Showing 126001 words to 129000 words out of 175796 words

Chapter 43 - AMIR DA AMIRA Complete by Maman Nusaiba.txt

07 Aug 2025

3351

ciwon,, junnu a razane ta farka " har jike tayi sharkab,, kamar an zuba mata ruwa, , addu'a ta ringa yi,, , yashafa,, tanason komawa bacci amma ya gagareta " tana tunano abinda tagani a mafarkin ta.....





*ko meye ameera tagani a mafarki oho*




*thank you my fans ina godiya da addu'o'i ku agareni Allah yabar kauna*
[30/10, 17:51] MRS. MU'UTASIM: *🌟AMEER DA AMEERA🌟*


*STORY AND WRITER*
*BY*

*MAMAN NUSAIBA CE ✍️*



💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️*


https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl

_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_

*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*




*73—74*



Tagumi ameera tayi tana tunano abinda tagani a mafarkin nata ,, anty karima ce tagani wasu mutane najanta ,, tana kiran sunan ameera kizo ki ceceni kada kibari sutafi dani " please ameera....ta fada da karfi


Da gudu ameera tabisu harta kama anty karima zasu gudu wani daga cikinsu ya bige ta akai nan tafadi,, ihu anty karima keyi saboda ganin abuge ameera tana jijjiga,, ta nan sukazo suka dauke anty karima " wani daki suka sakata,,, ajiyar zuciya tasauke bayan tadawo daga tunanin mafarkin data yi sosai jikinta yayi sanyi tashi tayi tashiga toilet , tayo alwala nan ta soma jero nafila


Umar ma , yadda ameera tayi mafarkin shima haka yayi,, da sauri yadiro daga kan gadon yana safa da marwa ,, shi yakasa gane wannan dakin acikin gidan bauta a wani waje yake babu inda bai sani ba gidan bauta amma wannan dakin baisan shiba kai dasake lokaci yayi da zai je gidan bauta yaduba lungu da sako saiya gano wannan dakin ,, yaga ko karima na ciki ganin hakan ba mafita bane yasa shi tashi yayo alwala yasoma nafila ,, yanakai kukansa wajan Allah daya bayyana mishi matar shi ya kareta aduk inda take


Su bilal abin nema yasamu sai nan nan ake da jamila ita har mamaki ma yake bata in yanayin wani abun, ,, da wuri yake dawowa daga wajan aiki yazo " yayi tawa cikin jamila magana wai yana magana da babyn shi

Dariya jamila keyi duk lokacin daya soma wannan abun

Yauma suna zaune ya kara kunnanshi ajikin cikin , dagowa yayi yace habibty wllh baby yana motsi ,, yasan babanshi na kusa dashi

Kallon shi tayi tana murmishi tace, eh nima naji yana motsi " kasan dani zaiyi kama bada kaiba


Harara ya aika mata yace, tab wllh baki isaba dani zaiyo kama yarinya ,, nasha wahalar samar dashi amma kice dake zaiyi kama, ninefa nafi yin aiki wajan samunsa

Dariya sosai jamila tayi tace habiby wannan maganar haka bakajin kunya,, to naji yayi kama dakai shikenan

Murmishi yayi yace ai dole ma kibar min maganar insha Allah dani zaiyi kama

Tace ameen

Shafa cikin yayi yace waida watan shi nawa cikin nan

Bakwai ta bashi amsa

Yace kai ashe nakusa zama daddy wllh Allah yamiki albarka habibty Allah yasaukeki lfy

Tace ameen habiby. ,,Fatima kuwa haihuwa ko yai ko gobe insha Allah

Bilal yace eh wllh bakiga yadda cikin ya keretaba idan kika ganta abin tausayi ,, kai Allah yasakawa iyayenmu da Alkhairi ,, Jamila tace ameen ya Allah ,nan sukaci gaba da hirarsu ta masoya



