Showing 1 words to 3000 words out of 83936 words

Chapter 1 - KUSKUREN SO Book Complete by Feedohm.txt

Feedoms   

21 Sep 2025

1688

[5/17, 8:18 PM] RN Feedoh: 💧💧 *KUSKUREN SO.*

FREE BOOK.

*HASKE WRITER'S ASSO.*


*FEEDOHM*
Wattpad@Feedohm


  _WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA NAFEESA MUHAMMAD SULE ALHERIN ALLAH YA ƘAI MAKI A DUK INDA KIKE._


*001*


Sautin ƙidan da ke tashi ya hana min jin abinda Teema ke faɗa, don haka na ja hannun ta muka bar falon ina tambayar "Ina make up kit ɗin da na ce ki ɗauko mini?"

"Ummi ce ta ce in dawo in kira ki."

"Lafiya dai ko?"

"Ban sa ni ba, amma na ga kamar Baba Abu ke jiran ki zaku tafi wani wuri."

Wani wuri? Na maimaita a raina, kawai dai ta ce min bata san kiran da ake min ba, amma maganar fita wani guri da baba Abu bana jin aƙwai ta, don haka na yatsina fuska na ce "Koma ciki ki ɗauko min hijabina."

Babu musu ta koma, da ya ke ƙanwata ce ta kusan biyar, kuma tana da matuƙar hankali da bin na gaba, duk da dai ba ita kaɗai ba, duka yaran gidan mu haka suke, na saka hijabin har ƙasa sannan na ɗaura niƙabin da ke jiki, muka kama hanyar gida ina tambayar ta "Da mutane cike a gidan ko?"

Ta gyaɗa kai "Har ƴan maiduguri sun zo, yaya kin ga ƙwalaben turaren wutar da Yadikko ta kawo maki? Tab, wallahi aƙwai ƙyau, please idan kin gama amfani da su ki aje min, idan na tashi aure sai ki bani."

Murmushi kawai na yi ba tare da na ce komai ba, duka nawa take da zata fara tarin aure? Har muka ƙarasa gida tana ƙara jaddada min ita fa tana so kar na fasa, na bi ta da to, da ya ke babu tazara da gidan mu nan da nan mu ka isa.

A falon baba na iske Ummk ita kaɗai, tana tattara kayana, sabida da marece ƴan jere zasu je su yi, na raɓa kusa da ita ina murmushi domin har ga Allah bana jin aƙwai abu mafi soyuwa a raina bayan uwata.

"Sannu da aiki Mom, Ummi, Umma, Mami, Sweetheart, Dearie..

"Ya ishe ni haka." Ta faɗa tana jefa min hararar wasa, sanin idan ina cikin farin ciki zan iya kiranta da sunayen duniya masu daɗi.

Na murmusa "Gani to."

Bata ɗago ba ta ce "Ki kira shi anjima da daddare zaku je a maku test ke da Baba Abu sabida  kin san 11am za'a ɗaura auren."

"Test."

"Eh, kin san dai ba'a ɗaura aure ba tare da shi ba ko?"

Na gyaɗa kai, yayin da yanayi na ya canza, don har ga Allah wannan kalmar na matuƙar ɓata min rai bare ma idan na ji an ce an fasa aure sabida ita, na kalle ta a sanyaye na ce  "Ummi, what of idan genotype ɗina AS ne shima na shi AS ne?"

"Sai a fasa." Ta faɗa kai tsaye ba tare da ta kalle ni.

Gabana yayi mummunar faɗuwa, ba don tana uwata ba, abinda zan faɗa mata ba zai mata daɗi ba, a hankali na ce "A fasa fa kika ce bayan gobe ne ɗaurin aure?Haba Ummi wannan fa kamar yi ma Allah shishshigi ne, su mutanen da da suke auren su ba tare da wani gwaji ba shin sun fasa rayuwa ne?"

Ta juyo ta kalle ni, ina da ƙyaƙyƙyawar alaƙa da uwata, babu kunya bare ɓoye ɓoye duk abinda ke raina bana shayin faɗa mata, na san ta sani sarai ina buƙatar aure, a hankali ta ce "Shiyasa tun tuni na yi ta maki magana ki je a maki test, amma kika ƙi, kuma wannan ba shishshigi bane Nafisa, na san kina da hankalin da zaki fahimci abinda ake nufi."

