Showing 69001 words to 72000 words out of 83936 words

Chapter 24 - KUSKUREN SO Book Complete by Feedohm.txt

Feedoms   

21 Sep 2025

1701

adadin suka ɗarsu a zuciya ta, ba fice zuciyata na tuƙuƙi na samu napep na hau, maimakon na wuce gidan Sufyan sai na ji ina buƙatar zuwa gidan mu, ina buƙatar na ga Maama, domin wofitar da ni da suka yi ba ƙaramin tasiri ya yi a zuciya ta ba.

A lokacin da na shiga gidan a tsakar gida na iske Maman bisa tabarma ta zabga uban tagumi ita kaɗai, tana jin sallama ta ta ɗago a firgice, sai kuma na ga ta waske kamar irin bata damu ba, na saki murmushin takaici domin ba zata iya ɓoye ƙaunar da take min ba, ba zata iya ɓoye wannan tausayin ba, sai na ji wani irin tausayin ta da ƙaunar ta ya ɗarsu.... Na lumshe idona, a lokacin da na tuno ni ba zan samu ɗiyan da zan nunawa haka ba, ba zan samu ƴaƴan da zasu tausaya min su ƙaunace ni kamar yadda na ke ji game da Maama ta, wallahi na ɗauka abin sauƙi ne dashi, na ɗauka bayan cire mahaifar zan mance da komai na cigaba da holewa da Sufyan, amma sai na ga kamar ba haka ba, sai na ga tankar wani sashe na zuciyata ya so ya zautu akan soyayyar ƴaƴa, sai na ga tamkar wannan sashen na so ya fifita soyayya ƴaƴa fiye da soyayyar Sufyan...

Na zubar da takarcena gefe ɗaya, yayin da na ƙarasa kusa da ita na zauna na ɗaura kaina bisa cinyoyinta na rushe da wani azabbaben kuka ina girgiza kai.

Duk yadda ta kai ga daurewa wallahi kasawa ta yi, ta ɗaura hannun ta saman kaina tana tambayar "Me ya faru? Me ya same ki Nafeesa?"

"Ki yi haƙuri Maama, ki yafe min dan Allah, ki yafe min Maama."

Muryarta na rawa ta ce "Kina bani haƙuri ne sabida ban je jinyar ki ba?"

Na girgiza kai "Aa, ina baki haƙuri a matsayin ki na uwa, bisa tarin laifukan da na miki, dan Allah ki yafe min, ni ba zan ga ɗiyan da zasu bani haƙuri ba Maama..."

A firgice ta ɗago kaina tana tambayar "Me kike faɗa Nafeesa."

"Ba zan haihu ba Maama?" Na faɗa kai tsaye.

"Wa ya faɗa miki haka?"

Na runtse idona gam ina jin ba zan iya faɗa mata sabida ina son na zauna da Sufyan na zaɓi na zauna babu ƴaƴa ba, ina tsoron na faɗa mata sabida ina son Sufyan na zaɓi na rasa soyayyar uwa da ƴaƴa, wallahi abin ba mai sauƙi ba ne, ba kuma zaka gane ba, sai a lokacin da ka rasa damar haka..

Tsinkayar na yi tana faɗin "Ƴaƴa rahama ne Nafeesa, kar ki yadda soyayyar da kike ma mijin ki ta hana ki soyayyar uwa da ƴa...

To ina saura ma? A hankali na ce "Ina son shi Maama."

Ta girgiza kai "Ki cigaba da son shi Nafeesa, Allah yayi maku zaɓi na alheri."

Na maida kaina a bisa cinyar ta, ina cigaba da neman gafarar ta, ban kuma daina ba har sai da na tabbatar da ta yafe min, kuma har ga Allah da zuciya ɗaya na nemi yafiyar ta, ina jin har abada ba zan kuma aikata mata abin da nayi ba, ba zan haihu ba, ita kaɗai ce gare ni..

Anan gidan na ƙarashe wuni na cikin tarairaiya da gata, don har ƙyaƙyƙyawan wanka na samu daga gare ta, ta gashe min jikina, ta dama min kunun kanwa, da tuwona na dawa mai rai da lafiya wanda ya ji man shanu, ai kam tunda na ci na ƙoshi na haye gadon ta sai ga bacci.

