Showing 39001 words to 42000 words out of 83936 words

Chapter 14 - KUSKUREN SO Book Complete by Feedohm.txt

Feedoms   

21 Sep 2025

1712

a mota na hango shi can nesa kaɗan da gidan, yana ganin na fito ya buɗe marfin motar da azama ya tare ni yana faɗin "Yanzu na ke ƙoƙarin shiga ciki in ɗauko ki da kaina."

Na zunɓuri baki na zagaye shi na buɗe motar na shiga na zauna na jingina da kujerar sosai.

Sai da ya tayar da motar sannan ya kalle ni yana murmushi ya ce "Sweetie iyayen yaji..."

Na watsa mashi hararar wasa na ce "Ai wallahi don baka da lafiya ne yasa na dawo."

Ya lakace min hanci "Ba wani nan, bara ki iya rayuwa babu Sufyan ɗin ki ba."

Na watsa mishi harara na ce "Kai ma ai..."

"Yes, amma ke gashi kina so ki tangalar mana da auren mu."

Na kalle shi na ce "Kamar ya?"

Ya ɗage min gira ɗaya tare da kanne ido ya ce "Yes, idan har zaki kai ƙarar mijin ki gidan ku, ai kin ɗauki hanya Sweetie, kuma fa kin sani a gidan na ku aƙwai waɗanda tunda suka ga irin gidan da kika shiga suke miki baƙin ciki....

" Teemah.... " Na faɗa kai tsaye tare da ƙwafa.

"Disaster, wannan yarinya ta fi kowa baƙin hali, sam bata da kunya tun abinda ta min ta fice a raina."

Na share hawayena ba tare da na ce komai ba, a wani ɓangare na zuciyata sai na ke jin tamkar ban ƙyautawa Maama ba, don haka na janyo wayata na tura mata ɗan guntun message

" _Ki yi haƙuri, ni fa wallahi ina son mijina, kuma ku kukace in bishi sau da ƙafa._"

Na kulle wayar baki ɗaya na maida a jikka....

*********************

"Ki yi haƙuri a zubda wannan cikin Nafeesa.."

Cikin tashin hankali na ke kallon shi, yayin da zuciyata ke bugawa da ƙarfi da ƙarfi "Sabida me Sufyan?"

Ya dafa kafaɗata "Sabida na san crisis na masu sickler, kuma wallahi ba zan iya ba Nafeesa, mu yi zaman mu a haka ba tare da haihuwa ba, idan har muka kuskura muka haihu wallahi ƙwanciyar hankali ta gagare mu."

Idona ya soma zubda ƙwalla masu zafin gaske, cikin rawar murya na ce " Amma ƙwanaki ka ce min aƙwai hanya ana embr.....

Ya dakatar da ni "Ana yi, amma ba'a yin shi anan, kuma na faɗa don na ƙwantar miki da hankali ne, sannan maganar zamu iya haihuwar normal yaran Nafeesa ba mai yiyu ba ce, try to understand me, ina son ki, ina so na, ya ishe mu rayuwar duniya.."

Na hau girgiza kai "Aa Sufyan, ba haka muka yi ba, ina so na haihu kamar yadda kaima kake da ƴa ƴan ka..."

"Ƴa ƴa na ba naki bane...?

Na dafe kafaɗata tare da zamewa gurin na hau girgiza kai ina kuka "Ina so na haihu Sufyan, ina son ƴaƴa ko ya suke.."

Ya sassauta murya "Wallahi cutar su zamu yi, ko mun haife su mun masu babbar cuta, kuma bai zama lallai su rayu ba.."

"Ina so haka nan, ba zan iya zubda cikin da nake jin motsin shi a jikina ba..."

Ya furzar da iska, tare da miƙewa fuuuuu ya fice daga gidan baki ɗaya, ni kam sai na ji duniyar baki ɗaya ta min zafi, har ga Allah ina son cikina, kuma ba zan iya zubda shi ba, na shirya ɗaukar kowanne abu ne a kan shi, sai na ji kaina ya kulle, ina buƙatar tattauna wannan matsalar da wani ko zan ji daɗi, na lumshe idona yayin da na kasa hango wacce zan kira, na san dai ban isa in kira Maama ba domin tun daga waccen ranar duk abinda ya shafi Sufyan bata maraba da shi.

