Showing 54001 words to 57000 words out of 83936 words
tunani, idan na amshe ta, banda inda zan kai ta a siya babu ƙwali ko reciept, na ja siririn tsaki ina faɗin "To ka siya kawai."
"Ah to, amma kin ce jingina, yanzu nawa zaa bar mun ita?"
Ban wani tsaya ciniki ba, don haka nace kawai ya bayar.
"42k, don ma kece wallahi."
Na lashi laɓɓana na ce "To."
"Ina ƙwali ko reciept?
Na dalla mishi harara cike da ƙosawa na ce "Dan Allah babu ko ɗaya, kasan dai ba zan kawo maka abin sata ba ko.?"
Ya saki murmushi yana faɗin "Haka ne, amma tunda babu gaskiya 38k zan bayar, idan wani ne ma ba zan siya ba."
"Na ji."
Ya bani kuɗina na zuba jikka, daga nan gidan su Fannata na nufa, wallahi ko tana so ko bata so dole ta raka ni dan uban ta, da Maman su na fara karo a tsakar gidan, ta kalle ni cike da mamaki tana tambayar "Nafeesa, lafiya kuwa?"
"Lafiya lau, Fannata na nan."
"Eh, amma mai ya fito da ke kina idda, ba sai ki kirata tazo ta same ki a gida ba?"
"Ai ya maida ni." Na bata amsa a gajarce, da addu'ar Allah ya sa Fannata bata min ɗimin masifa ba, ta faɗa mata yadda muka yi jiya.
Ta washe baki "Masha Allahu, tana ciki."
Na ƙarasa ina zunɓurar baki, sai ka ce kaina farau sakin aure, da kowanne banza sai ya ji, ko da ya ke laifina ne da har na faɗa, da ace lokacin da ya sake ni ban dawo gida ba, na koma gidan shi kai tsaye, na riƙe wuta ban saku ba tunda ba cikin hayyacin shi yayi sakin ba, ai da yanzu babu wanda ya ji bare ya gani, na ja siririn tsaki na zauna gefen Fannata da ta tashi zaune tana jefa min kallon mamaki.
"Wai ba ki shirya ba?" Na faɗa ina jefa mata harara ƙasa ƙasa.
"Shirin me?"
Ƙasa na yi da murya a tausashe na ce "Gidan su Sufyan mana, ko kin manta abinda na ce miki jiya."
Ta ƙwashe da dariya, irin dariyar da su Maama su ka min jiya, dariyar da na rasa ta mecece, sannan ta kalle ni sheƙeƙe tana faɗin "Wai kina nufin biko zaki je Nafeesa? Yaushe kika yi wannan lalacewar?"
Kamar na ce mata, lalacewa ta wuce har yanzu ba ta yi aure ba, sai kuma na daure na haɗiyi ɓacin raina don ina buƙatar ta raka ni, na lashi busassun laɓana na ce "Komai zaki faɗa daidai ne, ni dai ta shi ki rakani, tunda lalacewar a kaina ta ke."
Ta watsa min harara "Wa? Wallahi babu gidan ubanda zan je."
Na yi rau rau da ido kalar tausayi, yayin da na lanƙwaahe murya na ce "Dan Allah ki dubi girman Allah ki zo ki rakani na bata haƙurin nan Fannata wallahi ba zan iya rayuwa babu Sufyan ba, shi kuma idan har ban je ba, ba zai maishe ni ba, dan Allah ki rufa min asiri Fannata, duk duniya bani da wanda zai min haka idan ba ke ba, ki taimaka min ki gyara min auren."
Kai tsaye ta ce "Allah ya sani ban rako mata duniya ba, ba zan iya wannan abin kunyar ba Nafeesa, kuma ni gaskiya ba zan dinga yawo da zawara ba ana kallona."
Na sani sarai rama wa ta yi, domin nima ai na sha faɗa mata kar ta sake zuwa gidana, Sweetie ya hanani mu'amula da irin su marasa aure, na lumshe idanuwa, na shanye don na tabbatar maganar ba har cikin zuciyar ta ta faɗa ba, don ina ganin yadda jikinta ya yi sanyi ta zuba min ido tana karantar yanayi na.
