Showing 75001 words to 78000 words out of 83936 words
gudan jinin shi, to wallahi idan ma wani abu ne a ranki ki kiyayi cikin can, don har Umma ta san da shi, kuma ba zata ƙyale ki ba muddun wani abu ya same shi, ki yi haƙuri da ƙaddarar ki mana.. "
Na zuba mashi ido yayin da hawayen suka tsaya cak, idan na fahimta da ƙyau shine mutun na farko da ya fara min gorin haihuwa tun kafin na warke? Bayan shine wanda ya tunzura ya sa aka cire min mahaifa? Shiga ɗakin da suka yi shine ta karanta mishi ina baƙin ciki da cikin da nake ma kallon tunbi? Na lumshe, bana buƙatar wani ƙarin bayani kuma, Sufyan bai sa aka cire min mahaifa ba sai da ya tabbatar da ya maida Asiya sannan tana ɗauke da gudan jinin shi, Zuciyata ta yi wani jimgin wani abu ya tokare min maƙoshi, sai na ke jin anya ba wani KUSKURE na aikata ba da Allah ya jarabce ni da Sufyan? Anya ba haƙƙin iyayena bane ke bibiyata? Na lumshe ido ina ƙoƙarin fiddo da hawaye ko na samu sauƙi amma sukaƙi bani haɗin kai, sai wani ɗaci ɗaci da ke yawo a maƙoshi na, yadda na ke kallon shi ne yasa ya daburce ya hau borin kunya "Ai ban miki dole ba gun cire mahaifar bare ki zuba min idanu, sannan maganar da kika faɗi ɗazu, an ji an miki laifi ki yi haƙuri duk da ba'a faɗa ba..."
Na lumshe idanuna, sai yanzu na tabbatar da maganar da ake cewa namiji ƙanin kunama, na girgiza kai yayin da na kasa cewa komai, so nake ma na buɗe baki na gwada mishi halin ƴan gheto amma na kasa, don wallahi ina buɗe baki kuka ne zai biyo baya, ni kuma ina jin tamkar an wuce lokacin da zan ma Sufyan kuka, domin ya min mugun tabo a zuciya da bana tunanin zai warke.
"Ki ɗan dunƙule kujerun ki guri ɗaya, itama zata zuba nata gefe ɗaya gudun gori." Na tsinkaye shi yana faɗa babu kunya babu tsoron Allah.
Na murmusa, wanda ake cewa ya fi kuka ciwo, idan da dane sai na ce asiri aka mashi ziryan amma yanzu duka na tattara maganar asirin na ci kutmar uban su, kafin na gama tunanin amsar da zan bashi ya juya koma ɗakin ta yana waigena kamar munafiki, ko da ya ke meye banbancin su tsakanin shi da munafikin? Abu ɗaya ne kawai, Sufyan na ƙasan shi a Jahannama ranar alƙiyama.
Kusan minti ashirin ina tsaye sannan na ja ƙafata na koma bedroom ɗina, wai sai da na shiga sannan na ji kuka ya ƙwace min, na kuwa durkushe na cigaba da rera shi ko zan samu rangwame daga abinda ke zuciya ta, amma kamar ana ƙara hura wuta a cikin ta, yayin da kalaman Sufyan na yaudara ke dawo min ɗaya bayan ɗaya, sai na tuna lokacin da nake faɗa ma Fannata ta waya take ce min ƙarya ya ke kar na yadda, sai na tuna lokacin da na fifita shi fiye da kowa na wa? Sai na tuna lokacin da nake ganin ya fi uwata da ƴan uwa a so na? Turrr na furta, ina jin tsanar kaina mai yawan gaske...
Sai da na ci ku kana mai isata sannan na miƙe na shiga toilet na watsa ruwa, na ɗauro alwala na dawo na yi sallah, na miƙe ƙafafuna na janyo wayata na kira Maama.
"Assalamu alaikum."
Ai ban ma amsa sallamar ta ba na fashe da kuka ina faɗin "Maama Sufyan ya ci amana ta, ya cuce ni, ya yaudare ni, ashe shima namiji ne?"
"Subhanahi, neman maza ya ke Nafeesa?" Ta tambaya a ruɗe
"Fiye da haka Maama, wallahi ya fi haka."
