Showing 36001 words to 39000 words out of 83936 words

Chapter 13 - KUSKUREN SO Book Complete by Feedohm.txt

Feedoms   

21 Sep 2025

1703

kika yi yaji kika taho, sai ki jira Baban ki ya dawo ya ji dalili, sakarar banza shashasha, wato ya kiraki ya narka miki ƙarya shine har kin yadda."

Na kalle ta raina a ɓace na ce "Ba zai min ƙarya ba Maama, ni kam dan Allah ki barni in tafi."

"Wallahi idan kika fita sai na sheme ki dan uban ki."

Auta da shigowar shi kenan ya ce "Mamaa in rufe miki ƙofar?"

Na bita da kallon Mamaki ban taɓa ganin wannan ƙarfin halin ba sai yau, cike da ƙosawa na ce "Maama ina ce yajin nan ni nayi shi, kuma babu wanda ya sani, to na fasa.."

Ta yi watsi da ni, yayin da Teema ta ce "In miƙo miki muciya ko taɓarya?"

Na fashe da kukan takaici, tare da watsa ma Teemah harara ina faɗin "Uban taɓarya zaki miƙo, ni fa banzo dan ku kashe min aure ba, zuwa na yi ku ɗan ja mishi kunne, kuma na fasa na yafe mishi, don me zaa hanani tafiya gidana Mamaa?" Wallahi gaba ɗaya hankalina ya koma ga Sufyan, yayin da jikina ke rawa, ina jin shigowar kiran shi gabana na daɗa faɗuwa.......



UWAR SUKUM.
[5/17, 8:21 PM] RN Feedohm: 💧💧 *KUSKUREN SO.*

FREE BOOK

*HASKE WRITER'S ASSO.*

   *FEEDOHM*
Wattpad@Feedohm



  _Ga ba ɗaya littafin nan sadaukarwa ne ga NAFEESA Muhammad SULE, maman jinjiri, Alherin Allah ya kai maki a duk inda kike._

_Ina kike Aunty Zainab Abubakar Kotorkoshi? Ke ma ina maki fatan alheri._


*023*


Da ƙyar na daidaita numfashina tare da ɗaure fuska na juyar da kai gefe ɗaya, sai na ji duk wani tsoro da fargabar bashi ya tafi, don wallahi yadda nake jina babu dalilin da zai sa na zubar da wannan ciki, bayan ina jin yadda uwar shi ke magana akan rashin haihuwata, bayan ni ba juya ba ce.

"Da wa kike waya?" Ya faɗa a tsawance.

Kai tsaye na ce "Fannata."

Cikin ɓacin rai ya ce "Wai ke wace irin daƙiƙiya ce da komai sai kin ƙwashe kin faɗawa ƙawar ki.?"

Na ɗago na kalle shi da kalmar "Daƙiƙiya." A bakina, wannan ne karo na uku da ya zage ni a rayuwata, idona ya cika da ƙwallah.

Shima daƙiƙiyar ya maimaita yana kallona sai dai yanayin shi ya canza daga ɓacin rai zuwa walwala, sannan ya ɗaura da "Me ya kawo daƙiƙiya kuma a maganar mu Nafeesa?"

Cike da zallar mamaki na ce "Ai kai zan tambaya Sufyan, tunda a bakin ka na ji ta."

Ya waro ido waje yana faɗin "Dan Allah rufa min asiri yaushe na ce haka? Kar ki juya min magana."

Da ido na bishi cike da mamaki na kasa ce mashi komai, idan har kunnena lafiya lau ya ke kuma ina cikin hankalina to wallahi ya kirani da daƙiƙiya yanzu, ya katse ni ta hanyar faɗin "Ina tambayar ki kin min shiru, wace irin daɓeɓiya ce da komai sai kin ƙwashe kin faɗi ma ƙawa Sweetie? Haka ake fisabilillahi, ke baki san aure sirri bane? Ko da ya ke an ci kuɗina an ƙoshi an koma daɓeɓiyar, babu sirri." Ya dungure min kai.

Na saki murmushin yaƙe, yayin da wani sashe na zuciyata ya sanar min, kawai ya waske ne don ya san komai zai iya faruwa, yayin da gudan sakaren sashen ya tabbatar min da tun farko ban ji da ƙyau ba, kafin na ce wani abu ya zauna a gabana ya ɗaura hannun shi a saman cinyata da wani ƙaramin ƙwali na magani yana faɗin "Duk mu bar wannan maganar, ni yanzu ma na bar jin haushi tunda na fahimci bakin da Allah ya ɓarka baa isa a hana shi surutu ba."

