Showing 57001 words to 60000 words out of 175796 words

Chapter 20 - AMIR DA AMIRA Complete by Maman Nusaiba.txt

07 Aug 2025

3345

ba da farar safiyar nan amma ki sauke min fada, koda yake da yunwa ma



Yana zaune sai murmishi yake,, yace,, beauty ya kike ya tunani na nayi missing dinki sosai jiya muna ta,, zirga zirga ban samu nakira kiba,



Jamila tace lfy lau nake ina fatan habiby na ya tashi cikin koshin lfy,, kasan nafika kewar ka jiya kadai dabamu yi magana



Murmishi bilal yayi yace haka dai,, kikace amma nasan nafiki, ankusa kawomin ke muzauna a gida daya daki daya muci abinci a kwano,, muyi bacci a gado daya mu rufa da bargo daya yakai karshen maganar yana murmishi



Kunya ce takama jamila,, kamar yana ganin ta, ta rufe fuska tace, kai habiby wannan, zaro batu haka,, ai wllh harnaji kunya,,,,



Dariya yayi yace to shikenan kinga anass da ameer suna nan dana fada miki wata magana,



Itama dariyar tayi ,,, tayi saurin kashe wayar ta tana jin dadin samun bilal a matsayin mijin dazata,, aura




Shikuwa, Bilal yana kashe wayar dukan wasa, Anass yakai mishi yana cewa kaifa, wllh dan iska ne, indai soyayya ce munga *ameer da ameera* ma ba kai ba


Dariya bilal yayi yace to kaima kayi mana, inka isa,, haushi, ne yakama, shi yace to shikenan, bari kaga video call ma zan kira Fatima,,



Wayar shi ya fiddo daga aljihun,, sa yana kiran member,, Fatima,, lokacin tayi wanka ta saka kaya tana kwalliya, ganin kiran anass da sauro ta dauka tace hello yaya anass, yakake


Lumshe ido, yayi jin muryan sahibar tashi yace lfy lau Fatima yakika tashi tace lfy lau


Tace wai kasan me yaya, yana murmishi yace a a saikin fada, dariya " tayi tace kaga kwalliya nakeyi, kallon wayar yayi,, yaga tamishi kyau " shagwabe fuska tayi, tace yaya wai bazaka zo kakaini,, shan iska ba ,, Anass yace to shikenan zanzo anjima,, " cikin farin ciki ta, yiwa wayar kissing, har sau uku,, Anass cewa yayi wow my dear wannan duk nawane,, tace eh yaya maza kazo karka ki, zuwa yace, to badole nazoba " nan ya kashe wayar, yana kallon, su



Dariya ameer yayi yace,, aikin banza duk kanku baku,, iya soyayya ba kowa acikinku yasan neni oganku,,



Har haden baki suke anass da bilal suna cewa haba dai malam,, waya fada maka,, banza ya musu cen kuma yace ai dai nafiku,, my wife kwana nan zakuga ta haifa min twins mace da namiji, dariya sukayi bilal yace, kilama,, sai beauty na ta riga haifamin nawa babyn,, kyalesu yayi dan ya lura suna son sakashi yin magana dayawa yace,, banzaye kawai,, sai kuyi ai dariya suka sakeyi yace wato kun maidani kakan ku ko, to kutashi mutafi nan suka fita wajan,



Masu iya magana sukace, rana bata karya saidai uwar diya taji kunya, yau ne ranar daurin auren, Jamila da , Bilal gidajen biyu, kowa sai shirye shirye suke mazan sun tafi wajan daurin aure matan kuma zasuje,, dinner




Su ameera ansha kyau mai kwalliya ammi ta dauko har gida aka musu ameera da Fatima da nafeesa, sai yayyun bilal mata, zarah da khalisat,, dan haka sai yauk'i akeyi su nafeesa ,,




Bayan anyi sallar jumma'a,, aka daura auren bilal da jamila,, akan sadaki naira dubu hamsin, masu shedawa suka soma sanar wa,,



Amarya tasha kyau kamar ka saceta ka gudu sai murmishi take zubawa,, sosai saboda anass ya turo mata messenger ta dauki,, wayar, ta soma karanta sakon kamar haka,


Assalam alaikum Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah,, Alhamdulillahil lazi bini"imatihi tatimu salihati,, dukan yabo da godiya sun tabbata ga allah tsarki ya tabbata ga Allah , Allah nagode maka daka nuna min wannan rana mai albarka mai cike da farin ciki daa annashuwa,,,


