Showing 138001 words to 141000 words out of 175796 words
Chapter 47 - AMIR DA AMIRA Complete by Maman Nusaiba.txt
taga , karima na motse hannun ta
Murmishi tayi tace to kiyi hakuri mana ameera ki kyale ,, muje waje doctor dazaizo yana hanya inaga aikin dare ma zaa mata ,
Fita zukayi , waje suka zauna amma ameera taki dena kukan ,, kallon umar keyi ,, cike da tausayi " yace muje gida idan tasamu sauki saiki zo ", dama saida nace bazakizo ba saboda , wannan kukan naki maza shige muje gida yana mikewa
Doctor aisha ce tafito tana kallon su tace ,, to bata dena kukan ba , umar yace inafa gida zan kaita " da dare zan dawo
Kin binshi tayi , juyowa yayi yace wai ameera ina wasa dake ne nace kishige muje gida ,, yanzu saboda wannan kukan saiki jawa kanki ciwo , to muje
Binshi tayi suka tafi suna , , fitowa daga hospital din motar su ameer na sayo kai ,
Ameera taji gabanta ya fadi kallon motar tayi , har suka shiga ciki ,, su kuma sukayi gida
Ana sauke ameer ,, ya fito yabiya mai motar kudin shi , kafin yayi cikin hospital din
Da farin ciki doctor aisha ta ,, tareshi tana fadin oyoyo jikana , gaskiya kunyi sauri
Murmishi yayi yana gaishe ta , amsawa tayi nan sukayi office din ta
Saida yadan huta tukun,, yace muje naga marar lfyr , nan sukayo dakin da karima ke ciki
Shiga suka , baki sake ameer ke kallon fuskar karima " yace kakata ,, kinga abinda nagani kuwa
Kallon shi tayi kafin ta kalli karima , itama sai yanzu taga yadda suke tsananin kama da karima , tace ikon Allah wllh kamar ku daya Allah buwayi gagara musali ,
Ameer yace gaskiya , Allah mai iko , nan yadauki kayan aiki yaduba ta nan yaga dai sanyi ne ya tsayar mata daduk wasu abubuwan dake mutsi ajikin dan adam, , kallon doctor aisha yayi yace gaskiya wannan akaita dakin da ake gashin basu shanyayyen ,, jiki a mata gashi kuma yau da dare saboda sanyi yashigeta , sosai , yanzu zanje hotel , na huta bayan sallar isha"i " sainazo muyi aikin
Doctor aisha tace to shikenan ,, Allah yakaimu daren lfy nan suka fita
Ameer ya wuce hotel nan yakama daki ya shiga wanka yafara yi kafin yabatar da sallar isha"i karfe 9:00 PM dai dai tamishi a cikin hospital ,, dama tuni doctor aisha tazo shi take jira ,, nan aka turo karima zuwa dakin da za'a mata aiki
Koda su ameera sukaje gida sai tunanin motar data gani takeyi , ganin abin zai bata wahala yasa tayi watsi da tunanin ,, ta dauko alqur"ani mai girma taringa karantawa,, saida tasoma jin bacci tukun ta ajiye , tayi addu'a ta kwanta ,
Su ameer nashiga,, nan aka zonawa karima kayan aiki tukun suka soma ,, aikinsu ,
Umar da muhammed na waje ,, sai zarya sukeyi suna addu'ar Allah yasa ayi a sa'a
Bayan awa uku aka bude kofar,, da sauri suka kalli kofar ameer ne yafito , doctor aisha na biye , dashi ,, tsayawa sukayi a wajansu umar
Umar ko kallon ameer yakeyi kamar yasamu tv , yace doctor wllh kana kama da matata
Murmishi ameer yayi yace ,,haka ne nima nagani wllh haka Allah yake mutane ,, masu kama daya
Umar yace hakane ya jikin ,, doctor aisha tace Alhamdulillah munyi nasara ", insha Allah tana tashi nomal zata tashi
Cike da murna ,, sosai umar ke musu godiya , hadda dan kukan shi ,
Ameer yace tinda angama aikin,, ni gobe insha Allah zan koma kano idan ta tashi saiki ,, dubata " doctor aisha tace ,, ok amma gobe zaka tafi baka barin zuwa jibi sai ka tafi
Ameer yace no inada aiyukane sosai agabana barinsu nayi nazo to tinda angama ,, saina koma gida ko
Doctor aisha tace to shikenan Allah yakaimu goben , amma kabiyo tanan kafin katafi ,,,Ameer yace to insha Allah nan ya tafi zuwa hotel din daya kama mamakin " wannan kamanni daya gani sunayi shida karima ,, ahaka har bacci yayi gaba dashi
Umar ko cike yake da farin ciki yana dawowa yafadawa mama da ameera ,,anyi aikin lfy gobe zata tashi ,,dan haka da karfe goma sutafi su duka asibitin ,
Ameera ko kan murna har sujjada tayi na mika godiyar ,, ta ga Allah sosai taji dadi zata ga anty karima dinta
Doctor aisha ma tayi farin cikin samun nasarar ,, dasukayi na aikin nasu
Washe gari tin karfe 8:30 am , ameer yabar hotel din yaje hospital din ,, yana zuwa yaga muhammed ,, a zaune wata yarinya na kuka a gaban shi yana , rarrashin " ta amma taki dena kukan