Sai na ji ta shiga tashin hankali tana tambayar me ke faruwa a ruɗe..
"Maama ya cuce ni, maƙaryaci ne ya maido Asiya, sai wulaƙanta ni ya ke, Maama ba zan zauna dashi ba, sai ya sake ni wallahi."
"Shine kika tashi hankalin ki haka? To Allah ya ƙyauta, dama ai mijin mace huɗu ne, kuma kafin ki aure shi ita ta fara, maganar saki kuma ki aje ta gefe, kin san dai hukuncin macen da take faɗin mijinta ya sake ta ko.."
So na ke na faɗa mata ya saka an cire min mahaifa, amma na rasa ta inda zan fara, sai na cigaba da rera kuka, yau da ace maido Asiya ya yi kawai ba tare da ya cuce ni ba, wallahi da sauƙi, ita kam da alamu bata ga komai ga maido da Asiya ba, don haka ta yanke wayar ta tana faɗin "Allah ya ƙyauta."
Ina aje wayar na ganshi gaban wadrope yana haɗa kaya, na bishi da kallo lokacin da yake faɗin "Bana so na takura miki, shiyasa zan ƙwashi kayana zuwa can, kin san dai idan mace ta haihu sai ta yi arba'in take amsar miji.."
A fusace na ce "Mijin ya ci kam uban shi, Sufyan ka tattara ka koma gun Asiya wallahi na tsane ka, na tsane ka."
Ya aje kayan ya tako kusa da ni yana murmushi "Ban ɗauka kishin ki ya kai haka ba Nafeesa, a tunanin yadda kike sona zaki so farin cikina."
Na kalle shi sheƙeƙe na ce "Wai har yanzu baka tuba ba? To bari ka jii ni tuni na tuba a kafircin ƙaunar ka.." Na ƙarashe maganar kamar idanuna zasu faɗo ƙasa, don sai nake ganin kamar so ya ke ya cinna min hauka.
"Wani ke zugaki ko?" Ya wani narke murya.
"A yanzu bana buƙatar zuga Sufyan.."
Ya maƙe ka faɗa "Tunda haka kika zaɓa shikenan, amma fa ki sani, hakan bai isa ya sa na sake ki ba har sai ma yi niyya.." Ya fice daga ɗakin yana ƴar waƙa, yayin da na bishi da kallon mamaki, sai na ke ganin kamar ba Sufyan ba...
******************
"Tun farko kin yi kuskure Nafeesa, kin yanke hukunci ba tare da tunanin gaba ba."
Cikin kuka na ce "Shi na ke so na gyara Fannata, wallahi na tsane shi, bana son zama da shi, na ce ya sawaƙe min ya ƙi, idan har na cigaba da zama dashi Fannata baƙin cikin su ne zai kashe ni."
Fannata ta sauke ajiyar zuciya tana faɗin "To ya zaki yi Nafeesa? Da shi kika yi ɓannar da dole ki zauna dashi, idan har kin kashe auren ki, wa zai aure ki haka Nafeesa? Bayan kin san kowanne mutun burin shi ya yi aure ya haifafa, to ke ba zaki haihu ba, tsohon da ya gama haihuwa zaki faɗa mawa..?"
Wani abu ya cake ni, na lumshe ido da sauri ina nishi sama sama, kalmar ba zan haihu ba ko da na auri AA ta min tsauri da yawa, na ɗaura kaina bisa cinyar hannuna hawaye na bin gefe kunnuwana.
Na rushe da kuka ina tambayar ta "Ya zan yi Fannata?
Kai tsaye ta ce "Haƙuri zaki yi, ki cigaba da son Sufyan kamar yadda aka fara.."
"Na daina ai Fannata, bana son shi yanzu.."
"Da saura Nafeesar Sufyan, a lokacin da nake faɗa miki halin maza wane irin cikin mutunci ne baki min ba?"
"Dan Allah mu bar wannan maganar, ki nema min mafita Fannata, duk duniya babu wanda ya san wannan sai ke."
"Har Maama.?
"Uhmm. "
"Ya kamata ta sani. "
Yadda ake buga min ƙofa ya sa na miƙe a fusace na aje wayar ina tambayar "Waye ne?