Ban ce komai ba na miƙe na bar mata gurin, sai dai ina jin a raina ba zan iya haƙura da Sufyan ba, ina son shi kamar yadda ya ke sona, infact Sufyan yana da duk wasu qualities da nike buƙata a wajen ɗa namiji, haka nima ya sha faɗa ina da qualities da ya ke so, sannan shekarata ashirin da baƙwai ban yi aure, kuma sai ace a fasa bayan tsawon lokacin da na ɗauka ina jiran wannan ranar? Shin mutane ma mai zasu ce?

Na faɗa saman lafiyayyen gadona tare da dafe kaina da hannuna da ya sha jan lalle, na sani sarai ni AS ce kuma shima AS ne, domin tun lokacin da Umma ke mitar mu je, mu ka je aka mana, mun ɓoye ne sabida kar a kawo mana wata matsala, so gashi yanzu suna neman kawo mana ita bayan muna gab da cikar burin mu.

Na janyo wayata tare da danna lambar shi, sai da ta ƙare ringing sannan ya kira, cikin taushin murya shi ya mani sallama "Assalamu alaikum, rabin rai na."

"To shi fa rabin na waye?" Na faɗa cikin zolaya, domin duk lokacin da ya faɗi haka nima sai na tambaya.

Amsar shi kullun ɗaya ce "Na rabawa babies ɗin da zamu haifa." Kuma bai canza ba hakan ya faɗa.

Na murmusa ina faɗin "To ina wuni."

"Lafiya lau Alhamdulillahi."

"Hidima fa.? Na tambaya cikin annashuwa.

"Ga ta muna ciki, yanzu haka mun je za'ayi decoration gurin da za'ayi kamu." Ya faɗa a nutse, yana cikin abinda ya sa na aminta dashi, yana da natsuwa da sanyi.

"Huh."

"Ya dai?" Ya tambaya.

Na tausasa murya na ce "Habibi kana so na ko?"

"Tambaya ma ki ke? Kina shakku akan son da ni ke maki?"

Na girgiza kai "Bana shakku kawai dai ka faɗa mani, kasan bana gajiya da jin kalmar so daga bakin ka." Na ƙarashe maganar a shagwaɓe.

"Fiye da so ni ke maki."

Na lumshe ido tare da langwaɓe kai lokaci ɗaya na ce "And you promise zaka kasance da ni a kowanne hali ko?"

"Ba ki yadda ba ne?"

"No, ina so dai ka sake faɗa."

"Wait ma, duk waɗannan maganganun na meye Nafee? Go straight to the point mana."

"About that genotype, ina tsoron ya rabamu Sufyan, wallahi ba zan iya rayuwa babu kai ba, you know.."

Ya katse ni "Dakata please, zaki iya rabuwa da ni ne Nafee?"

"No."

"To meye na waɗannan maganganun, bana jin aƙwai abinda zai iya datse alaƙa ta da ke, ba genotype ba, wallahi ko HIV ke jikin ki zan aure ki a haka, su mutanen baya da suke aure haka nan fa? Kuma suyi rayuwar su normal, ko an faɗa masu lallai sai mun haifi sickler, Please kar ki haɗa min zafi."

A sanyaye na ce "Sorry."

"Ok, sarkin sorry, I love you, an kawo maku drinks ɗazu?" Ya canza maganar.

Na gyaɗa kai kamar yana kallo na "Hum."

"Ok sai me kuke so?" 

A hankali na ce "Babu, komai ya wadata."

"Mun gode Allah."

Na ɗan jirkirta kafin na ce "Ummi ta ce in faɗa maka, idan an yi magrib ka zo zamu je a mana test."

"Allah ya kai mu da rai da lafiya."

Ban san me ya taka ba, domin cikin ƙwarin guiwa ya faɗa duk da ya san cewa ni da shi duka AS ne kuma abu ne mai matuƙar wahala a bar mu muyi aure haka, na sauke ajiyar zuciya ina cizan lips ɗina na ƙasa, Allah ya sani jikina ya yi sanyi, sai dai ƙwarin guiwar da na ji a tattare da Sufyan shi ya bani damar nima dole na jajirce komin runtsi mu mallaki juna.

