Showing 9001 words to 12000 words out of 83936 words

Chapter 4 - KUSKUREN SO Book Complete by Feedohm.txt

Feedoms   

21 Sep 2025

1720

yawo a ƙirjina, ban san lokacin da hawaye suka wanke min fuska ba, ko wacece waccen Hanifar ba mai ƙauna ta ba ce, kuma dan uwarta da take maganar haihuwa da mutuwa ƙarya ta ke yi, Ni As ce shima As ne, ba duka yaran mu bane zasu zo a sikila, dole wasu normal wasu kuma kariya, wasu sikila, kuma Sufyan ya ce zamu iya tsarawa.

Sai na ji tamkar na je na cakumeta ta bar min gidan dan uban ta.



*UWAR SUKUM.*
[5/17, 8:18 PM] RN Feedohm: 💧💧 *KUSKUREN SO.*


FREE BOOK.


*HASKE WRITER'S ASSO.*



*FEEDOHM*
Wattpad@Feedohm


_Wannan littafin gaba ɗaya sadaukarwa ne ga NAFEESA Muhammad SULE Alherin Allah ya kai maki a duk inda kike, maman Jinjiri Salman.._





*006*


*IDAN KAJI GUƊA DA LABARI...!!!*

_INA MASOYAN ASMY B ALIYU? ALBISHIRIN KU? KUCE GORO....! OHO... HO.. HO... KO KUNSAN A SABUWAR SHEKARAR NAN TA SHIRYA KAWO MUKU DADDAƊAN LABARI MAI SUNA Muhabbatil Qalb? TAFIYAR TA FARA NISA, WASAN KUMA YANA TA DAƊI._


_*SHIN KINSAN YADDA AKE SHIGA CIKIN RAYUWAR ƊIYA MACE A LALATA MATA MUTUNCI, A TARWATSA DUK WANI KYAWU NA TA? KUNSAN YADDA ZAMANI YA CANZA? KI SHIGO CIKIN TAFIYAR DAN KISHA ROMAN ILIMI DA KUMA HANYOYIN DA ZAKI SAN ANA BI DAN SHIGARKI CIKIN WANNAN HATSARIN.*_

ASMY B ALIYU KUNSAN BATA WASA A CIKIN TAFIYAR TA. KARKI BARI AYI TAFIYAR BABU KE. SAMUN ILIMIN KADAI ABIN ALFAHARINKI NE MAI SIYA.

*MUHABBATIL QALB*🔥
*MUHABBATIL QALB*🔥
*MUHABBATIL QALB*🔥

AKAN NAIRA 300 Kacal ne.

0004157137
Asma'u Buhari Aliyu
Jaiz bank

Ko katin waya ta 07043079282
Shaidar biya ta 07065283730 view WhatsApp





**********************

Ya aje ledar da ya shigo da ita a gaban Umma, ya durƙusa fuskar shi ɗauke da fara'a yana faɗin "Umma ai ba ku faɗa min zaku zo ba, da na je da kaina na ɗauko ku."

Umma ta ja ledar ta buɗe ba tare da ta amsa maganar shi ba, sannan ta kalli Hanifa ta fiddo ido waje ta ce "Shagali, tashi ki ɗauko plate kaji ne."

Bata ko kalli inda ni ke ba, ta wuce kitchen ɗin, sai ga ta da sabon plate ɗina wanda ban taɓa amfani da shi ba, sai na ji raina ya sosu, na sadda kai ƙasa ina wasa da yatsuna, ban taɓa ganin wannan bala'in da uwar miji zata zo gidan ɗanta da bai yi wata da aure ba, ta zauna har da ma wata banza can kalar dangi.

"Shalele ba oyoyo.? Sufyan ya katse ni.

Sai na ji sanyi, a tunani na zai share ni a gaban uwar shi da ƴar uwar shi, amma sai na ga ba haka ba, sabida cike da soyayya ya yi maganar.

Na ɗan murmusa tare da kau da kai cike da kunya na ce "Sannu da zuwa."

"Au haka ake min dama?" Ya ƙanne min ido ɗaya.

Na kalli Umma na ga sam ba ta mu ta ke ba, na ɗan mashi alamun ba mu kaɗai bane a gidan, amma sai na ga ya fuzge tare da miƙewa tsaye ya kamo hannuna yana faɗin "Mu je ki haɗa min ruwa in watsa, na ƙwaso gajiya, kuma ki saki jikin ki, Umma bata da matsala, zata fi so ma ta ga kina kular mata da ɗa yadda ya kamata."