"Hmmm." Kawai na faɗa ina kallon shi.

"Tashi ki sha wannan maganin duka huɗun, bara na sanya handglove na yi maki inserting biyu." Ya saƙa hannu ta cikin siket ɗina ya shafi pant ɗina tare da ƙanne min ido yana faɗin "Ko mu yi banƙwana tukun?"

Na ɗauka kaina gabana na faɗuwa, na ƙi karɓar maganin bare har na yi niyyar shan shi, ganin banda niyyar hakan ya sa ya kuma ƙwantar da murya "Please tashi mana, ayi a gama, bana so sai dare yayi wata matsalar ta ɓullu."

Na watsa mishi harara ina faɗin "Akan me zan sha?"

Ya kama hannuna yana murzawa ya ce "Ya fita mana Nafeesa, ba zaki gane wahala na masu sikila sai kin haife su."

A fusace na ce "Mun haifa dai, Sufyan ka san da haka tun farko ka yadda muka yi aure? Ko ka mance alƙawarin da muka ma juna, na zamu zauna a haka sannan mu kula da abinda zamu haifa duk wuya duk runtsi, sai yanzu kake so ka canza min magana? Bayan kai kana da ɗiyan ka?"

Ya murmusa yana faɗin "Ban manta ba Nafeesa, ina nema mana mafita ne, wallahi idan har kika yadda aka zubar da cikin nan, na miki alƙawarin da ke kaɗai zan zauna har abada ba zan taɓa maido Asiya ba bare na auri wata, idan kuma har kika dage sai kin haihu Nafeesa ba zan yadda na zauna wahala ta kashe ni ba, don ba zan taɓa samun farin ciki a tattare da ke ba, kullun zarya asibiti da wahalhalu zasu ɗauke miki hankali, dole na nemarwa kaina mafita.."

Na zuba mishi ido zuciyata na min saƙe saƙe, yayin da wutar kishi da soyayyar Sufyan ke ruruwa lokaci guda, duk da ina son na haifi nawa yaran amma ina son zama da Sufyan har abada ba tare da wata ta shiga tsakanin mu ba, na lumshe ido ina jin ina buƙatar tabbacin haka domin ba zan yadda wannan tayin ya wuce ni ba.

Kamar ya san me nake tunani, ya saki hannuna ya miƙe tsaye, ya ɗauko ƙur'ani cikakke yana faɗin "Idan na rantse miki da alƙur'ani zaki yadda da magana ta?"

Da sauri na miƙe na amshe ƙur'anin na aje gefe ɗaya, na kalli cikin idon shi na ce "Idan ka karya alƙawari fa?"

"Wallahi, tallahi ba zan taɓa ƙaryawa ba, ina son ki Nafeesa wannan ya ishe mu zaman duniya, idan ƴa ƴa kike so wallahi zan karɓo miki na Asiya, na maishe su na ki halak malak, Nafeesa ina tausayawa ɗiyan da zamu haifa, da kuma rayuwar da zasu kasance a gaba, dan Allah ki fahimce ni.."

Na lumshe ido na koma na zauna, yayin da ya saƙa min maganin a hannu yana faɗin "Ki yadda da ni, ba zan taɓa sauya miki magana ba muddun kika aikata abinda nike so."

Na jijjiga kai tare da damƙe maganin a hannu na, ya tallabo kumatuna da hannayen shi biyu yana tambaya ta "Zaki sha?"

Na gyaɗa kai jikina a sanyaye, yayin da na sa ɗayan hannun nawa na shafi marata, har ga Allah ina son na haifi wanda zai min addu'a ko yaya ne, sannan ina so na zauna da Sufyan ni kaɗai, kuma dole na zaɓi ɗaya..

Ya sa hannu ya ɗauke hawayen tare da sumbatar goshina ya miƙe yana faɗin "Bara in ɗauko handglove ɗin sai na sa miki na vagina ɗin, insha Allahu within hours zai fita, kuma aƙwai drip da magani da nurse zai zo ya sa miki, wanda zai taimaka yayi flushing cikin da sauri, am here with you, ba zaki ji ciwo irin wancen ba, zan baki extra care + love. " Ya ƙanne min ido ɗaya.

