Showing 171001 words to 174000 words out of 175796 words

Chapter 58 - AMIR DA AMIRA Complete by Maman Nusaiba.txt

07 Aug 2025

4523

yatafi

Ameera na zaune sai cika take tana batsewa saboda ameer yaki dawowa da wuri kuma gashi ba kowa muhammed dinma yana wajan mommy tace a wajanta zai zauna

Da sallama yashigo amsa mishi tayi tana kauda kanta gefe , murmishi ameer yayi dan yasan ta zauna zaman jirane

Zama yayi kusa da ita yace wifey na bako sannu da zuwa ma ,banza ta mishi tana aika mishi da harara

Yace wifey kinsan meya hanani zuwa da wuri ? Nan ma shareshi tayi yana karkada kafa sai wani cin magani takeyi

Dariya ma tashi amma saiya danne yace yau na hadu da wannan mutumin daya taimakeki lokacin da aliyu ya daceki nan yabata labarin da sulaiman yabashi


Da sauri ta juyo tana murmishi tace Allah Allah sarki shima kaddara tafada mishi to Alhamdulillah tinda yafito anwanke shi daga zargin da akemishi

Murmishi yayi yace a wifey iyayen masifa koda yake anyo gado ba karanbani ba abin ajinin ki yake

Filow ta dauka ta wurgo mishi , da sauri ya cafe yana dariya yace kefa dadina dake idan gadon hajiya inna mai duniya yatashi saifa a hankali

Kuka ameera tasaka tana dira kafa gefe ta kalla aikuwa ta wata sanda yar siririya mai tsayi dauka tayi tana fadin ni kake cewa mai masifa wllh saina zaneka kuma sainayi yaji naje wajan inna , tana bishi da gudu


Biye mata yayi suka ringa zaga falon tana kuka tana magana fadi take saifa tayi yaji taje wajan inna ko saitayi shekara

Shikuwa ameer dariya yake mata , yace ai indai nine bazaki kamoni niba sai kin gajiyar da kanki tukun na tsaya


Haka suka ringa zagaye falon saida ameera tagaji sosai faduwa tayi a kasa tana sakin sabon kuka , tsayawa ameer yayi ya koma inda take ya dagota
Kamar jira takeyi dama tashige jikinsa tana kaimai duka a kafada


Daukarta yayi suka zauna yace haba wifey wai duk kukan nan na miye daga magana yana kunshe dariyar shi dan yau ya lura yan rigimar ne akusa


Sake shigewa tayi jikinsa tana shakar kamshin turansa mai sakata jin dadi tace ba kaine ba kake demin nayo gadon masifa , bubbuga bayanta yayi yace to kiyi hakuri muje natayaki girki yunwa nakeji fa

Dagowa tayi tana dariya ta mike daga jikinsa tace yauwa muje nima ita nakeji

A tare suka jera zuwa kitchen , jollof suka daura ameera na fata kwanika ameer yana wankewa bayan ta hada komai kafin yagama wanke kayan data bata ta goge saman da ajiye kayan tana daurayewa suka fito falo ameer yafara zama ameera ta haye cinyarsa tana dariya , hancinta yaja yace badai son jikiba to kwanta ko .kwanciya tayi nan sukaci gaba da hira




Yau anass yazo ganin fatima da baby iman a falo ya zauna mommy tashigo ganin anass tace a a lale da dan sanda abokin kowa

Kasa dakai anass yayi ya durkusa yace mommy ina yini nasameku lfy

Amsawa mommy tayi ds lfy yasu ammi naka ,Anass yace suna lfy tace na gaisheku

Mommy tace ina amsawa nan takoma dakinta

Fatima ce ta karaso falon da baby iman a hannun ta ,Anass yamike ya amso iman suka zauna tare

Kallon shi fatima tayi tace sweetheart yanaga karame ko bakada lfy ne

Fuskar tausayi yayi yace ba gyara rashin lfy ba da wannan azabar da ake ganamin, dafe kirji fatima tayi tace nashiga uku azaba kuma sweetheart wayake gana maka azaba

Anass yace ke mana kinki komawa gida kullin ni daya nake kwana babu mai bani abinci abaki bamai shiryani idan zanje office bamai tararraya ta idan nadawo daga aiki komai ninake ai dole na rame

Ajiyar zuciya fatima tasauke tace wllh nadauka wani abunne yasameka, Anass yace awoo bakima damuba kenan ko

Fatima tayi saurin fadin ba haka nake nufi ba ai gobe zamu ko ma nina daukama daukata kazoyi


Washe baki anass yayi yace kai haba nifa wllh na manta kawanan ku nawa agidan nan ashe gobe zaku koma amma naji dadi

Murmishi fatima tayi tace eh insha Allah


Daga bayansu sukayi ana fadin innalillahi wa inna ilaihin raju'un yauga yan iskan yara nizaku maida sakarya , a ni maryama yanzu ke fadimatu baki da kunya ashe kema wannan dununun ya koya mishi rashin kunya to wllh baku isaba

Kai dan sandar uba waye yace kazo shine ka lallabo ka lalubeta ko to kafita a idona bazata koma ba sai yarta tayi kwari tukun

Wato ku ga futsararru ku to zakuga abinda zanyi

Anass dake dariya yace dama nasan za'a rina hajiya inna ai nazo da maganin ki , ledar hannun shi ya mikawa inna yace innar baffa ga kaji da lemo da goro na kawo mishi

