Showing 42001 words to 45000 words out of 83936 words
ƙara sautin kukana, ya kalle ni ya taɓe baki ya ce "Kin ci abinci kuwa?"
"Uhm uhmm."
"Garin yaya?" Ya kafe ni da ido.
A shagwaɓe na ce "Wanda aka kawo mani ɗazu ni da wata mata ce mai goyo, kafin na ankara ta cinye."
"To ba sai ki yi magana Jamila ta kawo miki wani ba?"
"Ai na yi mata ta nuna babu, kuma ina kallo aka shiga da abincin gun..."
Ya katse ni "Ƙyila bata ji bane."
Takaici yasa na yi shiru kaina a ƙasa, ji nake kamar na ƙwaɗe shi, yau da ace shine mamana ta yi ma haka wallahi sai na ɗauki mataki, amma shi da ya ke bai san darajar mata ba, yana neman ya watsar da abin, tsinkayar shi na yi yana tambayar "Wannan abun ya fita?"
"Me?"
Ya kalli cikin idona sannan ya kalli cikina ba tare da ya ce komai ba, nima taɓe baki na yi na girgiza mashi kai na ce "Aa."
Ya buɗe baki da niyyar ya min magana sai ga Umma ta faɗo ɗakin tana faɗin "Shine ka zo nan ka zauna ina ta neman ka tun ɗazu?"
Ya sosa kai tare da zame hannun shi cikin nawa ya ce "Mutanen sun tafi ne, kuma na leƙa ɗakin ki na ga mutane ciki."
Ta maka mishi harara "Su waye mutanen ciki banda surukan ka da matar ka.?"
Gabana ya faɗi damm, na ɗago na kalle ta, ko bata faɗa na san wa take nufi, nan da nan kishi ya turnuƙo ni, na buɗe baki da niyyar na gyara mata zancen ta ko manta, na tunatar da ita tsohuwar matar shi dai da tsofaffin surukan shi, sai na tuna marin da ya faska min ranar da na zage shi, yanzu ma yana iya cewa rashin kunya na mata, don haka na kama bakina na kalli ƙasa zuciyata kamar zata fito don masifar kishi, sai na ke nadamar maganin da ban sha ba cikin ya ɓare, da yanzu hankalina ƙwance ina da yaƙinin duk bala'i duk runtsi ba zai taɓa waiwayar Asiyar ba, abinda ma ya haɗa su yanzu babu shi.
Na lumshe ido, ina tunanin idan har cikin bai ɓare ba aka sa ya canza maganar fa? Na zaro ido ina salati a zuciyata, yayin da wani sashe a zuciyar ke nutsar dani duk runtsi duk wuya Sufyan ba zai taɓa karya rantsuwar shi ba.
"Kun ma gaisa da su kuwa?" Na tsinkaye ta, tana tambayar shi idon ta a kan shi.
"Eh Umma, ai na gan su lokacin da zasu shigo gidan."
"Wannan gaisuwa ce cikin mutane? Ka fa sani sarai abinda ya raba ka da Asiya rashin daraja iyayen ta, don haka tashi maza ka je ka gaishe su."
Ya ɓata fuska yana faɗin "To, amma Umma dan Allah a kawo ma Nafeesa abinci wai bata ci ba."
Umma ta dafe baki ta ce "Eyehhh, sharrin da zaki mana kenan?"
Na girgiza kai da sauri ina kallon shi, bakina na rawa na ce "Wallahi aa, ba haka na ce ba."
"To ya ki ka ce? Ƙarya ya miki kenan? Idan yunwa kike ji shi kika gani a gindin tukunyar ko yaya ne da zaki mishi magana, koko ƙarfin ki min magana kika yi?"
Na yi tsuru ina kallon ta, babu abinda nake gani a ƙwayar idon ta sai zallar tsanata, na lumshe ido hawaye na bin kumatuna, kuma fa da ba haka bane tana so na duk da ba can ba, da ta ji idan na haihu zan haiho sikila in ɗaura ma ɗanta wahala shine ta tsane ni, ban aune ba sai na ji ya zunguro ni yana faɗin "Baƙya jin ana miki magana."
"Ban ji ba wallahi." Jikina har rawa ya ke.
