Showing 78001 words to 81000 words out of 83936 words

Chapter 27 - KUSKUREN SO Book Complete by Feedohm.txt

Feedoms   

21 Sep 2025

1702

har da award ta rashin hankali da sanin ya kamata..

"Kina lafiya? Na tsinkaya shi yana faɗa a tausashe.

Na girgiza kai alamun aa, ina faɗin "Dan Allah zan iya ganin ka?

Ya gyaɗa min kai "Mu je.."

Ya shige gaba ina biye da shi har office ɗin shi, sai da na zauna sannan na fara magana cikin rawar murya ina wasa da yatsuna "Dan Allah, uhmmm zaa iya maida mun, uhmmm mahaifata."

Sai na ga ya ƙwashe da dariya, sai da ya yi mai isar shi sannan ya tambaye ni "Tana ina?"

Na ware hannaye na, alamun ban sani ba, ya miƙe ya zuge labulen tagar da ke kusa da shi yana faɗin "Zo ki gani...

Babu musu na na miƙe na leƙa jikina na rawa, ban ga komai ba sai manyan karnuka da ke shawagi a cikin asibitin, na kalle shi a razane da alamun ina buƙatar ƙarin bayani, kamar kuwa ya sani ya cigaba da faɗin "Sun cinye, na tabbatar i zuwa yanzu har kashin ta sun yi Nafeesar Sufyan."

Na lumshe idona da sauri, yayin da jikina ya cigaba da rawa, na dawo jagwab na zauna bisa kujerar nan da nan hawaye suka soma wanke min fuska, shi kenan komai ya ƙare min, me yasa? Me yasa na yi haka? Me yasa na yadda da shi? Me yasa na kasa tuna shima namiji ne..

"Mahaifa ba wutar lantar ki bace da zaa iya cirewa a mayar a duk lokacin da aka dama Nafeesar Sufyan.." Ya furta idanun shi a kaina.

Ban san me yasa ya ke son haɗa sunana da Sufyan ba, ban san me yasa ni kuma na tsani hakan ba, ban ce mishi komai ba, na miƙe jikina na rawa na soma tafiya jiri na ɗibata, ban yi zato ba sai tsinkayar shi na yi yana tambayar "Duka ko wata ɗaya baayi ba Nafeesar Sufyan, me yasa kike son mayarwa, bayan da amincewar ki akayi komai..

A zafafe na ce "Sabida shima namiji ne, tsinanne, wulaƙantacce, mugu maƙaryaci."

Ya tallabe fuska yana kallona, kamar yadda nima kallon shi na ke yi, sai na kuma dawowa na zauna bisa kujerar da na tashi hawaye na fita daga ƙwayar idona, wannan karon cikin rawar murya na ce "Dan Allah ka taimaka min, ko ta roba ce ka saka min likita, na yi kuskure wallahi, bai kamata ba na amince da shi haka, ka taimake ni Sufyan ba zai zauna da ni ba, bama son juna, dole na matsa wani guri, babu kuma wanda zai ƙarɓe ni a haka, dan Allah.! Na fashe da kuka tare da kifa kaina bisa tafukan hannaye na.

Ya murmusa ba tare da ya ce min komai ba, don haka cikin kuka na soma zayyana mishi duk abinda ya faru sai ka ce ya tambaye ni, ku fahimce ni aƙwai lokacin da idan baka furta abinda ke ranka ba, wallahi zuciyar ka na iya bugawa, nima cikin wannan yanayin na ke, sai dai har na gama faɗa mishi bai ce da ni komai ba, don haka zura mishi ido tsawon minti biyar ina jiran ko zai iya taimako na,  amma bai ce da ni komai ba, kuma baya da niyyar tankawa amma ina iya hango tsananin tausayi a ƙwayar idon shi, zaman dai ya ishe ni, don haka na miƙe a sanyaye na fice ina ƙoƙarin riƙe kukana, amma ba zan iya ba, shi kaɗai na ke iya yi na samu sauƙi.

