Showing 18001 words to 21000 words out of 83936 words

Chapter 7 - KUSKUREN SO Book Complete by Feedohm.txt

Feedoms   

21 Sep 2025

1711

ya ce "What ever, ta koma gidan su."

"To akan me? Bayan turo ta akayi ta taimaka min.?"

"Babu abinda ba zan iya maki ba, don haka bama buƙatar ta anan."

Raina yayi masifar ɓaci, sai ga hawaye na bin kumatuna, a hankali na ce "Sauƙin abin ma tana da gidan uba. "

"What ever." Ya faɗa yana ɗage kafaɗa.

Na wuce fuuu na fice daga ɗaki, sai dai a falo na tsaya ina ƙoƙarin samo ƙaryar da zan mata ta tafi ba tare da ta ga laifin Sufyan ba, amma wallahi na rasa.

Na fi minti goma a tsaye, na tsinkayi muryar shi yana faɗin "Idan bara ki iya faɗa mata ta fi gida ba, ni bara in faɗa mata, ta bar min gida wallahi, babu gun ƙwanan ta anan."

Na yi ɗakin da sauri har ina tuntuɓe, don na san zai iya ƙwaɓa komai, kuma ina tsoron itama ta yaɓa mashi magana, don gwalɓi ce, bata barin ta ƙwana, a zaune na iske ta bisa katifar da ke yashe tsakar ɗakin, na ƙarasa na zauna kusa da ita, na kamo hannunta ina faɗin "Teemah ko zaki tafi gida, Maman shi ce bata jin daɗi shine ya ce in shirya mu tafi, kuma ƙyila mu ƙwana acan."

Ta ƙura min ido "Ke dai kawai ya ce in bar mashi gida.

"Aa wallahi, ya za'ayi ya ce haka, ai rashin lafiyar ta ce ma ya sa duk kika ga ya canza."

"Allah ya sawaƙe.." Kafin na sake magana har ta finciki jikkarta ta miƙe tare da turo kallabinta gaban goshi, ta fice daga ɗakin tana hura hanci, ta wuce shi falo ta ƙara sama da kai abinka da balaga na gaya mata banza banza ba.

Ya bita da harara "Ki gaida gida." Ya ciro 1k ya miƙa mata ya ƙara da faɗin "Amshi ki hau machine." Ina jin shi ƙasa ƙasa ya cigaba da faɗin "Haka kurun ka auro ɗaya a cika maka gida dan masifa, to ni ba zan ɗauka ba wallahi."

"Ba'a ƙafa na zo ba." Ta bashi amsa tana wani munafukin murmushi tare da bugun jikkar ta.

Sai kuma na ji ba daɗi da ta gaya mashi magana, don na fahimci ya gane abinda ta ke nufi don har ya canza fuska, na bita da sauri na tare ta bakin gate ina aikata mata da harara "Meyasa baki da kunya?"

Ta kalle ni sheƙeƙe ta ce "To me na yi?"

"Abinda kika ce ma Sufyan ya dace?"

"To a ƙafar na zo? Ko shi ya bani kuɗin abinda ya kawo ni? Ke ni fa yaya wallahi bazan kuma zuwa gidan ki ba, ai ni ba yarinya ba ce da zaki min wayau, tunda ya shigo na fahimci baya ƙaunar zuwa na, kuma ai kafin na zo wasu sun zo, abinda ya min shi ya masu, nan auta ya zo kina ciki ya hana shi shiga, kuma wallahi na san kin sani amma baki mashi magana ba."

A fusace na ce "Uban wa ya ce miki hana shi shigowa ya yi.?

"Dole ki zage ni, ke mai miji, ni wallahi ko aure na yi namiji bai isa ya wulaƙanta min ƴan uwa ba, amma ke ki......

Daga bayana muka ji muryar Sufyan na faɗin "Ashe baki da kunya Fatima? Au faɗa mata kike ta ci mutuncina don na ce ki tafi gida?"

Na juya a razane ina faɗin "Dan Allah Sufyan ka yi haƙuri ka koma, ba h...

Ya ɗaga min hannu "Dakata Nafee..

Teema ta zunɓuri baki gaba tana hura hanci, yayin da ya tako kusa da ita ya na jefa mata wani mugun kallo, ya nuna mata ƙofa "Fita..."