Umma ta daka min tsawa ta ce "Cewa na yi ki tashi maza ki je ki taya Jamila kauda tsakar gidan, sannan ku ɗaura mana tuwo an cinye abincin gidan, idan an gama ƙya ci."
Na kalle shi na yi rau rau da ido, ina jiran ya faɗa mata bana jin daɗi laulayi na ke, tunda ai cikin bai fita ba, kuma ya san jikina babu ƙwari, domin Allah ya sani ba zan iya wannan wahalar ba, bare ma yadda tsakar gidan ya ke kaca kaca, na ja siririn tsaki a zuciya, don ban isa na yi shi a fili ba, mutun na zuwa gidan surukai ana tattashin shi amma ni ana neman ɗaura min bala'i.
"Ta shi mana." Na tsinkaye shi yana faɗa a tausashe.
Zan yi magana ya katse ni "Umma ce ke miki magana ba wata ba, ki tashi ki yi abinda ta ce."
A haka na miƙe jikina a sanyaye na fita, na iske tsakar gidan sai ka ce na mahaukata, Jamila na gani na ta ɗauki hijabi tana faɗin "Umma daddawar mu ta ƙare, bara na je na amso da kaina."
Umma ta ce "To, ai ga Nafeesa nan sai ta cigaba ka fin ki dawo."
Ta fice, Umma kuma ta shige ɗakin ta, inda aka aje sarauniya, wallahi da ba ƴaƴan ta suka rasu ba, sai dai ta fito mu yi tare, ina kallon Sufyan ya shige shima don gaisawa da su.
Na tattare ƙwanukan, da tabarmu sannan na share tsakar gidan tas, na hau wanke wanke sai ka ce baiwa, kuma har na gama Jamila bata dawo ba, dama raina ya bani wallahi guduwa ta yi, na samu gefe guda na zauna ina jin yunƙurin amai, tun ina riƙe wa har na soma sheƙa shi, wanda kakarin ya janyo hankulan su.
Sufyan ya kamani yana min sannu yayin da Umma ke mana kallon tuhuma, ya taimaka min bayan na kuskure bakina ya kaini ɗakin Jamila, ta kuwa bi bayan mu tana tambayar "Aman menene Sufyan? Kar ka ce min wannan yarinyar ciki ne da ita?" Ta cuno ni da baki.
Ya sun ne kai yana faɗin "Eh Umma."
Ta hau taɓa hannu "Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un, shin ba cewa aka yi sikila zata haifa maka ba? Kan ka ɗaya kuwa Sufyan da zaka yadda ta haihu ta ɗaura maka wahalar duniya? Wahalar da baa taɓa warkewa? To bari ka ji, wallahi haihuwar sikila asara ce, haka zaka yi ta kashe kuɗin ka a banza ƙarshe su mutu su barka wayam."
Jikina ya soma rawa na zuba mata ido har ta kai Aya, sannan na kalli Sufyan ɗin ina sauraron ya faɗa mata haihuwar sikilar ba nawa ne ni kaɗai ba, kuma nima ba sikilar ba ce, amma sai na ji yayi shiru kan shi a ƙasa.
Ta daka mishi tsawa "Ka min shiru, ka shirya a tatike ka tsab ƙarshe a mutu a barka babu wan babu ƙanin?"
Cikin inda inda ya ce "Ai shiyasa muka yanke a zubar da cikin..
Ta rafka uban salati "Shine mafita? Idan an zubar gobe ba wani zata sake ƙunsa ba? Sufyan wannan ba matar a zauna da ita ba ce, lafiyayya kake buƙata kamar Asiya kana dai ganin abinda ya faru....
Cikin kuka na katse ta "Lafiya ta lau Umma, ni da Sufyan duka AS ne, idan mun haifi...
Ƙwaf ya buge mun baki yana aika min da mummanan kallo, cikin ɓacin rai ya ce "Tana magana kina yi don baki da kunya Nafeesa? Ko kin manta da Ummana ce a gaban ki?"
Umma ta ce "Barta ta yi Sufyan, ai ba ni na haife ta ba."
"Ko ba ki haife ta ba kin haifi mijin da take aure, kuma dole ta daraja ki wallahi..."Ya bata amsa yana kumfar baki.
#UWAR SUKUM.