A take Fannata ta faɗo min, na miƙe da ƙyar na shiga bedroom na ɗauko wayata na kira ta, ringing ɗaya ta ɗauka tana faɗin "Yau kuma an tuna da mu?"

"Fannata dan Allah zaki iya zuwa gidana?"

Da sauri ta ce "Wa? Dan Allah rufa mun asiri, ko menene ki faɗa min ta waya amma ba zan zo gidan ki ba."

Na sauke numfashi na ce "Sufyan ne ya ce in zubda cikin da ke....

Daga bayana na ji an warce wayar an naka da ƙasa, na juyo a firgice ina kallon shi, sai na ji jikina ya soma rawa, yayin da hankalina ya yi masifar ta shi, ganin yadda ya ke sauke numfashi sai ka ce wanda ya yi faɗa da ƙatti ko kuma yana shirin faɗa da ƙattin.




#UWAR SUKUM
[5/17, 8:21 PM] RN Feedohm: 💧💧 *KUSKUREN SO.*

FREE BOOK

*HASKE WRITER'S ASSO.*

   *FEEDOHM*
Wattpad@Feedohm


  _Ga ba ɗaya littafin nan sadaukarwa ne ga NAFEESA Muhammad SULE, maman jinjiri, Alherin Allah ya kai maki a duk inda kike._

_Ina kike Aunty Zainab Abubakar Kotorkoshi? Ke ma ina maki fatan alheri._

*024*


Raina ya dagule, sai na ke ganin wannan rashin adalci ne, don haka a fusace na ce "Amma wallahi da baku ƙyauta ba, a ce ƴa ƴan mijina su rasu su uku sannan ba zaku zo gaisuwa ba? Anya kun yi mishi adalci kuwa Maama? Mijin ƴar ku fa? Ai ina ce daga ke har Baban da Fatima da auta zaku zo har ayi baƙwai tukun ku koma, sannan ki dawo addu'ar arba'in, idan da mutun ƴaƴan Sufyan ai jikokin ku ne. "

"Idan babu mutuncin fa? Anya kina da hankali kuwa Nafeesa?" Ta faɗa cikin fushi.

"Ni dai bance haka ba, amma ai abinda ya kamata ayi na ke faɗa, wannan bawan Allah ƴar ku ya ke aure amma ace..

Ban sani ba ko takaici ya sa ta yanke wayar ta ba, don sai dai na ji dimm, na lumshe ido ina cije laɓɓana, kafin na kalle shi a sanyaye na ce "Ka yi haƙuri wai su Maama ba zasu je ba, amma bari in kira Baaba na san ba zai yi wannan ɗanyen aikin ba."

Bai dai ce min komai ba, na ɗaga waya na kira Baaba, shima kamar shanyayye sai cewa yayi wai in turo mishi number Sufyan ɗin da Umman shi zai kira ya masu gaisuwa, ba zai samu zuwa ba, na yanke wayata ba tare da na bashi amsa ba ina faɗin " Bazan tura ba wallahi, a ce dai kuɗin mota 1500 ta hana ku zuwa gaisuwa? Sauƙin ma rasuwar kowa zaa masu, idan shima bai zo maku ba ai baƙwa ji haushi ba. " Na share hawayen da suka biyo kumatuna, yayin da takaici ya min dirar mikiya, sai na ke ganin kamar ba su yi min kara ba, don haka na turawa Maama message _Ni dai dan Allah ku zo, idan kuma kuɗin motar ne babu sai in turo maku 20k ta account ɗin Fatima yanzu._

Message ɗin na shiga kiran Maama na shigowa, na saki murmushi, dama ƙyila rashin kuɗin ne, kafin na ɗauka na kalli Sufyan na ce "Dan Allah aƙwai 20k account ɗin ka?"

"Me zaa yi da ita?"

Na sunnar da kai ƙasa cike da kunya na ce "Zan turawa Maama ne su yi kuɗin mota su zo gaisuwa, kasan month ya zo ƙarshe, wata ƙyil babu kuɗin ne shiyasa ba zasu samu damar zuwa ba."

Ya kalle ni fuskar shi babu annuri ya ce "Dan zasu zo min gaisuwa sai na tura masu kuɗin mota Nafeesa? To su yi zaman su bana so, kuma wallahi kar ki yi tunanin zaa maku rasuwa nima in je."