Har ya juya ya kuma juyowa yana faɗin "Ba fa da ruwa zaki sha ba, ƙasan tongue ɗinki zaki sa yana narkewa a hankali kina haɗiyar saliva ɗin."

Na bishi da kallo ya fice daga ɗakin, sannan na bi maganin da kallo hawaye tab da ido na, wallahi sai na ji kasa shan shi gabana na faɗuwa fiye da zatona, ina nan zaune har kusan 30minutes bai shigo ba, jin shirun yayi yawa ya sa na cire maganin cikin ƙwalin na ɓalle shi, wannan na jefa ƙwayar bayan gado, na miƙe jikina babu ƙwari na nufi ɗayan bedroom ɗinmu, inda na iske shi ya haɗe kai da guiwa yana maimaita "Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un, Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un."

Na ƙarasa cikin azama ina tambayar "Lafiya? Me ke faruwa?"

Na kalli wayar shi da ke gefe da alamu waya ya gama, jin yayi shiru bai ce mun komai ba, ya sa na kai hannu na ɗauki wayar ina bin calls ɗin, sai na ga da Umma ya gama wayar, don haka na kira ta, ringing ɗaya ta ɗauka, kafin na ce wani abu na ji tana faɗin "Ya zamuyi Sufyan, Allah da ya bamu su ya fi mu san su, yanzu haka gamu nan zaa bamu gawar mu taho da ita gida, dan Allah ka taho ayi jana'izar da kai."

Jikina ya ɗauki rawa, ina tambayar "Waye ya rasu Umma?"

"Ina Sufyan ɗin?" Ta faɗa a daƙile

"Dan Allah Umma waye ya rasu?" Na kuma tambaya a ruɗe, don wallahi halin da ya ke ciki ba ƙaramin tada min hankali ya yi ba.

Ta daka min tsawa "Ke bani son iya yin banza, yana ina ne?"

Da ya ke anan jin maganar ta, sai ya karɓe wayar shi, na bishi da kallo cikin tashin hankali ganin hawaye na bin idanun shi, kuma hawaye ba irin wanda ya saba mun ba, nima sai na ji hawayen, a dakushe ya ce mata "Gani nan Umma, insha Allahu yanzu zamu taho."

Ta sassauta murya "Allah ya kawo ku lafiya, dan Allah ka ƙwantar da hankalin ka, Allah da ya baka shine ya amshe."

Bai ce mata komai ba ya aje wayar, ya dafe kan shi da hannu biyu yana maimaita "Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un."

Muryata na rawa na ce "Dan Allah waya rasu Sufyan, ka faɗin mun."

"Su Airah ne suka yi accident Nafeesa..." Abinda ya faɗa kenan ya fashe da kuka.

Jikina ya ɗauki rawa, nima na cigaba da maimaita "Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un ɗin." Bala'in tausayin shi ya kamani, da ƙyar na yi Jarumtar dafa kafaɗar shi na ce "Airah kaɗaice ta rasu a cikin ku?"

Ya girgiza kai "Su duka ukun, sun je gun mahaifiyar su ne, hanyar dawowa tirela ta take su...."

Na lumshe idona na yi shiru kamar wacce ruwa ya ɗauke, jikina na rawa, ya kalle ni cikin tashin hankali ya ce "Tashi ki shirya mu tafi."

Jiki babu ƙwari na miƙe, na sauko jikka na saka mana kayan mu kala uku uku da abubuwan buƙata, sannan muka kulle gidan muka ɗau hanya..

A hanya na kira Maama, ringing ɗaya ta ɗauka, ko gaisawa bamu yi ba na fashe da kuka ina faɗin  "Maama rasuwa aka mana."

Cikin tashin hankali ta ce "Waya rasu Nafeesa.? '

"Su Airah suka yi accident su uku duka sun rasu har da driver, gashi muma zamu tafi yanzu."

"Su Airah kuma? Su waye hakan?"

"Waɗannan yaran da kika tadda gidana ƙwanaki, ƴaƴan Sufyan."

"Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un, Allah ya gafarta masu, ya sa masu ceto ne." Ta faɗa cikin sanyin jiki da takaicin yadda na dage ina kuka.

