Showing 12001 words to 15000 words out of 83936 words
ke magana ba, a dai iya karatun addinin da nayi, na san ba zan fallasa abinda ake kira da sirrin aure ba, kuma Mama ba zata bani wannan fuskar ba.
Bayan ya aje ni ya ɗauki 1k ya bani ya ce na riƙe ko zan yi wani abin, na ƙarɓa na yi godiya na shige gida cike da farin ciki, ina shiga ciki da Amadi na fara haɗuwa ya wani ɗauke kai yana zunɓurar baki.
Murmushi kawai na mashi don na son zancen, ko jiya ya faɗa min ba zai kuma zuwa gidana ba, wai mijina baya barin a shiga, a jiyan ma don mama ta matsa masa da ba zai je ba.
A Falo na iske Mama tana cin wainar fulawa, tun kafin na ƙarasa na ji wani irin wari ya daki hanci na, na toshe hanci ina kallon ƙwanon ina yatsina fuska, sai na ji duk duniya babu abinda na tsana sama da wainar fulawar, ban san lokacin da na ce "Mama dan Allah ku kauda wannan abin in shigo, wallahi warin shi ba daɗi."
Mama ta juya Plate din hannun ta, a hankali ta ce "Wainar Fulawa ce."
Na runtse ido ina ƙoƙarin maida aman da ya taho min "Eh bana so dan Allah."
Kafin ma ta ɗauke na ji aman ya taho, don haka na ruga da gudu bakin tap na shiga sheƙa shi, Mama ta biyo ni da sauri tana min sannu, sai da na amaye duk abinda ke cikina sannan na kuskure bakina muka shiga ɗakin tana jera mun sannu.
"Ba ki lafiya ne?" Ta tambaya bayan ta miƙo min zoɓo a cikin cup.
Na girgiza kai "Lafiya ta lau."
"Uhmm."
Na karɓi zobon na cigaba da korawa muna gaisawa, sai na tana yi tana kallo na, cike da bayanai a fuskar ta, ni kam har ga Allah ban kawo komai a rai na ba.
Amadi ya shigo da rake a hannun shi, na zabura na amshe ina faɗin "Mara kunya, idan ba ka je gidana ba mutuwa zan yi?"
Mama ta ce "Yauwa kin tuna min, Nafeesa ina kike zuwa da duk lokacin da mutane suka je gidan sai ace baƙya nan?"
"Wa kuma ya je Mama?"
Ta watsa min harara "Banda Amadi har Aunty ki Fati da Luba babu wanda bai je ba, sannan daga nan maƙwabta ma sun je aka ce baƙya nan."
Na haɗiyi yawu ina ƙoƙari samo ƙaryar da zan yi na kare mijina, don wallahi na san shine da wannan aika aikar, kuma fa babu inda na ke zuwa.
Sam barka Amadi ya ɗauko tashi wainar fulawar kafin na yi wani yunƙuru amai ya sake ƙwace min, wannan karon a falon na yi abina, kuma shi ya ƙwace ni daga bayanin da zan ma Mama.
UWAR SUKUM.
[5/17, 8:18 PM] RN Feedohm: 💧💧 *KUSKUREN SO.*
FREE BOOK.
*HASKE WRITER'S ASSO.*
*FEEDOHM*
Wattpad@Feedohm
_Wannan littafin gaba ɗaya sadaukarwa ne ga NAFEESA Muhammad SULE Alherin Allah ya kai maki a duk inda kike._
*008*
Sai da ya lafa tukun na balbale shi da masifa "Wallahi fita, kar ka kuma shigowa da wannan abin, ka tsaya can ka ci abin ka a waje."
Mama ta kalle ni yadda kasan an kubto maganar daga bakinta ta tambaye ni "Nafeesa ciki gare ki?"
Na kalle ta firgice ina girgiza kai, so na ke na ce mata aa amma magana ta gagara fitowa daga bakina, sai dai tsuru tsuru da na yi da idanu ina kallon ta.
"Tambayar ki na ke?" Ta kuma faɗa a tausashe, har lokacin idon ta yana kai na.
Da ƙyar na tambaye ta "Wane irin ciki kuma Mama? Ni banda wani ciki."
"To baki lafiya ne da kike da sheƙa amai tun zuwan ki?"