[5/24, 8:54 PM] RN Feedohm: 💧💧 *KUSKUREN SO.*
FREE BOOK
*HASKE WRITER'S ASSO.*
*FEEDOHM*
Wattpad@Feedohm
_Ga ba ɗaya littafin nan sadaukarwa ne ga NAFEESA Muhammad SULE, maman jinjiri, Alherin Allah ya kai maki a duk inda kike._
_Ina kike Aunty Zainab Abubakar Kotorkoshi? Ke ma ina maki fatan alheri._
*026*
Bance komai ba illa sadda kai da na yi ƙasa hawaye na bin kumatuna, na tabbatar idan na sake magana babu abinda zai hana Sufyan tsinka min maruka, ƙarshe ma ina iya yin ta bakin aure na, ina tsaye Umma ta gama balbalin bala'in ta, sannan ta juya ta wuce abin ta kamar zata tashi sama.
A zatona bayan ta fita, zai rungumo ni ya bani haƙurin abinda ta min, don na tabbatar shima ba da son ran shi hakan ta faru ba, amma ina sai tsinkayar shi na yi yana faɗin "This is my last warning, kar ki sake mahaifiyata na magana kina yi, ba zan jure ba Nafeesa, zan iya rayuwa babu ke, amma ba zan iya rayuwa babu ita ba, muddun tana numfashi a doron duniya.."
Ya bi bayan ta ranshi a ɓace har da tuƙuicin tsaki, sai na ji hawaye wani ya bin wani, yayin da abinda na ma tawa mahaifiyar ya dawo min fil, wato ya kamata na gane mahimmancin mahaifiyata daga Sufyan, amman KUSKUREN SO ya hana na ga haka, na yi zaman dirshan kamar wacce aka kashewa iyaye, kafin na yunƙura da ƙyar na janyo wayata na yi dialing number Maama.
Na mata kira ya fi goma bata ɗauka ba, kuma na san tana gani, na lashi laɓɓana tare da tura mata ɗan guntun message _DAN ALLAH KI YI HAƘURI DA ABINDA NA MIKI, KI YAFE MIN MAAMA._
Sannan na sake kira, still dai ƙin ɗauka ta yi, na kira number Teemah shima shegiyar yarinyar nan ta ƙi ɗauka, dama na gama fahimtar bata ƙaunar ta ga ina mutunci da uwata, na ja tsaki na koma na zauna yayin da maganganun Umma suka soma dawo mun a ƙwalwa ta, har ga Allah na rasa wace irin al'umma mu ke ciki da duk abinda ya faru mace ne ke da laifi, indai ta ɓangaren aure ne, wannan ma da muka taru muka aikata da sanin mu ya zamana kenan laifina ne duk abinda ya biyo baya? Me yasa ba zaa ga laifin Sufyan ba, bayan shi ne yayi encouraging ɗina da mu yi auren sabida muna son juna...
"Iska na wahalar da mai kayan kara." Muryar Jamila ta daki dodon kunnena.
Na ɗago na kalle ta, ta ɗage kai sama tana taunar cingum, yayin da ta tsugunna gaba ta ce "Shi fa haka ya ke, abinda ya raba shi da Asiya kenan, akan waccen ƴar tsohuwar babu abinda ba zai iya ba, sabida ta wahala ga rainen su, har ya kawo inda ya ke yanzu, idan kina son zaman lafiya ki fa riƙe mashi uwa..
Wato shi ya san darajar tashi uwar ni ce ban san tawa ba, ni fa sai na ke ganin wallahi tamkar Asiri Asiyar da Umma su ka mishi, don su ƙuntata min, na yi ƙwafa na koma na ƙwanta.
Washe gari na ga ko irin kulawar nan ban samu ba, sai wani ɗaure ɗaure ya ke, sai na ji duk na damu, gashi koko suka dama gidan, bana sha'awar shan shi, ina buƙatar wani abun daban, bayan mun gama wanke wanke na koma ɗaki na kira wayar shi.
Ciki ciki ya amsa gaisuwa, ban wani damu ba, sabida fushin shi ɗaga min hankali ya ke, na ƙwantar da murya ina faɗin "Am sorry my love."
"Sorry for your self." Ya faɗa a daƙile.
Na shagwaɓe murya, cikin salon da na san yana rikita shi na ce "Ni dai dan Allah ka yafe min, na amshi laifina."
