Showing 144001 words to 147000 words out of 175796 words
Chapter 49 - AMIR DA AMIRA Complete by Maman Nusaiba.txt
yaran albarka , Ikram dama ita so take yace tazo da dan gudun su suka nufi ameer
Saukowa yayi daga kan kujerar , y durkusa ,, bude musu hannu yayi suka shige jikin sa,, Ikram tace daddy cike da murna ameer yace na'am my daughter ,, na ashe dai ,, ke jinina ce shiyasa ganin farko " kika makale min , nima kamar na sace ta naji ,a lokacin ashe jinina ce
Doctor aisha tace ,, haba koda naji fa yarinya daga ganinka ,,taki yarda ku rabu ashe ita dumin babanta taji
Sakinsu yayi yace kuje mommy na kiranku ,, wajan mommy muhammed ,, yayi yana dariya ganin suma dariyar sukeyi , Ikram ko tana jikin ameer , ko matsi batayi ba " itadai ,daga anjima tace daddy shikuwa ,, Ameer yabiye mata sai yaketa amsawa
Daukar muhammed mommy tayi , tana fadin mai gida oyoyo ,,nan kowa yayi ta daukarshi ,, Ikram kuwa ko kallon inda suke bata yiba ,, tayi kwanciyar ta , jikin babanta ,, duk wanda yace zo ikram "" bata fuska takeyi tace daddy ta dago ta kalli ameer ,, shafa kanta yake yace daughter ,,kwanta abinki " idan kika huta sun ganki
Hajara ko murna kamar tayi rawa haka takeji sai rungume ,ameera takeyi tana shafa fuskar ta
Murmishi ameera tayi tace , to mage ashe dai baki dena son jiki ba ,, yar dariya hajara tayi tace ,ai kinfini ingaya miki ,
Doctor aisha ce ta kalli ikram tace babyn mommy zo mutafi mana kinsan anbani rikonki " tin kina jaririya to yanzu munzo gun babanki ban saniba kozai banike
Murmishi ameer yayi , yace ai indai nine " bakida matsala ,,dago da ikram yayi yace daughter , maza jeki wajan kaka ,
Kallon shi tayi zatayi kuka muhammed ,, yace babyn mommy ,,zo nan juyowa tayi,, ganin muhammed ne yasa ta sauka daga kan ameer ta tafi inda muhammed yake,, tace daddy , daukarta yayi yace kinga mommy na kallon ki maza jeki wajan ta , mikawa doctor aisha hannu tayi " daukar tayi ta rungume tana shafa kanta har bacci ya dauketa ,
Baba laraba ce tashigo gidan ,da sallama daga,, kasuwa take ,niki niki da kaya ganin falon cike da mutane,, tace sannunku baki , ,, dagowa tayi zata wuce bazata ga ", da sauri ajiye kayan hannun ta ,, tace hajiya koda gizon ne dana saba yi ameera nake gani ", mommy tace babu gizo itace
Wulli baba laraba tayi da c, kayan hannun ta ta nufi ,Ameer tana kuka ,,, itama ameera mikewa " ta taro baba laraba , rungume ta sosai
Baba laraba tace ya'ta kece ashe , ba gizo bane ashe zan sake, ganinki yar lelen ameer ' waiyo Allah Alhamdulillah ,
Share hawaye ameera tayi , tace nice baba laraba " gani nadawo gareku ba mutuwa nayi ba ,,, ina raye
Sakinta baba laraba tayi, tana dariya sosai najin dadin dawowar " Ameera cikinsu ,, mommy tace baba laraba ki mana girki dayawa ga hajara ,nan zata tayaki da fauziya " Baba laraba tace to hajiya nan tayi kitchen din don , daura girkin
Daddy ne ya kalli ,, Inna yace inna ashe dai ameera tana wajan danginta ,, to amma daughter ya akayi suka tsince ki , keda kukayi accident ,a kan hanyar ku ta zuwa nan
Zama ameera ta gyara , tace daddy lokacin da motar mu , tashiga dajin dake gefen titi , kawai gangara wa nake ina daga kwance , wata bishiya " na buga daga bansan inda nake ba, ashe lokacin dana buga kaina cikin wani kogin dake " gindin bishiyar na fada yayi ta tafiya dani har kogin su yaya umar na bayan gari " anan ya tsinceni ,,,da farko sun dauka ni anty karima ce " saboda na manta komai na rayuwa ta na baya , shiyasa saida " nadawo haiyacina , tukun nace bani bace karima ,, nan ta kwashe labarin komai tabasu har cututtukan datashayi ,, da sokar ta da akayi da wuka " da mutanen garin da sunfi rabi duk sun musulinta ,
Su mommy sai kuka ,, suke jin abubuwan da ameera ta fuskanta , amma Alhamdulillah tinda har mutanen garin sun musulinta , kadan ne basu musulinta ba
Sake rungume ta , Inna tayi tace Alhamdulillah jikata Allah yakara daukaka musulinci akan kafirci , ashe kece hasken ahalina , Allahu akbar Allah mai girma Allah Allah yakarawa annabi daraja s.a.w. ,,,, yan falon sukace ameen
Mommy tace inna zamuso ,, kibamu tarishin ku na rayuwar ku dakukayi a baya kuma ya akayi kuka baro garinku kuka dawo jahar katsina ,,da zama
Zama inna ta gyara tace , kozan baku labarina ,, sai kowa yazo dan kowa yaji ni da babanku suwaye mu