Ta watsa mashi harara tana faɗin "Sauƙin abin kafin na taka gidan ka, kai ka fara taka gidan ubana, kuma gidan ka da nace ba zan ƙara zuwa ba, wallahi na fasa tunda abin rashin mutunci ne, sai na shigo ɗin ni da ka riƙa sintiri gidan mu na kore ka ne?"

Ya ɗaga hannu ya ƙwashe ta da mari, sai na ji wani walau kamar ni ya mara.




*UWAR SUKUM.*
[5/17, 8:18 PM] RN Feedohm: 💧💧 *KUSKUREN SO.*

FREE BOOK

*HASKE WRITER'S ASSO.*

   *FEEDOHM*
Wattpad@Feedohm



  _Ga ba ɗaya littafin nan sadaukarwa ne ga NAFEESA Muhammad SULE, maman jinjiri, Alherin Allah ya kai maki a duk inda kike._

_Ina kike Aunty Zainab Abubakar Kotorkoshi? Ke ma ina maki fatan alheri._



*012*


Duk tunanina Teema zata ɗaga hannu ta ƙwashe Sufyan da mari, kamar yadda ya mareta, don wallahi na fi kowa sanin halinta, don haka na yi tsalle na shiga tsakanin su, hawaye na bin kumatuna, na haɗe hannaye na guri guda ina kallon ta a raunane.

Dafe kuncin ta yi tana murmushin da ke nuna asalin jin zafin da tayi ta ce "Bar kau da Fuskar ka mijin Yaya, ba zan rama ba, ko ba komai ka ci darajar ƴar uwata da kake aure, amma dai a kula, kar a sake wannan dabacin, don na gaba nima sigari zan sha, na maka daidai da tunanin ka."

Ta watsa min banzan kallo ta ce "Ai ba zan rama ba Yaya, ko ba komai ya ci darajar auren ki da ya ke yi, amma dai ki faɗa mishi a kula."

A sanyaye na kira sunan ta "Teemah."

A fusace ta ce "Dan Allah ki yi shiru sarauniyar aure, amma ki sani idan har mijin ki zai cigaba da wulaƙanta ƴan uwa ki a gaban idon ki, to kar ki yi zaton kin tsira, gidan ki kuma ko gobe na bushi iska sai na zo, babu ubanda ya Isa ya hanani raɓar ƴar uwar ta."

"Ƙarya kike wallahi, tunda babu sisin ubanki a gina shi." Ya faɗa kamar zai kai mata duka.

Daga haka ta wuce ta barni tallabe da kumatu hawaye na bin kumatuna, har ga Allah ko a mafarki ban taɓa zaton Sufyan zai mari Teemah ba, bare idan na tuna tsantsar shaƙuwa da suka yi da Ita kafin aure, na ɗaga idona da ƙyar da niyyar na yi mashi maganar banji daɗi ba, amma sai na ga ya wuce tamkar kububuwa ya fice daga gidan, da alamun ɓacin rai a tattare da shi.

Na girgiza kai cike da takaici, ni da ya kamata na yi fushi ban yi ba sai shi da ya ci mutuncin ƴar uwata a gaban idona? Sai na ji wani sabon kukan ya suɓuce mani, na shige ciki da sassarfa na baje ƙasa ina fitar da sautin kuka ƙasa ƙasa.

**************

Ashe Sufyan daga nan bayan Teemah ya bi ya nufi gidan mu, da yake ita sai da ta nemi abin hawa sai ya kasance ya riga ta zuwa gidan mu, ya yi sallama Auta ya leƙo, yana ganin shi ya zunɓuri baki ya gaida shi, bai amshi gaisuwar ba ya ce yayi mashi iso cikin gidan, kai tsaye auta ya juya sannan ya dawo ya ce ya shigo.

Fuska a murtuke ya gaida su Mama.

"Sufyan lafiya dai ko?" Mama ta kasa haƙuri ta tambaye shi ganin fuskar shi murtuk sai ta yi tunanin ko matsala muka samu.

Kai tsaye ya ce "Kashedin waccen mara kunyar na kawo."

Baaba ya kalle shi a ɗan razane "Subhanallahi, me Nafeesa ta yi maka.?