Na tsagaita da kukan na ce "Amin, yanzu zaku taho ko?"

Cikin rashin fahimta ta ce "Ina?"

"Garin su Sufyan ɗin mana, me zaku jira, mu ma gamu a hanya yanzu. "

Kai tsaye ta ce "A'a."

Na buga salati ina tambayar "Sabida me Maama? Ko baki ji ƴaƴan shi bane na asali, shi fa ya haife su."

Ta ce "Allah ya gafarta masu, yasa masu ceto ne."

Kai tsaye na ce "Amin, in kira Baban in faɗa mishi ya iske ku a motorpark sai ku taho tare, koko in ce mashi zaku wuto kawai ya iske ku nan garin ɗin, kin ga ai baa tsaya sai ya dawo ba, kar ya yi ta ɓata lokaci kin san Baaba da nawa..."

Cikin ƙosawa Maama ta ce "Nafeesa ba sai mun je ba, ki turo min number Umma ta shi, insha Allahu zamu kira mu yi masu gaisuwa, idan kun dawo sai mu zo har gida ayi mashi, ai ba gari ɗaya muke ba."

Wani takaici ya rufe ni, sai na ke ganin har ayi ma Sufyan rasuwa mijina amma uwata da ubana da ƴan gidan mu su gagara zuwa garin yi masu ta'aziyya? Mijina fa? Ai ina ce da su zaa yi addu'ar baƙwai a can, anya kuwa sun san darajar aure? Sun san darajar siriki?



#UWAR SUKUM.
[5/17, 8:21 PM] RN Feedohm: 💧💧 *KUSKUREN SO.*

FREE BOOK

*HASKE WRITER'S ASSO.*


*FEEDOHM*
Wattpad@Feedohm




_Ga ba ɗaya littafin nan sadaukarwa ne ga NAFEESA Muhammad SULE, maman jinjiri, Alherin Allah ya kai maki a duk inda kike._

_Ina kike Aunty Zainab Abubakar Kotorkoshi? Ke ma ina maki fatan alheri._


*022*





Teemah da ranta ya gana ɓaci ta ja dogon tsaki ta ce "Maama ki ma girman Allah kar ki barta ta tafi, bata buƙatar a ɗauki mataki me yasa bata yi haƙuri ta zauna ba tunda ya fi uwar ta daraja, mutun sai ka ce bugun iska? Sai ka ce kan shi aka fara aure a duniya? Kin san baki son a kashe miki aure don me baki je gidan su ba?"

Maama ta daka mata "Ya ishe ni haka, bani son rashin kunya."

Cikin kuka na ce "Ba dole ta yi rashin kunya ba, tunda an nuna mata ni banza ce yanzu."

"Koma ciki..." Ta Nuna min ɗaki fuskar ta murtuk.

"Ni gaskiya gidan mijina zan koma, daga ɗan zuwa sai a nemi kashe min aure? Shekara nawa ban yi auren ba? Wallahi ban shirya zawarci ba." Na faɗa ina ƙara sautin kukana tare da dire ƙafafu ƙasa.

"Sai ki tafi mu gani."

Ta ja da baya, kamar in tafi ɗin sai kuma na kasa, na shige ɗaki da gudu na faɗa saman katifa ina kuka, tare da janyo wayata na kira Sufyan ina faɗin "Sun hanani in taho."

Cikin ɓacin rai ya ce "Asin how? Su waye?"

"Maama ma na, wai sai mijinta ya dawo ya ji dalilin zuwana gida."

Ɓacin rai ya bayyana a muryar shi "Me kika ce masu na yi maki Nafeesa? Shin baki san tsakanin mata da miji ba aƙwai sirri?"

Na tausasa murya na "Wallahi ni fa ban faɗa masu komai ba, na ce kawai mun samu matsala."

"Daga faɗar haka shine suka hana ki dawowa gidan mijin ki? Sun mance da yanzu ikon ki ya dawo hannuna?"

Na yi shiru ina gunjin kuka.

Cikin sigar lallashi ya ce "Ok, bari in zo in ɗauke ki, sai in ga wanda zai hanani tafiya da mata ta."

Na ce "To, amma ya jikin na ka?"

"Ba sauƙi.." Ya faɗa tare da furzar da iska daga bakin shi.