Kunya ta kamani na janye hannuna, lokacin da Umma ta ce "Ni dai indai zaa haifa min jikoki an gama da ni."

Sufyan ya ƙwashe da dariya yayin da na yi ɗaki cike da kunyar ta, ya biyo bayana yana min dariya, ya matse ni jikin shi yana kallon fuskata, tare da ɗago haɓata ya ce "Ya kika ga Umman tawa?"

"Lafiya lau."

"Uhmm, bata da matsala, sannan kar ki damu da abinda ta ke faɗa wasa ta ke maki."

Na gyaɗa kai tare da zagaye shi da hannuna, a kunnen shi na raɗa mashi "Ita fa waccen?"

"Hanifa?"

"Uhmm..."

"Ɗiyar ƙanwar Umma ce, mahaifanta sun rasu tun tana ƙarama, a gidan mu ta tashi."

Na haɗiyi yawu na ce "Uhmm."

Ya ɗago ni daga jikin shi, tare da kama kafaɗata ya ce "Ta miki wani abu ne?"

Na girgiza kai.

"Na fa san halin ta, bata da kirki, kuma tana da ɗaurin gindi gun Umma, you have to be very careful kafin su tafi."

Na ce "Bakomai."

"Na sani baki da matsala Nafee, kuma ba zasu fi 2days ba zasu koma, dan Allah komai zata miki ki kauda kai kin ji ko? Kuma nima bazan yadda wani abu ya taɓa mutuncin ki ba."

Na gyaɗa kai tare da sakin lallausan murmushi, sai dai ina jin tamkar waccen zata kawo min matsala a rayuwar aure ta, ina so na mashi maganar Amadi da yazo ya ƙi barin shi ya shigo amma na danne, ina jin tunda sau ɗaya ya faru ya kamata na share, bai dace na soma ƙorafi ba, kuma sai wani sashe na zuciyata ke tunar min da ƙyila zumar amarci ce, baya so wani abu ya kawo mana waigi a tsakanin mu.

Don haka na share, na taimaka mashi ya yi wanka, sannan muka koma gun su Umma, sai dai abin mamaki kamar wasu mayu sun cinye kaza ɗaya da rabi, rabin da suka bar mana ma duk an yakushe tsokar, sai na ji ba daɗi, na ƙwashe sauran na miƙa mashi.

"Bara ki ci ba?" Ya tambaye ni.

"Na ƙoshi."

Ya murmusa "Ban taɓa ganin mai gudun nama ba irin ki."

Hanifa ta amshe "Ko kuma tana gudun sauran surukar ta."

Na ɗago na kalle ta, na sunne kai ina ina faɗin "A'a wallahi, ta ya zan guji sauran mahaifiyata, ai Umma ba suruka ba ce, uwa ce." Yayin da a zuciya kuma na ke faɗin "Shegiya, banza, sakara, uban wa zai ci sauran ki? Bazan ci ɗin ba, idan kin isa ki tursasani."

Sufyan ya ce "Rabu da ita Shalele, neman magana ne."

Ni kam ban ƙara cewa uffan ba, ina dai ganin yadda ta taɓe baki tana hararar mu sama da ƙasa, yayin da Umma ta yi kamar bata san me muke ba, ta ɗaga kai tana sakuce tana kallon Arewa24.

Ƙwana biyun da suka yi, sai na ji ni a takure, bana wani samun sake wa da Sufyan kamar baya, ga ƙa'idoji daga gun Umma, bata cin kaza bata shan kaza, duka dai wannan ban ɗauke su a bakin komai ba, domin uwa na ke kallon ta, matsalar waccen ƴar iskar Hanifa ce, da ko cokali ta yi amfani dashi sai na kauda mata, ga wani kallon banza da ta ke bina da shi, ƙiri ƙiri ta ke nuna min tsana.


*********************

Saƙon Fannata ya shigo waya ta "Ina ta kiran ki baƙya ɗauka ina ce lafiya Nafee?"

Na karanta yayin da jikina ya yi sanyi, ina son bin maganar Sufyan kuma ina ganin tamkar ban ƙyautawa abota ba, domin tun muna ƙanana muke tare, da daɗi da ba daɗi, hasalima tindaga nursery, primary, secondary har tertiary a tare muka yi, na lumshe ido ina lasar laɓɓana, ban san me yasa ya ɗauki fushi da ita har haka ba, bayan ni ban ɗauki maganar ta da wani fa'ida ba, kuma Fannata ba ta ce in rabu da Sufyan ba, ba ta ce in daina son shi ba, bata ce in bar yi mashi biyayya ba, ba ta ce in bar yadda da maganar shi ba.