Sallama yawa muhammed ,, ya amsa nan suka gaisa
Kallon " yarinyar yayi yace, Muhammed wannan mai kama dani , dinfa
Kallon shi yayi ya kalli ikram yace , gaskiya kuna tsananin kama ,, wllh wannan diyar sister din karima ce
Ameer yace , eh gashima suna kama da karima din , yace zo nan baby tana mikawa ikram hannu
Dena kukan tayi ta dago tana , kallon ameer dake mata murmishi sai kuma ta kalli muhammed ,, tace daddy mommy tana nuna dakin da doctor aisha tashiga,,
Dagota muhammed yayi yace , to kiyi shuru mommy yanzu zata fito kije uncle na kiranki , yana nuna mata ameer
Sauka tayi daga jikin shi ta nufi ameer , tana bata fuska kamar zatayi kuka ,, ,hannu ameer ya bude mata , tana zuwa ta shige jikin sa , ta kuka tace daddy
Wani sanyi ameer yaji na ratse shi daya rungume ikram , yana jin yadda sonta ke shigar shi,, wai shine ake kira da daddy ,, yanzu da ameera , na nan tashima ta haifa mishi ,, masu cemishi daddy ,, jin takara saka kuka ,, ya ce yi shuru baby yanzu zatazo " suna a haka saiga doctor aisha ta fito , tana nufosu ,
Murmishi tayi tace , yarinya ta ce zo inji waya taba min ke
Makale kafada tayi tana kara kwanciya jikin ameer
Dariya doctor aisha tayi tace ,, to kai ameer kasamu diya , takizuwa
Murmishi ameer yayi yace dan Allah kibani ita yarinya tashiga raina ,, doctor tace tab , aikuwa bazaka samu ba " muma rikonta aka bani , mamanta ", kanwar wannan marar lfy ce
Ameer yace eh muhammed ya fadamin to ni zan wuce ,, sai kuma wani lokacin yana ,, mike ganin ikram ta sauka akanshi
Ikram ko na ganin yamike ", takama hannun shi tana fadin daddy , daddy , daddy
Dariya sukayi jin tana kiranshi kamar waka , doctor aisha , tace to anturo kudin zan turama ta account bank dinka ,,
Ameer yace no basai anbiyani , kyauta na mata nizan wuce, kar jirgin mu , ya sauka banje ba
Da kyer aka raba ameer da ikram tana kuka tana mika mishi hannu fadi take daddy ,,Ameer ko ji yayi kamar ya sace yarinyar sutafo yadda take, kuka har cikin zuciyar shi yakejin kukan nata haka dai yatafi gida
Ikram ko tana kuka har tayi bacci , rungume ta muhammed ,, yayi yace kaji yarinya yar nema ,, kamar ta taba ganinshi ta ringa kuka irin wannan ,
Su ameera ne suka shigo ,, zama sukayi aka gaisa suna jira karima ta tashi
Wata nosee tafito tana fadin ranki yadade ,, marar lfyr mu ta tashi
Da sauri suka shiga ciki , ameera ta rigasu shiga tana son karima ta fara tozali ta ita , ganin karima ,, a zaune da sauri ta isa " tace anty na tana rungume ta
Itama karima sai kuka takeyi tana fadin kanwata ,, kece dagowa ameera , tayi tace eh anty nice gani
Zama tayi kusanta tana fadin kin gani ,, mafarkin naki danakeyi gashi yazama ,, gaskiya nazo garinku danginki sun musulinta ,, ga kuma yaranmu
Da sauri karima ta kalli ameera jinjina , kai ameera tayi alamar , da gaske take
Abubakar da mufeeda , ko wajan su suka matso , Abubakar " yace mommy wannan wacece mai kamarki , ko sister dinki ce " mufeeda ma kallon Karima tayi sai kuma ta kalli ameera ,, tace to mommy wannan tana kama dake , sister kine ko
Karima ko kallon su take sosai tana hawaye tace nima mommy dinkuce kuzo
Makale kafada abubakar , yayi yace a a ga mommy nan " saidai muce miki anty ,, mommy kinji tace itama mother , dinmu , ne wai
Murmishi ameera tayi tace eh mommy dinku ce ,, ita ta haifeku , kuje inda take
Zuwa sukayi ta rungume su sosai , take kuka umar ne yakaraso , shima rungume shi tayi tana godiya ga Allah daya kawota ahalinta ,
Su mama ma rungume ta sukayi sosai suke farin ciki ,, doctor ko tasha godiya sosai wajan su mama da umar har ameera , nan aka basu sallama sukayo gida
Sosai mutanen garin ke al"ajabin wannan lamari ,,wai ashe yan gidan abin bauta ne suka dauke karima sosai ake zuwa ganin karima,,
Yanxu karima na samun sauki sosai , Dan haka suka shirya tafiya kano kai ameera gida
Doctor aisha ma tace itama zataje nan sukaje kasuwa akaiwa su ameera sayayya sosai sai yamma suka dawo gida , da dare ko kusan kwana sukayi suna hira dan gobe zasubi jirgin safiya zuwa kano
Washe gari da wuri kowa yashirya ,, aka shiga mota zuwa legos ,, nan da nan sukaje ,, basu jimaba jirgin kano yazo