"Uwar ki ne, haba da Allah tun ɗazu ana ta fama kiran ki amma kin shige ɗaki kin kulle sabida baƙin hali?" Mai buga ƙofar ta bani amsa a hasale.
Nayi tsaye ina kallon mai maganar, ko baa faɗa min ba na san yayar Asiya ce, domin tsabar kamar da su ke, na kalle ta sheƙeƙe ina jinjina zagin da ta min, ban fa taɓa ganin ta ba, babu wani abinda ya haɗa ni da ita, ta shigo har gidana tana auna min zagi.
"Ki fito ki ja kayan ki gefe ɗaya, za'a zuba na masu gida." Ta faɗa kamar idon ta zai faɗo ƙasa
Na ja tsaki zan koma ciki don na fahimci kamar da wata jiƙaƙƙa ta tare da ita, ai kuwa wani fizgo ni waje tana tambayar "Ni kike ma tsaki?"
A fusace na ce "Da Allah malama sake ni, an yi ɗin.."
Ta ɗaga murya "Bebi, Hanny, ni wannan ƴar hau ɗin zata ma rashin kunya? Ai kam gidan ta kika zo.."
Bata rufe baki ba sai ga ƴan mata biyu zaga zaga da alamun rashin kunya tattare da su, suka wani kalle ni sheƙeƙe lokaci guda sannan suka ƙwashe da dariya ana faɗin "Shegiya mai siffar mayu, Yaya idan ba zata ƙwashe kujerun nata ba mu banka masu wuta kawai... '
"Idan kin fasa kin raina Allah da ya halicce ki." Abinda na faɗa kenan wallahi suka rufe ni da duka.....
#UWAR SUKUM.
*TAGWAYE PHONE STORE.* 💥🔥
*FEEDHOM*💥
*SLIMZY*✍🏻
Idan kin san baƙya ciko, kalli ƙasa😂, idan ma kina cikon shima dai kalli ƙasa...
Ina kuke? Ina kuke? Ina kuke makaranta littafan Hausa? Na ce Ina Kuke? Kun san dai idan kukaji kira ba banza ba.....!
Ƴar uwa kin karanta littafin RUƊANI? ƘADANGARUWA fa? Au har kin tuna Meena ko? Shine har da murmushi? To albishirin ki, kin san dai SLIMZY bata rubutu banza, ƴar uwa idan ana maganar littafai na jinsin mutun da aljan, kin san dai dole a sara mata, ita ce mai rubuta labarin da ke fasai, ita ce mai rubuta labarin da ke jijjiga makaranta, ita ce mai rubuta labarin da ke saka shauƙi da nishaɗi, ita ce ke rubuta labarin da zaki maimaita sau babu adadi baki sani ba, kin san ma ƙarin daɗin? Tafe ta ke da TAGWAYEAN ta, wato tun kafin na faɗa har kin murmusa, sabida kin tabbatar da duk inda aka ga wata zaa ga zara, to kin canka daidai FEEDOHM na tabbatar da kin karanta ISHARAH, kuma baki tsallake KUSKUREN SO ba, itama ai ba daga baya ba kema kin, rubutu mai tsayawa a rai, mai faɗakarwa, mai nishaɗantar wa.
TAGWAYE BIYUN marubuta ne da suka kere sa'a, Hajiya shiyasa wannan karon suka fito da zafafan littafan su har guda biyu rak... Masu tafiya da zukatan marubuta, wato kin ƙosa ko?To gasu da babban baƙi, domin sai da suka kashe darare da yawa don zaƙulo abinda zai jijjiga ku.
DUHU DA HASKE....Slimzy
Tare da
ƘALUBALEN RAYUWA.. Feedohm.
A cikin sauƙi da sauƙaƙawa, duka biyun zaki same su 700, sun yi sauƙi ko? Kun san ai suna son ku, dole su sauƙaƙa, yayin da ɗaya kuma 400...ƴar uwa kin san dai ba'a raba zarah da wata, don haka more dukkanin littafan biyu ta hanya biyan kuɗin ki ta wannan asusun 9994468172 Access bank fiddausi musa
Ko katin Mtn ta wannan lambar 08036953516 tare da shaidar biya ta 08036953516 ko 07042277401...