Kiranta ya shigo waya ta, sai da na yi Astagfurillah sannan na ɗauka, don ji na ke saɓawa Sufyan kamar saɓawa Allah ne, kuma dole idan ya dawo na nemi yafiyar shi.

Bata amsa sallama ta ba ta fara da "Dama ance sai gama wasan ƙasa tare, sannan ka gama wahala da yarinya ka kaita ɗakin mijinta, da ta san daɗin abin sai ta nuna ta fi ƙarfin ka."

Ciki ciki na ce "Ba fa haka bane."

"To ya ne? Haba Nafee a zatona ko da zaki rabu da ƙawayen mu ban dace ki rabu da ni ba."

"Wai waya faɗa miki rabuwa na yi da ke?

" Koma dai menene, ni zo ki buɗe min gate gani ƙofar gidan ki, ko yau ɗin ma baƙya nan, kamar shekaran jiya.?

Na yi jim, ban dai isa na ce bana nan ba, domin yanzu almajiri ya fita siyo min ruwa, da ya ke na mu ya ƙare kuma Sufyan ba yanzu zai dawo ba, na miƙe a sanyaye tare da aje wayar, na hau safa da marwa, shin in buɗe mata ko in kira Sufyan na fara neman iznin shi.?

Daga ƙarshe dai na yi dialing number shi, bugu ɗaya ya ɗauka yana min kirari "Shalele, sarauniyar zuciyata, mata ɗaya tal a gidan Sufyan, hasken da ke haskaka...

"Sufyannnnn....." Na katse shi cikin wata rikitattar murya.

"Matar Sufyan."

"Wai Fannata ce..." Na faɗa a shagwaɓe.

"Ba na ce kar ki ƙara waya da ita ba Nafee."

Na shagwaɓe murya "Tana ta kira nq bana ɗauka, shine ta kirani da wata lambar, ina ma jin ita ne sai na yan ke, to yanzu na aiki almajiri ya siyo mana pure water, shine sai ganin ta na yi cikin gidan, please dan Allah ka min iznin ta shigo, ka san dai babu wanda ya isa ya canza min ra'ayi a kan ka ko? Please Sufyan ba zan iya korar ta ba, tun muna ƙanana muke tare, kuma duk abinda na mata zata je ta faɗawa Mama, please Sufyan."

Ya ɗan yi jim kafin ya ce "Ni fa bana son ƙawayen da zasu zo su hargitsa min gida."

"Idan ka ce in kore ta sai na yi Sufyan, bazan so na ɓata maka ba ka sani, bara na ce ta tafi kawai."

"No ki barta ta shigo, amma ki kula da magulmata, sannan if possible, ki min recording in ji abinda zata ce kin ji Shalele na. "

"Recording.? Na maimaita.

"Yes, baki san yadda na tsani duk wani abu da zai shiga tsakanin mu ba ko? Baki san yadda ni ke mutuwar son ki ba ko Shalele? Komai fa zan yi don ke ne."

A sanyaye na ce "To."

"Za ki yi ko.?"

"Uhmm.."

"Good, Allah ya miki albarka kin ji ko, yau ki huta, zan taho mana da abinci,i love you.."

"I love you too.." Na yanke wayar sannan na je na buɗe mata ƙofar, yayin da ta watsa min harara "Ai na ɗauka ba za'a barni na shigo ba har ina ƙoƙarin juyawa."

Na saki murmushin yaƙe na ce "Ni na isa."

Muka ƙarasa falon, na danna recording sannan na aje wayar bayan na kawo mata yoghurt da cake, sabida bani da ruwa ko kaɗan a frigde.

"Ina Sufyan ɗin, zuwa na yi in mashi tsiya, shekaran jiya fa na san kina nan, amma ɗan tahalikin nan ya hanani shigowa."

Na ce "Ai ko bana nan."

Ta watsa mun harara "Da Allah, kar ku raina min wayau mana, ba na ga lokacin da almajiri ya fito da abinci ba, kuma na tambaye shi ya ce matar gidan na ci, dan Allah yana ina? Ni fa ruwa na yi na roƙe shi Allah kar ya raba ni da ke, kin san dai ban da aminiya sama da ke ko.?"

Na ce "Hmm, yana aiki."

Ta kauda maganar "Ya gidan? Ya amarci? Kin ga yadda kika yi fresh kuwa?"