Sai gab da magrib ta ce in tashi in koma gidana, a karo na farko da na ji nan gidan ya fiye min can sau dubu, a karo na farko da na ji ina buƙatar zama da ita fiye da Sufyan, na lumshe ido, a lokacin da na tuna irin azabar da na sha lokacin da wannan ɗan tayin ya fito, na kalle ta, ni mai ɗan tayi na ji hakw, to ina ga ita da lafiyyayen mutun ya fito daga ƙasanta, sai na ji ina buƙatar na ji yadda ta ji, sai na ji ina ma zan maida hannun agogo baya.

"Sai da safe zan gobe." Na furta zuciyata na ƙuna, ni kaina mamakin kaina na ke, yadda na ji wannan canjin lokaci guda.

"Shi yace ki ƙwana anan?"

Na girgiza kai alamun A'a, sai na ga kamo hannuna tana faɗin "To ki kira shi ki tambaye shi idan ya amince ki ƙwana."

Babu musu na ɗauko wayata ba kirashi, cikin rashin saaa wayar shi a kashe, don haka ta tilasta min in koma gidan, idan da matsala in kira ta.

A tausashe na ce "Zaki zo?"

Ta girgiza kai "Ba zan zo gidan ki Nafeesa, ba kuma zan tura Fatima ba."

Ban ce komai ba sai hawaye da suka ɓalle min, sai ta yi kamar bata gani ba, ta aika Auta ya taro min napep da ya ke Teemah bata nan, sannan ta raka ni har ƙofar gida bayan ta cika min ƙwano da tuwo.

*********************

Haka na ƙwana gidan ni kaɗai kamar mayya, washe gari tunda safe wajen 6:30am sai ga kiran Sufyan, wani ɗan sanyi ya ratsa ni, na tabbatar da ni ya ƙwana a ran shi wallahi, shiyasa ya kasa haƙurin gari ya ƙarasa wayewa, yayin da gudan ɓangare na zuciyata ya ƙaryata hakan, sai ma ƙoƙarin cusa min haushin shi ya ke, da ƙyar na daƙilar da shi.

"Ya ƙarfin jikin na ki?" Ya tambaya bayan mun gama gaisa wa.

"Da sauƙi alhamdulillahi." Na furta kamar bana so.

"Masha Allah, ya ƙwanan kaɗaici.?"

Na yatsuna fuska ina shafa inda ya ke ƙwanciya, a tausashe na ce "Ba daɗi." Don wallahi duk yadda ɗayan sashen na zuciyata ke neman na ji haushin shi ba zan iya ba, muddun ina jin zazzaƙar muryar shi.

"Why? Bayan ko ina nan babu abinda zaki min."

A sanyaye na ce "Me yasa?"

"Sabida kina buƙatar hutun 40days." Ya furta kamar mai raɗa.

Na waro idona waje "Why? Ni da ba haihuwa na yi ba?"

"To me kika yi? Ko kin manta har an gama halittar babyn mu? Premature birth ne ba miscarriage ba."

"Uhmm, shine kuma zaa bani hutun 40days?"

Ya saki murmushi mai sauti ya ce "Yeah, ko ma 60days ba."

"Kuma zaka iya?"

"Me zai hana?"

A sanyaye na ce "Ba zaka yi missing ɗina ba?"

"Indai zaki samu cikakkar lafiya me zai hana Nafeesa? Sabida ke zan yi."

Ɗan murmushi na yi na canza maganar ta hanyar tambayar shi "a
Amma da safe zaka taho ko?"

"Me kika tanadar min?" Ya furta kamar mai raɗa.

Ɗan murmushi na saki kamar ba shine ke faɗin hutu 60days ba, amma har ya fara tambayar me na tanadar mashi, dama na tabbatar ba zai iya ba, a tausashe na ce "Me kake so.?

Ya ƙara ƙwantar da murya, cikin sigar lallashi ya ce "Za ki iya girki Nafeesata?"