Tagwaye Phone store.
[7/9, 5:22 PM] RN Feedohm: 💧💧 *KUSKUREN SO.*
FREE BOOK
*HASKE WRITER'S ASSO.*
*FEEDOHM*
Wattpad@Feedohm
_Ga ba ɗaya littafin nan sadaukarwa ne ga NAFEESA Muhammad SULE, maman jinjiri, Alherin Allah ya kai maki a duk inda kike._
_Ina kike Aunty Zainab Abubakar Kotorkoshi? Ke ma ina maki fatan alheri._
*044*
Muna cikin wannan kiciniyar na ga Asiya ta janyo wayarta, da fari ban san wata kira ba, sai da na ji tana faɗin "Gaskiya Sufyan ba zan iya da rashin mutuncin matar ka ba, ta ya daga zuwan ƴan uwana sai ta hau zagin su tana kiran su karuwai, to wallahi duk matakin da suka ɗauka ba zan hana su ba, babu ruwana na faɗa maka, ina ta basu haƙuri tana ƙara ɗura masu zagi? To suma sun iya, darajar ka ta sa suka ƙyale ta, amma tunda bata gani ba zan ƙyale su."
Ban san me ya faɗa mata ba sai na ji ta cigaba da faɗin "Kana ji ko? Kana jin ta fa? Kana ji uwar mu da ke ƙasa ta zaga, sannan ta ƙwashe baby da mari, to wallahi na zare hannuna su yi mata abinda suka ga dama." Ƙittt ta kashe wayar ta.
Na saki baki yayin da a raina na jinjina mata da kalar nata munafunci, wallahi ta fa sani sarai su ne suka fara zagina, kuma yanzu da take maganar ɗaya na bisa ruwan cikina ta ya zan zage su? amma shine zata wanke su, shine zata tare duk wani abu da zai sa ace su ne da laifi, kuma fa ina ganin tana wayar tana masu alama da su cigaba da jibgata.
Raina ya ƙara ɓaci, yayin da na ƙara ƙaimi wajen ramawa, an ce sarkin yawa ya fi sarkin ƙarfi, wallahi tun ina ƙoƙarin ramawa har dai suka fi ƙarfina, yayin da suka min mahaukacin duka har na fita hayyaci, ni kam dai ma ban ƙara sanin inda kaina ya ke ba, sai dai farkawa nayi na tsinci kaina ƙwance bisa gadon asibiti, jikina ya min nauyi, fuskar nan a tamke, ko ban duba madubi ba na san ba ƙaramin kumbura ta yi ba.
Na kalli Sufyan da ke zaune yana latsa waya, na sani sarai yanzu haka ƴan uwan Asiya na police station, duk da dai na sare da lamarin shi, amma dai na san ba zaa dake ni har cikin gidana ba, a ce an daki banza, na lumshe ido ina jin idanuna a tamke.
Ban ɗauka waya yake ba sai da na ji yana faɗin "Ki basu haƙuri Asiya, wallahi bata ƙyauta ba, kuma zan ɗauki matakin da ya dace."
Na ƙura mishi ido, ban fahimci su wa zaa bawa haƙurin ba, shin iyayena koko ƴan uwan ta? Na cije laɓɓana lokacin da na ji yana cigaba da faɗin "Ai na sha faɗa mata, yadda take ma iyayen ta rashin kunya ba wanda zai yadda a yi ma na shi, banda ma rashin arziki irin na Nafeesa ta ya zata kalli tsabar idon su ta zagar masu uwa? Ai dole su yi mata abinda ya fi wannan, ni dai dan Allah ki taya ni ba su haƙuri kafin na dawo gidan.. "
Sai yanzu na gane inda ya dosa, wato ni ce mai laifi, duk abinda ta faɗa gaskiya ne, ba zai yi bincike ba, sai na ji hawaye na bin kumatuna, na juyar da kai daga barin kallon shi, don idan na kuskura na cigaba da kallon mummunar fuskar shi mai kama da ta alade wallahi sai na auna mishi zagin da ban masu ba, ni fa ban ma san bajejen hanci ne dashi ba sai yanzu, dole ma Fannata ta ce uban me na gani jikin shi na nace mishi har haka.
