Showing 57001 words to 60000 words out of 83936 words

Chapter 20 - KUSKUREN SO Book Complete by Feedohm.txt

Feedoms   

21 Sep 2025

1704

wallahi ba zan amince da shi ba.

"Idan ma bata yadda na, kan ta." Ta furta tana jefa min mummunan kallo.

Kafin ta aje wayar ta juyo gare ni fuskar nan tamke tana faɗin "Zai maishe ki, amma sai idan kin yadda da sharuɗɗana."

Na zuba mata ido tare da gyaɗa kai ina faɗin "Na yadda Umma."

"Idan har kin amince zaki tsayar da haihuwa, don ba zan yadda ki haihu ki ɗorawa yarona masifa ba, kullun yawo asibiti, shan jini kamar ƴan mafiya, sannan kuɗin shi a gantale."

Wata irin zufa ta keto mun, na shafi ɗan tululun cikina, lallai wannan matar bata da imani wallahi, kenan muddun ina son zama da Sufyan sai dai na zauna haka ba tare da na ga jini na ba? Ba zan ga ɗan cikina ba? Ya kamata ta fahimci laifin ba nawa bane ni kaɗai, na share ƴan guntayen hawayen da suke bin kumatuna, cikin rawar murya na ce "Lafiya ta lau Umma."

Ta watsa min harara tare da ɗauke kanta gefe tana faɗin "Ba ni zaki ma ƙarya ba, na sani sarai ba zaki haifi yara masu lafiya ba."

Ba zan haifa ba ko ba zamu haifa ba, cikin kuka na ce "Zan haifa Umma."

"Ban miki dole ba."

Jameela ta tare "Aa fa Nafeesa, jinin ki AS ne haka ma Yaya, sikila zaki yi ta haifa mashi."

Na kalle ta a raunane, idan na fahimta daidai har da ita ke ƙara zuga Umma akan wannan haihuwar, amma me yasa ba zata faɗa mata ni da ɗanta duka ɗaya ne ba, ko dan ina mace? Tsinkayar ta na yi tana faɗin "Idan ba ki yadda ba tashi ki bani guri."

"Ina da ciki Umma.."

Ta kalle ni sama da ƙasa sannan ta ce "Na gani sai ki zubar."

"Wallahi ba zai zubdu ba, ya yi ƙwari Umma, ki taimaka ki rufa min asiri, wallahi daga shi na yadda da sharaɗin ki." Na hau mata magiya ban sani ba, ko ta yadda ne ko akasin haka, na ji dai ta yi shiru.

Sai kuma na ji ta cigaba da faɗin "Sannan kuma kar ki sake ina magana da ɗana ki sa min baki, idan kuma kika sake a bakin auren ki."

Na yi shiru ina kuka, Jamila ta yi ƙasa da murya ta ce "Sai Asiya."

Ta dalla mata harara "Ita ɗin banza da zan yi maganar Asiya a tare da ita."

Ban ce komai ba na cigaba da rera kukana, kafin ta ɗaga waya ta sake kiran shi, cikin isa da izza ta ce "Ka maida ta."

Ina jin ta cikin wayar ya maida auren mu, sannan ta yanke tana faɗin "Ƙya iya tashi ki tafi, babu abinda zaki min, amma fa a kiyaye."

Babu abinci, babu ruwan sha, mutun ya ƙwashi awa biyu yana tafiya sannan a ce ya koma, gashi ko gidan ban tsaya na yi kalaci ba, na miƙe jiki babu ƙwari na tura mata ledar da na zo da ita, yayin da ta saka ƙafa ta yi ƙwallo da ita tana masifa "Ni zaka yaudara? Ko an faɗa miki ni maƙwaɗaiciya ce da zaki ƙwaso wata banzar leda ki miƙo min, wato munafunci, da can ba zakiyi ba sai yanzu." Ta kalli Jamila a harxuƙe ta cigaba da faɗin "Maza ƙwashe tsiyar nan ki zuban ita a bola Jamila."

Ina kallon kuɗin Maama da na ɗauko da wayar Baaba aka ɗauke su aka zuba a bola babu halin in ce a bani abina, ta bini da harara "Duk abinda baki min ba a da, bana buƙatar shi yanzu jarababba.."

Ni dai na miƙe na soma tafiya da ƙyar sabida yunwar da ni ke ji, ga shi banda kuɗin mota ban rage komai ba, ga takaici da bakin ciki da ke addabar zuciyata.