"Ba Nafeesa ba, Teema ce ta je har gida ta ci mutuncina, sannan ta ke zuga matata akan ta daina min biyayya, toshine na zo na faɗa maku gaskiya ku yi ma ƴar ku gargaɗi, ni ba zan ɗauki iskanci ba, don wallahi ta kuma je min gida sai na ɓalla mata ƙafa, don na lura ƙwata ƙwata bata da tarbiyya, kar ta ɓata mun mata." Ya ƙarasa maganar yana kumfar baki.

Takaicin su ya ishe shi, duk da basu san me ya haɗa shi da Teemah ba. Amma bai dace a matsayin su na surukai ya zo yana masu magana haka ba, sannan ko ba komai tarbiyyar da yake magana da ita da matar tashi duka iri ɗaya suka samu.

Da ƙyar Baaba ya buɗe baki ya ce "Insha Allahu zan ja mata kunne, dan Allah ka yi haƙuri, gidan ka kuma ba zata ƙara zuwa ba."

Ya miƙe yana cika yana batsewa ya fice ba tare da ya ce komai ba.

A bakin ƙofa suka yi kicibus da Teemah, kamar zata tanka mashi sai kuma ta fasa, tana murmushin irin banzan kallon da ya ke mata, ita fa sai yanzu take mamakin banda farin uban me yaya ta gani ta liƙe ma wannan mara mutuncin, sai kuma ta saki murmushi, don ta san bata isa ta kushe Sufyan ba, kawai dai rashin mutuncin da yayi mata yasa ta gano munin shi, ta yi sallama babu kowa a tsakar gidan, ta nufi hanyar ɗaki ta ji Mama na ƙwala mata kira daga ɗakin baki, don haka ta canza akalar ta, ta nufi ɗakin kai tsaye.

Tun kafin ta zauna mama ta tambaye ta "Me ya haɗaki da mijin ƴar uwar ki? Dama da niyar rashin kunya kika je gidan?"

Bata ɓoye masu komai ba ta faɗa masu abinda ya faru, tun daga shigowar shi har marin ta yayi mata, amma maimakon a giya mata baya sai faɗa da mama ta turnuƙe ta dashi "A gaban ki ya ce ki bar mashi gida? Je ki ma ya ce, gidan uban ki ne da zaki ji haushi?'

Baaba ya dakata da ita" Teemah ta ki tafi.'

*************

Ina ƙwance ya shigo ya giftani ya shige ɗaki, kamar na ƙyale shi sai kuma na ga idan abin ya huce a zuciyata ba zan mashi maganar ba, dan haka ba miƙe tsam na bi bayan shi, na taras da shi zaune gefen gado ya dunƙule hannu ɗaya sai naushin ɗayan ya ke, da ya ke nima raina a ɓace ya ke daga tsayen da nike na ce "Ban ji daɗin abinda ka yi ma Teema ba gaskiya, ko ba komai ta ci d......

Ya daka min tsawa "Shhhhhhh, au bayan ta kike ma? Ni ne na yi ba daidai ba ko? Nafeesa kin san darajar miji kuwa? Ina da mutunci da daraja a idon ki da har zaa shigo gidana a ci min mutunci sannan ki ce ban yi daidai ba?" Ya furzar da iskar bakin shi sannan ya cigaba da faɗin "Thank you, ai na ɗauka ke ce mai ɗaukar mataki idan aka ci mutuncina a gaban ki, amma yanzu na fahimci da ni da kare mai haushi bamu da maraba a gurin ki..."

Sai na ji jikina ya ɗauki rawa, yayin da duk wani ɓacin raina na nemeshi na rasa, sai na ke jin darajar miji ya wuce duk inda nake tunani, kuma bai cancanci wani ya nuna shi da yatsa a gabana ba ba tare da na karya yatsan ba, wasu hawayen daban suka soma sunturi a kumatuna, na ƙarasa kusa dashi ina faɗin "Ba haka ni ke nufi ba Sufyan, dan Allah ka yi haƙuri na san bata...

Ya ɗaga min hannu, tare da zagaye ni ya fice daga gidan baki ɗaya. Gefen gado na yi zaman dirshan na soma rera kuka, kafin na janyo wayata a fusace na turawa Teema message.

