Showing 72001 words to 75000 words out of 83936 words
asibiti ya ce Uwarsa na kiran shi wato zuwa yayi aka maida auren su da Asiya? Maganar ta ta katse ni "Ina awaran, kasan idan magaji ya nemi abu ya rasa da prob.." Ta tuntsure da dariyar shaƙiyanci.
Kamar zautatta bakina a buɗe na bi ta da kallo, idona ya tsaya kan ɗan ƙaramin cikin ta da ke kama da na mai juna biyun wata huɗu, sai kuma na ga hannun Sufyan a bisa ciki, na girgiza kai da sauri a lokacin da wata zuciyar ta sanar da ni tumbi ne, sabida indai jiya aka ɗaura auren babu maganar ciki sai dai tunbi, to idan ba jiya aka ɗaura ba fa? Idan ya daɗe da maida auren su bai sanar min ba fa? Na hau girgiza kai kamar zararra tare da dafe bango a lokacin da na ji jiri na neman kayar da ni ƙasa, amma duk da haka sai na yi tangal tangal zan faɗi.
Uwar Sukum.
[7/3, 9:12 PM] RN Feedohm: 💧💧 *KUSKUREN SO.*
FREE BOOK
*HASKE WRITER'S ASSO.*
*FEEDOHM*
Wattpad@Feedohm
_Ga ba ɗaya littafin nan sadaukarwa ne ga NAFEESA Muhammad SULE, maman jinjiri, Alherin Allah ya kai maki a duk inda kike._
_Ina kike Aunty Zainab Abubakar Kotorkoshi? Ke ma ina maki fatan alheri._
BARKA DA SALLAH, ALLAH YA MAIMAITA MANA, YA SA WANI SHEKARAR MU YI A GABAN KA'ABAH.
*042*
Na yi tunanin zai saki Asiya ya watso da gudu ya rungume ni gudun kar na faɗi ƙasa, amma sai na ga sam ba ta ni ya ke ba, na dafe bango da ƙyar kaina a ƙasa hawaye na ɗiga bisa tiles ɗin wajen, yayin da na ji kaina ya min wani irin gingirigimm kamar zai faɗo ƙasa.
Ina jin lokacin da suka shige bedroom ɗin suna dariya ƙasa ƙasa, sannan suka ƙullo ƙofar kamar da gayya, yayin da ni kuma zuciyata ke harbawa da ƙarfin tsiya, na ɗaga idanuna da ƙyar na zubawa ƙofar ido, wai Sufyan ne a ciki? Sufyan ɗina da Asiya, ya barni gantale riƙe da bango, wallahi na yi tunanin ko da maido Asiyar yayi sai na lallashe shi zai shiga gurin ta, na cije leɓena na ƙasa kamar zan cizgashi, sai na ke jin tamkar a mafarki, sai na ke jin tamkar hakan ba zata taɓa faruwa ba har abada.
Ban san lokacin da na zube ƙasa ba ina wani irin gunjin kuka mai ban tausayi, a lokacin da na tabbatar Sufyan ba zai fito ba, sai na ke jin tamkar Sufyan bai mun adalci na, ya watsar da ni asibiti ya je ya dawo da wata? Bayan ya san a lokacin na fi buƙatar kulawar shi, anya abunda ya ke faɗa min a baya gaskiya ne? Anya ba yaudara ta yayi ba yana son Asiya.. Anya ba su daɗe da maida auren su? An ya ba tun lokacin da na koma gidan mu suke tare ba? Sabida abinda na gani a jikinta ya tabbatar min da sun daɗe a tare, duk da wani sashe na zuciyata na ƙaryata haka.
"Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un.." Na furta tare da haɗe kaina da bango ina kuka.
Ina zaune a gurin da sa ran Sufyan zai fito ya lallashe ni ya faɗa min uwar shi ta matsa mashi daga zuwan shi aka maida auren su da Asiya, sannan ya tabbatar mun dama Asiya na da ƙaton tunbi ba abinda na ke zargi ba ne, kamar dai yadda wani sashe na zuciya ta ke karanta min, amma shiru har na sharari awa ɗaya babu shi babu dalilin shi, kai ko motsin su kusa kusa ma bana ji, don haka bisa tilas na ja jiki don ba ma zan iya miƙewa ba, na shige ɗaki na yi zaman dirshan ina rizgar kuka.