Habibty na ina godewa Allah daya bani ke a matsayin mata Allah yabar mu tare Allah yabamu zaman lfy da zuri'a dayyaba, my beauty na ina sonki ina kaunar ki, daga mijin uban ya"yan ki masoyin ki bilal Allah yamiki albarka mrs. Bilal,, tana kai karshen karanta messenger din taji wani farin ciki ya mamaye ta




Dariya ce ta subce mata,, su samira sukace ke kuma,, lafiya ,, kike dariya "Jamila tace ba komai nan ta,, kalli wayar tashiga wajan,, messenger din ta soma rubutu kamar haka:,

Mijina ina addu'ar Allah ya albarkaci auren mu yabamu zaman lafiya " mai daurewa na har abada, ina cikin farin ciki da Allah yabani kai a amatsayin miji "Alhamdulillah ala ni"imatullah tana kai nan ta tura mishi ta kashe wayar


Lokacin dayaga sakon,, da karfi yace yessss my habibty na,, baisan lokacin dana rungume anass ba dariya ameer " yakeyi harda rike ciki yace anass kasan fa farin shiga soyayya " kamar zararru,, suke komawa " dariya anass yayi yace eh ai naga alama,, dan iska kawai ni cika ni kawani makaleni,, kamar nine jamila " Allah dai yasoni da nima zanyi auren nan wani kwanakin,,



Ido lumshe bilal yace friends baza ku gane bane,, habibty na ta daban ce,, kyaleshi sukayi , Anass yace malam katashi kashirya kasan,, ana yin la"asar zamu tafi dinner party yau ko kayi kashirya,, " nan ya tashi yashiga,, toilet




Su ameera,, ansha kyau" kayan ankon su zasu saka ,, breziya zata balla amma hannun ta ya kasa kaiwa,, wajan Fatima ta nufa tace please ballamin,, wannan tana nuna mata breziyar hannun ta "", banza ta mata, kusan minti uku tukun,, tace kije yaya ya balla miki,, bazan iya ba " fuskar tausayi tayi tace haba sister nice please ballamin,,, tace a kuma sai kiyi ai juyawa,,, ameera tayi " ta rasa ya zatayi kuka tasoma , duk Fatima najin ta ta shareta, hijab dinta ta saka ta nufi part din bilal tana kuka




Tana tafiya kuma bata dena kukan ba,,zarah ce ta ganta,, zata fice tace ameera lfy kike kuka batayi magana ba sai kara sautin kukan ta da tayi da mamaki zarah ke kallon ta tace kiyi magana,, mana sai a lokacin tace ni wajan yaya zanje " murmishi tayi tace to shine kuma na kuka jeki to nan ta fice tana rera kukan ta duk wanda yamata magana,, bata kulashi har ta kai part din bilal "



Kofar sukaji ana bugawa,, ga kuma sautin kuka " saurarawa ameer yayi da sauri yamike yace wannan wife ce kowa yatabo rigima, bude kofar yayi


Kamar tana jiran shi take da sauri ta fada jikinshi tana kuka,, rungume ta yayi yace,, waya taba min ke ne yanzu yaga hukunci,, dagowa tayi tana kallon shi


Tace yaya ba fatima bace jin haka anass yace kar ayima sweetie na sharri turo baki gaba tayi tace wllh yaya anass babu wani shiri ameer yace kyaleshi muje wancen dakin kifada min ,, nan suka tafi anass yace kundai jidashi iyayen rigima kyaleshi ameer , yayi yace banida " lokacin ka ta matata ", nakeyi nan yabi bayan ameera




Suna shiga yace zo nan,, ba musu ta karasa,, inda yake zaune janyota yayi jikinsa,, yace menene fatima tayimiki "" shagwabe fuska tayi tace ,, wai nace ta ballamin breziya na shine fa tace bata mun saidai " nazo kayimin,, murmishi yayi yace to yanzu ina breziyar "" shijabin ta cire tace gata,, ajikina amma na kasa ballawa "" da sauri ya cafko na fulanin ta,, a tare suka ja numfashi



Cikin kasa da da murya yace,, wife please na rage zafi yau kwana uku fa baki kula dani. Kinzo gidan ammi kin tare,,