_Hankalin ki ya ƙwanta, kin kawar da farin ciki a gidan ƴar uwar ki! Kin haɗa ni da mijina._

Ina zaune na haɗe kai da ƙafa ya dawo, ya zauna Gefena tare da kama hannuna yace "Is ok tunda kin fahimci ƴar uwar ki ce me laifi, gaskiya raina ya ɓaci, ban yi zaton Teemah bata da kunya ba sai yau, look at yadda ta ke min magana kamar tsaran ta, ban ji daɗi ba wallahi Nafee, am very disappointed, ai na ɗauka ƴan gidan ku na kallona kamar ɗan'uwan su...

A sanyaye na ce "Am sorry."

Ya ƙara danne ni ta baya yana shinshinar wuyana ba tare da ya ƙara cewa komai ba, duk yadda na so na zame kasawa na yi, yayin da ya cigaba da raɗa min yaudararrun kalaman shi a kunnuwa, bai kuma rabu da ni ba sai da ya tabbatar ya goge laifin shi a zuciya ta, sai da ya tabbatar ya sa min farin ciki a raina, sannan ya miƙe ya ɗauke ni cak muka koma falo ya zauna ƙasa ya saka ni tsakiyar ƙafafun shi yana karanta mana wani ƙaramin littafin mai ɗauke da hikayoyi.

Wayar shi da ta yi ringing ya sa muka maida hankalin mu gun, ya sa hannu ya janyo ta, ya kan ga a kunne yana faɗin "Har kun iso?"

Ban san me aka faɗa mashi a ɗayan bangaren ba, sai na ji ya amsa da "Ok, ka tsaya gidan mai na Total ina zuwa yanzu."

Ya yanke wayar tare da janye ni daga jikin shi yana faɗin "Har sun iso."

"Su wa?" Na faɗa cikin mamaki don bai faɗa min wasu zasu zo ba.

Ya janyo hannuna ya miƙar dani yana dariya "Tashi raguwa, idan mun je can zaki gani, ina so na yi suprising ɗin ki ne."

Na taɓe baki ina kallon shi, da takaicin shi lokaci guda, ina tsaye ya ɗauko min hijabi ya zura min, ya kama hannuna muka fita.


********************

Da kallo kawai na ke bin shi dashi, tunda muka ɗauko yaran ya ke wani rawar ƙafa, ya kasa zaune bare tsaye, na ja siririn tsaki lokacin da idona ya ciko da ƙwalla, yanzu ya gama korar ƴar uwata amma shi ga nashi ƴan uwan har guda uku, waɗanda bara su tsinaman komai ba, hasalima nice a wahale.

"Wai ba zata ci jallop ba." Ya katse ni yana dariya.

Na ce "Allah sarki." Na juyar da kai na ɗauke ƙwallan da babban yatsa na.

"To ko zaki dafa masu indomie please."

Ban ce komai ba na miƙe na shiga kitchen na silala masu indomie na juyo a plate na kawo masu.

Ƴar ƙaramar mai suna Aira ta ce "Aunty babu ƙwai."

"Aƙwai mana." Ya bata amsa kafin na amsa.

Sannan ya kalle ni yana washe baki "Dan Allah ki ɗan dafa masu ko guda uku ne."

Na juya a sanyaye na koma kitchen ɗin ina mamakin shi, wato shi na shi zasu iya zuwa na masu wahala amma nawa ne bara su zo ba? Ai kam wallahi da sake ba zan iya ba, yadda baya ƙaunar ƴan uwa a su zo, to shima na shi su zauna, duk da dai na san wannan laifin Teemah ne, amma su Auta fa da ke zuwa yana korar su, na yi ƙwafa na ɗauki ƙwan biyu na kunna gas, ina tsaye ya dahu, na ɓare sannan na kawo masu, na juya zan shige ɗaki na ji ɗaya ta ƙwala ƙara tana harba ƙafa "Soyayye na ke so...."

Ya ƙwashe da dariya tare da ƙwala min kira "Aunty, aiki fa ya same mu...