"Dan Allah Fannata..." Na fashe da kuka, wanda ya janyo hankalin Maama su ta shigo tana tambayar lafiya.
Kai tsaye na ce "Zuwa na yi ta rakani gidan su Sufyan na bawa Umman shi haƙuri akan abinda na mata, shine ta ce ba zata je ba."
"Sabida me?" Maama ta tambaya tana kallon su.
Caraf Fannata ta ce "Sabida sai ta bata haƙurin tukun zaa maida ta."
Na tari numfashin ta "Aa Maama ya maida ni, shi ya ce in je in bata haƙuri sabida ranta ya ɓaci akan rashin kunyar da na mata, dan Allah ki sa baki ta raka ni."
Maama ta kalli Fannata tana faɗin "Babu laifi ko abin kunya idan har ta je bawa macen da ta haifar mata miji haƙuri Fannata, sabida idan uwar ta ce bata buƙatar wani ma ya faɗa mata ta...
"Wallahi idan Maman su ce, ba zata iya bata haƙuri ba.. " Fannata ta Faɗa da sauri tana hararata.
"Ban tambaye ki ba, ta shi ki shirya ki rakata dan Allah, tunda har ya maida ta, dole ta bi umarnin shi.."
A take soyayyar Maman Fannata ta shiga raina, dan Allah kin ga uwa ta gari, ba irin ta wa ba mara fahimta, sai na ke jin ina ma mu yi musaya? Na lumshe ido ina binta da kallo, yayin da tunanin idan mun dawo na zo gare ta, ta nemawa Sufyan maganin asiri ya ɗarsu a raina, na san zata iya fiye da tunani na, na goge hawayen ƙaunar ta da ya ɗarsu a raina ina murmushi.
Sai da ta kira Baban Fannata ta sanar dashi, sannan ta ɗauki 10k ta bamu ta ce mu ƙara mu hau mota, ta min wa'azi sosai tukun mu ka tafi, Fannata na kumbure kumbure, yayin da na tattarata na watsar, ko dai tana so ko bata so dole a raka ni, kuma wallahi wannan ɗan wulaƙancin da ta min dole na rama shi...
Kafin mu shiga mota na sake gwada kiran wayar Sufyan, cikin hukuncin Allah ta shiga, har ta kusa katse wa aka ɗauka, sai dai sam ba muryar shi ba ce, wata zazzaƙar murya ce ta daki dodon kunnuwa na ana faɗin "Baya kusa, idan ya dawo ki sake kira..." Kittt aka kashe wayar.
Wani abu ya daki ƙirjina, yayin da raina yayi masifar ɓaci, na kalli Fannata na ce "Wata shegiya ce ta ɗauki wayar shi fa."
Ta taɓe baki ba tare da ta ce min komai ba, wanda hakan ya ƙara hasala ni, a take na kawo ma raina Wallahi Jamila ce, wato dan uwar ta har ta kai matsayin da zata ɗauki wayar mijina? Ai kam da sake...
Na sake kiran wayar raina a dagule, wannan karon shi ya ɗauka muryar shi mai kama da ta mai bacci ya kira sunana "Nafeesa."
"Wacece ta ɗauki wayar ka?" A faɗa a harzuƙe.
"Waya kuma? Ban sani ba."
Na san ba zai min ƙarya ba, ƙyila wani munafurcin ne aka haɗa, kafin na yi magana na tsinkaye shi yana faɗin "Naga message ɗin ki jiya, kin tafi?"
"Eh muna a mota."
"Ke da wa?" Ya tambaya babu yabo ba fallasa.
"Ni da Fannata zata raka ni."
"Oh, again Nafeesa, wai har yanzu baki fahimci bana son ƙwashe ƙwashe ba ne? Zuwa bawa Umman ma haƙuri sai ki min ƙwashe ƙwashe? Mai zai hana ki zauna gida sai ki tura Fannata ta bata haƙurin ita kaɗai mana kin ga idan da rabo sai a maida auren a kan ta.." Ya ƙarashe maganar a fusace.
Gabana ya faɗi damm, na kalli Fannata da har ta shige motar abin ta, sai na ji ma jiri na neman ɗibata, na dafe jikin motar da ƙyar ina faɗin "A'a, A'a, ni kam na shiga uku Sufyan.."