Zuciyata babu daɗi ko kaɗan, na sani tunda aka fara maganar Asiya dole zasu sa Sufyan ya maido ta, to sauƙina ma sai dai a takura mashi ya maida Asiya ba wai don yana son ta ba, don wallahi na tabbatar da uwar shi hanyar jefa min miji Jahannama ta nema,  domin yadda ya ke masifar sona wallahi ba zai iya adalci a tsakanin mu, na saki murmushi takaici haka kurum a kawo min ƴar tayin aiki a gida da sa ido, don ba zan iya kiranta kishiya, bayan ina da tabbacin Son da Sufyan ke min ba zai barshi ko tsome tsomen nan ya yi ba.

Bayan na sauka mota maimaikon na wuce gidan mu, sai na ga babu wani dalili tunda dai mijina ya maida ni, to uban me zan je in yi kuma? Salon ma na je su riƙe ni su ɓata mun lokaci, don haka kai tsaye na wuce kasuwa, islamic chemist ɗinnan, na haɗo tarkacen emergency bashi na taho da yake mu ɗan saba, so na ke na rikita shi a daren yau yadda zai mata saki uku bai sani ba tun kafin a maida auren...

A bakin gate na yi kiciɓus dashi yana ƙoƙarin rufe ƙofar zai fita, na zuba mashi ido ina kallon shi, maimakon ya rame ya yi baƙi kamar yadda na yi tunani sai na ga akasin haka, yayi ɓul ɓul abin shi, ga wani uban ja da ya ƙara sai ka ce dama ni ce matsalar shi.

Ya waro ido yana kallona tare da murmushi a fuskar shi, kafin ya fasa kulle gidan ya yo kaina hannun shi a buɗe alamun na faɗa ciki, na ɗauke kai na sallami mai napep ɗin, duk da haka sai da rungumo ni ta gefe yana kissing gefen kuncina, sauƙin ma unguwar ta mu babu irin yawan mutane masu giftawa, muna kuwa shiga harabar gidan ya caɓeni yana faɗin "Oyoyo My Sweet heart."

Bai dire ni ko'ina ba sai bisa doguwar kujera, ya zamo ƙasa ya tsugunna ya riƙe min hannu yana ƙare mun kallo, ciki sanyin murya ya ce "Kin canza Nafee."

Na zunɓuri baki, don wallahi ban yi zaton haka zan iske shi ba, irin kamar bai yi missing ɗina ba.

"Fushi kike, maimakon ki yi murna kin dawo gidan Sufyanun ki?" Ya faɗa kamar mai raɗa

"Ƙiba fa ka yi." Na furta kamar zan yi kuka.

Ya saki dariya ƙasa ƙasa, sannan ya kalli kan shi yana faɗin "A haka? Lallai kin daɗe ba ki ganni ba."

"Ba wani..." Na ja mishi hanci.

Sai ya saki maganar ya kama wata "Na ɗauka gidan ku zaki wuce, sai na zo biko.

Na taɓe baki ina faɗin "Wa? Tab, Allah ya raba ni. "

Ya waro ido waje" Why? Ba gidan ku ba ne. "

"Gidan su Teemah dai, ai wallahi tunda na nuna masu na san darajar aure na babu mai ƙauna ta, suka bi suka tsane ni."

"Shiyasa na ga duk rame."

"Eh, sannan ci ma ba ɗaya ba."

Ya murmusa tare da lakace min hanci, cikin sigar zolaya ya ce "Mu je na maki wankan talauci..." Ya kama hannuna ya miƙar da ni, tare da sumbatar goshin yana kallon cikina da ya ɗan totso, sai na ga tsugunna ya sumbaci cikin yana faɗin "A na ci, ya na ce sai ya fito...

"Ba ka so? "

"Na faɗa? Ai yanzu ya yi ƙwarin da ban isa ba, kuma mai ina son yara yanzu."

Ni dama na sani, dama don yana da su Aira ne ya sa bai son haihuwar yanzu kam ai dole ya neme ta, a wani ɓangaren na ji sanyi sabida na fahimci baya Asiya, tunda ban ji ko alamun yayi maganar ta ba, kamar na mishi magana sai kuma na fasa, ya ɗauke ni cak muka shige bedroom ɗin, yayin da na iske shi tsab a gyare, dama Sufyan ɗina bai mai ƙazanta na ne.

Na shagwaɓe fuska "Yunwa na ke ji."

Ya fice da sauri sai gashi da takeaway da alamun shi yayo ya ci ya rage ko kuma bai ci ba, ya zaune gefen gadon ya soma bani a baki yana tambaya ta kalar rayuwar da nayi a gidan mu, sam ban ɓoye mashi komai ba, don nasan babu wani ɓoye ɓoye a rayuwar aure, ya dinga ke ta min dariya, wai dole na mare, na saba shan ice cream da pizza..