Kamar na koma gidan Sufyan sai wata zuciyar ta tunatar da ni, ina da iyaye, ina da ƴan uwa, waɗanda ke sona kamar dai Asiyar Sufyan, don haka kai tsaye na wuce gidan mu, cikin rashin saa na haɗe da Baaba a bakin ƙofa ya tare ni bayan ya gama kallona ya ce "Haɗari kuka yi?"

Na girgiza kai "Ƴan uwan Asiya ne suka dake ni."

"Asiya?"

Na ce "Eh, tsohuwar matar Sufyan da ta dawo."

"Me kika masu?" Ya faɗa da alamun ɓacin rai a tattare da shi.

"Babu komai.."

Ya girgiza kai "To hauka suke da baki masu komai ba zasu rufe ki da duka?"

"Aa zagina suka yi na rama."

Ya girgiza kai "To Allah ya ƙyauta." Sai na ga ya tsaya bakin ƙofar ya ƙi bani hanya na wuce

"Zan shiga Baaba." Na furta muryata na rawa.

"Lafiya dai ko? Gaishe mu kika zo yi ko ya abun ya ke Nafeesa?"

Na fashe da kuka "Auren ne na gama."

Baaba ya murmusa "Subhanallahi, ya sake ki ne?"

Na girgiza kai "Aa."

"Baa gama aure ba Nafeesar Sufyan." Shima ya furta, ai kuwa na yi saurin kallon shi, shin jamaa sun fahimci bana buƙatar sunan a yanzu shiyasa suke kirana da hakan ko ya abin ya ke.

Na daure na ce "Wallahi an gama auren Baaba, ba zan zauna dashi ba."

Ya girgiza kai "Idan na fahimce ki yaji kika yi?"

Na girgiza kai da sauri "Aa, sakina zai yi."

"To ki je idan ya sake ki sai ki dawo ki shiga Nafeesa, ba kuma saki ɗaya ba, sai dai idan kin tabbatar da babu aure ƙwata ƙwata a tsakanin ku, amma ba zan barki ki shigar mun gida ba da sunan yaji sabida ban san wannan karon wane irin rashin kunya zaki mana ba idan har mijin ki ya zo ɗaukar ki.... " Ya zura mun ido.

Na sadda kaina ƙasa, sai yanzu na fahimci me ya ke nufi, na sa babban yatsa na share hawaye na, amma ai na basu haƙuri, kuma sun yafe min, me yasa ba zasu mance baya ba....

"Dan Allah ka yi haƙuri Baaba, ku yafe min."

"An yafe miki Nafeesa, amma ki sani ba zaki sake shiga gidana ba, muddun da auren Sufyan a kan ki, ina tsoron ki, ina tsoron Allah Nafeesa, ki koma ki cigaba da son mijin ki, Allah ya baku zaman lafiya...."

Duk yadda na so na shiga gidan wallahi hanani ya yi, bisa tilas na juya ina kuka, me yasa komai ya ke zo min ba dai dai ba, me yasa komai ke juya min, haka na hau adaidaitar tunda dama ban sallame shi ba, ban da inda zan je, babu wani mutumi ɗaya da na ma mutunci a lokacin da na ke jin kaina sarauniya a gidan Sufyan, bare yanzu na lallaɓa naje can, don haka bisa tilas nayi gidan Sufyan bayan mun isa na ce da mai adaidaitan ya jira na shiga na kawo mishi kuɗin shi, ina shiga na tarad da kujeruna da duk wani abu da ya zama mallakina a cikin falon an watso shi harabar gidan, sai na ji wani abu ya dake ni, na runtse idona gam ina kiran sunan Allah, daƙyar na iya saita kaina na shiga ciki na iske Asiya da ƙannen ta zaune an baje ana cin abinci hankalin su ƙwance, sai ka ce ba su illata ɗiyar wani ba, yayin da Sufyan ke kitchen yana ƙaro masu stew, na lumshe ido na shige ɗaki na ɗauko 1k na koma na sallami mai napep ɗin, sannan na dawo na shige ɗaki ba tare da na kula su ba, duk da kuwa irin kallon banzan da suke mun.

Ina zaune gefen gado sai ga Sufyan ɗin ya shigo fuskar nan murtuk yana tambaya ta wai "Ya jikin? Har an sallamo ni?"