Shima ƙwantar da muryar ya yi ya ce "Is ok, amma kin san ba ni kika ma laifi ba ko?"
Bisa tilas na ce "Uhmm."
"To ki je ki bata haƙuri kin ji ko?"
Na lumshe idona, sam ban ga laifina ba, amma da ya ke ina buƙatar kan mijina dole na yi abinda ya ce, cikin sanyin jiki na ce "To, amma kai ka haƙura ko?"
"Dama bana fushi da ke ai, ke ma kin san ba zan iya ba." Ya faɗa a tausashe.
Na murmusa "Na sani Sufyan."
"Kin ci abinci?"
Na girgiza kai kamar yana kallo na "Uhm Uhmm."
"Why?"
"Bana son shan kokon ne."
"Ok, dama Umma ta kirani wai Asiya ba zata sha ba, zan je in samo mata abin breakfast sai in taho miki da shi, me kike so."
Wani baƙin ciki ya taso ya turnuƙe ni, wai Asiya, don me komai sai ta danganta mijina da ita?
"Baki faɗa min me kike so ba?"
"Na ƙoshi."
Sai na ji ya ƙwashe da dariya yana faɗin "Babyna ana kishi."
Na zunɓuri baki kamar yana gaba, duk da ina da 100% sure ba zai taɓa maida Asiya ba, amma dai ina jin haushin ta.
"Babyna.."
Daƙyar na haɗiyi malolon baƙin ciki na amsa "Uhmm."
"Kin manta alƙawarin da na miki? Ke kaɗai zaki mallaki Sufyan har abada? Ko kin manta?"
"Ban manta ba."
"To don me zaki riƙa ɓata ranki akan abinda kin san ba zai taɓa faruwa ba? Kina ji na ko? Dan Allah ki bar ta da hankalin ki, Sufyan na ki ke kaɗai muddun zaki min abinda na ke so, daga ke babu ƙari....
*******************
Idan na ce maku ban ƙosa mu koma gidanmu ba, wallahi na yi ƙarya domin yadda ka san baiwa haka Umma ta mayar da ni, kowanne aikin wahala kin ji an ce a kaima matar Sufyan da Jamila, a ƙarshe kuma Jamilar zamewa take ta barni da wahala.
Gashi ban isa na ce aa ba, hasalima duk abinda Umma ta ce ya zauna, don wata irin ƙauna da girmamawa Sufyan ya ke mata, ko musu bai bani damar na yi ba, don wallahi na san idan na kuskura na soma, tsab zan sha maruka idan ma ban yi a bakin aure na ba.
Ƙiri ƙiri Umma ta ke nuna min haihuwa da ni wahala ne, ni ban san uban da ya ce mata ba lafiyayya ba ce ni, ni ba sikila ba, amma ta bi ta ahe sikila zan haifa.
Har ranar daren da zamu koma ban ga Asiya ba, sai ka ce wata ƴar sarki uban komai sai an yi mata, sannan ni ban isa na shiga ɗakin Umman ba, bare in ce zamu haɗu da ita
Bayan magariba Jamila ta shigo ɗauke da kayan wanki cikin bokiti, ta aje gabana tana faɗin "Umma ta ce dan Allah ki ɗan saɓawa Asiya waɗannan kayan, gobe itama zata juya."
Cike da mamaki na maimaita "Asiya?"
Ta gyaɗa kai "Eh, ƴan kayan ta ne kala uku sai hijabai, kin san bata zo da kaya masu yawa ba, babu wanda zata saka gobe."
Wata uwar ashar na mulmulo na auna a zuciyata, don ba dai zai yiyu a fili ba, na gyara zamana ina kallon ta cike da takaici lokacin da ta ɗauki hijabi tana faɗin "Ki fara yanzu nima zan sawo hypo a sama farar hijabin."
Na ɗauke kai kamar ban ji ta ba, yayin da ta fice bayan ta ƙara turo min bokitin gabana, tana fita na auna ashar a fili, wallahi ban ga ta yadda zan ma kishiya wanki ba, ba ma zai yiyu ba, na koma na ƙwanta ina saƙa da warwara yayin da nike nemawa kaina mafita, don ban dai isa na ce bazan yi kai tsaye ba, kuma bana jin ko sama da ƙasa zasu haɗu zan iya wanke kayan ta, don har ga Allah duk da Sufyan ya min alƙawarin ba zata taɓa dawowa ba, zai rayu dani ni kaɗai ina matuƙar kishin ta, bare ma da na ga yadda Umman ke nuna fifiko tsakanin mu.