"Na shiga uku.." Na ɗaura hannu bisa kai tare da kurma ihu, shikenan Maama zata kashe mun miji a banza, eh mana, zata kashe shi, tunda da ta barni na tafi ai da ya samu sauƙi, bayan ita ga nata mijin nan suna rayuwa cikin farin ciki, yajin nan dai ni nayi shi, kuma na fasa don me ba zata barni na koma gidan mijina ba, na ƙara sautin kukana, wallahi idan har wani abu ya samu Sufyan ba zan yadda ba.

Ya yanke wayar yana wani irin numfashi, yayin da na koma na ƙwanta na cigaba da kukana.

Shigowar Teemah ce yasa kukan ya tsaya, na zuba mata ido cike da tsana, ta wani ɗauke kai tana faɗin  "Wai ke gani kike shi kaɗai ne ke son ki ko? To wallahi duk abinda zai miki bai kai ga mahaifiyar ba, kuma idan har baki nemi yafiyar ta ba sai kin yi nadama."

"To uban me na mata shegiya munafuka?"

Ta kalle ni sama da ƙasa haɗe da taɓe baki ta ce "Au duk rashin kunyar da kika mata baki ga abin neman yafiya ba? Anya kan ki ƙalau Yaya?"

Na jefa mata filo ina faɗin "Shegiya mai baƙin hali, duk wani munafunci a gidan nan ke kike haɗa shi, ta ya na zaki samu mijin aure? Ai sai dai ki mutu a haka."

Ta ja tsaki ta fice ba tare da ta bani amsa ba, yayin da na cigaba da surfa mata zagi a zuci da fili, kai ba ita kaɗai ba, hatta Auta sai da ya sha zagi, ina nan ƙwance na ji sallama yaro ya shi yana faɗin "Wai Nafeesa ta fito in ji Mijin da ta ke aure."

"Hmm, ji rashin kunya, to dama wa ya ce ba shi take aure ba?" Teemah ta faɗa cike da masifa.

Ni kam na yi  tsalle na saɓa hijabi na fito ina kallon sama idanun nan jawur kamar garwashi, sai da na kai sautin Maama sannan na saci kallon ta, sai na ga ta kafe ki da ido ranta a ɓace.

Ciki ciki na ce "Zan tafi."

"Shine kika kira shi yazo ɗaukar shi shi ga mara kunya ko?"

Na zunɓuri baki na ce "To ai shi yace zai zo."

"To ba zaki fita ba."

Na ɗaura hannu aka ina faɗin "Ni wallahi ko a ƙur'ani cewa aka yi in ma mijina biyayya, to don me zaki sani saɓa mashi, bayan shi ya kirani ya ce in fito mu tafi?"

Maama ta buɗe baki tana kallona, na ɗauke kai na cigaba da faɗin "Kin manta ƙissar matar da mahaifinta bai lafiya taƙi zuwa duba shi har ya rasu sabida bata tambayi mijinta ba? Ƙarshe aljanna aka sa shi...

Maama ta katse ni "Je ki, amma ki sani daga rana irin ta yau kar ki kuskura ki ƙara taƙo gidan nan da sunan kin kawo ƙarar mijin ki."

Na ce "Na ji, ba ma zan kawo ba wallahi."

Ta koma ta zauna daɓas kamar wacce ƙwai ya fashewa a ciki, yayin da na wuce a tsorace, don na yi tunanin zata biyo ni amma ko kallona bata kuma yi ba, sai muryar Teemah da na ji tana faɗin "Wallahi an ji haushi, anya mamaa ba asiri yayi mata ba?"

Daga inda nike na juyo na ce "Idan asirin ya min ma ai ya isa Fatima, ke ma idan kin isa ki je ki yi auren ki samu mai miki asirin."

"Iskanci ne Fatima, babu wani asiri." Ta bata amsa a daskare, sannan ta kalle ni ta ce "Insha Allahu zata yi, Allah ya shirye ki." Yanayin fuskar ta ya nuna ta fi Teemah jin haushin maganar

Ni kam juya na fice ina gungunai, gani na ke kamar Maama ta daina sona, ta koma bayan Teemah, wallahi da ba na san irin so da gatan da ta nuna min ba, da sai na ce ba ita ta haife ni ba, na ɗauke hawayen da suka gangaro saman ƙuncina, na cigaba da tafiya,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login