Ko kallon shi ban yi ba, don wallahi yadda na tsane shi ƙara na kalli fuskar kare sau dubu da kalle shi.

Ya daka min tsawa "Baƙya ji ne? Ko nima rashin kunyar zaki mun? Don na fahimci wani iskanci kike ji a gidan."

Still dai watsi na yi da shi, ya taɓe baki "Anyway na san dai kin ga kayan ki a waje, dama kin sani falon na Asiya ne tun kafin na aure ki, ita ta fara zama a ciki, bayan ta tafi ne kika zo har kika sa kayan ki, so yanzu kuma ta dawo shine take son abinta, kuma laifin ki ne, don sai da ta ce ki mayar da kayan gefe guda, itama ta sa nata amma kika zage su har suka dake ki, to yanzu ta fasa, sabida haka ki san yadda zaku yi da su, ko dai ki mayar gida a sayar a ƙara a yi cefane ko kuma ki samu inda zaki raɓa su ko da a cikin ɗakin mai gadi kafin na ga yadda zaayi.. "

A zafafe na ce "Baka ji kunya ba Sufyan?"

Ya ware ido da hannu yana kallo na, na miƙe tsaye na cigaba da faɗin " Dama kasan baka da inda zaka aje mace biyu ka maido da ita?

"Ko kuma na aure ki ba.? Ya bani amsa fuskar nan murtuk.


Na gyaɗa kai "Haka ne, kuma sakin ma na gare ka, idan ka so zaka iya sakina ka cigaba da zama da Asiya."

"Idan hakan ta kama ma za'ayi."Ya furta cikin halin ko in kula.

Duk da dai ba son shi nake ba, amma sai da maganar shi ta dake ni, na kulle idona gam ina furzar da zazzafar iska daga bakina.

Ya cigaba da faɗin "Wata ɗaya zasu yi, bana son rashin kunya, ki zauna da su lafiya, idan ba haka ba wallahi zan iya ɗaukar duk matakin da na ga dama, ko kuma na ƙyale ki dasu su yi maganin rashin kunyar ki."

"Sabida ƴan uwan Asiya ne.."

Kafin ya bani amsa Asiya ta faɗo ɗakin rai a ɓace tana faɗin "Dan Allah ta ya zaka bar su zaune suna jiran stew ka zo nan ka tsaya, ni fa kasan bana son haka, bana son a wulaƙanta min ƴan uwa, bana so Sufyan.." Ta ɗaga hannu sama idon ta a rufe.

Sai ya hau bata haƙuri "Dan Allah yi haƙuri, na shigo ina mata warning ta zauna da su lafiya, ta aje duk wani iskancin ta, nan gidan ƴar uwar su ne, suna da iko da daraja a cikin shi....

Ta kalle ni sheƙeƙe ta taɓe baki tana faɗin "Ya fi dai.."Ta juya ta fice, yayin da ya bi bayan ta yana ƙara bata wani haƙurin...



Albishirin ku makaranta littafan Hausa, kun san tagwayen littafan mu na hanya? Kun san an gama free pages na littafin DUHU da Haske, daga haziƙar marubuciyar ku SLIMZY?Sannan kuma ga littafin ƘALUBALEN RAYUWA, shima ya na gab da zo maku? Daga haziƙar marubuciyar ku FEEDOHM? Duka littafan akan 700,idan kuma ɗaya kike so 400, ƴar uwa ki shigo a yi tafiyar nan da ke, tafiyar da babu Nadama a cikin ta.

Ki biya ta wannan hanya 9994468172 Access bank fiddausi musa ko katin mtn ta wannan lambar 08036953516 tare da shaidar biya ta 08036953516 ko 07042277401..