Ya yanke wayar shi ƙittt ba tare da ya jira mai zan ce ba, yayin da zufa ta wanke min fuska, na dafe kaina da sauri lokacin da na ji yayi masifar sarawa, kafin na ji wani irin Haushin Fannata ya lulluɓe ni ba ki ɗaya, shegiyar yarinya daga faɗin sunan ta, tana neman ruguje min damata, anya kuma ba ita ba ce baƙar ƙaddara a rayuwar aurena ba? Saboda duk lokacin da Sufyan ya ji ko sunan ta sai mun samu matsala, na runtse idona gam, ina jin lokaci ya yi da ya kamata na datse duk wata alaƙa da ita, tunda har Sufyan ya fara tunanin jefa ta rayuwar mu, na lashi laɓɓana ina jin wani irin tuƙuƙin bakin ciki na yawo a zuciyata, kafin na ɗago idona jajur na taka na shiga motar ina kallon ta..
#UWAR SUKUM....
💧💧 *KUSKUREN SO.*
FREE BOOK
*HASKE WRITER'S ASSO.*
*FEEDOHM*
Wattpad@Feedohm
_Ga ba ɗaya littafin nan sadaukarwa ne ga NAFEESA Muhammad SULE, maman jinjiri, Alherin Allah ya kai maki a duk inda kike._
_Ina kike Aunty Zainab Abubakar Kotorkoshi? Ke ma ina maki fatan alheri._
*033*
Na so na na yi ma Fannata magana a mutunce ta sauko ta kama gabanta bana buƙatar rakiyar ta, kamar yadda na je har gidan su na ɗauko ta, sai dai ina, yadda zuciyata ke azalzala da masifar kishin Sufyan ya sa ba zan iya hakan ba, don haka kai tsaye na janyo wuyan hijabin ta da ƙarfi, na yo waje da ita ina aika mata da fitinanne kallo mai ɗauke da tsana da ban taɓa yi mata ƙwatanƙwacin shi ba, ban san me yasa wallahi na kasa controlling kaina, ita kam tsabar mamaki ya hana ta buɗe baki ta min magana har sai da muka fito daga motar sannan na sake ta idona na fidda ƙwalla yayin da mutane ke bin mu da ido, ganin dai a tare muka zo.
Da ƙyar ta haɗiyi yawu ta buɗe baki tana tambayata "Lafiya Nafeesa?"
"Ina fa lafiya kina so ki zame mun baƙar ƙaddara a rayuwata Fannata?"
Ta fiddo ido a kiɗime tana kallo na, cikin dakushewar murya ta hau jera min tambayoyi "Bangane ba? Kan ki ɗaya kuma? Kin san me kike faɗa.?
Na ɗaga mata hannu dama tare da kawar da kaina gefe ina faɗin "Ai ba zaki gane ba, ki je kawai Fannata, bana buƙatar rakiyar ki."
"Sabida me Nafeesa." Ta faɗa muryar ta na rawa, domin a iya tunanin ta, tunda muka baro gida babu wata magana da ta haɗa mu, bare ta ce ko laifi ta min.
Sai da na share ƙwallan da ke bin kumatuna, na lashi laɓɓana na ce "Sabida ke ce baƙar ƙaddara ta, Fannata wallahi ko da na je dake baiwa Umma haƙuri aurena ba zai gyaru ba sai da ya lalace, baƙar ƙaddarar da ta hana ki aure ita ce ke son kashe min nawa auren, dan Allah ki je, na fahimci komai yanzu, bana buƙatar sake rayuwa da ke Fannata, bazan sake neman ki ba, nima kar ki sake neman a har abada dan Allah, da ni da ke ƙaddarar mu ba iri ɗaya ba ce, kin ƙi auruwa ba zan yadda ki lalata min aurena ba."
Mutane suka zuba mana ido suna kallon mu, kamar yadda itama idon ta ke kae a kaina, sun yi jawur sai dai babu ko digon ƙwalla a cikin su, sai ma wani murmushi mai ciwo da ke shinfide a fuskar ta.
