Showing 147001 words to 150000 words out of 175796 words
Chapter 50 - AMIR DA AMIRA Complete by Maman Nusaiba.txt
sun karfe 2: pm na rana sukazo kowa so yake yaga ameera har turayya suke , ita kuwa ameera sai dariya takeyi, bayan sun gama ganinta ta nufi wannan umma da yaya safiyan
Ameera tace umma na abbana , tana kukan ganin su ...
[30/10, 19:20] MRS. MU'UTASIM: *🌟AMEER DA AMEERA 🌟*
*STORY AND WRITER BY:*
*MAMAN NUSAIBA CE ✍️*
💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️*
https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl
_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_
*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*
*81—82*
Ameera tayo inda , umma take da sauri tashige jikin umma tana kuka " Umma dinma hawaye takeyi sosai , tace yar inna kindawo garemu Alhamdulillah
Ameera tace umma nadawo dama kaddarar rayuwar dangina ce akaina ,, shiyasa nabar gareku , Umma ga dangin su inna ce da baffa
Dagoda ita tayi tace , to gaske kinga dangin inna
Murmishi tayi tace , eh umma kuje ku gaisa dasu mama da mama , anty karima , yaya umar , da nazeer da kaka usman , muje kigansu
Ciki suka karaso , nan ta zauna , suka gaisa sosai kafin ameera ta gabatar mata da su karima
Sosai umma ke kallon karima " tace lalle jini daya ba wasa bane wannan kama haka yanzu dai , acikin wannan family ku ukun ,, nan kunfi kama ameer da ameera da karima , ga yaranku ma duk masu kama daku
Dariya karima tayi tace , haka ne umma iri baya karya gaskiya ne wannan nan sukaci gaba da hira
Nafeesa ce tashigo gidan tana fadin besty na ina kike shin da gaske ne kindawo
Da sauri ameera ta mike tana nufar nafeesa tace oyoyo besty me welcome back , besty gani nice nadawo ,, rungume juna sukayi , sosai nafeesa ke kuka
Tace besty na ina kike duk wannan tsayin lokacin ,, gaskiya naji dadin dawowar ki garemu
Bubuga bayanta ameera take alamar hararrashi ,, tace kiyi hakuri haka ya isa haka , muzauna kinji
Zama sukayi nafeesa tace , besty ina cikin da kika tafi dashi ko , yazube ne lokacin da kikayi accident
Murmishi tayi tace gasu cen ta nuna mata muhammed
Nafeesa taje ta daukoshi ta rungume ,shi kuwa sai kallon ta yake yana shafa fuskar ta yace mommy ,,, murmishi nafeesa tace na'am my son
Su khadija sai yanzu suka karaso , ita da rashida ,, rashin gurine a motar yasa aka barsu agida saida aka kawo su umma ,, tukun aka koma aka daukosu
Da sallama suka shigo cikin falon
Khadija na baza ido taga inda ameera zata fito ji tayi an rungume ta tabaya
Juyowa tayi wa zata gani, Ameera da sauri ta rungume ameera tace waiyo Allah kawata ,, kece ashe da rabon zamu sake ganin juna
Murmishi ameera tayi tace ,, wllh kuwa gani aminiya ta ,,yasu baba ya mutanen kauye
Khadija na dariya tace suna nan lfy wllh yabayan rabuwa aminiya ta
Lfy lau ameera tace nan suka zauna
Muhammed ne yashigo da sallama dauke da ikram karama ,, tayi luf abinta
Murmishi ameera tayi tace , baban momsy na barka da zuwa
Harara ya aika mata yace kefa na lura , kin maidani kakan ki ko ,, ai yanzu ni yayan ikram ne yar mommy , kanwata ce
Dariya ikram tayi tace , tab wayagama yaya to ai shikenan
Muhammed yace,, dama mommy tace na kawo kanwata , akwai wanda zasu ganta
Inna tace muhammadu kai ne agidan , namu ina maman taka , bazata zoba da zauna ita kadai,
Zama muhammed yayi awajan inna yace eh tace hutawa " zatayi zatazo gobe kila
Flow inna ta wurgawa ,, Muhammed tace dan kan uba " makaryaci yo to inba karya ba yaushe tacema goben ma kila ne " a ina tama wannan magana sangangamin " banza kaima ina ganinka ,, yan kirki ashe kaidin dan uwan ameeru ne to kafita idona
Dariya suka yan falon sukayi ,, Muhammed ,, yace kai inna to mainayi " kike min baa haka ,, da nace dake zanyi maleji nayi wuff dake to ,, tinda naga alama fada gareki ,, bazan aureki na hakuri dama budurwa nake nema kinga sainaje na , aureta
Ameer ne yafito gaishesu yayi , san nan ya dawo wajan muhammed ,, suka yi musabaha
Kallon ikram yayi datayi luf abinta ko mutsin kirki batayi , tayi shuru ,,murmishi yayi yace babyn kaka ,, bako magana ma , taho mugaisa
Kallon ikram tayi , saida tagama mishi kallon tass tukun ta sauko kamar zataje wajanshi " sai ta kalli muhammed tace ,, daddy wannan tana nuna ameer