"Lafiya lau Alhamdulillahi."

Ta ɗauko yoghurt ɗin ta zuba a cup, sannan ta gutsuri cake ɗin tana faɗin "Wallahi kuwa Nafee, kin gan ki dan Allah?"

Na ce "Hmm, daga ina ki ke.?"

"Asibiti."

"Lafiya kuwa?"

A sanyaye ta ce "Wallahi Aunty Fati na raka, kin san ta sa inplan tun tana amarya, to kuma ta cire amma har yanzu babu ciki babu dalilin shi, gashi daga ita har mijin suna son haihuwa."

Na ce "Hmmm."

Ta ɗan zamo daga kujera ta ce "Nafee, ke ma na san halin ki, dan Allah kar ki yi wani planing har sai kin tabbatar da kina haihuwar, wallahi tausayi ta ke bani."

"Hmmm.." Na kuma faɗa.

Ta watsa mun harara tana faɗin "Ki ke ta wani hmm, ina magana."

"To me zan ce Fannata?"

Ta taɓe baki tana harara ta, yayin da ta cigaba da cin abinta sai da ta yi nak, tana jefa min fira sama sama, ni kam daga Umm sai hmm, daga ƙarshe dai ta auna min zagi, wai don ta zo gidana nake mata iskanci, ta miƙe ta fice abin ta.

Ban wani damu ba, na kashe record ɗin, sannan na faɗa toilet na silla wanka, na tsantsara ƙwalliya ta ke ce raini, yayin da wani bangare na zuciyata ke nunan kamar abinda na yi ban ƙyauta ba.




*UWAR SUKUM.*
[5/17, 8:18 PM] RN Feedohm: 💧💧 *KUSKUREN SO.*


FREE BOOK.


*HASKE WRITER'S ASSO.*



*FEEDOHM*
Wattpad@Feedohm



_Wannan littafin gaba ɗaya sadaukarwa ne ga NAFEESA Muhammad SULE Alherin Allah ya kai maki a duk inda kike, maman jinjiri Salman Allah ubangiji ya bawa Yaya lafiya, ya sa kaffara ne.._



*007*



Sai da ya ci abinci ya ƙoshi, sannan ya janyo ni jikin shi yana tambayar "Ina Assignment ɗina?"

Na saki murmushin yaƙe tare da miƙa mashi wayata a sanyaye, don wallahi sai na ke jin tamkar ban ƙyauta mata ba kuma na tabbatar abinda zai ji ba zai tsaya ya mata ƙyaƙyƙyawan zato ba, sai ma ƙara tsanar ta da zai yi, ya ƙarɓa ya bude, da ya ke hannun shi zai iya buɗe fingerprint ɗin wayar, ba buƙatar ya bani na buɗe.

Daga ni har shi muka saurara, na yi fiki fiki yadda kasan wacce ta gilla ƙarya, sannan ya aje wayar gefe ɗaya ran shi a ɓace yana kallona, kafin ya ce "Wannan Fannatar munafuka ce."

Na yi shiru jikina na rawa, ya ture ni daga jikin shi, ya gyara zaman shi sosai sannan ya cigaba da faɗin "Wallahi idan na kuskura na ƙara ganin ta ƙofar gidana sai na ci mutuncin ta, banda iskanci da munafunci ita ce zata faɗa maki kar yi planing? Kenan tana nufin komai za ki yi sai da iznin ta? Ita ke auren ki Shalele? Idan ina da ra'ayi fa?"

Na girgiza kai a sanyaye alamun aa, ya ƙara ɗaukar wayar a karo na biyu, ya shiga call log ɗina, ya saka number ta a black list, sannan ya juyo yana faɗin "Idan ta kira ki ba zai shigo ba, ke ma bance ki nemeta ba, tarayyar ku ba alheri ba ce, wallahi baƙin ciki take maki kin yi aure kin bar ta, shiyasa ta soma maki gutsuri tsoma, idan har ba mataki aka ɗauka ba, babu abinda ba zata faɗa maki nan gaba ba, banda ma iskanci uban me zai sa ta ƙwaso matsalar wani ta faɗa maki? Kenan kema ta ki zata ɗauka ta kai ma wata.?"

Na yi shiru ƙwalla suka taru a idona, ya sake kallona jin banda da niyyar yin magana, wannan karon a tausashe ya tambaye ni "Kin yi waya da Mama ko.?"

Na gyaɗa mashi kai ina share guntayen hawayen dake maƙale a idona.

"Me ta ce maki?"Ya jeho min tambaya tare da kafe ni da ido.

