Showing 18001 words to 21000 words out of 175796 words
Chapter 7 - AMIR DA AMIRA Complete by Maman Nusaiba.txt
to kuyi sauri kuci abincin mana
Kunya ce takama ameer ya juya,
Ita kuwa ameera so take yabata da kanshi , tayi kicin kicin,, da fuska kamar zatayi "'kuka
Daddy ya kula da hakan,, yace " daughter yadai ?
Kallon ameer tayi
Daddy yace,,, to kai ameer mai ka mata,?
Da mamaki yake kallon daddy yace wllh babu abinda namata ,,,
Ita kuwa ameera jin yace haka ,,,aikuwa sai hawaye suka soma zarya kan fuskar ta,,
Cikin damuwa mom tace ameera lfy ?
kuka ta saka
Ameer ya janyota jikinsa bako kunyar su dad da mom
saida tagama
Mom tasake tambayar ta wajan mommy takoma tana kwanciya kan kafadar mom bubuga bayanta ,,, take har ta dena kukan
dagowa tayi tace mom "amsawa tace da na'am daughter
,,Ameera tace bana son, surabani da yaya,,cikin kuka take maganar,
,ita kuwa abokiyar dramarta wato Fatima ,,itama tuni tasoma kuka,,saboda tana son ameera,, shiyasa data soma kuka itama tasoma nata kukan
Mommy tace waye zai rabaku nan ameera ta fada mata mafarkin da takeyi harda motar da take binsu kwana biyun nan,
Salati mom da dad suke,,kallon su suka maida ga ameer,
Dad yace son da gaske ne ana binku,,idan kunfita
Ameer yace eh daddy ,, amma bansan waye ba
Daddy yace,,,zankai,,report,,wajan yan sanda suke "' saka ido akanku,,, nan suka tashi ameera tayi sama
Anass ne ya kira abokin nasa ,,yace hello my friend
Dariya ameer yayi yace na'am ,yakake yace alhamdulillah,,, Ameer yace aboki inason ganinku inason muyi magana,,"wata matsala ce ta taso
Anass yace to shikenan,,nan sukayi sallama,,, haka yakira , Bilal yace zasuyi, magana "shima yace to ,,su hadu a gidan, su ameer
Yau sun fito,,, daga cikin aji Salim yace ameera wai jiya yaushe,,,kika dena kuka"" yana murmushi,, ya idar,, da maganar shi
Ameera tace ai nadena
Nafeesa tace wllh bestie jiya kinsaka mu,cikin damuwa, da harnace 'idan baki zoba zan je gidan ku,
Dariya tayi tace ' babu komai kada kudamu,,suna a haka direba yazo daukar ta nan sukayi sallama, ta yi wajan direban ta gaishe sa nan suka bar wajan
Su ameer da anass da bilal,,zauna suna gaisawa suka ce mishi ya akayi,,
Ajiyar zuciya ameer" yasauke yace wasu mutane ke bibiyar ,rayuwar mu
Atare sukace ,, what??
Anass yace suwaye ke binku ""
Bilal ma tashin hankali yashiga,yana tunanin to waye ke wa, abokin nasa barazana,,, da rayuwa,,,nan suka shiga jajantawa""
Suna nan ameera yashigo gidan a,, firgice,,sama tayo tana cewa,,yayaaa ina kake,,,waiyo ni ameera nashiga uku na,,tana kuka ,,ta haya samar,," kara kiran sunan sa tayi da cewa yayana,,shikenan sun daukemin shi ""
Da sauri ameer yayi falo jin tana sambatu,,,wajan ta yazo daga bayanta dafata yayi,,da sauri ta mike ganin ameer ne yasa tasake rufe idonta, dan tabbatar wa shi din ne dai da sauri ta zagaya inda yake ta rungume shi yana kuka, tace alhamdulillah Allah nagode maka daba'a sacemin,,,yaya ba
Tausayi tabashi,,yace menene ?
