Showing 9001 words to 12000 words out of 175796 words
Chapter 4 - AMIR DA AMIRA Complete by Maman Nusaiba.txt
ina abokina yake
tace yana dakinsa nan suka nufi dakin,
Ameer ne agaba Ameera nabiye dashi har suka shiga da sallama
abokin nasa ya rungume sa yana kai wai yau wata rana ce!!!
Harara yabanka miki ta wasa yace oho dai koma meye,
Juyowa yayi nan yaga ameera yace madam shigo mana
Kara rungume ameer tayi ta bayan shi
Dariya sukayi tare, ameer yace kaga Anass kaifa dan iska ne yanzu saika taromin ruwa kasaka min mata tsoro
Zaro ido Anass yayi yace to ikon Allah dama wannan itace amarya tamu!!
Ameer yace eh itace yabashi amsa yana hura hanci saboda kar arena mishi mata,
Dariya Anass yayi yace madam bako gaisuwa ma
Ameera da take a bakale a bayan" Ameer tace nidai yaya kace mishi karya kara cemin madam kamar wata babba
Dariya sukayi Ameer
yace to kaji dai kadena
Anass yace to shikenan tinda baki so yakai karshen maganar tasa yace to fito mana mugaisa"
Kanta ta leko taga Anass da askin nan irin wanda gayu keyi ita kuma bata taba gani a zahiri ba sai yanzu,,dafe kirji tayi tace kai kai kai yaya ?
Ameer ya kalle ta yace "manene
Tace dama shi abokin naka dan iska ne ,,
kallon anass ameer yayi don yaga menene na yan iska ajikinsa nan yaga sabon askin daya yi,,
Kawai saiya kwashe da dariya yace abokina kasan meye yasa my ameera tacema dan iska
.....Shikuwa harya hade fuska yace a a saika fada tinda kun maidani mahaukaci,
"Ameer yace wannan askin naka ne da kayi shine yasa take ganin kamar kaidin dan iska ne,,
Dariya anass yayi yace kai amma yarinyar nan kincika abin dariya"
Tsuke baki tayi dan ita "idan kanason ganin bacin ranta kace mata yarinya ita dai tana son girma..tace yaya mutafi gida
Anass yace to daga zuwa
ta murguda baki tace, to kai ina ruwanka
Anass yace ba ruwana kuwa
Ameer yadan hade rai yace Ameera wannan abokina ne ba dan iska bane karna kuma ji kince mishi "dan iska
Ganin babu wasa a fuskar shi tace to yaya nadena basu jima sosai ba suka koma gida
Suna shiga suka tarar da daddy yadawo, Ameera tayi wajan daddy da sauri ta zauna a kasa kusa da kafarsa ta daura kanta akan cinyarshi tace; daddy wani gida mukaje nida yaya
Murmushi daddy yayi yana shafa kanta yace kennan yau kinga gari
tace a a fa gida daya mukaje shima yace abokin sa ne
Mom tace to kije ki shirya kutafi islamiya keda Fatima
Ameera tace to mom
tayi dakinsu basu jima ba suka fito cikin shirin islamiya sunyi kyau sosai" sukace mom muntafi
Mommy tace adawo lfy
Ameer yace mom kinsan kuwa muna zuwa wajan abokina Anass kawai ameera taganshi yayi sabon iska tace wai dama abokin nawa dan iska ne"
Dariya sukayi mom tace gaskiya bana gajiya da surutun ameera musamman ma "idan fatima tana nan
Daddy yace yar gidan inna su inna yanzu ko andena kewar jikar ta ta mom tace to kila
Kusan magarib su ameera suka dawo a gajiye dan yau ameera tilawa tayi kuma tayi sosai,, suna shigowa ko zama basuyi ba aka soma kiran salla nan sukayi daki domin yin salla bayan sun gaba fatima tace""Anty ameera yau zamu zo muyi magana hausa cikin hausa wato karin magana,
Ameera tace to shikenan "idan mun gama cin abinci muka zauna hira sai na miki tambaya kibani amsa tace to
,, Bayan sallar isha'i suka fito falo harda daddy da ameer sukkansu, mommy ce tafito daga kitchen rike da kular abinci tace "idan kun shirya abinci yayi ready
suka ce to,,nan sukayi darning suna cin abinci fatima na mintsinar ameera
ita kuwa sai hararar ta takeyi tana mata nuni da zama rama,
,Murmushi tayi bayan sun gama ne suka koma falo fauziya ta kwashe kwanukan tayi kitchen dasu "ta wanke itama ta dawo falon
,,Ameera tace to yaudai karin magana za'ayi nida fatima mom idan ta fadi ba daidai ba kice yati error mom tace to muna jinku.