_A RANAKUNAN GOMA NA ZHULHAJJ Masu Zuwa, insha Allahu zamu kai sadaƙan ruwa asibiti, sabida su ma ƙwanaki ne masu dimbin daraja gare mu, da yawa ba zamu ƙara samun su ba, dan Allah ga wanda zai taimaka da ruwan ya tuntuɓi wannan lambar for location 08036953516, ga kuma wanda zai taimaka da kuɗin ko leda ɗaya 3126584401 first bank fiddausi musa sadaƙan ruwa falala ne da ita, mu yi da ƙyaƙyƙyawan zuciya._





#UWAR SUKUM

[6/18, 11:30 AM] RN Feedohm: 💧💧 *KUSKUREN SO.*

FREE BOOK

*HASKE WRITER'S ASSO.*

   *FEEDOHM*
Wattpad@Feedohm

  _Ga ba ɗaya littafin nan sadaukarwa ne ga NAFEESA Muhammad SULE, maman jinjiri, Alherin Allah ya kai maki a duk inda kike._

_Ina kike Aunty Zainab Abubakar Kotorkoshi? Ke ma ina maki fatan alheri._



*041*



Wallahi na ɗauka ni zai ce yana buƙata kamar ko da yaushe, amma sai na ji akasin haka, na lumshe ido ina tambayar "Me kake so a girka maka."

Kai tsaye ya ce "Awara please da fried rice."

Cike da mamaki na waro ido waje ina faɗin "Awara fa Sweetie?"

"Yes, ba aƙwai ina ake tupo ba can ƙasan mu? Sannan kuma aƙwai wanken soya a store, ki bayar a miki please Nafeesata, sai ki soya mana ita da ƙwai dan Allah, zan aiko a kawo miki cucumber da cabbage, dan Allah ki daka mana yaji mai tafarnuwa irin wanda bai dake ba."

Mamaki ya kamani, wannan salon kuma daga ina? Hala can ya je ya iske ana ci shine zai narka min aiki anan, a raunane na kira sunan shi "Sufyan."

Ya katse ni cikin sigar lallashi ya ce "Please, ba zaki iya ma mijin ki abinda ya ke so ba?"

Na yi shiru ina tunanin ta inda zan fara dukka wannan abun, ya hau min magiya "Dan Allah Nafeesata.."

Bisa tilas na amsa da "To."

"Za ki yi.?"

Na ce "Uhmmm."

Cikin farin ciki ya ce "Yauwa, Allah ya miki albarka kin ji ko? Then dan Allah ki gyara wannan bedroom ɗin na kusa da na ki, zaki ga aƙwai furnitures da na zuba lokacin da baƙya nan, ki kakkaɓe ki yi mopping, sannan aƙwai bedsheet a saman bed ɗin ki shinfiɗa kin ji ko Nafeesats, na san zaki iya."

"Yaushe ka ga keys ɗin? Kuma wannan abin duk sabida me Sufyan?"Idan ban manta ba tun dawowa ya ce min ya neme keys ɗin wajen ya rasa.

Cikin rawar murya ya ce "Shekara jiya da kina asibiti na gano su, dan Allah ki yi kin ji ko, zan taho da baƙi."

Ai ko bai faɗa min ba, na sani sarai Umman shi ce, wannan matar bata son zaman lafiya wallahi, wato bata kirani ta gaishe ni ba, sannan zata zo ta ɗaura mun wahala, wallahi da ina da hali da na ce kar ya ƙwaso min ita.

"Ki yi kin ji ko? Dan Allah, ko da matsala?"

"Babu.." Na faɗa rai na a dagule

"Ok, sai na dawo, me zan taho miki da shi."

"Babu." Na yanke wayata, na koma na ɗaura kaina bisa filo ina jin wani irin ɗaci a maƙoshina da bacin rai, ta fa san banda lafiya amma shine zata ɗaura min wahala, ina ma laifin idan ta zo ta gyara da kan ta? Gabana ya faɗi da na tuna wai ya zuba furnitures kenan zama zata yi da mu? Ai kam da na shiga uku, don ba zata taɓa bari mu zauna lafiya ba, na lashi laɓɓana zuciyata na ƙuna.

Kusan minti talatin sannan tashi zaune, wallahi ban ma san ta inda zan fara ba, ga dai ciwon jiki, ga kuma uban aikin da ya tila min, ko da yake ba laifin shi bane, suka tila min dai, kuma muddun ina son farin ciki ban isa in ce ba zan yi ba..