Na kawar da kai gefe ɗaya, ina jin wata irin kunya na tatsa jiki na, sai da na zunɓuri baki sannan na ce "Ni fa lafiya ta lau."
Ta gyaɗa kai ta ce "Allah ya ƙara lafiyar, amma wannan aman na ki ba haka nan ba."
Daga haka bata kuma mun maganar ba, yayin da ta bar ni da tunani fal a raina, kafin na yunƙura miƙe ta gyara gun tsaf ta goge, ta kunna tsintsiyar ƙamshi, sannan ta fita don ta ɗaura abincin rana, na bita ina tambayar "Me zaku dafa dan Allah?"
Ta kalle ni ta ce "Shinkafa da miya."
Na langwaɓe kai ina faɗin "Dan Allah Mama ki min ɗan waken rogo, na daɗe ban ci ba."
Ta ce "To."
Nan da nan ta bawa Amadi kuɗi ya siyo rogon ya kai niƙa, sannan ta jefa min ɗanwaken kafin ta ɗaura na su abincin, ta zubo min a plate yayin da na baɗe shi da yaji da man ja, na yanka tumatur da albasa na ƙwashi abina son rai na.
Ina nan har Babaa ya dawo, na je muka gaisa, muka ɗan taɓa fira sama sama sannan na dawo na zauna falo, maganar Allah na ji daɗin zuwa gidan.
Da zan tafi Mama ta kulle min sauran garin rogon ta ce idan ina so sai na jefa a gida, idan kuma ina buƙatar wani abu na kira ta waya sai a min Amadi ya kawo min.
Na ce "To." Ina mamakin wannan kulawar ta ta, ina ganin fa ita ta gama yankewa ciki ne da ni.
**********************
Tunda na aje jikkata a falo na ke tunanin maganar Mama, anya kuwa ba gaskiya ta faɗa ba? Na yi saurin buɗe App ɗina na Flo, na duba last Date da na yi period, na duba date ɗin yau, sai na ji gabana ya faɗi, domin na yi ƙarin 10days a ƙwanakin da ya dace in yi period.
"Baby." Na ƙwala ma Sufyan kira da ya je kitchen ɗauko plate zai juye abincin da ya yi order.
"Yes."
"Dan Allah zo ka ji."
Ya dawo ya tsaya gabana, yayin da na kamo hannun shi na janyo shi ya zauna gefe na, na kalle shi a raunane na ce "Ina da ciki.."
Ya yi dariya mai sauti yana shafa haɓar shi, kafin ya tambaye ni "In ji waye?"
"Mamana, sannan kuma na duba da gaskiyar ta."
"Ki ce faifai na kika buɗe mata." Ya ƙura mun ido
Na girgiza kai na ce "A'a, kawai dai na yi ta amai ne shine ta tambaye ni."
"Ita Maman likita ce? Ba wani ciki."
"Wallahi da ƙwai." Na faɗa kamar zan yi kuka.
Ya yi minti biyu yana kallona, sannan ya janyo ni jikin shi ya ce "Ya akai kika sani.?"
Na ƙwantar da kai na jikin shi sosai ina faɗin "Banyi period ba wannan month ɗin, sannan da na ji ƙamshin wainar flour na yi ta amai kuma da ina so."
"Kin tabbata?"
Na gyaɗa kai a raunane, ya miƙe ya koma kitchen ɗin, ya ɗauko plate ya dawo ya juye fried rice da moimoi da ya siyo, ya soma ci a hankali, yayin da na janyo wayata na shiga browser nayi typing Can AS and AS genotypes get married? Abinda na gani yasa gabana ya faɗi, za su iya aure amma dole ksu shirya amsar ƙalubalen rayuwa, domin aƙwai low chance na samun ɗiya lafiyayyu, baa ce ba zasu haifi AA AS ba, amma probability na samun su is 0.1, ai na ji ƙirjina na dakan uku uku, yayin da hawaye suka ɓalle min.
Ya kalle ni da murmushi a fuskar shi ya ce "Kuka?"
Cikin rawar murya na ce "Bana so na haifi sickler."
Ya ja ƙaramin tsaki yana murmushi, kafin ya aje spoon ɗin, ya ja karan hancina ya ce "Wa ma ya tabbatar da cikin bare mu je maganar haihuwa? Bara in dawo."