Ban san lokacin da ya shigo ɗakin ba, sai tsinkayar shi na yi yana faɗin "Kin cika rigima Nafeesa, me ye na tayar da hankali fisabilillahi?"
Na ɗago da sauri na zuba mishi ido, yayin da ya ƙaraso kusa da ni fuskar shi a sake kamar babu abinda ya aikata min, ya sa hannun shi na dama ya janye min hular kaina da ta zazzago ta rufe min fuska yana tambayar "Ina awarar?"
Wani abu ya dakar min ƙirji, a cikin raina na ce "Kutmar uban awara." Yayin da a fili kuma na ƙwantar da kai gefen haggu murya ta na rawa na ce "Mafarki na ke ko Sufyan?"
Ya murmusa "Ya kamata ki farka haka."
Na kamo hannun shi dukka jikina na rawar mazari "Dan Allah ka faɗa min ke da faruwa? Ka faɗa min Sufyan, wallahi zuciyata gab take da bugawa, dan Allah ka sanar min da abinda ke faruwa.."
"Bangane ba?"
Cikin rawar murya na cigaba da faɗin "Asiya ce ko? Asiya ce Umma ta tilas maka dawowa da ita ko? Wani abu suka baka ka sha ko Sufyan? A ƙwarya ko?"
Ya zame hannun shi daga nawa yana aika min da wani irin kallon da na kasa gane manufar shi, ya miƙe tsaye yana faɗin "Bana son shirme, ta shi dan Allah ki haɗa min abincin nan yunwa mu ke ji, ni ban ma san yaushe kika lalace har haka ba Nafeesa, mijin ki ya dawo instead of ki tarbe shi da kulawa sai ki tsaya wani shirmen banza? Oya miƙe da Allah ki ɗauko min na baro ƴar mutane ita kaɗai. " Ya wani ja ni da niyyar miƙar da ni.
Wannan karon kam hannun shi na make na miƙe ina aika mishi da mummunan kallo, cikin dakiya na ce "Da son ranka ka maido ita kenan?"
Ya gyaɗa min kai "Dama ai ban ɓoye miki ba.."
"Da son ranka ka watsar da ni asibiti?"
Ya kafe ni da ido ba tare da ya amsa min ba, ban damu ba na cigaba da tambayar shi "Tun yaushe?"
"Tun bayan rasuwar su Airahh.." Ya furta babu alamun kunya ko fargaba.
Gabana ya yi mummunar faɗuwa na ɗago a razane ina kallon shi "Duk abinda ka faɗa ƙarya ne?"
Ya tamke fuska "Bana son iskanci, ta ya zaki tasa ni gaba da tambayoyin rashin ɗa'a haka? Ko kin manta ni mijin ki ne?"
Na ɗauke ƙwallan da suka gangaro fuskata, don wallahi sai na ke jin ƙwata ƙwata na tsane shi, ban kuma taɓa zaton zan tsane shi har haka ba, na ɗauka Sufyan daban ya ke cikin maza, na ɗauka shi waliyyi ne baya ƙarya, na ɗauka komai daga gare shi tsabtatacce ni, ashe ba haka ba ne, a sanyaye na ce "Me na maka? Me na maka da ka min irin wannan cutar Sufyan? Ka san kana son matar ka, me yasa baka faɗa min ba? Me yasa ka min ƙarya baka son ta? Me yasa ka min ƙaryar zaka rayu da ni kaɗai? Me yasa ka sa na tsayar da haihuwa ta?"
Ya lumshe ido "Dan Allah zamu yi wannan maganar daga baya, yanzu dai ina abinci na."
"Ubanka ne abinci, wallahi ba zaku ci ba, banza mayaudari, ka cuce ni, ka zalunce ni, Allah ya isa ban yafe maka ba, dama ku maza duka halin ku ɗaya." Na furta zuciyata daskare, a yadda na ke ji ma zan iya kai ma shege duka, bare ma idan na tuna yadda ya nakasa min rayuwa baki ɗaya, sai yanzu na fahimce shi, Asiya ita ce uwar ƴaƴan shi, ni kuma majiyar daɗin shi..