Mun ɗauki lokaci mai tsawo muna fira, kafin na aje wayar na yi rigingine ina kallon silin idona a lumshe tare da tunani birjit a raina, kafin Fannata ta turo ƙofar tana faɗin "Ya zaki zo nan ki ƙwanta ki baro mutane na jiran ki?"

Na mirgina na tashi zaune ina yatsuna fuska, a hankali na ce "An kawo snacks ɗin ne?"

"Eh."

"Ok, ki je dan Allah, gani nan zuwa nima."

Har ta juya na kira ta "Fannata.! Bana jin ina ta ƙawar da ta fita, childhood friend ce, sannan tun daga nursery har university a tare mu ka yi, shiyasa duk lokacin da nike buƙatar shawara daga ita sai Ummi na ke tuntuɓa.

"Na'am."

"Dan Allah zo ki ji." Na faɗa a sanyaye.

Babu musu ta dawo gabana, na saka hannu na janyo ta ta zauna gefena muna fuskantar juna.

A hankali na ce "Ya ki ka ji ranar da aka fasa auren ki?"

A razane ta ce "Kema fasawa za'ayi Nafee?"

Na girgiza mata kai na ce  "A'a ina so na sani ne."

Ta dafe ƙirji tana faɗin "Wai Allah wallahi har gabana ya faɗi."

"Faɗa min dan Allah."

Idon ta ya ciko da ƙwalla, ta kamo hannuna cikin na ta ta ce "Me zan faɗa miki bayan kin san tashin hankali da na shiga Nafee? Na yi kuka Nafeesa kamar raina zai fita, sabida baƙin ciki  kuma kin san me yafi damuna daga baya? Ta yadda da mutane su ka riƙa cewa wai ni y'ar iska ce shiyasa mijin ya fasa ranar da za'a ɗaura aure, kin san da an fasa auren mace, ba zaa binciki dalili ba, sai a ɗaura mata laifi."

Na jijjiga kai gaskiya ta faɗa, ni kaina bayan fasa auren ta aƙwai ƙawayen mu da yawa da suka tare ni suna faɗar maganganun banza a kan ta, wasu na faɗin wai yawon banza ta ke yi, wasu na faɗin wai cutar ƙanjamau gare ta, wasu na faɗin wai ciki ne jikin ta, bayan duk ba haka ba ne, genotype type ɗin su ne, shi AS ne ita kuma SS ce, shine aka fasa auren.

Ta katse min ɗan gutun tunina "Kun san na ku hala?"

Na gyaɗa kai "Ni AS ce."

"Sufyan fa?"

"Shima haka."

Ta sauke ajiyar zuciya "Yo ai ke da sauƙi, zaku iya haihuwar AA, AS and SS, amma wallahi kar ki yadda a fasa auren nan sabida haka, idan ba haka ba zaa goga maki baƙin fenti, kuma ke fa kuna son juna fiye da mu, Allah kar ki yadda, ni ba gashi ba, bayan fasa auren how many years ko kare bai ƙara leƙo ni ba? Wallahi kar ki yadda Nafee ki kafe kai da fata zaki aure shi haka, abinnan fa duk na Allah ne, kuma dukkan ku kun san yadda zakuyi yi maintaining kar a samu sickler."

Gaskiya ta faɗa, ko babu surutun mutane yadda muke son juna ba zamu iya haƙura ba, don haka na tambaye ta "How?"

"Yo kawai crossing zaku yi, yaron farko suppose to be AA, na biyu SS, kunga sai ku zubar tun kafin ya zo duniya, na uku kuma AS, na huɗu ma AS shikenan fa, ke daga biyun ma sun ishe ku rayuwar duniya, amma wallahi kar ki sake ki yarda, ai yadda kika daɗe baki samu mijin nan ba, kuma Allah ya zaɓo maki gwarzo a maza, mai ƙaunar ki, da tausayin ki, idan kika sake shi kin kaɗe, ni dai na faɗa maki, ni kaina ina takaicin rashin aurena. "

Kalamanta suka ƙarfafa min guiwa, na murmusa na ce "Thank you Fannata.