Fatima tace to bari na lissafo miki questions kibani amsa gyara zama ameera tayi tace, ina jinki
fatima tace to gasu kamar haka
Abun da ka shuka?
Kowa ya deboda zafi?
Mutu ka raba?
Dan hakin daka rena?
Kowa yabar gida?
Fatima tace to bani amsa
Sudai su mom kallo ne nasu,
Ameera tace yarinya yanzu kuwa
Abin ka shuka =shi zaka ba shanunka
Kowa ya debo da zafi =yayi wanka da ruwan sanyi
Mutu karaba =akwatin karfe
Dan hakin daka rena =shi zaka kakkarya
Kowa yabar gida =gida ya rushe
Aikuwa me zasuyi inba dariya ba fauziya harda fadowa daga kan kujera tana dariya
,Fatima kuwa burgima take dariya ce taci karfinta
" Daddy kuma da ameer suma dariyar sukeyi,,
Aikuwa ameera ta shaka ta hade rai ta mike tace shine kuke min dariya tana bata fuska kamar zata yi kuka
wajan ameer tayi shima yana dariya yace to kece kika bamu dariyar "wannan amsa haka ,
Tace shine kaima kake min dariya ai haka naji kaka na fada
Fatima ce har yanzu bata dena dariyar ba
dama ameera haushinta take ji,,nan tayi kanta suka fara tsere
Mom nacewa kubari kunji kema zo ki mata tambaya ta baki amma basu kulata ba "
nan aka soma dambe ameera tace ni kike wa dariya saina lallasa ki a gidan nan
Ameer zai tashi daddy yace kyalesu tukun musha kallo
Fatima tasamu ta kwace daga rukon da ameera tayi mata tana mata gwalo
"Aikuwa suka ringa zagaya su mom fatima na dariya
Ameera kuwa har ta soma kuka tana cewa,,yarinya ki tsaya ko kuwa sai kinyi bacci na yanke miki gashin kanki irin na maza
Fatima tace anki din,,
Ameer ne ya tashi yayi caraf da ameera sai ta rushe da kuka janyota yayi suka koma kan kujera ya soma rarrashin ta,,yace to kiyi shuru mana
Tace yaya ba ruwana da Fatima tinda take min dariya
Ameer yace kiyi hakuri kinsan fa kece babba,
daddy yace to shikenan ameera kuje ku kwanta gobe kuna da school,
,Ameera tace daddy nidai bazan kwana da Fatima ba wajan yaya zan Kwana
Mom tace daddyn su gyara taje cen ta kwana idan aka barsu hallau fadan zasuyi
Yace to shikenan kuje kowa yaje yayi bacci,,
Ameera da ameer suka yi sama su Fatima suka yi dakinsu .....
.Suna isa yace baki dauko kayan bacci ba tace bari nadauko, sanin halinta yasa yace no bari na dauko miki tace to yaya "nan yafita ita kuwa sai kallon dakin takeyi tsarin dakin ya burgeta sosai ahaka yadawo ya sameta ,
,yace cire na jikin naki ki saka wannan tace to" nan tasoma cirewa shi kuma yayi toilet dan yayi wanka dama ita tuni tayi nata
,,A kan gadon yaganta tace nima zanyi nafilar yace to dauro alwala ta mike tayi toilet tayo alwala suka tada iq'ama
Bayan sun idar ne sukayi addu'a suka koma gado"
Ameera tace yaya ?
yajuyo ya kalleta yace na'am
Tace, dama namiji da macce suna bacci a waje daya ?