Turrrrr na furta tare da ƙawar da kai na ƙasa, yayin da shi kuma mamakin furucina ya hana shi cewa komai, na ɗago rinannun idanu na na cigaba da faɗin "Dan Allah ka fice min daga ɗaki, idan kuma ni zan bar maka gidan naka sai ka ƙarasa saki biyun ka."
Sai na ga ya murmusa yana faɗin "Ni kika zaga?"
"An zage kan dan Kutmar uban ka, munafuki macuci..." Na kafe shi da ido ina jiran na ji saukar hannun shi a jikina, amma sai na ga ya kaɗa kai ya fice ran shi a ɓace, don haka nima na sulale a gun, sai yanzu na fahimci komai.
Sufyan bai ɗauki mace a bakin komai ba, bana ce baya ƙaunar Asiya ba, amma na tabbatar da iri ya ke biɗa daga gare ta, amma ni baya ƙauna ta, ya aure ni ne ba don na haihu ba, ya aure ni domin ya more ƙuruciya ta, ya aure ni domin ya huta, na fashe da kuka ina girgiza kai na da ƙarfi...
Wannan daren ya kasance baƙin dare a gare ni, wallahi ko kaɗan na gagara runtsawa, bani bedroom ɗina bani ga ƙofar bedroom ɗin da suka shige, don bana jin zan iya kiran shi da nata, ko kaɗan na gagara gano wane mataki ya kamata na saka Sufyan, maganar asiri ko tilastawa na aje shi gefe, abu ɗaya na sani ya cuce ni, ya zalunce ni, kuma wallahi bana jin zan cigaba da zama da shi, dole ya sawaƙe min.
Na yadda bacci ɓarawo ne, domin sai kusan asuba sannan ya ƙwashe ni, ban kuma tashi farkawa ba, sai da na ji ƙamshin omlet ya cika min bedroom, na miƙe a firgice da tunanin ko aljanu ne ke soye soye domin dai na tabbatar ko hauka ba zai bawa Asiya damar shigar mun kitchen ta ɗaura wani abu ba, shi kuma Sufyan ba zai yi ba, sabida ko lokacin da nike amarya sai dai idan na shiga ya biyo ni ya taya ni, na sake baza hanci ina shaƙar ƙamshi yayin da nike jin ƴan dararraku ƙasa ƙasa a falo, ban san sadda na saki salati ina murje idanu na, kamar na shiga toilet na ɗauro alwala na yi sallah, amma sai na ji sam ba zan iya ba, ina buƙatar fita falo na ga abinda ke faruwa, ciki rawar jiki na zura takalma kamar zan kifa ƙasa, na fice da sauri gabana dakan uku uku..
"Na yi missing girkin ki, rabon da na ci abinci mai ɗanɗanon wannan tun hankalina na ƙwance.." Na tsinkaye shi yana faɗa mata dai dai zan shiga falo, wanda hakan ya tilas min jan birki hawaye na bin kumatu na, na zuba masu ido suna bisa doguwar kujera zaune, yayin da plate ɗin ke bisa cinyar shi, nima fa haka ya ke faɗa min kullun, amma yau shine ya juye ga wata, lallai a gaishe da namiji.
Ta ɗaura hannun ta bisa kafaɗarshi tana jefa mishi hararar wasa ta ce "Bangane ba? Yanzu hankalin ka tashe ya ke? Ina ce ana maka wanda ya fi na Asiya daɗi.?"
Ya ƙwashe da dariya tare da shafar sajen shi yana tambayar "Wa ya isa.?
"Matar ka mana."
Ya ƙwashe da dariya "Ke kin ga kalar gayu a tattare da ita? Da dai ace fagen kaɗa dambu ne da taliya ƴar murji sai in ce za'a fiki."
"Au haka?" Ya saki dariyar shaƙiyanci.
"Eh mana, wacce ta kasa zama gidan su sabida cimar ba ɗaya ba?" Ya ƙarashe maganar tare da ɗaura hannun shi bisa cikin ta.