Ya miƙe ya fice, yayin da ya barni tallabe da kumatu, bai wani ɗauki lokaci ba ya dawo da Pt strip a hannun shi, ya bani ƴar ƙaramar roba ya ce in yo fitsari a ciki, na miƙe jikina na rawa na yi na kawo mashi, yayin da ya tsoma tsinken a ciki, muka zuba ma shi ido muna jiran sakamako.
Layi biyu ne suka bayyana bayan ƴan mintuna, sai na ga ya goge gumin da ya keto mashi, ya kalle ni lokacin na buɗe baki sosai na soma rizgar kuka na, domin har ga Allah na ga yadda ɗiyan Aunty Fati ke cin wahala idan ciwon ya taso ma su, duk da dai ita As ce mijin kuma Ss.
"Wai kukan me kike?" Ya janyo ni jikinshi.
"Bana son sikila."
Ya ja karan hancina ya ce "To wa ya faɗa maki su zamu haifa?"
Na ce "Haka aka ce."
"Wa ya ce?"
Na cigaba da kuka na, ya ƙara janyo ni jikin shi, ya sa hannu ya share min ƙwallan, sannan ya sumbaci goshi na ya ce "Ba haka ba ne."
Ya tashi ya ɗauko pen da paper, ya zauna ya min crossing, inda ya nuna min zamu iya haihuwar AA AS da kuma SS.
Cikin rawar murya na ce "To ya zamuyi mu mu san wanda zamu haifa a ciki?"
Ya murmusa ya ce "Ban sani ba, amma yawanci yaron farko ne ke da matsalar, kuma ana iya zuwa idan cikin ya kai 10weeks ayi test na embryo genotype din, idan embryo din na da SS genotype sai a zubar."
Na kalle shi a raunane na ce "To shi zamu yi?"
Ya girgiza kai "Wannan wahala ne, kuma ga tsada, ina jin ya kai 250k, kuma Allah na iya nuna mana iyakar mu, kina so na ba?"
"Uhm.!
"Zamu iya rayuwar mu ba ƴa ƴa."
Ai da sauri na girgiza mashi kai hawaye na bin kumatuna, ya kama kafaɗata gam ya riƙe yana kallon cikin ƙwayar idanu na, sai da ya dai dai idanun mu sannan ya lumshe su, a hankali ya ce "Zamu zubar."
"A'a Sufyan, nima ina so na haihu, haka maman ka na son ganin jikokin ta."
"To sai me? Kin shirya wahala ne?" A tsawance ya yi maganar.
"Aa, amma sai mu yi test din da ka ce, idan SS ne na yadda a zubar."
Ya ce "To." Ya miƙe daga kujerar da ni ke, ya koma mai ɗaya, ya maida hankalin shi ga wayar shi, yayin da takaici ya sa na cigaba da rizgar kuka na.
Na san ba zai jure kukan ba, kuma hakan ta faru, domin kusa da ni ya dawo ya janyo ni jikin shi ya matse yana lallashi, bai rabu da ni ba, sai da ya ga na yi shiru, sannan ya hau min cakulkula, bisa tilas na dayaye na cigaba da harkokina, sai dai har ga Allah damuwa na cinkushe a raina.
UWAR SUKUM.
[5/17, 8:18 PM] RN Feedohm: 💧💧 *KUSKUREN SO.*
FREE BOOK.
*HASKE WRITER'S ASSO.*
*FEEDOHM*
Wattpad@Feedohm
_Wannan littafin gaba ɗaya sadaukarwa ne ga NAFEESA Muhammad SULE Alherin Allah ya kai maki a duk inda kike._
_Ina kike Aunty ZAINAB ABUBAKAR KOTORKOSHI? Wannan shafin na ki ne, kema Alherin Allah ya kai maki a duk inda kike._
*009*
Tunda ya shigo gidan ya ga su Aunty Fati na ga yanayin shi ya canza, ya gaishe su sama sama sannan ya shige bedroom abin shi, su kan su na lura sun gane bai ji daɗin zuwan su ba, don na ga yadda suke kallon juna, na miƙe a sanyaye na bi bayan shi, na iske shi tsaye jikin taga ya dafa bango, na ƙarasa na rungume shi ta baya ina faɗin "Oyoyo."