Murmushi yayi yace sosai makuwa idan miji da mata ne
Kallon sa tayi tace to kaidin mijina ne ?
yace eh nine mijin ki
tace amma maiyasa bama kwana a gado daya?
yace ke kikace awajan su fauziya za kike kwana shiyasa na barki,,
Tace to daga yau zamuke kwana tare "
Yace eh idan kinaso ba
Tace inaso nan suka kwanta ya janyota jikinsa,a tare suka sauke ajiyar zuciya ita ta gajiyar gudun da tayi "
shi kuma saboda yaji dumin jiki ta saboda ba karamin so yake mata ba tin tana jaririya yake sonta,..
Haka sukaci gaba da rayuwar su cikin farin ciki kuma yanzu ameera tana fashimtar karatu sosai daga boko har islamiya, ta dena kwana a wajan su fatima tare suke kwana da ameer shikuwa haka yayi mishi dadi dan yana jin dadin dumin jikin ta "ita kuwa sarkin son jiki kullin ajikin shi take kwana shine katifar ta,
Yau sun dawo daga school ameera tace mommy munyi hutu akaini naga Inna ta
Ameer yace,ba yanzu ba aikuwa tasaka kuka tana zama a kusa dashi tace,, nidai akaini naga inna ta
Mom tace kyaleshi kinji daughter ni zan sa akaiki kokuwa shi yakaiki kuje cen kuyi hutun,,
Sai tadena kukan tace yauwa mommy na nagode "
Harara ameer yamata ta murguda mishi baki nan yace zan kama ki ai
Dariya tamishi
kyaleshi ta yayi
sama tayi zatayi wanka "dan ta jima da komawa wajan ameer har kayanta dukansu,..
Bayan kwana biyu yau ne kuma su AMEER DA AMEERA zasuje kauyen su ameera sai murna take dan so take taga inna,,nan mutanen gidan suka zo har bakin mota
Fatima na kuka tace itama dole sai an kaita ameer kuma yace bata bisuba, daddy ne yace saita je
Ta dauko kayanta suka tafi,,
Suna hanya Fatima da ameer sai surutu suke kafin wani lokaci sunyi bacci,
Ameer yajuya dan yaji sunyi shuru kawai saiya ga sunyi bacci murmushi yayi yace iyayen zance surutu anyi bacci
ANAN ZAN TAKATA KUYI COMMENTS DA SHARE DIN SA NGD
[24/10, 01:45] MRS. MU'UTASIM: 🌟𝐀𝐌𝐄𝐄𝐑 𝐃𝐀 𝐀𝐌𝐄𝐄𝐑𝐀 🌟
𝙎𝙩𝙤𝙧𝙮 𝙖𝙣𝙙 𝙬𝙧𝙞𝙩𝙞𝙣𝙜 𝙗𝙮
𝐌𝐀𝐌𝐀𝐍 𝐍𝐔𝐒𝐀𝐈𝐁𝐀 𝐂𝐄✍🏻
7-8
Suna isowa kauyen su Ameera yayi anguwar su nan yashiga gidan,,
Yaran gidan suka yo wajan su "suna ga ameera ga ameera
Zantukan yaran ne ya tayar dasu ameera bude marfin motar sukayi suka fito,
Aikuwa kafin su yo kanta tayi sashen inna da gudu tana cewa,,Inna ta gani nazo
Inna na zaune jita kamar a mafarki takejin muryar ameera
bata yadda ba saboda ta saba jin murya ameera na mata gizo "dan kullun sai ta takurawa abba tana cewa yakaita kano gidan muhammadu sai ansha fama ake shawo kanta,, tace "idan ma siyar mata da ameera sukayi to wllh bazata yadda ba su koma inda suka siyar da ita su basu kudin su akawo mata ameera ta kullin haka takeyi bata idar da zancen zucin da takeyi ba taji mutum ya jikin ta da sauri tadawo,,takai dubanta da wanda ya rungume ta wazata gani ameera ce "ta murza idon ta dan tabbatar wa tagadai ba gizo bane ita din cedai aikuwa ta rungume jikar ta 'ta tana cewa dama ai nace musu babu wanda zaiyi min mafiya da jikata yazauna lafiya ya akayi kika gudo,
,dariya ameera tayi tace to inna yan mafiya kuma nida nake gidan daddy maiya hadani dasu
,,Ajiyar zuciya inna ta sauke tace a ni maryam Allah na gode maka daba siyar min da jika aka yi "
Ameer ne yashigo da sallama jin inna na zantuka kamar an jonata yace,,Hajiya inna ikon Allah kaga kakar, 𝐀𝐌𝐄𝐄𝐑 𝐃𝐀 𝐀𝐌𝐄𝐄𝐑𝐀 yana zama kusanta
Dariya fatima tayi tace to inna mu baki ganmu bane '?