Sai na ji tankar ya caka mun wani abu a ƙirji na, na ja numfashi da ƙyar tare da lumshe ido ina jin yadda bugun zuciyata ya tsananta, wallahi da ace wani ya faɗa min haka ba zan taɓa yadda ba, ko da ya ke don mai zan ji haushi? Bayan ni ce na fara faɗa mashi? Shi kawai maimaitawa ya yi, ban ƙara ƙidimewa ba sai da na ji yana faɗin "Ki bar haɗa kan ki da ita Asiya, rashin ki ya sa na aure ta, amma kin sani kin fita a ko'ina, kuma na fi ƙaunar ki fiye da ita, kawai dai ki ɗauka ƙaddara ce da tsotsai ya shigo da ita rayuwar mu.."
"Ba wani nan, me yasa ka ƙi faɗa mata tun wuri mun maida auren mu, har ka sa aka kirani da karuwa.? Ta langwaɓe kai tana kallon shi.
"Bana so ta tayar miki da hankali, don bata rasa gadon hauka ba."
"Ko?" Ta wani waro ido waje.
Ya kamo hannun ta "Yes, mu bar maganar nan, ki gama mu shiga ciki please, kin san bana gajiya da ke, ƙamshin ki kaɗai na iya gamsar da ni, taushin fatar jikin shi, laɓɓan ki, ni'imar ki, da komai na ki daban ya ke, please ki agaza tun kafin na fara tsiyaya.."
Ta maka mishi harara "Bana son zolaya, ka lallaɓa gun amaryar ka mana."Sai na ke jin tamkar da gayya ta ke maganar ta.
Ya wani janyo ta da ƙarfi jikin shi yana shinshinar ta "Ni ke nake buƙata, kin fita daɗi, kin fita ɗanɗano, kin fita ni'ima, kin fita matsewa, kin fita komai Asiyata, please ki taimaka min, ana maganar lambu wake ta dusa..."
*TAGWAYE PHONE STORE.* 💥🔥
*FEEDHOM*💥
*SLIMZY*✍🏻
Idan kin san baƙya ciko, kalli ƙasa😂, idan ma kina cikon shima dai kalli ƙasa...
Ina kuke? Ina kuke? Ina kuke makaranta littafan Hausa? Na ce Ina Kuke? Kun san dai idan kukaji kira ba banza ba.....!
Ƴar uwa kin karanta littafin RUƊANI? ƘADANGARUWA fa? Au har kin tuna Meena ko? Shine har da murmushi? To albishirin ki, kin san dai SLIMZY bata rubutu banza, ƴar uwa idan ana maganar littafai na jinsin mutun da aljan, kin san dai dole a sara mata, ita ce mai rubuta labarin da ke fasai, ita ce mai rubuta labarin da ke jijjiga makaranta, ita ce mai rubuta labarin da ke saka shauƙi da nishaɗi, ita ce ke rubuta labarin da zaki maimaita sau babu adadi baki sani ba, kin san ma ƙarin daɗin? Tafe ta ke da TAGWAYEAN ta, wato tun kafin na faɗa har kin murmusa, sabida kin tabbatar da duk inda aka ga wata zaa ga zara, to kin canka daidai FEEDOHM na tabbatar da kin karanta ISHARAH, kuma baki tsallake KUSKUREN SO ba, itama ai ba daga baya ba kema kin, rubutu mai tsayawa a rai, mai faɗakarwa, mai nishaɗantar wa.
TAGWAYE BIYUN marubuta ne da suka kere sa'a, Hajiya shiyasa wannan karon suka fito da zafafan littafan su har guda biyu rak... Masu tafiya da zukatan marubuta, wato kin ƙosa ko?To gasu da babban baƙi, domin sai da suka kashe darare da yawa don zaƙulo abinda zai jijjiga ku.
DUHU DA HASKE....Slimzy
Tare da
ƘALUBALEN RAYUWA.. Feedohm.
A cikin sauƙi da sauƙaƙawa, duka biyun zaki same su 700, sun yi sauƙi ko? Kun san ai suna son ku, dole su sauƙaƙa, yayin da ɗaya kuma 400...ƴar uwa kin san dai ba'a raba zarah da wata, don haka more dukkanin littafan biyu ta hanya biyan kuɗin ki ta wannan asusun 9994468172 Access bank fiddausi musa
Ko katin Mtn ta wannan lambar 08036953516 tare da shaidar biya ta 08036953516 ko 07042277401...
Tagwaye Phone store.
UWAR SUKUM..