"Su waye waɗan can?" Ya tambaya babu yabo ba fallasa.
"Aunty Fati ce, ba ka gane ta ba? Ƙanwar Mama."
Ya ce "Ok."
"Ya aiki?"
"Lafiya lau."
"Za ka yi wanka ne sannan ka ci abincin? Ko in kawo maka ka fara ci?" Har lokacin hannuna na zagaye da ƙugun shi.
"Abincin zan ci."
"Ok, bara in kawo maka nan?"
Ya juyo yana kallona, a hankali ya ce "Akan me?"
Na murmusa tare da rausayar da kai na ce "Na ga falon da baƙi ne."
"Sabida baƙi sai na ƙi cin abinci a inda raina ke so Nafee?"
Na ɗago na ƙura mashi ido, sam ban ga abin ɓacin rai ba, a sanyaye na ce "Allah ya baka haƙuri."
Ya yi banza dani, tare da juyawa ya shige toilet abin shi, ni kam jikina a sanyaye na koma falo, na iske har sun ɗauki jikkunan su zasu tafi, na saki murmushin yaƙe na ce "Ina zaku je daga zuwa, dan Allah ku zauna in kawo maku abinci."
Aunty Fati ta ce "A'a sauri mu ke, hakanan dama muka leƙo don na ji Amadi na faɗin baki da lafiya."
Na sunne kai, dai dai nan Sufyan ya shigo falon, ya kalle ta ya ɗauke kai, ya nufi frigde ya ɗauko ruwa ya soma sha, har sun kai ƙofa Aunty Fati ta juyo ta ce "Yauwa, aƙwai wata gumbar riɗi da aka kawo, halawa, zan aiko miki da ita sai ki soma saidawa, zaman hakanan ba zai yiyu ba, sannan na amshi copy na takardun ki, aƙwai wata private nan kusa daku, ku yi magana da mijin ki, idan ba matsala sai ki fara zuwa kafin a samu permanent."
Na ce "To Aunty, nagode sosai."
Na raka su har bakin gate sannan na dawo, na iske har ya soma cin abincin shi, na zauna gefen shi ya janyo spoon na samo ci ina faɗin "Ka ji me Aunty Fati ta ce? Wai zata aiko min da abin sana'a, sannan zata samar man aiki nan kusa damu."
"Na ji, har da tonan asirin da ƙanin ki ya min." Ya faɗa ba tare da ya kalle ni ba.
"Kamar ya?"
"Eh mana, ya je yana faɗa ma mutane baki da lafiya."
Na saki dariya mai sauti tare da taɓe baki na ce "To ai ba cewa yayi ina da ciki ba."
"Hmm."
"Zaka barni?" Na langwaɓe kai.
Ya aje spoon ɗin, ya ɗago ya kafe ni da ido yana faɗin "Talla ko yawo?"
Ɗauke da tsantsar mamaki na kalle shi, ya cigaba da faɗin "Bazan iya haƙurin mutane na cika min gida ba da sunan sun zo ganin ƴar uwar su, sannan ba zan iya haƙurin a cika min gida ba da sunan an zo siyayya, haka ba zan iya haƙurin matata na gantali a hanya ba da sunan ta tafi aiki.."
"Sufyan..."
Ya dakatar da ni ta hanyar ɗaga min hannu ɗaya "Bana son jin komai, kin ji ni kin kuma fahimci me na ke nufi."
Ya ture plate ɗin abincin ya miƙe ya koma bisa kujera, tare da janyo wayar shi da tunda ya fara magana take vibrating, gani na yi ya taɓe baki, sannan ya bi kiran da aka mishi, ya sanya speaker, ya ɗaura wayar a cinyar shi tare da janyo nail cutter ya soma yankar ƙumba yana faɗin "Ina jin ki Hanifa."
"Umma ce ke son magana da kai." Ta faɗa cikin salon kashe murya.
"Ok, ba ta."
Muryar Umman na ji tana faɗin "Yo mi kake tun ɗazu ake kira shiru baa ɗauka ba?"
Ya ce "Ina cin abinci ne, ina wuni?"
"Lafiya lau, me kuka dafa.?"
