi bane yake zagina shine jiya muka rama

kunnan ta ya murde ta saki kara tace waiyo Allah yaya akwai zafi tana yarfa hannu

Harara ya aika mata yace ai daukeki zanyi mukoma birni kowa ma ya huta da wannan fadan naki


Da sauri ameera tace da gaske yaya tana tsalle

yace gobe kuwa zamu tafi nan ta kama murna suka yo gidan


Abba ne zaune shida umma yana fada mata shawarar dasuka yanke na hada auren ameer da ameera

Sosai umma tanuna farin cikin ta taji dadi dan ta gaji da wannan fitinar na ameera tace Allah yasa haka shine mafi alkhairi kaga idan ta kara girma saita tare kafin lokacin tayi hankali


Abba yace hakane kinga zataci gaba da karatun ta acen


Su Ibrahim ne suka shigo shida hajara na biye da shi suka haye kan cinyar abba

Ibrahim yace abba wai sai yaushe zan girma nima kamar yaya safiyan

Umma tayi dariya tace sai ka kara shekara ashirin

Ibrahim yace to umma yaushene gobe idan natashi daga bacci zanganni babba kamar malamin mu na school

Hajara tayi caraf tace hmmm dallah cen bakauye kawai waya cema gobe zaka girma kuma malamin school dinmu uncle mustapha kake hada kanka dashi wannan garjejen k'aton dashi ta karashe maganar tana cuno baki gaba


Ibrahim yace yarinya idan nazama babba jirgi zan siyawa umma da abba suke zuwa saudiya da Dubai

Hajara tace to sai kayi tayi ai yaro

Umma tace to ya isa haka kufice kuyi wanka duba kuga yadda kukayi da kayan jikinku

Ibrahim yace umma anty hajara ce tace muyi gini na kasa shine fa muka bata kayanmu


Hajara a masifance tace mai karya asaka mishi rigar fatalwa ya kwana yana bingel bingel

Abba yayi dariya sudai kullin sai shirme akama gardama nan suka fuce


Abbu ma gidan yanufa shima yafada ma mama cewa gobe za'a daura auren ameer da ameera

Itama ta nuna farin cikinta tace Allah yasanya alkhairi cikin farin ciki abbu yace ameen masoyiya

dariya tayi dan tasan mijin nata badai barkonci ba yace ni ina su rashida kuwa

Tace suna daki yace ok nan suka kama hirar su na miji da mata



Daddy masaukin su ya nufa nan ya tarda ameer da ameera suna ta zancen su yaji dadi dan kuwa yasan irin son da ameer yakewa kanwar tasa

Sallama yamusu suka amsa gaishe shi ameera tayi tace natafi

Daddy yace to yar gidan inna, nan ta fice abinta


Daddy yace ameer gobe zaa daura auren ka

A razane yadago yana kallon sa yace dad aure na kuma nidawa


Murmishi daddy yayi ganin yadda ya rude alokaci guda yace kaida ameera


Ai tuni ameer yasaki fuska yace to amma dad ai ameera

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login