"Au to, tashi mu je dan Allah, har yanzu ba'a kawo ledan da za'ayi packaging ba."

Na dafe kai "Oh kinga na manta, amma nawa ledan?"

"900 guda 100 irin happy ɗin nan."

Na ciro 3k na miƙa mata "Allah ku je ku siyo."



*UWAR SUKUM.*
[5/17, 8:18 PM] RN Feedohm: 💧💧 *KUSKUREN SO.*

FREE BOOK.

*HASKE WRITER'S ASSO.*



*FEEDOHM*
Wattpad@Feedohm



  _Wannan littafin gaba ɗaya sadaukarwa ne ga NAFEESA MUHAMMAD SULE Alherin Allah ya kai maki a duk inda kike, maman Jinjiri (Salman)._



*002*

A sanyaye na ƙarashe yinin ranar, ina jin yadda friends ɗina ke man tsiyar wai har na fara missing gida, kar fa na masu kuka, wai sai ka ce ba Sufyan zan aura ba? Da ya ke gaskiya duk wanda ke tare dani ya san zazzafar soyayyar da ke tsakani na da Sufyan, domin kusan 3years muna tare, kuma bama iya ɓoye ƙaunar juna a ko'ina ne, sai dai na ce masu humm kawai, yayin da na cigaba da harkokin gabana a sanyaye.

Gab da magrib muka koma gida, na iske gidan cike tab da jama'u da yawan su daga nesa suka zo, sai na ji zuciya ta ta karaya, idan aka ce an fasa auren sanadin genotype ɗin banzar nan ya zasu ji? Sai ga hawaye na bin kumatuna, sai na ji dama tun lokacin da muka je muka yi na faɗa gida kuma na dage lalai shi zan aura, na san da tuni an wuce da level ɗin.

"Amarya baƙya laifi." Na ji muryar Sani abokin wasan mu.

"Hmm.." Na faɗa ina ƙoƙarin gifta shi.

Ya sha gabana "Ina kike ƙoƙarin tafiya? Ke da gidan ma barin shi zaki yi?"

"Sallah zan yi." Na bashi amsa a taƙaice wanda da da ne, da tsayawa zan yi mu fece juna, duk da dama ba irin dogon wasa nike dashi ba.

Daga haka na gifta na shige ɗaki, nan ma cike ya ke tab da ƴan biki, yo bikin farko ne fa da zaa fara yi gidan mu, na lumshe ido ina jin yadda suke nan nan da ni, masu tambayar na ci abinci daban masu tambayar ya nike daban, kun dai san yadda amarya ta ke da farin ciki, sannan kowa so ya ke ya ƙyautata mata, ni dai Allah ya sani murmushin yaƙe kawai nike bin su da shi, na tsafa na shiga toilet ɗin ɗaki na yo alwala, sannan na koma falon baba na kabbara sallah.

Bayan na gama na rafka tagumi ina jinjina yadda iyayena zasu amince da auren mu, duk da na san abu me mai matuƙar wahala su aminta, sai na ji ɗan kamun ma da za'ayi ya fita a raina.

Fannata ta shigo da mai make up tana faɗin "Kin san fa da an gama isha'i zaa tafi shine kuma kika zauna anan."

"Ni a bar make up ɗin nan dan Allah bana so." Na faɗa a sanyaye.

"Me yasa?"

"Haka kurum."

Ta girgiza kai "Aikam ba zai yiyu ba, tashi dan Allah."

Ta matsa min dole saj da aka fante fuskata, ina tsaka da saka kaya Ummi ta ce in fito ga Baba Abu nan na jirana, na lumshe ido ina faɗin "Wai ba zaku bar wannan abin ba? Wallahi bai da wani amfani?"

Ta tsura min ido na ƴan daƙiƙu, a hankali ta matso kusa da ni tana faɗin "Ko da matsala ne Nafeesa?"

Na zunɓuri baki ina girgiza kai sannan na ce "Kawai bana so ne."

"Ki faɗa min gaskiya tun kafin ku je idan da wani abu." A yanayin yadda ta yi maganar ne yasa na bita da kallon neman ƙarin bayani, don da alamu ta kaini inda ban je ba.