Ai da sauri inna ta karba tana washe hakora tabude kazar tagani gashashiya har biyu da goron ta ga lemo a gefe ,dagowa tayi tana kallon shi tace a a yaron kirki nagode sosai , kasan gobe ne fadimatu zata koma bari natafi dakina nan ta wuce

Dariya sukayi fatima tace a sweetheart yau kayi maganin inna anrufe bakin

Murmishi yayi yace aikuwa dan tabamu gurine

Washe gari
Aka kai fatima gidanta da babyn ta iman anass kamar zai maidasu ciki hakaa yakeji sai nan nan yakeyi dasu


Yaune su karima zasu koma garinsu anhada musu goma ta arziki su daddy zasu kaisu airport idan sunsamu lokaci zasuke zuwa ziyara kowa yazo za'a tafi rakiya zuwa airport


Ameera na saurin saka rigarta ameer yashigo yace wifey kefa nake jira sun shirya mu ake jira nace su wuce zamu samesu a airport din
Ameera tace to muje nagama tana saka hijab din ta ya saka mata takalmi nan suka fito sai airport

Suna zuwa suka angosu wajansu suka nufa karima na ganin ameera da sauri ta rungume ta

Aikuwa ameera taringa kuka , Karima dinma na tayata

Mama tace to kukan ya isa haka jirgi yace ansoma kira

Sakin juna sukayi amma ameera ta rike hannun karima gam

Abubaka da mufeeda da suka matso kusan su ameera

Mufeeda tace mommy aimu babu inda zamuje muna tare take ko abubakar ? ta juya da tambayar shi

Yace eh muna nan bazamu je dasu daddy ba

Da sauri ameera ta saki hannun karima ta rungume su mufeeda tana kuka hade da dariya

Dariya su fatima ke mata ,,Jamila tace a ni y'asu ameera wannan kuka kamar ance bazaki sake ganin anty karima dasu mama ba

Murmishi baban karima yayi yace jikata kiyi hakuri zamu sake dawowa bikin hajara zamuje mu daura daga inda kuka tsaya ne

Shara hawayen ta tayi tace to shikenan kakana nadena nima zanje wani lokacin bayan bikin hajara insha Allah

Umar yace to yaya Muhammed yaranka sunce anan zasu zauna gasunan munbaku su har abada

Wani farin ciki mommy da daddy sukaji inna kuwa kuka tasaka tana fadin Allahu akbar jikona jinina

Dariya umar yayi yace inna ke nabawa mufeeda yaya muhammed kuma abubakar , rungume shi inna tayi tana saka mishi albarka

haka suka tafi shiga jirgin sukayi suna daga musu hannu har jirgin ya tashi sama saida suka bacewa ganinsu tukun kowa yashiga mota
Inna takama hannun mufeeda tace zo nan ya'ta zaki maye gurbin ameera ta
Mufeeda na tsallan murna tace to inna ta nan kowa yashiga mota suka tafi gida

Haka sukaci gaba da rayuwar su mai kyau da tsafta , Aliyu yazo gidan su ameer yabada hakuri yanemi gafarar ameera da ameer nan take suka yafe mishi ,, yana ganin hajara baiyi nauyin bakiba yace yana son hajara abashi aurenta ,,Daddy yace yayi hakuri ansaka mata ranar biki amma zai bashi wata

Cike da farin ciki aliyu yayi godiya yace wa daddy yanason yaga yarinyar don yafada mata ko yamata zata iya aurenshi

Daddy yace tana kauyensu amma za'ayi bikinsu lokaci daya dana su hajara

Godiya sosai aliyu yayi tukun yatafi gida yana zuwa yafadawa mom dinsa taji dadin wannan karamcin nasu daddy mijinta nazuwa ta fada mishi shima yayi farin ciki yace gobe zaizo suje kauyen anemawa aliyu auren yarinyar


Ameera ta kalli ameer tace kowa daddy zai aurawa aliyu ameer yace ina tunanin ko rashida ko kanwarta acikinsu daya zai aurawa

Ameera tace tab ka manta rashida anmata miji kanwarta ko bata isa aure ba yanzu abinda zaayi na kira daddy nace mishi ya bashi khadija wannan shawarar tayi?

Kallon ta ameer yayi yace gaskiya kwakwalwar ki naja wifey na wannan abun yayi kawai kirashi muji maixaice
Cike da farin ciki ameera ta dauko wayarta daga caji ta shiga contact nember din daddy ta danna mishi kira ringing daya ana biyu ya dauka

Yace assalam alaikum daughter kece da daren nan


Gyara zama ameera tayi ta nutsu tace eh daddy ina yini ya gida

Murmishi yayi yace lfy lau ya yaran naku, tace lfy lau am dama daddy wata magana nakeso muyi

Daddy yace fadi kanki tsaye daughter ina jinki

Ameera tace wacce yarinya zaka bawa aliyu a kauyen mu

Murmishi daddy yayi yace eh bandai yanke hukunci ba da rashida zanbashi to ita ansaka nata bikin da dan mai gari , kanwarta bata isa aure ba , amma idan kina da wadda zaki bada saiki fada naji

Yar dariya ameera tayi tace eh daddy akwai

Daddy yace to ina jinki wacece

Ameera tace daddy maizai hana kuje anema mishi auren khadija tinda ita baa mata mijin aure ba amma yaka gani?

Daddy yace kai amma kin kawo shawara mai kyau nasan iyayen khadija zasu amince insha Allah baban aliyu yakirani zaizo gobe muje kauyen sai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login