Na miƙe na cire kayana, na shige toilet na iske ruwan zafin da na kai tun asuba ya sha iska don haka na shiga ciki na zauna ina tunanin yadda zan fara wannan uban aikin, yau da ace ban ɓata rawata da tsalle ba, da Teemah na kira ta ta taya ni, sannan ko irin maƙwabtan nan babu wanda nake kirki bare su taimaka min da yaran su, na runtse idona gam da na tuna a haka ba zan ƙare, ni kaɗai babu ƴaƴan da zasu taimaka min, sai na ji hawaye sun ɓalle min, na sani ko da Sufyan ya maido Asiya ta haihu, ya amshe su ya bani, su na nan dai a matsayin ƴaƴan ta, ban isa na canza wannan ba, kuma ƙarshe na gama wahalar da su su koma ga uwar su, wannan shine KUSKUREN SO....

Sai da ruwan zafin ya ratsa ni kamar yadda Maama ta min bayani, sannan na miƙe na yi wanka ma na fita na zunbula riga bubu, na ɗebi waken suyan, na fita da ƙyar na shiga maƙwabta na roƙi alfarmar yar su ta miƙa min aikatau ɗin, sam barka matar ta ce ta iya zata min, na yi godiya na bata na dawo gida.

Kai tsaye ɗakin na shiga zan gyara, mamaki ya kusa kashe ni wallahi, komai fa an zuba sabo, kuma masu tsadar gaske, sai ka ce zaa kawo amarya, sai na ji zufa na bin gefen fuskata, na sa gefen kallabin da ke kaina na share, ina cizon leɓena na ƙasa, Matar nan bata so na wallahi, tunda har ta ke niyyar dawo min gida, so ta ke sai ta raba ni da Sufyan tukun ta kawo mashi Asiya, amma kuma ai na tsayar da haihuwar, bai kamata ta mun haka ba, ban yi zato ba sai jin ƙwalla na yi sun cika min ido, idan har ta raba ni da Sufyan sun cuce ni, wallahi da tun baya ya mun bayanin uwar shi zata dawo da ban yadda aka cire mun mahaifa ba, haka na daure na kakkaɓe bedroom ɗin ina tunanin hanyar da zan ɗauki mataki ba tare da aurena ya gantale ba.


Kafin 1pm na gama komai, amma fa na wahala, kun san dai har lokacin jikina bai komai dai dai ba, don yajin ma sai dai na ƙara shiga maƙwabtan na bayar aka daka min, sabida neman suna ma har da coconut drink na haɗa masu, sannan na gyara gidana tsab na sa turaren wuta, na shiga ciki na yi wanka na kintsa cikin riga da siket na atampha, sai na fito ras da ni, dama abin ka ga ƙyaƙyƙyawa.

Wajen 2pm na komo falo na kunna kallo na ƙwanta bisa doguwar kujera, sai a lokacin ne na ji cikina ya fara ciwo sosai, bi ma'ana jijjigar da na yi zata fara tambaya ta, ina nan ƙwance na ji ƙarar buɗe gate, sai na ji gabana ya faɗi, yayin da na kasa tashi na je na tarbe su, na zubawa ƙofar shigowa ido ko ƙyaftawa bana yi har suka turo suka shigo, tsananin ciwon cikin da ke addaba ta bai hanani tashi zaune ba ina kallon su, yayin da na sa hannu biyu biyu ina murje idanun don sake tabbatar da abinda na gani, kamar dai Asiya na ke gani, kamar kuma gizo idona ke min, idan ita ce me ya kawo ta?

Domin dai na sake gasgata abinda na gani, cikin rawar murya na tambaye shi "Wacece wannan Sufyan?"

Ya ɗan juya ya kalle ta da murmushi a fuskar su, sannan ya waigo gare ni "Baki gane ta ba?"

Wannan karon a tsawance na sake tambayar shi "Wacece?"

Cikin halin ko in kula ya ce "Asiya ce mana, maman su Airah."

Sai na ji kaina ya juya gaba ɗaya, na dafe shi da hannu biyu biyu tare da runtse idona gam, kafin na dawo dai dai na ji yana ce mata "Ki shiga ki ciki mana ki huta ina zuwa."