Na kalle shi, matar da ba gari ɗaya mu ke ba, amma ita ke tambayar abinda mu ka ci, na lumshe ido tare da kauda ƙwanukan na miƙe.
"Tuwo.." Ya faɗa kai tsaye.
"Kai ɓurr." Sai ta sassauta murya ta cigaba da faɗin "Ni kam Sufyanu lafiya lau na ji shiru?"
"Ban gane ba Umma."
"Na ga Hajara ƴar kawun ka da aka yi bikin ku da sati biyu aka yi nata har ta samu ciki, ita kuma Nafeesa shiru ba bayani?"
Sai na samu kaina da shafar cikina, haɗe da lumshe ido ina godiya ga Allah a zuciya, a tunanina zai faɗa mata ina da shi, amma sai na ji ya ce "Haba Umma, wane irin ciki kuma bayan ko wata uku bamu haɗa ba?"
"Ban san zancen banza, kana nufin ba yanzu ba?"
Ya cire speaker ya maida a kunne yana faɗin "Gaskiya kam."
Daga haka na shige kitchen abina, yayin da ni ke mamakin azarɓaɓin ta, duka ko wata uku bamu yi amma har ta soma maganar ciki? Wannan da ace bana haihuwa fa? Ya kenan? Na lumshe ido, wani ɓangaren na zuciyata kuma tunanin dalilin da ya sa Sufyan bai faɗa mata ba, shin ko so ya ke sai dai kawai ace gashi na haihu? Wani lallausan murmushi ya suɓuce min.
Ina tsaye kitchen ɗin ya shigo hannun shi riƙe da cup ɗauke da ruwa, ya miƙo min da wasu tablet guda huɗu, na kalle shi na ɗage gira ɗaya alamun ƙarin bayani, yayin da ya kashe min ido, ya shafi marata ya ce "Tunda ba yanzu zaki fara zuwa ANC ba, kin ga dole mu nemi maganin ƙarin jini da kuzari, kin san bana so wani abu ya taɓa min baby."
Ha? Ya matse bakina, ya saka min tablets ɗin, sannan ya bani ruwa na kora ina murmushi.
"Na ta ya ki?" Ya karɓe sponge ɗin daga hannu na, ya ja ni ya zaunar bisa wani stool da ke cikin kitchen ɗin, sannan ya cigaba da wanken wanken.
Samun kaina na yi da tambayar shi "Wai ya kuke da Hanifa?"
Ya juyo ya ƙanne min ido ɗaya sannan ya ce "Ex."
Na watsa mashi harara na ɗauke kai, sai na ji wani irin kishin ta ma ɗawainiya da ni, kuma dama tun da suka zo na fahimci son mijina ta ke wallahi.
"A Baby an iya kishi." Ya tsinkaye shi cikin kunnuwana.
Na zunɓuri baki na ce "Ba wani kishi, abinda ma Ex ce.."
"Haba?"
Na share shi, na tashi daga kan Stool din na buɗe ƙaramin frigde ɗin da ke kitchen ɗin, na ɗauko mango na wanke na ɗauki wuƙa na koma na zauna ina kallon yadda ya ke kife ƙwanukan inda ya dace.
"Idan kika haifi baby boy Bello zan sa mashi."
Na ƙwashe da dariya "Ba wani Bello wallahi, SALMAN na ke so."
"Uhmm, na yadda zan sa SALMAN, amma idan macece Allah Basira zan sa mata."
"Basira? Na maimaita ina dariya tare da shafar marata da na ji ta ɗan katsa, na cije laɓɓana na ƙasa na aje mango ɗin na miƙe da ƙyar ina lumshe ido.
Da sauri ya kamani yana tambayar "Lafiya dai ko?"
"Marata ke ciwo."
"Subhanallahi, garin yaya? Sannu mu je falo ki zauna, bara in kira Doctor AA." Ya kamani yana jera min sannu.
A haka ya ƙwantar da ni bisa doguwar kujera, ya janyo wayar shi, bugu ɗaya wancen ya ɗauka, Sufyan ya ce "AA ya za'ayi dan Allah? Nafeesa ba lafiya."
Yayi jim ban san me aka ce mashi ba ba, sai na ji ya ce "Ok, sai ka zo." Ya aje wayar ya dawo ya tsugunna gaba na, tare