*UWAR SUKUM...*
[7/9, 5:22 PM] RN Feedohm: 💧💧 *KUSKUREN SO.*

FREE BOOK

*HASKE WRITER'S ASSO.*

   *FEEDOHM*
Wattpad@Feedohm



  _Ga ba ɗaya littafin nan sadaukarwa ne ga NAFEESA Muhammad SULE, maman jinjiri, Alherin Allah ya kai maki a duk inda kike._

_Ina kike Aunty Zainab Abubakar Kotorkoshi? Ke ma ina maki fatan alheri._


*045*



Ni kam na sulale ƙasa na fashe da kuka, sai yanzu na ƙara nadamar abinda na yi ma ƴan uwa na, sai yanzu na fahimci suma suna buƙatar daraja da mutunta ga mijin ƴar uwar su, na kifa kaina jikin gado, yayin da na janyo wayata na kira Maama, na ƙara neman gafarta, sannan na kira Teemah itama na nemi gafarar ta, sai na ji tana gargaɗata akan na fita harkar ƴan uwan Asiya, Baaba ya ce na masu rashin kunya sun dake ni, na lumshe ido, kowa fa gani ya ke laifina, kuma nasan hakan bai rasa nasaba da rashin kunyar da na yi a baya, na lumshe ido na dai ce mata to.

A ranar nan Umman shi ta kira ni, ina ɗauka ta balbale ni da faɗa, wai an ce na ci mutuncin ƴan uwan Asiya, ni fa duk ciki wannan kalmar ke ɓata min rai, sai ka ce wata bura uba ce a Asiyar, da ƙyar na taushi kaina na bata haƙuri, tana ta min barazana da banzan auren da bata san na gaji dashi ba, sannan ta yanke wayar....



**************

Kusan sati biyu ƴan uwan Asiya na nan ba su tafi ba, da na faɗa ma Fannata a waya sai ta ce min haka ƴan wajajen Maiduguri suke, sai su yi wata da watanni gidajen ƴan uwan su, kuma dole miji ya kula da su, ni kam Allah ya sani na gashi da su, sun bi sun takura mun, sun addabe ni, bani da damar ko fitowa falo, daga ɗaki sai ɗaki, kuma don masifa har kayan kitchen ɗina su tattara sun fiddo min su waje cikin buhunna, bisa tilas na ƙwashe su na maida su ɗakin mai gadin, gashi idan na kira gida na ce ma Maama zan dawo ta lallaɓa Baaba sai ta ce in zauna in cigaba da son Sufyan Allah ya bamu zaman lafiya, ni kam har yanzu na kasa fahimtar kalaman ta, na kasa gane me take son isar min..

Sannan abin takaici na kasa gane makomar aure na, na kasa gane matsayina, don wallahi a yadda na ke zaune, ƴar aiki ma ta fini daraja, sai fa a dafa a zuba min shi a plate a buɗe, a sa wata mara kunya ta kawo min shi ƙofar ɗaki ta aje, gashi shi kan sa Sufyan ɗin ban isa na gan shi shi ɗaya, indai yana gidan to yana zaune cikin su ana fira da dariya, idan na ce ina son zan yi magana da shi, sai ya ce wai na yi ta anan an riga an zama ɗaya, a ɗan lokacin na fige na lalace, sai ka ce ba ni ba, maganar abinci ma da na ce bana cin na su, sai ya ce wai ban san mutunci ba, babu wanda zai raba mishi abincin gida, a girka a bani don bana son zaman lafiya in ce bai min ba, to in yi yadda na ga dama, shima na kira Maama dai ta maimaita min, in cigaba da son Sufyan Allah ya bamu zaman lafiya, bisa tilas na cigaba da cin abinci, idan ma na ce ba zan ci ba ni yunwa zata illata.

Ganin abun ba mai ƙarewa bane yasa na kasa daurewa, kuma ba wai kuma ina buƙatar Sufyan ba ne, bawai ina buƙatar soyayya daga gare shi ba ne, aa ina buƙatar ƴanci na ƴa mace, ina bukatar ƴanci irin na mai aure, ko kuma ƴancin irin na jawara.

Ina fitowa daga ɗaki na wuce bayan gida, na ɗauko galon na petrol na dawo na shiga kitchen suna bina da kallo na ɗauko ashana, sannan na dawo falon na yi tsaye bisa kan shi, kamar dai kullum a bisa doguwar kujera suke, ƙannen ta kuma na tsakiyar falon suna lido, takaici ya kamani, kamar dai ba shi bane da baya buƙatar wani ya zo gidan shi, na shanye hawayena kafin su fito, da ya ke raina ya gama dagulewa kuma na shirya ma komai zai faru ya gari don haka fuska a murtuk, cikin tsawa na ce "Ina son magana da kai ka taso."