Na sa hannu na tureta daga jikin motar sai ka ce ta ubana ina faɗin "Ki je dan Allah, kar ki lalata min aure a banza."
Ban yi zato ba sai na ji saukar maruka a fuskanta, ta buge hannuna da ke jikinta, cikin zafin rai ta ce "Na ɗauka bayan yanke alaƙa dani har taɓa ni ya haramta gare ki Nafeesa, shiyasa na mare ki bisa taɓa baƙar kaddara da kika yi, na yadda ni baƙar ƙaddara ce, kuma ita ta hanani aure, amma ni ba jahila bace, shashasha ballagaza irin ki, ni kawai baƙar ƙaddara ce, wacce Allah ke saukarwa bawa a duk lokacin da ya so, amma fa gareki kawai nake haka, kuma wallahi tallah Billahi na bar rayuwa da ke har abada Nafeesa, ba ke ba, hatta gidan ku ba zaki ƙara gani ba har abada, ki je KUSKUREN SON da kikai ya ishe ki darasi na har ki mutu..."
Na hau mata eho ina bugun laɓɓana, lokaci guda ina faɗin "Na ji, ki je Fannata, a haka sai zaki ƙare, tun farko ya kamata na gane baƙya sona, kuma insha Allahu bana tare da nadama har abada, mayya, wacce ta gagara auruwa.." Da har zan ciro 10k da Maman su ta bamu mu ƙara in watsa mata a fuska, sai kuma na ga ai ba da kuɗin na yi faɗa ba, da Fannata ne, don haka na sake matse kuɗina a jikkata na shige motar ina hawaye, yayin da jahila ciki da basa bincike suka hau goya min aya, suna tambayar me ya faru, bayan tare suka gan mu yanzu.
"Ƙawata ce, amma tunda na yi aure na ke samun matsala da mijina a duk lokacin da ya ji sunan ta." Na basu amsa lokacin da na ƙara rungume ledata da muka tsaya muka ma Umma tsaraba.
Wata ta cafke "Ai dama haka ƴan matan nan su ke, sun ƙi auruwa sannan su nemi fiddo na ciki, wallahi ki riƙe auren ki."
Yo har ma sai an faɗa min in riƙe aure? Bayan bana jin duk duniya aƙwai wanda ya kaini sanin darajar aure? Na lashi laɓɓana tare da ƙurawa wata mata da ke gefen hagguna ido lokacin da ta ke faɗin "Idan kika bibiya ƙyila ma mijin ki ta ke so."
Gabana ya faɗi rass na ce "Ke ma dai aniyar ki ta bi ki wallahi, ai tun ina amarya Sufyan ya min alƙawarin ni da kishiya har abada.."
Ban ƙara sauraren su ba, na kifa kaina a cinya na yi shiru ina jin suna ƙananan surutai akan ƴan mata da ke bibiyar mazan mutane, duk da dai bana zaton Fannata da hakan, amma har ga Allah sai na ji na ƙara tsanar ta.
*************
Da sallama na shiga cikin gidan su Sufyan, yayin da gabana ke dakan uku uku, don ban san me zan taras a gun Umma ba, babu kowa a tsakar gidan, don haka kai tsaye na yi hanyar falon Umma, yayin da na yi tozali da Jamila tsaye tsakiyar falon tana magana da Umman, tana gani na tayi ƙasa da murya tana faɗin "Umma ga anacen ki nan ta zo."
Ban wani ji haushi ba, dama na sa ma raina ko da buguna zasu yi wallahi ba zan ji komai ba, ni dai burina Sufyan ya maida ni gidan aurena, na yi bauta kamar kowacce ƴa mace, don haka na sakar ma Jamilar Murmushi ina ƙara sallama.
Na ɗaga ƙafa zan shiga ciki na ji Umma ta daka min tsawa tare da tsayar da ni tana faɗin "Kar ki sake ki shigo min falo wallahi, ni ai mara kunya bai isa ya shigo wajen ba dan uban shi."
A bakin ƙofar na zube ƙasa na fashe da kuka ina roƙon ta Dan girman Allah ki yi haƙuri ki yafe min na yi kuskure Umma, ki yi haƙuri na tuna, dan Allah ki yi haƙuri kar ki kore ni."