Sake shigewa tayi jikin sa,,
Su Bilal ne suka fito shikuwa Bilal ganin ameera yasa yaji sanyi aranshi dan yanzu ba karamin,,, so " yake mata ba sai kuma tabashi tausayi ganin yadda take kuka da gaske,,,
Anass yace aboki lfy wai,,,
Kallon sa ameer yayi da fuskar tausayi ,yace nima bansan me tagani ba najiyo muryar tadai,,tana cewa wai ta shiga uku ansace,,ni,,
Cikin damuwa Bilal yace ameera please maiya faru a school din ,,,
Dagowa tayi tana k'are musu kallo,, da tazo kan Bilal ta aika mishi harara ,,, dariya ma tabasu""murmushi sukayi yace to shikenan,,, fada mana kinji yar kanwarmu ajiyar zuciya ta sauke tace,,
Alokacin da muka taso daga,,school na fito bakin get ""sainaga wani,,mutum babba kamar irin na tv,,, yana kallo na sainaga yaciro waya,,, yana magana kasa kasa bansan mai yace,,ba na fice na siyo buskota na,, najuya kadan, "sainaji yace eh oga kaganta,,nan tafito amma wajan,,, akwai mutane sosai bazan iya sace taba,,, bansan ""mai na wayar yaceba sai,,yace oga saidai mubisu,,,abaya idan suhau,,, kan titi ,,saimu kwamushe ta kaga idan ameer yaga haka zai zo da kansa wajanmu saimu kashe shege ita kuma mukaiwa oga,, ko
Ban tsaya jin sauran ba maganar ba nayi sauri nacewa,,baba direba yayi,, sauri ""mutafi,, nan muka taho"" tinda mukayi nisa nake kiran wayar,,,ka baka dauka,,, hankali na ya tashi sbd bana,, samunka,, bamu jima ba mutanen nan,, suka biyo mu abaya nacewa,,baba binmu akeyi yakara gudu suma suka,,,gudu da sukaga haka shine suka harbi motar mu amma basu same,,mu ba,, ana haka cikin,, ikon Allah wata babbar mota tashiga tsakanin mu dasu,, shine baba yayi sauri muka karaso,,gida, takai karshe maganar. tana sake komawa jikin ameer tasaki wani,,, sabon kukan mai taba zuciyar mai karatu
Anass yace dole naje office nasaka yara na su binciko,, wannan mugayen mutanen
,Bilal ma yace nima zan tayaku bincike sosai sukayi,, ta alhinin,, lamarin tukun suka tafi gida har waje ameer yaraka su
Ameera na makale dashi wajan, baba direba yaje ya tambayesa abinda ameera tafada mishi haka shima yafada mishi duk abinda ameera tafada mishi
Komawa ciki dukayi sama sukayi don ya kwantar mata da hankali,,tadena damuwar
Koda su Bilal suka fita kowa da tunanin dayake sakawa a ransa Bilal na mamakin, waye wannan ke takurawa ameera,,
Shikuwa Anass tunanin yadda zasu bullowa lamarin,, yake (saboda,,shi, anass police ne kuma babba shine D,P, O a cikinsu )
Suna zuwa ya zaunar,,da ita ya dauko ruwa,, yabata tasha taji sanyi kuma,, kirjinta "yadena mata zafi ""kayan school din ya cire mata ya cire takalman,,, tukun ya sauya mata wasu toilet yayi,, yahada mata ruwa,,, yace tashi kije,,,kiyi wanka tashi ""tayi, taga ya zauna tace muje kayimin,,,
Ameer yace to nan sukayi toilet,,, bayan sun fito,, bata jimaba bacci yadauke ta shikuwa zama yayi,,yana kallon ta cike da so,, da kauna dakuma tausayin,,halin da take ciki,,
Ameer ne yasamu daddy da zancen abinda ameera ta fada miki "da kuma tashin hankalin, data shiga ,,
Damuwa ce kwance,, akan fuska daddy and mom,,
mommy tace wai ni na rasa,, waye yake,, neman rabaku da nutsuwar ku,
,daddy yace,, ai yanzu na kira Anass nake fada,, mishi nan ya shedamin,, cewa,,suna nan lokacin da ameera tashigo,, gida a firgice,,
Mom tace ina take ameer yace tana sama,, basu rufe baki ba ta sauko fuskar nan ta kunbura,, idon ta yayi ja saboda kuka
Mommy tace zonan daughter
Ahankali taje wajan,,mommy tasaki kuka tace mom wai mai muka musu ne suke damun rayuwar mu,,
Rarrashin ta ' mom take saida tayi shuru
mom tace kiyi shuru ai yanzu mun sanar wa da yan sanda komai insha Allah babu abinda zai faru
Da dare bayan anci abinci to dama gobe ba school suma,, su fatima da fauziya,, sunji ""komai gashi ameera takasa cin abinci sai kuka duk inda ameer yayi tana,, makale da shi kowa agidan yana cikin damuwa,,,
Cen fatima ta je wajan ameer tace yaya ahankali dan kar ajita tace yanzu zan saka anty ameera farin ciki,,
ya kalle ta yace to tayaya fatima ?,
Tace kaidai bari kagani,, idan kaga ta warware,, to kace muyi kafce irin film kai zaka dauke mune a wayar ka,,, murmushi yayi yace to
Duk abinda sukeyi,,su mom najinsu "'kuma sunji dadi da fatima zata saka ameera farin ciki,,,
Fatima taje daf,,da ameera tace antyna wai kin manta gobe,, week ne kin manta ""da damben mu
Tashi ameera tayi kowa kallon ta yake tace kinga na manta to gobe mai zamuyi idan mukazo yin damben
Dariya,,Fatima tayi tace ""yanzu zamu soma ne
Ameera tace,,da gaske
Fatima tace eh yau kafcen film zamuyi nice matar gida,,, kece mijin "'
Dariya tayi,, tace to shikenan amma na kauye zamuyi
ganin tana dariya yasa ameer cewa,, eh a kafta mana,, na kauye suma su mom sukace eh,, muna so
Ameera taje dakin su fatima ""da dauko kayan kwalli tayiwa fatima,, itama tayi,, na kauye ""
Su fatima ansha bakin baki da wata gira kamar zamiyar zakara,,
Dariya duka falon sukeyi
Ameer yafiddo wayar shi yace idan na kirga uku saiku soma sukace to,, nan yace,, daya ""biyu ""ukku...