Fatima ce tafito , tana tafiya da kyer anass ne ya taimaka mata,, ta zauna ahankali

Kallon ta yake cike da tausayi yana matukar tausaya mata ,, yadda cikin ya hanata komai amma duk da haka,, bata hanashi hakkin sa " gaskiya yana jinjina wa fatima kukan tane yadawo dashi da sauri yarike ta yace yadai



Kwantar da kanta, tayi a kafadar shi tace sweetheart


Juyowa yayi yana kallon ta yace na'am meke miki ciwo ne

Kwabe fuska tayi tace , cikin nan yahanani zama irin nakowa, ko bacci ban iyayi na kirki ,ga bayana namin mugun ciwo ,, dana fadawa mom cemin tayi wai idan mace ' ta kusan haihuwa haka take fama da wannan ciwon bayan " har ta haihu ,, nidai wllh nagaji da ciwo nan please ka amsa nima nahuta,, kona sati biyu ne kayi sweetheart yana kai karshen maganar tana dagowa daga kafadarshi

Danne dariyar shi yayi tana rarrashin ta,, har bacci yayi gaba da ita yace fatima rigima kenan inbanda abinki ina maza ke daukar ciki, ai sai mata Allah Allah yasaukeki lfy,, nan yaringa matsa mata kafafunta dasukayi,, kumburi yana murmishi,, yakusa zama daddy




Alhamdulillah yau ameera takoma islamiya,, kuma taji dadi makotansun nan suma suna zuwa sosai , lokacin da aka ce musu an doki ameera ,, mai gidan saida yakai reported wajan sanda amma aka kasa gano mutumin " haka suka hakura amma yace duk lokacin da suka ganoshi, su fada mishi ' shiyasa yau da umar yace musu zatazo suke ta murna

Assalam alaikum ameera tace lokacin datazo bakin kofar shiga


Amin wa'alaikum salam suka amsa mata matan da sauri sukayo wajan ameera ' suna nuna farin cikin su da ganinta


Murmishi tayi tace, kuna lfy daiko ,, a tare suka amsa mata da lfy lau,, ya saukin naki '' Ameera tace Alhamdulillah,, nan suka zauna aka kama karatu



Bayan antashi kowa yatafi gida,, Ameera ta dauko jakarta, har taje bakin kofa saita dawo,, wajan muhammed


Kallon ta muhammed yayi , yace kanwata yadai,,, ko kewar ikram kike ne

Yar dariya tayi,,tace tab kewa fa aiko shekara zatayi bazanyi kewarta ba haba yarinya sai rashin jin tsiya

Murmishi yayi yace to shikenan kibamu ita kyauta " dama bamuda mace agidanmu , shikenan

Ameera tace to nabaku ai inda ikram ce gata gaku, asha zama lfy

Tace am dama inason muyi wata magana ne

Muhammed yace ina jinki kanwata

Numfashi ameera taja tace wllh yayana wani mafarki nayi mai ban tsoro kuma nakasa samun nutsuwa

Muhammed yace subhanallah to mai kikagani acikin mafarkin naki kanwata

Tuni har ameera tasoma kuka tace matar yaya umar nagani acikin wani hali tana kirana amma wasu suka bugeni nafadi nakasa manta abinne

Muhammed yace ban ganeba ameera dama umar yana da mata shin dama su abubakar sadeeq da mufeeda ba ke kika haifesuba ,, kaina fa yakulle kanwata kiyimin bayani ta yadda zan gane


Ciki kuka ameera tace,, yayana niba matar sa bace bakaga sai wannan shekarar suka musulinta ba su din kaddarar rayuwa tane,, shiyasa Allah yajefoni cikinsu bansan suba anty karima kadai nasani itama a mafarki nake ganin ta sau daya naganta afili sanye da kayan likitoci