Na lumshe ido, dole ma ya ji haushi, ai abun yanzu biki ne, sai an yi maka kai ma kake yi, ɗiyan ka sukutukum su rasu ace ba zaa zo gaisuwa ba daga gidan matar da kake aure ba? Ko dan ba ƴaƴa ba ne? Ba su san da ni da Sufyan mun zama one ba yanzu? Na yi ƙwafa ina kallon kiran Mamaa da ya shigo na biyar kenan, sai da ya kusa katse wa sannan na ɗauka, don ban ma san yadda zan ce mata kuɗin basu samu ba, duk da dai ba ita ta buƙata ba ni na ce, ai kafin na ce wani abu ta rufe ni da masifa "Ai ban ƙara sanin ke wawiya ba ce sai yanzu? Ni zaki kalli ki ce zaki turo mana kuɗin mota mu zo gaisuwar mijin ki? To baki yi wannan arzikin ba Nafeesa, kuma har abada ba zaki yi shi ba, gaisuwa kuma baa zuwa, idan ke kike iko da mu ki turo a sace mu akai miki, sakarar banza mara wayau, wacce bata san darajar iyayen ta ba, ina ce mutun yana girma yana ƙara hankali amma ke kullun baya kike ci." Ba ta jira me zan ce ba ta yanke wayar ta.

Ni kam Hmmm kawai na ce, don ni banga abin ɓacin rai ba, na fa san gidan yadda ya ke idan wata yayi ƙarshe, kuma ma don na ce zan tura masu kuɗi ai ba wani abu bane, ni ƴar su ce, na daure da ƙyar na tura mata message _Allah ya baki haƙuri Maama, ni ba haka ni ke nufi ba, na ga wata ya zo ƙarshe._

Bata maido min reply ba, na kuma ƙara kira bata ɗauka ba, Sufyan dake driving dai bai ce min komai ba, ni kam tunani wanda zai min kara ya zo mashi gaisuwa na ke, don bai kamata ace daga waje na babu wanda ya zo ba, gashi ko ƴan mutanen arziƙin nan na anguwa ban yi ba, na lumshe ido lokacin da na tuno Fannata ce kaɗai zata rufa min asiri ta min kara, don haka na yi dialing number ta, sai da ta kusa katse wa tukun ta ɗauka.

Na lanƙwashe murya na ce "Fannata an mana rasuwa, ƴa ƴan Sufyan su rasu, dan Allah komai kike ki baro ki taho Kano yanzu."

Cikin jimami ta ce "Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un, Allah ya ji ƙan su, amma ba zan iya zuwa ba Nafeesa ina da uzuri wallahi."

Cike da takaici na ce "Fannata uzurin ki ya fi rasuwar ƴaƴan Sufyan?"

"Ban gane ba? Wallahi babu halin zuwan ne Nafeesa."

"Kuɗin motar ne babu?" Na faɗa a ƙulafance.

"Kamar ya? Kin san dai ai kuɗin mota sai dai na bayar, kawai dai ina da uzuri ne, kuma ko babu Nafeesa ba zan iya zuwa sabgar Sufyan ba, Allah dai ya ji ƙan su da rahama, zan tura mashi saƙon gaisuwa ta waya."

Na danƙara ashar "Yanzu kina nufin ba zaki zo ba? Amma wallahi ban taɓa sanin ba ki da kirki ba sai yau Fannata.."

Sufyan ya fizge wayar a kunne na ya latse ta, cikin ɗaga murya ya ce "Dan Allah kar ki dame ni Nafeesa, ki barni na ji da abinda ke damuna, kin bi sai roƙo kike azo min gaisuwa sai ka ce ni na saki, ko na faɗa miki banda jama'ar arziki ne, ko ko ƴan gidan na ku waliyai ne da idan suka zo, za su tayar da su Airah? Dan Allah ki bar ni na ji da damuwata, ke ma idan ba zaki je ba zan iya tsayawa ki sauka babu dole.. "

Na langwaɓar da kai ina faɗin" Dan Allah ka yi hakuri, ina faɗa masu ne don babu daɗi ace ba su je."

Ya hayayyaƙo min" To sai me? Kar Allah ya sa su zo ɗin, ko na ce miki ina buƙatar su ne gurin?"