Ameera ce ta nada wani mayafin ta akai wato alamar malam,,
ita kuwa Fatima ta yafa wani zani itace matar gidan zama tayi tana daukar kwanon gabanta tace,,
Kai nima Allah yahadani da miji mai shegen rowa,,, kalli fa wannan dan amincin ,, to ko ni bazai,, isa ba na koshi,, bare yaran nan da suke ""dab da dawowa ""daga islamiya,
Ameera ce ta bude ta fito daga inda ta rufe kanta da labule,,tayi gyaran murya,,,
Fatima ta banka mata,, harara,, tace haba malam wai ni kai wani irin wulakanci ne wannan,,
Ameera ta kalli fatima tace, ban gane ba kefa Wllh jummala bakida godiyar,,,Allah kullin sai kinyi masifa duk makota na jinki sai zaginki,,,ake yi a anguwa
Mikewa Fatima tayi tayi tsukiya da zanin data yi lullubi dashi,,,tana jijjiga tace,
Iyee to sannu malam nace sannu bakin munafuki,,,algungumi kennan zuwa,, kake kana bazani "a gari ko to wllh yau bamai rabamu nidakai
Ameera tace,,kinji dai dashi masifaffiyar,,, mata kawai kullin idan zan shigo gida har gabana faduwa yake yi saboda fitinarki,,
Fatima tace to,, baka isa kaci abinci agidan ba
Ameera tace wannan kuma ya rage naki,, sakarya kawai,, aure ma zan kara na huta dake,,
Fatima ta cakumi rigar ameera ,, tace wllh kayi kadan baka isaba,, kayi min kishiya...
Dariya suka kwashe ,, dashi har su mom da dad fauziya kuwa dama ba'a magana
Ameer ne,,, yace wannan kafce yayi kuzo mugani nan aka zauna gani sai dariya sukeyi,, hamdala kowa,, yayi "' ganin ameera ta dena damuwa
Hhhh bari dai na hau mota naje na gano hajiya inna ikon Allah,,
Inna ce zaune ita da abbu sai fada take kamar ba gobe ,, tace bukari,,wllh kakaini kano yau ko na tafi dakaina,,
Abbu yace kiyi hakuri inna ai ameera takusa zuwa hutu,,, fir inna tace batasan zancen ba
Umma dataji taje bata baki tass,, ta wake ta da ruwan masifa tace wai ni sadiya wllh daba a hannuna kika haifi ameera ba sainace bake ce uwar ba,, yoto inba shirme ma ba hadda zuwa bani baki to bazan jiba
Abbu ya ce to inna fito mutafi da murna taje ta musu sallama hajara ma tace saita je
Inna tace yauwa zo mutafi ba yadda umma ta iya tabar hajara suka tafi sai kano tadabo....