Jamila ta ce "Umma dan Allah ki barta ta shigo mana, baƙya ganin uwar hanyar da ta ƙwaso."
Ta girgiza kai "Aa Jamila, ta dai tashi ta shiga ɗakin ki ina zuwa, haka kurum na sani ko wani abin aka zo a zuba min, ni fa ban yadda da ita ba."
"Haka ne kuma, ga katsinawa da shegen asiri."
Cikin kuka na ce "A'a allahi ban zo da komi ba sai alheri, dan Allah ki gafarta min Umma sharrin shaiɗan ne." Wallahi ni fa kaina ban san abinda na mata ba, kawai dai na ɗauki laifin da ban san da shi bane.
Ta min banza, yayin da Jamila ta ce "Ki tashi ki shiga ɗakina ta na zuwa."
"Dan Allah ki taya ni bata haƙuri Jamila, wallahi na tuba na bi Allah na bita, hakan ba zai sake faruwa ba."
Jamila ta yatsina fuska tana faɗin "To, amma dai gaskiya ni kaina ba zan goyi bayan ki shigo mata ɗaki ba, don ban san da ke kika zo ba."
Na ware hannuna na ce "Wallahi banzo da komai ba Jamila."
"Babu fa tabbas.."
Na yi shiru ina kuka tare da kallon Umman a raunane, amma sai na ga ta kawar da kai tana girgiza ƙafa, na cigaba da roƙon ta, roƙon da ko uwar da na haifa ban taɓa yi ma irin shi, sai da ta mula ta mulmule sannan ta ce "Shigo, amma a kula duk wacce ta raini mijin ƙwana 1000 shi na farko da ta fi ƙarfi a yi sa'in sa da ita."
Na hau gyaɗa kai "Wallahi sharrin shaiɗan ne, insha Allahu hakan ba zata sake faruwa ba."
"Ah to a dai kula."
Na miƙe da leda ta na shiga cikin falon yayin da na durƙusa gaban ta na cigaba da neman gafararta, har sai da ta ce "Ya wuce a dai kula."
Sannan na ɗan ɗosana ɗuwawuna na zauna kaina a ƙasa kamar zan kifa, kusan minti lalatin babu wanda ya ƙara kula ni a cikin su, sai firar su da suke da jefi jefi suna dariya, babu wanda ya yi tunanin kawo min ruwa bare abinci ga wata uwar yunwa da ake azalzalata, don wallahi har ƙoƙon cikina ke wani yamutsawa.
A sanyaye na zaro wayata, na turawa Sufyan ɗan gajeran Message _Umma ta yafe min!_
Saƙon na shiga na ji wayar Umma na ringing, ta kalle ni ƙasa ƙasa sannan ta ɗauki wayar a saka a hands free tana faɗin "Sufyanu."
"Naam Umma, ina wuni?"
"Lafiya lau Alhamdulillahi."
"Wai Nafeesa ta zo.?
Ta kalle ni sannan ta ce "Au har ta faɗa maka sabida shegen surutun su na gado?"
"Eh Umma."
Ta yatsina fuska "To ai shikenan, ka maida ta, amma fa da sharaɗi idan ta yadda."
#UWAR SUKUM.
[6/5, 8:52 PM] RN Feedohm: 💧💧 *KUSKUREN SO.*
FREE BOOK
*HASKE WRITER'S ASSO.*
*FEEDOHM*
Wattpad@Feedohm
_Ga ba ɗaya littafin nan sadaukarwa ne ga NAFEESA Muhammad SULE, maman jinjiri, Alherin Allah ya kai maki a duk inda kike._
_Ina kike Aunty Zainab Abubakar Kotorkoshi? Ke ma ina maki fatan alheri._
*034*
Kai tsaye ya ce "Ku yi magana da ita Umma ai na san zata yadda da ko menene."
Gabana ya yi masifar faɗuwa, na zuba mata yayin da zuciyata ke rawar mazari, sai na ji na ƙosa ta yanke wayar ta faɗa min kowanne irin sharaɗi ne wannan da har sai na amince dashi tukun zata yadda Sufyan ya maishe ni, a take na shirya karɓar shi muddun zan gyara aure na, amma fa ba da sharaɗin maido Asiya, don