'kallon su tayi da mamaki tace a a harda ke aka zo ashe kuna tare
Tashi tayi kawo musu tabarma suka zauna nan aka gaisa, take tambayar yasu mommy suka ce sunce ma a gaisheku
...Inna tace ina amsawa
Su Ibrahim ne suka shigo hajara tace anty ameera sannunku yaya ameer la hadda fatima tana tsallen murna
Ibrahim ya zauna kusa da ameer ita kuma Hajara tayi wajan su ameera suka kama hira.
....Bayan sallar azuhar suka yi sashen umma suna zuwa ameera ta zauna ta kwanta kan ciyar umma tace,,umma na nayi kewarku
Murmushi umma tayi kuma taji dadi sosai ganin yar ta, ta takara girma tayi kyau sosai
""Ameer ne ya durkusa har kasa yake gaishe da umma cikin jin kunya yake gaisheta
Umma ta amsa tace ya maman naku yace lfy,,umma tace to su fatima ne a garin namu zo kusa na kizauna
,,ta matso kusa da umma ta saki jiki aka suka soma bawa umma labari dan fatima babu ruwan ta da bakunta
,,Yaya safiyan ne yashigo yaga su ameer yace a a yau mutanen kano ne a garin namu
Ameer yace mune dan uwa jan ameer yayi sukayi dakin yaya safiyan yabar su ameera anan ,,
Umma tace kuje ki gaishe da mama nana tace to umma na
Nan suka fita sukayi sashen mama ,,da sallama suka shiga kausar ce da Usman zaune suna wasa, suka amsa sallamar kausar tace ga anty ameera da Fatima oyoyo
suka isa ciki mama ce ta fito daga dakin ta jin kausar tana cewa ameera tazo gani tayi da gaske take ""
tace marhabin ku mutanen kano nan suka gaishe ta ta amsa da fara'ar ta dan itama tayi kewar ameera duk da rashin jin da takeyi agarin amma tana da dadin zama
Tace,,bari nadauko muku abinci
Ameera tace a a mama munci abinci a wajan inna, Mama tace to shikenan amma da dare kuzo nan kuci tace to mama ina, Abbu da rashida da sauran ?
Mama tace abbun ku baidawo daga kasuwa ba Rashida kuwa suna makaranta basu tasoba nasan yanzu sun kusa zuwa gida
Ameera tace shikenan idan sunzo kice mata muna wajan inna,,,Mama tace to shikenan zan fada mata nan suka fito daga sashen mama sukayo na inna
Suna zuwa ameera tace inna idan anyi la'asar zanje gidansu khadija inna tace to shikenan kinsan kullin sai tazo tana cewa baki dawo ba nace mata ai su bukari ne suka siyar dake,,
Dariya sukayi tace inna bafa siyar dani aka yiba""ina cen ina karatu na hadda na islamiya fa nakeyi ko fatima ta ida zancen zuwa kallon fatima,,
Fatima tace eh inna karatu takeyi sosai
"" Inna baki har kunne dan taji dadi sosai tana son ameera tazama likita
....Bayan sallar la'asar ameera da fatima suka tafi gidan su khadija suna shiga da sallama,,khadija ce zaune tana kunce kitson kanta taji muryar kawar ta, ta kamar daga sama ta kalli kofar gida taga ameera ce dai da gudu ta tashi tana cewa,,waiyo Allah kawata nayi kewar ki
Ameera na dariya tace nima haka kawalliya na ""nan suka karasa
Fatima ce ta tsaya tana kunbura baki ita anshare ta duk da bata taba ganin khadija ba amma taji tana sonta,,juyawa sukayi ameera na cewa fatima wannan ce kawata khadija tayi shuru shine suka juyo "ganin ta sukayi tana turo baki gaba sai harara take banka musu