Na yi saurin kallon shi cike da mamakin furuncin shi, a hankali na ce "Kamar ya?"

Ya sake ɗaure fuska "Kin fahimci me na ke nufi ai, ko laifi ne don na bibiyi lamarin ki?"

"Gaisawa mu ka yi." Na bashi amsa idona na kan shi nima.

"Kaɗai?" Ya ƙanne min ido ɗaya.

"Uhm."

Sai na ga ya saki murmushi tare da janyo ni ya rungume yana shafa fuska ta "Matar so fa ce ake kula da lamurran ta, kar ki ji ba daɗi, ina matuƙar ƙaunar ki Nafee, kuma bana so duk abinda zai kawo matsala a tare da mu."

Kamar na tambaye shi, yana zaton Mamana zata so matsala a tsakanin mu bare har ta haifar da ita? Sai kuma na share sabida daddaɗan kalaman da yayi amfani da su daga ƙarshe, na ƙara lafewa jikin shi ina shaƙar ni'imtacce ƙamshi daga gare shi.

Tsawon minti biyar yana shafa bayana, sannan ya ce "Na faɗa maki ina da Yaya da ke aiki Saudiyya ko?"

Na gyaɗa mashi kai, ya cigaba da faɗin "Tana da yara uku dake hannun Yaya Auwal, shine suka sa rigima wai zasu zo miki hutu nan da sati ɗaya."

A sanyaye na ce "Allah ya kai mu."

"Ba su da matsala, babbar shekarar ta tara, sai mai bi mata shekara 7, ƙaramin ne ke da biyar, ko aikin gida sun taya ki kafin su koma."

"Uhmm." Na faɗa tare da mamakin shi, wato shi na shi ƴan uwan suna iya zuwa gidan shi, amma ni nawa ne banza, da duk lokacin da suka zo sai ya tare su bakin ƙofa ya ce bana nan, anya dai dai ne kuwa, anya babu KUSKURE a SON da nike ma Sufyan?

"Nafeesata.....! Ya kira sunan cikin ƙauna.

"Na'am."

"Ina son ƴan uwana, dan Allah ki so su."

Samun kaina na yi da faɗin "Nima."

Sai ya share zancen, ya canza salo baki ɗaya, yayin da ya ɗauke ni cak muka faɗa bedroom.


*****************

"Please dan Alllah in shirya ka aje ni gida? Idan ka tashi daga aiki sai ka biya ka taho da ni." Na ƙarashe maganar tare da langwaɓe kai.

Sai da ya yi jim, tukun ya aje turaren da ke hannun shi, ya matso sosai ku sa dani, ya janyo ƙuguna jikin shi, cikin kunnena ya raɗa min " Me zaki yi?"

"Na yi missing ɗin su ne, kuma jiya Amadi ya ce min Baaba bai jin daɗi."

Fara'ar fuskar shi ta ɓace, abinda na fahimta baya ƙaunar mutane na zuwa gidan, muddun ba dangin shi ba ne, a hankali ya ce "Yaushe ya zo?"

Nima fuskar na ɗaure na ce "Da marece."

"Aiko shi aka yi?"

"Uhmm."

"Ok." Ya sake ni ya ƙarasa jikin gado ya ɗauko kayan shi ya saka, yayin da nike bin shi da kallo cike da ƙauna ganin ya ƙara masifar ƙyau, dama can Sufyan ba daga baya ba, don zan ma iya cewa ya fini ƙyau.

Na ɗauki agogon shi na matsa na ɗaura mashi, tare da fesa mashi turare sannan na ɗaura mashi hula na ja da baya ina murmushi, kafin na ɗauki fito ina faɗin "Ka yi ƙyau Habibi..."

Ya sumbaci goshina cike da annashuwa, na gama fahimtar ba mata kaɗai ke son a yabe su ba, hatta maza suna shiga shauƙi a duk lokacin da muka yabe su.

Ganin yana niyyar fita ya sa na tari gaban shi, na langwaɓe kai tare da marairaicewa na ce "Please."

"Ɗauko hijabin ki."

Na ɗan yi tsallen murna sannan na ɗauko doguwar har ƙasa na sa, shi da kan shi ya ɗaura min niƙabi.

A mota ya ke ce min wai banda ƴan maganganu, kar na saki jiki na ƙwashe sirrin mu na faɗa ma Mama, dan Allah na riƙe sirrin gidan shi.

Ni dai to kawai na bishi da shi, don ban fahimci sirrin da ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login