"Dole ki kawar da kai mana, kin zubar min da daraja gun ƴan uwan matata." Ya furta lokacin da ya tako ya zo gaban gadon ya dafa ƙarfen da hannu biyu biyu.
Na juyo idona tab da ƙwalla ina kalle shi, takaici yasa na rasa me zan ce mishi, sai na maida idon na kulle ina wani gunji mai zafin gaske, bana jin zan iya buɗe baki na ce mashi ba haka ba ne, domin ko kaɗan babu abinda hakan zai haifa min sai ɓacin rai.
Ya ƙwashe da dariya "Allah ya ƙara, kuma wallahi ya zamana na farko na ƙarshe da ƴan uwan Asiya zasu zo ki ci mutumcin su.."
Ƴan uwa! Na furta a raina, a lokacin wasu hawaye masu ɗumin gaske suka silalo daga idona, na jin ya bini da tsaki sannan ya fice yana mita..
Na bi bayan shi da ido, har ga Allah raina yayi tsananin ɓaci akan rashin ɗaukar mataki daga Sufyan, na ɗauka ko da yatsa aka tsina min ba zai sauka lafiya ba muddun Sufyan ya san da haka, na ɗauka ko da dungurina aka yi sai inda ƙarfin shi ya ƙare, amma sai na ga ba haka ba, an dake ni, an sumar da ni, an daki banza, sai ma tuƙuicin Allah ya ƙara daga gare shi, an ya duk abinda ya ke faɗa akan Asiya gaskiya ne? Anya ba rashin samu ta da bai yi ba ya sa yake furta kalmar ƙiyayya a gare ta? Na lumshe idona, a lokacin da wani sashe na zuciyata ya tabbatar mun da irin yaudarar da na yi ma kaina, yaudarar yardar da ni yi da Sufyan na cewa babu macen da yake so a duniya in ba Nafeesa ba, yaudarar da na kasa gane duk macen da ta zauna da namiji shekara sama da biyar ƙarya ne ace baya jin ta, yaudarar da na kasa gane duk macen da namiji ya fara sani a rayuwar shi, ƙarya ne ace baya jin ta, lallai na yaudari kaina, domin Sufyan bai yaudare ni ba, kawai dai ya min ƙarya sannan kuma ya zalunce ni, sai na ke jin ko da Asiya asiri ta mashi ba ta yi laifi ba..
Na ƙura ma ceiling ɗin ɗakin ido, hawaye na bin kumatu a yayin da na ke kallon yadda fankar sama ke wulwulawa, sai na ji wani ja'irin murmushi ya suɓuce min, kamar dai haka Sufyan ya riƙa wulwula da zuciyata.
Ni kaɗai asibitin ya tsallake ya bar ni, babu shi babu ƴan uwana, kuma ban yi ƙoƙarin kiran Maama ba, don wallahi kunya na ke ji, duk da dai ta yafe min, amma sai na ji ba zan iya ba, ƙara na zauna ni kaɗai kafin ruwan da aka sa min ƴa ƙare, na je gidan an yi duk wacce zaayi, don wallahi ba zan cigaba da zama da shi ba,ni ban ma ga dalilin sa ruwan ba, duk da dai ban san irin mahaukacin dukkan da aka min ba.
Ruwan na gama ƙarewa aka sallame ni, daga ni sai hijabina na zura na fice zuciyata na tuƙuƙi, gashi ko kuɗin da zan hau a daidaita banda shi, a bakin gate ɗin na yi karo da likitan da ya min aikin cire mahaifa, sai da gabana ya yi mummunar faɗuwa, na tare shi da sauri ban san lokacin da na furta "Ka gane ni kuwa ba?"
Ya kalle ni na ƴan mintuna sannan ya saki murmushi yana shafa ƙasumbar shi, a tausashe ya ce "Ya zaayi na ƙi gane ki Nafeesar Sufyan, a wannan shekarun ke ce macen da tafi kowa wauta a gare ni."
Na lumshe ido tare da buɗe su tar ina kallon shi, mancewa ya yi ba wauta kaɗai ba ya kamata a bani