[7/3, 9:12 PM] RN Feedohm: 💧💧 *KUSKUREN SO.*
FREE BOOK
*HASKE WRITER'S ASSO.*
*FEEDOHM*
Wattpad@Feedohm
_Ga ba ɗaya littafin nan sadaukarwa ne ga NAFEESA Muhammad SULE, maman jinjiri, Alherin Allah ya kai maki a duk inda kike._
_Ina kike Aunty Zainab Abubakar Kotorkoshi? Ke ma ina maki fatan alheri._
*043*
A wannan gaɓar kasa daurewa na yi na ƙarasa gaban su idanuna jajur kamar wacce aka jeho sai uban huci na ke yadda kasan na gama faɗa da ƙatti, na kafe shi da idanun yayin da nike jin wata irin tsanar shi na ɗawainiya a rai, shima sai ya kafe ni da ido cike da rashin kunya, na yi sauri na kawar da kaina gefe don ko ganin shi ma bana son yi, yayin da maganganun shi ke ta yawo a kaina, na lashi laɓɓana ina murmushi takaici a lokacin da na tuna ya faɗa min irin waɗannan ga Asiya, kuma cike da jin daɗin su na ke sauraren shi, duk da basa tare, ashe nima zai faɗa mata fiye da irin su, itama ta saurara cike da annashuwa kamar dai ni, na lumshe ido.
"An kenan tashi marasa kunyan gheto.? Ya faɗa irin kamar babu abinda ke faruwa, sannan ya cigaba da tambayar "Lafiya kika mana tsaye haka? Babu ko ƴar ina ƙwana? Nafeesa me yasa kike so ki lalace da rashin ɗa'a?"
Kafin na bashi amsa ta miƙe tsam zata bar gurin, ai kam na fizgota a fusace ina faɗin "Gidan uwar wa zaki je? Ina ce dake aka gama zagina yanzu? Sai ki tsaya na baku amsa dai dai da abinda kuka faɗa."
Ta ɗaure fuska tana kallon shi, rai a dagule ta ce "Sufyan matar ka ta fita a idona." Kamar fa irin bata da lokacina, na lura kuma tun farkon haɗuwar mu gidan su Umma haka ta ke min.
Ya wani daka min tsawa yana faɗin "Bansan hauka Nafeesa sake ta tun kafin na ci mutuncin ki."
Cike da takaici na ce "Mutunci har na nawa Sufyan? Wane mutunci ya rage baka ci min ba a gaban ta? Cewa fa ka yi banda ɗanɗano, ta fi ni komai..." Maganar ta tsaya cak sai hawaye da suka fara ambaliya a fuskata.
Sai na ga jikin shi ya yi masifar sanyi, don bai taɓa tunanin na ji abinda ya faɗa ba, cikin rawar murya ya ce "Koma dai menene ki sake ta, je ki ma an faɗa, ai ni na faɗa ba ita ba, wai me yasa baƙya son zaman lafiya ne Nafeesa? Matar nan daga zuwan ta gidan nan jiya babu kalar iskancin da baki mata ba, to ya isa haka nan, yadda kike jin ke matata ce haka itama take matata, tana da isa fiye da ke sabida ita har da gudan jinane a tattare da ita."
Hawayen da ke bin kumatuna ya hanani magana, yayin da zuciyata ke ƙona, Asiya ta watsa min wani wulaƙantaccen kallo tana faɗin "Idan har hannun ki ya kuskura ya sake taɓa jikina wallahi sai kin raina kan ki, ni ba ɓallagaza ba ce da zan tsaya faɗa da kishiya, ki yi ta kan ki kin ji ko."
Ta juya ga Sufyan tace "Ka faɗa ma matarka cikine da ni, ta kula da ƙyau da irin haukan da zata riƙa min.." Ta wuce fuuu yayin da ya bita yana bata haƙuri, suka barni tsaye kamar dusar ina kuka tallabe da hannaye.
Mintuna kaɗan sai gashi ya dawo kamar kububuwa yana faɗin "Kin wani janyo ta idan da ta faɗi ƙasa fa? Ko baƙya gani cikine da ita? Ko shima kishin kike da shi? Anya ma kuwa ba da gayya kika fizgota ba Nafeesa? Wato tunda ba zaki haihu ba, bari ki hana kowa ganin