Dariya Muhammed yayi yace shima daddy kinefa kije ,bak'e kafada , tayi alamar bazata jeba muhammed yace haba ,ke kuwa yar mommy kije
Murmishi ameer yayi yace,, harta manta ni ne lalle yarinyar nan ,Mika hannu ,, yayi zai dauketa
Ita kuwa ikram ,, ganin zai taba ta da sauri ta shige jikin muhammed tasa kuka tace daddy wannan ,, ta nuna ameer da hannu
Dariya sukayi mommy tace tab ,,kaji yarinya yar nema wai uban nakinne wannan
Muhammed yace ,,ai mommy ta manta shine , shiyasa ma take kinsa
Ameer ya kalli ,, Inna yace hajiya inna mai duniya ,, yadai naga sai wani cika kike kina batsewa ,
Muhammed yace wai dan nace nadena auren ta ne fa shine take fushi
Hannu ta daura a kanta tasaka kuka ,,tana fadin innalillahi wa inna ilaihin raju'un
Da sauri su maman karima tayo wajan ta , tace yaya maryame lfy
Ameer ya kalli maman anty karima yace babu wani abu rigimar tace ta motsa ba wani abu bane yafaru
Inna tace ,, kai ameeru uwarka kakewa wannan futsarar,, dan iska marar mutumci ,, dama nasan aiba kaunata kakeyi ba babu ruwana dakai dan banza kawai
Dariya sukayi mata ,,Ameer yace Allah yabaki hakuri inna mu ,, keda zamu baki ikon diya idan wife ta haifo wasu
Inna ta washe baki tace a to shikenan yanzu nadena fushi dakai
Yauma haka suaksha hira abbu ne bai zoba yayi tafiya zuwa abuja inna tace bazata basu labarin ba indai har abbu bai zoba dan , kar ayi babu shi ,, hakura sukayi sai abbu yadawo din ,,suji story din inna da baffa
Bayan sallar isha"i ,su Muhammed suka shigo gidan , ikram na ganin muhammed ta nufesa ,, tana kuka fadi take daddy wannan ,,, da sauri yakarasa yace kai yar mommy waye yatabamin ,, ke har yasakaki kuka
Mama tace babu wanda yataba " ba kawai rigima ce irin ta ta ,,kamar wanda zamu cinyeta danye ,,, kana tafi sallar isha"i tin lokacin take kuka ,, sai da taganka tadena yi wannan rigimar ta ,ai saikai
Daukarta yayi yace haba dai mama kodai kun Mata ,, abinda bata sone shiyasa take wannan kukan , nasan yar mommy akwai rigima amma ,, wannan kuka haka
Hararar shi inna tayi tace ,, kai Muhammed yo mizamu mata ne , yarinya sai shegen kuka to kutafiyar kuma kubar mana gida duk ta ishemu , da kukan ta
Ameer yace haba inna kiyi hakuri dama gidan zasu tafi basai kin fadaba
Banza inna tayi mishi batako kalleshiba ,tayi gaba abinta
Muhammed na ganin inna zata shiga daki yace saida safe inna idan muka tafi sai abbu yadawo zamu zo da ikram dina yaganta ,, yar tsohuwa mai ran karfe
Juyowa inna tayi tace kai dai kazama sallamanme , yanzu dakin ma dazanje bazaka barni natafiba ,, to ina ruwana ma da tafiyar ku dan butar ubanka idan kunje karku dawo ko Abubakar dinma yace ni kaga tafiya ta ,, hutawa zanyi duk kun hanani wali yara kamar haihuwar rana to bazan dauka ba na wuce ,, ta shige dakinta
Dariya suakyi ,ameer yace inna badai masifa ba ,, ai Allah Allah nake abbu yadawo cikin satin nan ,, dan naji story din inna nasan zamusha dariya sosai
Muhammed yace to Allah yakawo shi lfy mu zamu wuce gida
Ameera ta taso tazo inda suke hannu tamika tace yar momma zomuyi sallama ma ,,, mak'alewa ikram tayi ajikin muhammed tace daddy mommy
Murmishi yayi yace to tace bazata zoba ko ana dole ne mayya
Dariya ameera tayi tace ,, asauka lfy ni dama , bandeba tana dangware wa ikram kai
Hannun ta ameer yabuge yace iyee hadda duka haka wife aikuwa zaku bata da kaka wllh ba ruwana
Muhammed ko dariya yayi yace , kunga saida safe , karku sakamin kanwa kuka , nan tafi
A hanya yaga hajara ta labe , fitowa tayi tabi bayanshi saida yace har bayan mota " tukun tace yaya muhammed ,,, bani ikram nagani
Da sauri yajuyo yana kallon ta badan ba ,, yasanta to zaice ameera ce ,, saidai tafi ameera jiki kuma bata kai su ameera farin fataba ,,
Hajara ko ganin ya tsura mata ido ko k'iftawa babu , yasa ta murguda mishi baki tace ,, hala kai baka taba ganina ba kake wani kallona kamar wani tsohon maye ,, tana aika mishi harara
Ajiyar zuciya yasauke yace , a Allah yabaki hakuri sarki fada naga kinmin kyaune fa,
Rufe fuska hajara tayi tana dariya wai taji kunya ance tana da kyau
Murmishi yayi yace to ikram bacci take kibari sai abbu yazo zan kawota insha Allah kwana ma zatayi
Hajara ta leka motar tawa ikram kiss a goshinta tukun ta mishi sallama tayi ciki , shima ya shiga motarshi " yana murmishi sai tuna rashin kunya da hajara tamishi yake yana dariya yace kai