Da sallama tashigo falon ,,hijab din a hannu har dan kwalinta ,, tana fadin babyn momsy baby ina kike
Kowa kallon ta yake cike da tausayin yadda take kuke
Da gudu ameera , ta nufi ikram tana " fadin waiyo momsy na ,, momsy na rungume juna sukayi ikram ta rungume ameera sosai ,, saida suka jima sosai , a haka kafin suka zauna
Ameera tace momsy na , waya fada miki ,, nazo " Ikram tace Fatima ta kirani , ta fadamin wai nazo kindawo , kamar almara " naji kawai nace bari nazo nasan fatima ,, bazata min wasa ba ashe da gaske ne,,, baby ina kike a wannan tsayin lokacin ,,,, Ameera ta bata labari bayan accident din su " sosai ikram tayi kukan tausayin ameera ,, ta kumayi madallah da Allah Allah yasa , mutane da dama sun musulinta , taji dadi sosai
Ameera tace , Momsy ina kannuwa na
Murmishi ikram tayi tace , gasunan a kusanki
Juyowa ameera tayi ,, tace kai momsy haka takwara da mijina suka girma " masha Allah kuzo nan kannuwa na ,, wajan ameera sukazo ta zauna dasu a gefenta ,, tace kusanni
Ameer yayi caraf yace mommy kullin ,, tana dauko photonki sai take kuka tana kallon photon ,, tace ke sister dinmu ce
Murmishi tayi tace eh kunga,, gani nadawo nice sister dinku ,, takwara bakiyin magana ta kalli ameera
Turo baki ameera tayi ,,tace anty meyasa ,, Ameer yayi magana ni banyi yake ta magana ,,, murmishi ameera tayi tace , haba yar kanwata ai yanzu tare zamuje yawo dake ,,, fuskanta tasaki tace da gaske anty "" Ameera tace sosai makuwa
Ikram tace baby , cikin jikin ki ,, ko zubewa yayi " ??
Yar dariya ameera tayi tace gasucen mai sunanki ,, da mai sunan daddy na
Da sauri ikram tace , ina take mai sunan nawa " doctor aisha tace gata nan bacci takeyi tana mikawa " Ikram ,,yarinyar , amsa tayi tana Allah sarki yaran albarka ,, Muhammed , ya karaso wansu shima ikram ta hadasu ta rungume , sosai
Su jamila ne suka shigo da gidan da cikin ta da kyer take jan kafa ,, Ameera na ganinsu ta mike tana fadin anty jamila , itama , jamila dariya take hade da kuka tana fadin kanwata kece ashe zan sake ganinki , a rayuwa ta ,, kamata ameera tayi takaita kan kujera taimaka mata , tayi suka zauna " Jamila ta rungume ameera tana fadin Alhamdulillah " ashedai kina raye kanwata munyi kukan rashinki ,, a tare damu , yanzu gashi kindawo garemu Alhamdulillah
Murmishi ameera tayi tace ,, kina gani anty jamila , ga yaranki nan tana nuna mata muhammed da ikram
Sosai jamila tayi murna ganin yaran nan tayita rungume su ikram ko dama bacci takeyi
Hira sukeyi sosai ,, yaudai wannan family kana ganinsu kasan suna cikin farin ciki sosai hakan ,, ya nuna a fuskokinsu dama zuciyoyinsu ,, bayan sallar azuhar , aka gama girki daddy yakai ,, mazan sashen baki matan kuma suna zauna a falo " aka fara cin abinci bayan angama cin abinci ,, doctor aisha tace zasu tafi gidan sister dinta
Mommy tace ta tsaya su zauna anan amma tace a a zasu dawo gobe in ana son ganin ikram ,zata kawota
Ikram tace naso abani takwara amma tinda ke kika dauka duk dayane
Doctor aisha tace Allah Allah yasaka da alkhairi wllh harna fara fargabar ,, zaku kwacemin ,Ikram yarinya tashiga rena sosai shiyasa tin acen nace abani ita
Murmishi mommy tayi tace , ai bakomai da nakowa ne indai ikram karama ce munbaki ita har abada
Sosai doctor aisha taji dadi harda hawayen ta na jin dadin amvata ikram dama batada mace muhammed ,, shi kadaine danta , shiyasa ta kwallafa rai akan ikram , Sallama suka musu sukatafi ,
Daddy na murna yace bari na kira yaya Ahmed da Abubakar ,, na fada musu dawowar daughter ,,nan ya yadanna kiran abba ,, tana ringing daya yadauka " da sallama ,, amsawa yayi suka gaisa kafin ,yake sheda mishi ameera ta dawo kuma da alhalin inna da baffa
Abba yace kai nuhammed nasan dai bakamin irin wannan wasan,, da gaske ne
Daddy yace wllh yaya da gaske yaba ameera wayar
Jin muryar ameera yayi yace abbana nice gani Allah yadawo dani gida,, Abba kace kaga sister din inna da anty karima mai kama dani
Abba sujjadar godiya ga Allah yayi tana tasbihi ga Allah ,, dake jin komai itama hamdala tayi ,, sosai suka shiga farin ciki , abba yace gasunan gobe insha Allah
Yana kashewa ya fadawa abbu sosai gidan yacika da farin cikin dawowar ameera kowa ya matsu gobe tayi dan yaje yaga ameera ,, Khadija ko baa magana kusan kwana tayi a zaune
Washe gari