Luf tayi ajikinsa,, bata ce komai ba dan ,, itama tana kewar mijin nata,, a hankali tace,, indai zai faranta maka rai ka yi yay " bata kai karshen maganar ba ,, ya hade bakinsu "" duk abinda yamata saita maida mishi , sosai ta taimaka mishi,, sunfi minti,, ashirin kafin ya saketa,, suna maida numfashi saida yasaita kanshi,, kafin ya balla mata,, ya gyara mata sket dinta, "



Yace wifi na Allah, yamiki albarka,, tace ameen yaya rungume ta,, yayi kafin yasaketa, ya kama hanun ta suka fito,




Suna fitowa suka ga su bilal dariya anass yayi yace kaga nasoyan asali " boyewa tayi a bayan,, Ameer tace yaya nidai ka kaini falo,, hannun ta yakama suka, tafi su bilal na musu dariya, Anass yace shege abokina yasamu yar karamar,, yarinya sai sheke ayarshi" yakeyi, dariya sukayi nan suka fita



Suna fita sauran abokansu,, suka zo kowa da motarshi,, gidan su amarya,, jamila suka nufa ", suna zuwa nan aka soma daukar kawayen amarya ana kaisu hotel din da za'a dinner party din


Bayan kowa ya tafi sai ameer da bilal , ameer ne zai dravin dinsu,, suna nan zaune,, aka fito da amarya,,



Ameera ce agaba sai su samira a bayan amarya,, nan suka saka Jamila cikin motar,, tana zuba kamshi mai sanyaya zuciya,, cikin kwalliyar ta na blue din Les mai daukar, hankali



Ameera ta zagaya zata shiga wata kawar jamila tace. Ke yarinya ni zan shiga gaba kallon bakida hankali ameera tayi mata tace ban gane ba ,, wannan ai babu mai ikon zama anan sai ni a kufule,, matar tayo,, kan ameera,,, ta wanke ameera Da mari tana huci tace ke har kin isa ina magana kina maidamin,, ta juya kenan zata dawo tashiga taji itama an wanke ta da mari har hudu ko ina biyu²,, a gigice ta dago tana,, neman wanda ya mare ta,, kai ta daga taga,, Ameer yana huci kamar wani maciji



Ameer yace wllh kinci darajar jamila da saina miki dukan da ko wani,, yace miki ki maran mini mata bazaki kalleshi ba ke har kin isa na zauna waje daya dake kucaka kawai bagidajiya,, to wllh ki kula babu wanda ya isa taba jikin ameera yazauna lfy yana kai karshen maganar tasa ya matsa kusa da ameera



Bude mata hannu, yayi fadawa jikinsa tayi tana kuka bubuga,, bayanta yayi " yana rarrashin ta kafin tayi shuru yace na rama miki maza



Wacce aka mara kuwa haushi da kunya da danasani ne yakamata,, ashe dama matar shice kuma sai taga,, suna mugun kama,, tace wannan kila auren gida ne a kunyace,, ta shiga wata motar,,



Bilal da jamila basuji dadin abinda ya faruba,, haka suka bar gidan sukayi hotel din da ake dinner party din



Abokin ango ne suka tsaya,, a waje saida DJ yasoma kiran amarya da ango da abokan su zasu shigo kowa yashirya nan kowa ya zuba idonshi akan kofar shigowa,,


Jeruwa sukayi bilal da jamila agaba ameer da ameera a bayansu, Anass da fatima abayan su ameer ,, tukun saura mutane suma suka jera ,, nan aka soma shiga,, kida aka kunna " na soyayya,, nan suka shigo, kowa sai kus kus yake yi wasu kuwa, sun dauka ameer da ameera ne,, amarya da angon,, saboda yadda sukayi kyau sosai ga kamannin su da suke da juna


Nan ango da amarya suka zauna,, tukun abokai,,



Nan aka bukaci abokin ango yatashi yabada dan takaitaccen tarihin ango,,, Ameer yakalli anass yace kaje kai kabada, Anass yace kai yafi dacewa kabada ba niba


Ameer yace nifa natsani wai bada wannan tarihin banaso,, Anass yace ka daure mana ,, nan ya mike


Ganin hakan yasa ameera ta mike tace,, yaya zanje wata daga cen tace kai kalli wannan yarinyar duk inda gayen nan yayi sheta bishi dayar tace yayan tane fa ko bakiga suna kama ba,, tace eh kuma hakane da alama ita autarsu ce



Hannun ta yakama,, nan suka je wajan da ake DJ din yabawa, Ameer spika yasoma,, bada tarihin ango,, amma gajeren bayani yabada saboda shifa ya tsani yazo biki yaji ana bada wannan tarihin na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login