Na buɗe idona da sauri ina kallon inda zata shiga, shin ɗakina koko ɗakin da yasa na gyarawa su Umma, mamaki ya ishe ni, lokacin da na ga ta saka hannu cikin jikkar ta ta fiddo Key ɗin bedroom da tun da na dawo Sufyan ya hanani shiga, hasalima ce min yayi key ɗin ya ɓace sai yau da yace ya gano na shiga ba gyara, to wannan na hannun ta ina ya same shi? Dukkan su fa ya ce sun ɓace, na maida kallona ga bisa tv stand na aje wanda na buɗe na gyara, yana nan dai inda ya ke, wani ne gurin ta, ai ban san lokacin da na yi tsalle na dira gabanta ina faɗin "Ba zaki shiga ba wallahi."

Ya tamke fuska yana tambayar "Sabida me.?

Na jefa mashi muguwar harara ina faɗin "Sabida bazan yadda ka kawo min ita ba, ta yi haƙuri har sai an maida auren."

Sai na ga ta saki murmushi tare da girgiza kai tana ƙoƙari gifta ni, tun a baya na fahimci shu'uma ce wannan matar wallahi, na janyo mata gyale baya ina faɗin "Are you not ashame of your self? Baƙya jin komai kin ƙwaso ƙafa kin biyo mutun har gidan shi kamar karuwa?"

"Karuwa?" Ta maimaita tana kallona.

Na gyaɗa kai "Eh menene Banbancin ku to, tunda babu aure a tsakanin ku, Kin wani ƙwaso jiki kin biyo shi gidan shi na aure, wannan halin karuwai ne."

Sufyan ya daka mun tsawa ranshi a ɓace yana faɗin "Bana son hauka banza Nafeesa, me yasa baƙya tashi rashin hankalin ki sai ina tsaka da farin cikina?"

Na kalle shi da sauri ina tambayar "Hauka? Ni? Akan wannan ƴar iskar kake kiran matar ka mahaukaciya?" Na Nuna ta da yatsa.

Ta taɓe baki, lokacin da ta kai hannu saman hancin ta tana faɗin "Da Allah zaki iya matsawa, wallahi bana son warin turaren ki, Sufyan ka ma matar ka magana ba zan iya da wannan akuyancin ba." Ai kafin ma na bata amsa har ta soma sheƙa amai a jikina.

Sufyan ya riƙe mata kafaɗa yana jera mata sannu, ni kam kamar icce haka na yi tsaye hannayen mijina bisa kafaɗar Asiya, sai na ji kaina na juyawa, ƙwalwa ta na yamutsa wa, na kasa hasaso abinda ke shirin faruwa da ni..

"Suf, dan Allah matar ka ta matsa, bana son warin turaren ta." Na Tsinkaye tana sake maimaitawa a karo na biyu, kuma a daidai lokacin Sufyan ɗin ya sa gefen rigar shi yana goge mata gefen bakin ta.

Ya kuwa juyo ya dama min tsawa yana faɗin "Baƙya ji ne me ta faɗa? Me yasa baƙya son ƙwanciyar hankali? Daga dawowata Nafeesa? Haka ake tarbar miji? Tarbiyyar da aka baki kenan? Da Allah ki matsa tunda dai ta ce bata son warin turaren da ke jikin ki, and daga yau kar ki kuma sashi a nan gidan ki fito falo. "

A lokacin komai ya ƙwance min, sai ido da nike bin su dashi, yayin da zuciyata ke min zafi tamkar ana dahuwar ganda a cikin ta, wai ƴan hawayen ma sun tsaya cak, banda idona bana jin aƙwai abu mai amfani a tattare da ni.

"Maganar karuwa kuma, kina zaton mijin ki ɗan iskane da zai kawo karuwa a gida Nafeesa? To ki bata haƙuri Mata ta ce.." Na Tsinkaye shi yana faɗa cikin kakkausar murya.

Sai na ga ta saki murmushi ta ce "Ba buƙatar haƙurin ta Suf, ta je kawai.."

Sai na ji kafata tana neman gagarar ɗaukarta, idan na fahimta dai dai, watsar da ni da yayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login