"Eh, idan da matsala ki faɗa min, don haka kawai ba zaki ce baƙya son zuwa ba." Ta jaddada mini tana ƙare min kallo.

"Me kike nufi Ummi? Wace irin matsala?" 

"Ya za'ayi in sani? Ke na ke tambaya nima."

A raunane na girgiza kai ina faɗin "Babu." Na ɗauki hijabina na saka na zura takalmi na yi gaba da saƙe saƙe tab a zuciyata.

A harabar asibitin muka iske Sufyan, tun kafin na fito daga mota na zuba mashi ido, yana sanye da lallausan farin yadi da yayi matuƙar ƙara mashi ƙyau, kan shi sanye da baƙar dara, wallahi ko maƙiyi ya ga Sufyan ya san ya haɗu, kuma irin shi ɗaya ne a cikin dubu, ta haske fitilun dake harabar asibitin ina iya hango yadda lips ɗinki ke glowing lokacin da yake gaisawa da wani nurse da ya gifta, na bi hannun shi da yake ƙoƙarin sauƙewa fari tas mai yalwar farin gashi, kai da ganin skin ɗin kasan hutu da jin daɗi sun zauna gurin na lumshe idona a hankali ina girgiza kai, a hankali na tabbatar wa da kai na "I can't bear to loss Sufyan no matter how wallahi."

"Me kike tunani?" Babu abu ya katse ni, wai ashe har ya fita a motar ya zagayo ya buɗe ƙofar waje na.

Na sauke nannauyar ajiyar zuciya tare da girgiza kai alamu babu komai yayin da na sauko ƙafafuna, na soma tafiya tamkar wacce ƙwai ya fashewa a ciki, ji nake kamar na faɗa masu kar suyi asarar lokaci da kuɗin su, domin already mun san makomar mu, kuma a hakan we are ready mu rayu a tare.

Da sauri ya tare mu, ya rusuna haɗe da damƙe hanun Baba Abu da hannayen shi biyu ya gaisar da shi cikin dattako da mutuntawa, kafin baba Abun yayi gaba ya barshi a baya, sannan ya yo tako biyu baya, ya jera dani yana aika min da wani irin tattausan murmushi da ya sa har ban san lokacin da nima murmushin ya suɓuce min ba.

"Na ce wani abu?" Ya raɗa min a kunne.

Na jefa mashi hararar soyayya ina faɗin "Kin yi ƙyau Nafee!

Ya ware lumsassun idanun shi yana faɗin "Au har ma kin san abinda zan faɗa?"

Na ɗage gira ɗaya "Humm, ko da wani abu?"

Ya girgiza kai "I love you."

"Thanks.."

Bai ce dani komai ba, sai hararar da ya jefa min mai cike da tsantsar soyayya, yayin da na murmusa ina ganin asarar da ake shirin yi min wacce bana tunanin zan iya ɗaukar ta.

Lab muka je aka ɗauki jinin mu, sannan muka koma inda mutane ke jira, ni kam har ga Allah zuciyata ta gama tsinkewa, addu'a ni ke Allah ya sa test ɗin ya bayar da ba dai dai ba, ko kuma na'urar ta lalace gaba ɗaya, yayin da Sufyan ke gefena yana min fira jefi jefi.

Bayan ɗan lokaci kaɗan result ya fito, still dai ni da shi duka AS ne, tun a lokacin na fara hawaye, jin yadda doctor ke ƙoƙarin haramta mana auren juna, yana ƙoƙarin dole sai ya canza zanen ƙaddarar mu, ni kam tashi na yi na fice daga office ɗin, yayin da na bar Baba Abu da kawun Sufyan suna tattaunawa da doctor.

Jikin mota na tsaya na juya baya na kifa kai a jiki ina rera kuka, ina jin saukar lumfashin Sufyan a bayana, yayin da ya ke ƙoƙarin kai hannu ya taɓani sai kuma ya fasa sanin har yanzu ba mu zama mallakin juna ba.

Can ƙasan murya na ji ya kira sunana "Nafee...!

Ban jiyo ba, sai dai kukana da ya tsaya cak, jin muryar tashi ta tsirga ni tun daga kaina har yatsun ƙafata.

"Kukan me kike? Shin kina tunanin zaki rabu da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login