************

A gida kam ashe hankalin su ya yi masifar tashi, ganin har taran dare babu ni babu dalilina, Maama ma kasa cin abincin dare ta yi, ta kalli Teemah a sanyaye tana faɗin "Wannan fa yarinyar bata da hankali, bata san zuru ba.."

Teemah ta taɓe baki ta ce "Dan Allah ki rabu da ita Maama, ai ta san inda ta bar mu, kuma ba yarinya ba ce."

"Kayya dai, abinda ta ke ko yarinyar ba zata yi ba.

"Dan Allah ki rabu da ita Maama, ki yi ƙwanciyar ki." Teemah ta faɗa cikin halin ko in kula

Maama ta riƙo hannun Teemah a sanyaye ta tsare ta da ido tana faɗin "Ni Uwa ce Fatima, ba zan iya bacci ba tare da na san ba inda ƴata take ba.."

"Amma fa kina gani sai da kika ce kar ta fita ta fita, sannan sabida bakin hali ta ɗauke kuɗin islamiyyar mutane da wayar Baaba don ta yi kuɗin mota, ba tare da ta yi tunanin halin da zata bar mu ba.."

"Ko da kafin ta fita ta zage ni, ta dake ni, Fatima ba zan iya runtsawa ba tare da na san inda ta ke ba.."

Ƙura mata ido Teemah ta yi, yayin da ƙauna da tausayin ta suka ƙara yawaita a zuciyar ta, gaskiya ta faɗa ita UWA ce, mai ƙarɓar ƴaƴan ta a cikin kowanne hali, sai ga hawayen tausayin Maama na zuba daga ƙwayar idon ta, sam bata fata ta yi ko ɗaya a cikin goman abinda Nafeesa ta ma uwa ta, kuma tana fata ta dawwama tare da ita, da dai ta auri mijin da bai san darajar iyayen ta.

A sanyaye ta ƙara danƙe hannu Maama ta ce "Maama yanzu ya zaayi?"

"Tunda wayar ta bata shiga ki kira Fannata don na san dole ta je ta raka ta."

Teemah ta yi dialing number Fannata, sai dai har ta ƙaraci ringing ɗinta bata ɗauka ba, ƙarshe ma alamu ya bata an saka ta black list.

"Maama busy, kuma ba waya ta ke ba."

"Mu je gidansu.." Ta miƙe jikinta na rawa.

Teemah ta maida ta ta zaunar tana faɗin "Dan Allah ki bari in je."

Da ƙyar Maama ta yadda ta ta fi ita kaɗai bayan ta mata kashedin a kula sosai.

A lokacin da Teemah ta isa gidan jikinta ya yi sanyi ganin irin tarbar da Fannata ta mata, don bata taɓa mata irin ta ba.

"Ai mun ɗauka tare da Yaya kuka tafi." Teemah ta faɗa a sanyaye bayan Maama su ta basu guri.

"Eh, amma tun a tasha muka rabu, rabuwar da nike fata ta har abada."

Teemah ta dafe kai "Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un, dan Allah me ta miki Yaya Fannata."

"Wulaƙanci Teemah, wanda ban taɓa zaton ko mahaukaci zai min shi ba.." Hawaye suka ɓalle mata.

Ita kanta Teemah sai samun kanta ta yi tana kuka tare da rungume Fannata tana faɗin "Shine dalilin da yasa kika canza min Yaya Fannata? Ashe dama idan babu Yaya ba zaki taɓa ɗauka ta ƙanwar ki ba? Ashe baki ɗauki Mama yadda ta ɗauke ki ba? Dan Allah ki yi haƙuri ki yafe mata, muma haka muke haƙuri da ita..

"Ku Allah ya ɗaurawa haƙuri da ita Fatima amma ba ni ba..."

"Na yarda, ki rabu da ita har abada amma kar ki rabu da Maman mu, ta ɗauke ki tamkar ƴarta kamar yadda na ɗauke ki tamkar ƴar uwa, dan Allah ki yi haƙuri yaya Fannata.."

Jikin ta ya yi masifar sanyi, tabbas bai kamata laifin Nafee ya shafi ahalin ta ba, domin sun mata abinda har abada ba zata taɓa mantawa ba.

Ta share ƙwallan ta tare da ɗago fuskar Teemah ta ce "Ya wuce Teemah. "

"Nagode Yaya Fannata."

Teemah ta miƙe ta masu banƙwana, har ta kai ƙofa Maaman su Fannata ta ƙwala mata kira "Ki faɗa ma Maamar ku gobe zaa kawo kayan sa ranar Fannata insha Allahu."