Zama muhammed yayi yana dafe kai yace to kanwata " kince su kaddarar rayuwar kine to kuma naga su abubakar suna tsananin kama dake " babu wanda zaice bakece mamansu " ba duk da ana samun masu kamanni amma basuda,, hadin dangi haka Allah yakeyinsu kama daya " amma naga shakuwar da kukayi da yaran abin yana bani mamaki ,, kanwata shin ke wacece daga ina kikazo nan " da ciki ajikinki ina baban yaran da kika haifa please kiyimin bayani



Share hawaye tayi " tace hakane yaya muhammed nima abin yana bani mamaki sosai yadda muke kama da yaran har mamansu , ita munfi kama sosai.
Nan tabashi tarishin rayuwar ta da yadda akayi aurenta da lokacin da anty karima " take zuwar mata a mafarki, da kalaman datake mata har zuwa rabuwar dasukayi ita da ameer din ta da yadda " tayi luzing din memory dinta " har zuwa yanzu tana saka kuka mai taba zuciya " saboda ta tuna yadda ameer ke sonta na riritata kamar jaririya da kulawar shi,, amma yanzu gashi kaddarar rayuwa ta rabasu.
Tace ninasan yanzu sun dauka na mutu kawai yanzu shekara biyu da rabi ,,kenan rabona da family na


Baki da hanci muhammed yasaki yana kallon ameera " da tagama bashi tarishin wannan rikitaccen,, lamarin ,share zufar dake karyo mishi yayi yace kai amma kanwata na tausaya miki " insha Allah kinkusa komawa wajan mijinki,, wannan mafarkin yana nunin ,, muje cen gidan abin bautar tasu,, mu bincika mu fiddota " kisamu ki koma ahalinki " ki kara hakuri kinji kuma kici gaba da addu'a zan tayaki,, dani zamuje amma mubari sai dare mutafi muduba


Dagowa, tayi tana kallon shi tana dariya da kuka a hade, tace nagode sosai yaya Allah yasaka da alkhairi


Ameen sukaji ance daga bakin kofar " da sauri suka juya ,, Umar suka gani yana share hawaye karasowa " yayi ciki


Zama yayi yace tabbas hakane nima nayi wannan mafarkin jiya ashe kema kinyi to mubari gobe insha Allah da dare lokacin babu kowa agidan abin bauta " saimu je amma fa muje da shirinmu dan akwai masu tsaro


Jinjina kai sukayi ameera tace insha Allah hakan zamuyi nan sukafito daga cikin islamiyar,, Muhammed yayi gida suma suka shiga gida



Fatima tafito daga daki tayi fayawo,, abinta , sai k'aton cikin dake rinjayar ta a hankali take tafiya harta karaso cikin falon ,, Anass ne ya kamata ta zauna


Wayar tace tayi kara dubawa tayi ganin sunan yasa tayi murmishi tace momsy,, Allah yasa su ameer ne, dagawa tayi tana fadin assalam alaikum

Daga cen bangaren ikram sai taji,, su ameera ne ameer yace hello anty fati ", mommy mu tace zaki haifa mata baby ni mace nakeso sai muke kwana tare " anty fati aidai mace zaki haifamin muke wasa ko

Dariya fatima tayi tace ,, kai dama nasan kune kuka kira yan rigima kawai , to nima dai ban san mai zan haifaba idan na haifa saina kai muku shi gidanku,


Kwace wayar ameer yayi yace anty fatima brother " nake so ki haifa mini kinji sai muke zuwa wajan wasa dashi daddy,, zaike kaimu ko ???

Fatima dai dariya take musu jin ansoma fada tsakanin ameer da ameera " yasa tayi saurin fadin ameer ameera ku tsaya ,, kuji yan uku zan haifa muku kunji saina dauki daya nabaku biyu


Ihun murna sukasa suna fadin yee muma zamuyi sister and brother , mommy zoga anty fatima kuyi magana tace uku zata haifa tabamu biyu tadau guda

Dariya ikram tayi tace , to naji iyayen

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login