Wayata na janyo na kira fannata, ina jin gun ta kawai zan samu shawara, duk da itama da haushin rashin zuwan ta har yanzu bai bar ni ba, sai da ta katse tukun ta kira ni, bayan mun gaisa ta ke tambayar "Ya ƙarin haƙuri?"
"Angode Allah."
"Allah ya sa masu ceto ne."
Na amsa da "Amin." Sannan na cigaba da faɗin "Kin san wani abu?"
"A'a sai kin faɗa."
"Shawara zaki bani dan Allah."
Cikin halin ko in kula ta ce "Allah shi sa ba ta masu aure ba ce."
Ban damu ba na cigaba da faɗin "Uhmm, kin san uwar yaran nan ta zo, tsohuwar matar Sufyan, to wallahi yadda uwar shi ke min abu ya ɓaci Fannata, sam bata ƙauna ta, ta fi ƙaunar wacce yanzu ma basa tare da ɗanta."
Fannata ta ce "Ai da yake uwar shi ce, ita ta haife shi, ki yi haƙuri komai zai wuce."
Na girgiza kai haɗe da cije laɓɓana na sama ina faɗin "Ba zaki gane bane Fannata, sabida fa tsabagen rainin wayau, yanzu fa wankin ta aka kawo min in yi mata tana ƙwance kamar ƴar saki."
"To ya zaki yi Nafeesa, dole ki yi, ki yi haƙuri Allah ya ƙara maku zaman lafiya da mijin ki."
Cike da mamaki na ce "Kina nufin in yi wankin wai?"
"To ni na isa in ce kar ki yi? Aure fa kike? Ki yi sabida darajar auren ki."
Ta yanke wayar ta, sai na ji ta kuma haɗa min zafi, kamar fa baƙar magana ta yaɓa min, na ja siririn tsaki, na koma na ƙwanta ina saƙa da warwara.
Ina a ƙwancen Jamila ta dawo, a zaton ta na gama wankin, na kalli agogon wayata na ga kusan 45mints da fitar ta, na taɓe baki na yi kamar bacci na ke yi.
Ta kalli kayan wankin sannan ta kalle ni cike da gadara ta ce "Wai ba ki fara wankin ba?"
Daga ƙwancen na amsa "Eh."
"To ki tashi ki yi, zan tattara ɗakin."
"Ki bar ɗakin na tattara, bana jin daɗin jikina, ba zan iya wani wanki ba gaskiya, kuma ita Asiyan me ya same ta da ba zata fito ta wanke kayan ta ba?"
Ta buɗe baki ta ce "Amma dai Nafeesa ba ki da imani, matar nan ta rasa ɗiyata har uku sannan ki ce ta fito ta yi wanki a ƙwana na baƙwai.?'
Na watsa mata harara "To ai ke sai ki mata, ni kam bana jin zan iya wanki yanzu, kaina ke ciwo ma. "
Ta kalle ni sheƙeƙe ta karkace kai tana faɗin " To bara in faɗawa uwar mijin ki, ai aikin na ta ne.."
Ta juya ta fice tana huci, yayin da na koma na ƙwanta zuciyata na azalzala.
#UWAR SUKUM.
[5/24, 8:54 PM] RN Feedohm: 💧💧 *KUSKUREN SO.*
FREE BOOK
*HASKE WRITER'S ASSO.*
*FEEDOHM*
Wattpad@Feedohm
_Ga ba ɗaya littafin nan sadaukarwa ne ga NAFEESA Muhammad SULE, maman jinjiri, Alherin Allah ya kai maki a duk inda kike._
_Ina kike Aunty Zainab Abubakar Kotorkoshi? Ke ma ina maki fatan alheri._
*027*
Wani irin fargaba da tsoro ya kamani, lokacin da na fahimci bayan Umma har da Sufyan suka dawo a tare, sai na ji tamkar na ɗauki bokitin na fice tun kafin su iske ni a ɗakin na