*UWAR SUKUM.*
[5/17, 8:18 PM] RN Feedohm: 💧💧 *KUSKUREN SO.*


FREE BOOK


*HASKE WRITER'S ASSO.*


   *FEEDOHM*
Wattpad@Feedohm



  _Ga ba ɗaya littafin nan sadaukarwa ne ga NAFEESA Muhammad SULE, maman jinjiri, Alherin Allah ya kai maki a duk inda kike._

_Ina kike Aunty Zainab Abubakar Kotorkoshi? Ke ma ina maki fatan alheri._


*013*


A lokacin da na turawa Teemah wannan saƙon ashe wayarta, tana hannu Maama, ta zuba ma wayar ido cikin tashin hankali yayin da ta karanta message ɗin ya fi sau goma cikin kaɗuwa da mamaki, kanta ya ɗaure ta soma auna maganganun Sufyan da Teemah a sikili, shin me ke faruwa? Wake da gaskiya a cikin su? Kusan minti goma tana zaune gurin riƙe da wayar, sannan ta miƙe jiki babu ƙwari ta shiga can cikin uwar ɗaka ta zauna gefen gado tare da  janyo wayar ta da ke ƙasan Pillow ta kira waya ta, sai dai kafin ta soma ringing ta yanke, tana tunanin kamar maganar ba ta waya ba ce, kamata yayi ta je har gidan don ta taji me ke faruwa, amma dai ba yanzu ba, sai komai ya ƙara lafawa.

Sallamar Fannata ya sa ta fito falo ta zauna, bayan sun gaisa Mamaa ke tambayar ta "Kina kuwa leƙawa gidan ƙawar ki Fannata?"

"Wa? Ai wallahi Mamaa mijinta bai da kirki, baya so a je gidan shi." Ta bawa Mamar amsa kai tsaye.

Cikin halin ko in kula Mamaa ta ce "Shine ya nuna maki baya so kina zuwa?"

"Mamaa kai tsaye fa yake nunawa."

A sanyaye mama ta ce "Subhanallahi, shi kam ai ba'a haka, mutane rahama ne, kuma anya Fannata ba da iya shege kuke zuwa gidan nashi ba?"

Ta girgiza kai "A'a wallahi Maama, ina ga shi dai haka halin shi ya ke, ko fa waya ya hana mu yi da ita, ƙwanaki ma wata ƙawar mu ta ce min taje gidan ya tare ta bakin ƙofa yake faɗa mata bai gina gidan shi da zawarawa ba."

Mama ta ce "Allah ya ƙyauta, ai ba'a biye mashi ba, ya kamata ki kira ta ki gaida ta bata ji daɗi ba, ba'a yanke zumunci Fannata, zumuncin da bai san lokacin da ya ƙullu ba."

"Maama bata lafiya ne?"

"Au baki sani ba? Ƙwanaki jin bai mata daɗi ba, amma yanzu ta ce da sauƙi."

Teemah da ta shigo ta yi karaf ta ce "Yanzu fa sai ki ce zaki kira ta?"

Mama ta kai mata duka ta goce, ta shige ɗaki tana surutai ƙasa ƙasa.

A take jikin Fannata ya yi sanyi, domin har ga Allah tana jin Nafeesa tamkar ƴar'uwarta ba ƙawa ba, shiyasa ko kaɗan bata iya fushi da ita, sama sama suka jefa fira da Maama, sannan ta miƙe tamkar wacce ƙwai ya fashewa a ciki, yayin da zuciyar ta ke azalzalar ta da son ganin halin da ƙawar ta ke ciki, duk da dai a baya ta yi alƙawarin ba zata kuma zuwa gidan Nafee ba, amma a yanzu sai take jin ba zata iya cika wannan alƙawarin, ta tsayar da Napep ta hau ta nufi gidan Nafeesa kai tsaye don ganin halin da take ciki.

Ina tsefewa Aira kai na ji knocking ƙofar, har ga Allah sai da gabana ya faɗi ina tunanin wanene zai zo yanzu, na kalli ƙofar bedroom ɗin mu na lumshe ido tare da addu'ar Allah ya sa ba wani ɗan uwana ba ne, na miƙe a sanyaye na ƙarasa na buɗe, lokaci guda na yo baya sai ka ce wadda ta ga wani mugun abu, sai na ji raina ya dagule, na sake kallon ƙofar bedroom ɗin da addu'ar Allah ya sa Sufyan bacci ya ke, ban san me yasa suke son ɓata min farin cikin gidan aure ba, ban san me yasa suke nacin zuwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login