"Allah ya baka haƙuri, tunda ma ba zasu zo ba ai shikenan."

Ya ja dogon tsaki, sannan ya maida wayar bayan sit ya cigaba da driving cike da damuwa da ɓacin rai, lokaci zuwa lokaci ina jin yana sakin ɗan siririn tsaki, ni dai ban ƙara ce mishi komai ba, hasalima ƙwantar da kaina na yi ina kallon hanya, kafin ya juyo babu yabo ba fallasa ya tambaye ni "Kin sha maganin?"

Wallahi na ɗauka tashin hankalin da ya ke ciki zai sa ya man ta, gabana ya faɗi, da ƙyar na gyaɗa mishi kai ba tare da na yi magana ba.

"Kin tabbatar?"

"Uhmm.."

Bai kuma ce min komai ba, har bacci ya ƙwashe ni.

*********************


Mun iske gidan cike da jamaa, gaskiyar Sufyan yana da mutanen arziki fiye da tunani don haka baya buƙatar kalar dangi, ban damu da rashin tarbar da na samu ba, domin babu wanda ya kula ni, na masu uzurin da yanayin da suke ciki ne ya sa, don haka na samu tabarma cikin ƴan gaisuwa na zauna na yi jugum jugum ina ƙananan hawaye da jikka a gabana don ban san inda zan kai ta ba, hasalima wannan ne zuwa na na farko gidan, amma fa shi Sufyan ya samu tarba, don rungume shi Umma ta yi tana bashi haƙuri, ni kam tun daga gaisuwa ko inda nike bata kalla, bana ma tunanin ta amshi gaisuwar.

Bayan an rufe yaran sun dawo, Sufyan ya sa Jamila ta ɗauki jakkar ta shigar da ita, ni dai ina nan inda nike zaune, daga "Su Nafeesa ne." Babu abinda ya ƙara haɗa mu.

Aka kawo shinkafa ana ta rabo, aka aje min plate ɗaya ni da ta kusa dani, ga yunwa ina ji gashi ina ganin kamar bai kamata ƴaƴan mijin ka sun rasu ba ka kama kandamar abinci ba, kar ace ko don ba kai ka haife su ba, don haka na haƙura da abincin nan har waccen matar ta cinye kamar mayya, lokacin sallar la'asar yayi na miƙe na kalli Jamila da ke ta yawo na ce "Zan yi sallah."

"Ki shiga wancan ɗakin da na kai jikkar ki, aƙwai toilet da ruwa a ciki."

Na ce "To."

Har na wuce na kuma janyo rigar ta ina faɗin "Jamila tunda muka zo banga Umma ba."

Ta kalle ni sheƙeƙe ta ce "Tana wancan ɗakin, mu je ku gaisa."

Na ja ƙafa jiki babu ƙwari na bi bayan ta, don ban san irin tarbar da zan samu ba, ina jin mutane na tambayar amaryar Sufyan ce tana basu amsa da eh, a haka muka shiga gurin Umma tana zaune cikin mutane a falo ana gaisuwa, Jamila ta matsa kusa da ita ta ce "Nafeesa ce ta ce baku gaisa ba."

Ina jin Umma ta ce "Ban san sharri, gaisuwar da muka yi da ita lokacin da suka shigo fa?"

Jamila ta taɓe baki ta ce "Haka dai ta ce."

Na rusuna har ƙasa ina faɗin "Ina Wuni Umma.."

Kafin ta amsa Jamila ta ce "Umma ga su Asiya sun iso, wayyo Allah..."

Umman ta miƙe da sauri tare da fashewa da kuka, gurin ta tsallake ni, na tuntsira ƙasa da yake dama a tsugunne nake, ta yi kan Asiyar ta rungume tana faɗin "Bar kuka Asiya, Allah da ya ɗauke maku su, shine zai baku wasu, bar kuka ƴata."

Mutanen falon suka ɗauki salati da jimamin tausayin ta, yayin da Umma ta shige ɗaki da ita suka barni mirgine takaici ya hana ni tashi...