Dariya sukayi, Khadija tace wai dama da soba kikazo shine kikaki nuna min ita,
Ameera tace eh kanwar yaya ameer ce suka koma Fatima ta juya musu baya
Ameera na murmushi tace waiyo my kanwa am so sorry kinji ta , juyo tace shine kuka shareni
khadija tace kiyi hakuri ai yanzu kin zama kawar mu, tasaki fuska suka shiga tare "suka gaisheda maman khadija tace a su ameera mutanen birni ina ameer din naki
rufe fuska Ameera tayi tana dariya wai ita taji kunya,, dariya khadija tayi tace mama kunya fa takeji
murmushi maman khadija tayi tace to shikenan aka rufe fuska
suka koma gindin wata bishiya wanda take a tsakar gidan
khadija ta kalli ameera tace, ,Ameera kinsan kuwa bayan kin tafi kano maman su kamal tazo neman mu takawo kashe gidan mu wai munyi wa yaran ta duka harfa gidan ku taje kinsan me inna tace mata
""girgiza kai ameera tayi alamar a a khadija tace inna cewa tayi wai su abba sun siyar dake jin haka yasa ta koma gida amma fa tace duk ranar,,da kika dawo sai su kamal da Haneefa sun rama dukan da muka musu,
Ameera tace to mugani idan har zasu iya ramawa inda rabon musake zanesu ba
Dariya sukayi nan sukaci gaba da hirar su,,Khadija na bata labarin abinda akayi bata nan
tace yau ai kinzo muje wasa ko ?
Ameera tace,,eh mana hadda kema fatima zaki bimu ko ?
Fatima tace eh zanje naga yadda kuke wasan
Sun jima gidan su khadija har kusan magarib kafin suka tafi akan cewa "' bayan sallar isha'i zasuje wasa
suna zuwa gida wajan inna sukayi , salla suka faraji tukun suka zauna sai ga su Ameer da safiyan sun shigo da sallama nan suka amsa,
,Fatima ta tashi taje wajan yaya safiyan tace la yaya safiyan kai kaga kuwa yadda kake
yana murmushi yace mai nayi,,
Fatima tace kazama babba kamar yayana
dariya sukayi yace to ai yayan naki nafishi
Fatima tace shiyasa kazama babba kamar irin sharukhan na tv
"dariya suka sake yi yaya safiyan kuwa yace eh lalle su Fatima dama haka kike da zaro magana kamar BBC ,,
Dariyar itama tayi tace nidai bankai kaba nan suka zauna
Inna na bankawa su yaya safiyan harara tace,,ku masu kirar mutanen farko kun wani zomin gida kun zaune min kai dama sangangamin banza da wofi, yaushe rabonka da kazo nan ka gaishe ni
Dariya yaya safiyan yayi yace kai inna, wannan ba'a haka ke yanzu kinga kirar mutanen farko din
Tsuke fuska tayi tace to zaneni zakayi saina fada ma,,kai safiyanu wllh kafita idona inba haka ba yanzu zan, tumurmusa ka anan, marar kunya kawai ni wllh nama rasa maiyasa ba'a maka aure ba kabar mana gida kaje cen wani gidan,,
Ameer na dariya yace inna kinsan fa bashida budurwa kuma shida zai koma kano wajan daddy dan yayi karatu sosai yasamu aiki irin na daddy na,,
hararar shi inna tayi tace to shikenan ai iyayen boko nidai bada niba babu ruwana da bokon ku suna haka aka kira sallar isha'i. Su ameer suka tafi maseejit don yin salla
Bayan su ameera sunci abinci suka fito daga dakin inna ameera tace inna zamuje wasa hadda Fatima
Inna tace to karku dade kuma kada kibari a taba Fatima tana murmushi tace to inna nan