"Ina jin ki." Ya faɗa ba tare da ya kalli inda ni ke tsaye ba.

Suka kalle ni suka taɓe baki, yayin da Asiya ta gyara kanta sosai bisa cinyar shi, tana wasa da yatsun hannun shi, na ɗauke kai na ce "A ɗaki na ke son maganar..."

Sai suka ƙwashe da dariya, babban cikin su ta ce "Jarabar ta motsa ƙanwata." Sai ta maki ƴar uwar, irin kamar ba da ni suke ba, kuma wallahi daga ni har shi mun san da ni suke, kawai dai da yake shanyayye ne ba zai tanka ba.

Bance da su komai ba, na ƙura mishi ido ina jiran na ji daga gare shi, yadda zan maida mishi dai dai shi.

"Asiya da ƙannenn mu ne, ki faɗa kawai." Ya maimaita wannan karon fuskar shi a murtuk.

A zafafe na ce "Wallahi sai ka taso, na gaji da wannan bura ubar da iskancin, Sufyan ka taso ka faɗa min matsayina tun kafin na ƙwashi kutmar uba anan, dan wallahi tallahi zan iya ƙona mu duk mu mutu dan uban mu.."

Asiya ta miƙe yana faɗin "Dan Allah je ka, kar ta tayar min da hankali anan, kasan ni yanzu ba hayaniya na ke so ba."

Yayar ta su ta ce "Yo uban wa ke tsoron mutuwa anan?"

Asiyan ta ƙwaɓeta "Yaya wannan faɗan miji da mata ne, babu ruwan mu.." Suka ƙwashe da dariya.

Ya miƙe kamar sakarai ya biyo ni, a da zan iya cewa asiri ne, amma yanzu na fahimci babu wani asiri, shi namiji indai zai ji sabon gurin, babu iskancin da ba zai maka ba, na ja tsaki lokacin da na ji suna wani iya shege.

Sai da na tura ƙofar ɗakin don na tabbatar zasu iya biyo mu, a dagule na ce "Menene matsayina?"

"Matata.." Ya bani amsa babu yabo ba fallasa, kamar dai ba Sufyan ba, kamar ba mutumin da ke min magana a tausashe ba cike da ƙauna.

Na ciji laɓɓana na ce "Ƙarya kake Sufyan, tuni ka yi wancakali da wannan alaƙar, tun daga ranar da ka cuce ni ka sa aka cire min mahaifa, tun daga ranar da ka tafi ka barni asibiti sannan ka dawo min da tsarabar Asiya.."

Ya hau jujjuya kai, irin na dame shin nan, cikin fushi ya ce "Kin cika jaraba wallahi Nafeesa ban san me kike so ba kuma."

"Haƙƙina ko saki? Na ma fi buƙatar sakin fiye da gyaran.."

"Wane haƙƙi?" Ya zura min ido.

Na watsa mishi harara "Bana so Sufyan, bana girki, baka kulani, baka ƙwana ɗakina, abinda ya fi kawai ka sake ni.."

Ya ja tsaki yana faɗin "Jarababba, ko arba'in ba ki yi ba amma kin fara neman namiji, ina ce idan mace ta haihu sai ta yi arba'in take amsar mijinta."

"Yaushe na haihu.?

Bai bani amsa na, sai na ga ya ɓata fuska, ya wani tuɓe rigar shi ya zare wando yana faɗin "Ina jin wannan kike ma wa, zo ki amsa... " Ya kama bananar shi yana jijjigawa.

Ya wani fizgo ni ya jefa bisa gado ina faɗin "Bana so, bana buƙata Sufyan, dan Allah ka rabu dani, bana so wallahi, sakin kawai na ke buƙata, ka daina taɓa ni, bana son ka wallahi.."

Ya wanka min mari a zuciye yana faɗin "Ƙarya kike Nafeesa shi kike so, idan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login