MUHADU a gobe insha Allah domin taryar hajiya inna zata je birni
Kuyi comments da share
[26/10, 20:11] MRS. MU'UTASIM: 🌟𝐀𝐌𝐄𝐄𝐑 𝐃𝐀 𝐀𝐌𝐄𝐄𝐑𝐀 🌟
𝙎𝙩𝙤𝙧𝙮 𝙖𝙣𝙙 𝙬𝙧𝙞𝙩𝙞𝙣𝙜 𝙗𝙮
𝐌𝐀𝐌𝐀𝐍 𝐍𝐔𝐒𝐀𝐈𝐁𝐀 𝐂𝐄✍🏻
15—16
Daddy ne,,,zaune shida mom sauran yan gidan duk suna daki "" Abbu ne ya kira daddy,,,a waya yana,,shida mishi zuwan"" hajiya inna,, murmushi daddy yayi yace ,, eh lalle Abubakar ""kace yau munada manya,, baki agidan nan" dariya shima abbu yayi yace wllh tinda,,, su ameera suka "" koma kullin inna saita zageni tass 'tace naje nakawo mata diyar ta wai munsiyar ,, mata jika
Dariya daddy "" yayi yace,,,to muna kallon hanya bari mutanadi tuwo da miyar"" saboda kar a sauke mana gajiyar,,hanya, ahaka sukayi sallama
Su ameera kuwa,,ana kurya "adaki sai dariya take saboda video su na jiya da suke kallo,, ita da ameer ,,,tace yaya , kallon ta yayi ya mata murmushi,,, tace wllh video nan yaban nishadi,,, musamman ma "" inda fatima take cewa wai ban isaba na mata kishiya
Shima dariyar yayi dan yaji dadin ganin yadda take cikin jin dadi ,,, yace nikuwa kinsan ina yake bar dariya,,, tace a a ""yace inda kike cewa fatima masifaffiyar mata kawai,, aure ma zan kara na huta,, da masifar ki ""
Dariya sukayi a tare ,,, kiran wayar shi ne ya katse musu hirar dasuke ,,, ganin mom ne yasa yayi saurin tashi daga kwanciyar da suke ,, ita kuwa mage lafewa tayi ajikin sa dan ita dai,,, a rayuwar ta tanason"" kwanciya,, a jikin ""yayan nata,, kuma mijin ta,,
Ameer yace, hello mom sai kuma yace, batayi ba,,, yace ok gamunan,, sauka,, nan yakashe "" kallon shi tayi tace yaya wanene,, yake kiran ka ,, kumatun,, ta yaja yace "my wife mom tace mu sauka zata mana albishir, mai dadi da sauri ta mike tace to muje yaya nan suka sauka
Anass ne zaune,, a office yana tunanin ""ta ina zai fara wannan bincike,, kofar ce aka,, buga "" nan yace yes come in ,, wani dan sanda,,, ne yashigo"" yace good morning sir,, amsawa yayi da morning "
Anass ya tsuke fuska kamar bai taba dariya ba yace ;,, ishaq, ina son ka binciko min sashen Camara bakin babban titin,, dazai sadaka da unguwar nasarawa J. R.A. yace yes sir ya kame,, tukun yabar wajan
Hajiya inna ikon kennan,,kakar, *AMEER DA AMEERA*,,, ankaraso kano""ta dabo ,, sai raba ido take,, tace kai "" Rabe to amma,, dai baka kaine gidan Muhammadu,, din ba ko
Murmushi ,, rabe yayi yace kai inda kin ,, cika surutu,, ai gamu a anguwa,, mun zo gidan ne "' dai bamu karasowa,
caraf inna ta,, amshe zancen,, da cewa ""saidai in uwarka ce ladidi,, mai surutu,, gaka nan kagirma "kazama gardi ba ,, aure ai wllh su ladidin su suka kyaleka,, yoto,, dama wacce '" yarinya zata soka a haka garjejen basamude,, ai dole ""mata suke tsoronka,,, dan iska,, marar mutumci,,,wllh yanzu ""sai infita,, in kakkarya maka,, kafafu,, hadda cewa,, wai nacika,, surutu,,,
Shikuwa ""dariya yakewa inna wai shi, zata karya,, hadda kiransa,, da basamude, kai tsohuwan,, tacika neman masifa,,
Suna zuwa wajan,, mom suka zauna a falo ""nan mom take sheda musu,, cewa inna tana hanya ""dan har ta saka mai aikinsu tayi Mata,,tuwo da miya ,, aikuwa ameera kamar tayi waje ta taro inna haka take ji
Shikuwa ameer bata fuska yayi sbd yasan halin inna yanzu nan zata ce ameera awajan ta zatake kwana shikuma bazai iya kwana a daki ba batare da ameera
Karar mota ne yasa,,Fatima da ameera fitowa,,, da gudu domin tarbar inna,,,ita kuwa inna fitowa tayi tana karewa gidan kallo nan sukayo kanta, suna oyoyo granny,, kallon su tayi taga Fatima da ameera ,, itama murna tayi ""na ganin ameera nan sukayi cikin gidan da sallama suka shiga ciki,,
Mom ce ta tashi tana yiwa inna sannu dazuwa nan aka kai kayan inna dakinsu,, fatima ta hada mata ruwan wanka
Bayan tayi wanka ne ta zo falo daddy yafito yana,,murnar ganin inna,,""Inna tace ai nadauka siyar min da jika kukayi,,ashe tana nan lfy
Dariya sukayi"'ita kuwa ameera tana zaune kusa da inna sai dariya take tace kai inna nafa ce miki,, babu wanda yasiyar dani ina nan
Ameer ne yashigo yace ,, kaka sannu da zuwa tace yauwa ameeru
Bata,, fuska yayi yace haba inna ""meye kuma ameeru
Harara ta aika