#UWAR SUKUM.
[5/18, 8:36 PM] RN Feedohm: 💧💧 *KUSKUREN SO.*

FREE BOOK

*HASKE WRITER'S ASSO.*

   *FEEDOHM*
Wattpad@Feedohm



  _Ga ba ɗaya littafin nan sadaukarwa ne ga NAFEESA Muhammad SULE, maman jinjiri, Alherin Allah ya kai maki a duk inda kike._

_Ina kike Aunty Zainab Abubakar Kotorkoshi? Ke ma ina maki fatan alheri._

*025*

Tsabar takaici da kunya ya sa na kasa tashi daga inda ni ke hanɓare, har sai da wata baiwar Allah ta dafa ni tana tambayar "Lafiya ke kau baiwar Allah tun ɗazu kike ƙwance guri ɗaya.?"

Ban iya bata amsa ba sai dai hawayen dake bin kumatu na, ta taimaka min na miƙe, kaina a ƙasa na bar ɗakin na koma gurin ƴan zaman gaisuwa tsakar gida na zauna bisa tabar ma zuciyata babu ɗaɗi, har ga Allah ba ƙaramin wulaƙanci Umma ta min ba, ni ce wacce ya kamata ta runguma ta nunawa soyayya da tausayi kasancewa ta matar ɗanta, ban ce kar ta ma Asiya ba don ita aka ma rasuwa, amma nima ɗiyan mijina ne suka rasu, kuma zuwana na farko ne gidan, na kifa kaina a cinya ina hawaye, yayin da gefe ɗaya mutane ke tausaya min da jajanta min don gani suke kukan rasuwar su Airah ni ke.

Ɓangare ɗaya kuma yunwa ce ke nuƙurƙusata, ina ganin lokacin da Jamila ta wuce da narkekiyar kula danƙare da abinci ta kai ma su Asiya, sannan ta sake fitowa ta aiki yaro ya siyo mata peak ta ruwa da bournvita ta kanga ruwan zafi ta kai masu, don ina jin tana faɗi ma wata mata wai Uwar yaran ce ta kasa cin abinci Umma ta ce a ɗaura mata ruwan tea.

Na yafito Jamila kamar wata almajira, ko da yake a gidan na ga alamun banda maraba da su, wannan da ace ƴan uwana sun zo ai da na ji kunya yadda nike rawar ƙafa kan Sufyan.

Murya ƙasa ƙasa na ce "Jamila babu sauran abincin nan?"

"Bangane ba? Ina wanda aka aje maku ɗazu?"

Bata ma saurare ni ba ta wuce abun ta, na bita da kallon mamaki, sai na tuna lokacin da suka je gidana babu irin rawar ƙafar da ban yi a kan su ba duk da dama can ba wani kunya ta cika ba, sai ga shi yanzu tana neman maida ni banza, sai yanzu na soma yadda da maganar mutane da suke cewa dangin miji basu da mutunci, kuma tilas Sufyan ya ɗauki mataki.

Bayan an yi magrib ga Sufyan ya shigo gidan fuskar shi ɗauke da damuwa, ya yafito ni da hannu na tashi na bi bayan shi muka shiga ɗakin Jamila da yake babu mutane sosai, daga Asiyar da har yanzu ban san kammanin ta ba, sai Umma, Jamila da mutun biyu da nake tunanin ƴan uwan Asiyar ne.

Gefen katifar ya zauna ya janyo hannu na ya zaunar da ni gefen shi, wallahi ban san lokacin da na fashe da kuka ba.

A ruɗe ya tambaye ni "Lafiya? Me ye na kuka Nafeesa?"

Da fari ƙin cewa komai na yi don na tabbatar ko na faɗa ba zai ga laifin uwar shi ba, sai ma ni ya ga laifina, sai da ya matsa min sannan na ce "Umma ce kamar bata so zuwa na, na je in gaishe ta ɗazu ta hankaɗe ni na faɗi ƙasa."

"Amma dai bata gani ba ko?"

Da sauri na ce "Ta gani wallahi, murnar zuwan maman su Airah ce ya sa ta min haka, bayan ni ya kamata ta yi murnar zuwana."

Cikin halin ko in kula ya ce "Gaskiya ba zata miki haka da gangan ba, kawai dai tsegumi ne irin na ku na mata, kuma banda abinki ita Mamansu Airah a yanayin da ta ke ciki ai dole a tausaya mata, da Allah ki bar wannan maganar."

Na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login