Teemah ta waro ido cike da farin ciki sannan ta juya ta kalli Fannata da ta sadda kai cike da kunya ta ce "Da bata faɗa mun ba, kenan ba zaki faɗa mun ba Yaya Fannata."

Fannata ta watsa mata hararae wasa ta ce "Wuce ki tafi dare na ƙara yi, idan kuma anan zaki ƙwana to."

Ta juya cike da annashuwa har ga Allah ta yi matuƙar farin ciki da zaa kawo kayan auren Fannata, ko babu komai zata huta da gorin Nafeesa, ta murmusa Allah kenan, ɗazu an mata wulaƙanci gobe zaa sa mata rana ta ɗaga hannu sama tana faɗin ," Ya Rahman, Ya Allah ka bawa Yaya Fannata mijin da ya fi Sufyan ɗin Yaya Nafee tausayi, imani, soyayya, daraja, da wadatar zuciya, Allah ya bata mai arziƙi da ya san darajar ta da iyayen ta, mai tarin ilmin addini .."

"Amin Ƙanwata.." Fannata ta faɗa lokacin da ta biyo bayanta don ta ga yadda zata samu abin hawa ba tare da ita Teemah ta sani ba, sai ta iske wannan daddaɗar addu'ar da ta yaye mata baƙin cikin ta..

"Ashe kina bayana.."

Fannata ta gyaɗa kai sannan ta kama hannun ta tana daɗin "Na biyo in ga kin samu abin hawa ba tare da kin sani ba, sai kuma na ci karo da mutuntaka...

Sai da ta raka ta har ta samu abin hawa sannan ta juyi, ita kam Teemah bayan ta isa gida ta faɗa ma Maama Nafeesa bata can, hankalin ta ya ƙara tashi, ta kira wayar Sufyan a kashe, ai kam ta ce ta tashi su je gidan shi ta san dai yanzu yana can, alabashshi ya kira gidan na su ya tabbatar da Nafeesa na can, hakan ne kaɗai ƙwanciyar hankali ta, ta san idan ta tura Teemah kaɗai da matsala, sannan tana tsoron Baaba ya je, Sufyan ɗin ya mishi abinda ba zai iya ɗauka ba.

"Maama gidan Sufyan fa."

"Eh...c

Teemah ba ta de komai ba, Maaman ta hijabi suka kai Auta maƙwabta, sannan suka kama hanya bayan ta kira Baaba ta sanar da shi halin da ake ciki..


#UWAR SUKUM
[6/7, 9:42 PM] RN Feedohm: 💧💧 *KUSKUREN SO.*

FREE BOOK

*HASKE WRITER'S ASSO.*

   *FEEDOHM*
Wattpad@Feedohm

  _Ga ba ɗaya littafin nan sadaukarwa ne ga NAFEESA Muhammad SULE, maman jinjiri, Alherin Allah ya kai maki a duk inda kike._

*035*

Sun kusa minti ashirin a bakin gate ɗin suna bugawa, amma baa buɗe ba, kuma gashi alamu sun nuna aƙwai mutun a ciki, tunda ta ciki aka kulle ƙofar.

"Ko dai baya nan?" Maama ta faɗa a sanyaye.

Kafin Teemah ta bata amsa ya fito cikin ɗaga murya da alamun harzuƙa a tare dashi yana tambayar "Waye cikin wannan daren sabida rashin hankali ya ke buga min gida sai kace ya bayar da bashi?"

Ya buɗe ƙofar da ƙarfi yana huci, ganin su Maaman bai wa ya sassauta haushin shi ba, sai ma tanƙe fuska da sake yi yana faɗin "Su Maama ne a wannan tsohon daren? Ina wuni? Lafiya kuwa? Me ke tafe daku?" Ya riƙe ƙofar gam kamar sun ce ya basu guri zasu shiga.

Teemah ta yi karaf ta ce "Yaya ce bata dawo gida ba, kuma ta ce gidan ku zata je."

"To sai aka yi yaya?" Ya maka mata hararar tsana.

Mamaa ta haɗiyi wani ƙololon baƙin ciki ta ce "Zuwa muka yi mu roƙi arziki ko zaka kira gidan naku ka tabbatar da tana can ɗin, yadda hankalin mu zai ƙwanta, sabida wayar ta bata shiga, kai ma taka shiru, bare daga can mu roƙi alfarmar number su Umman."

Ya kalle su sheƙeƙe sannan ya ce "To ina zuwa.. " Ya maida ƙofar ya rufe gam suna waje, yayin da Teemah ta kai wuya ta yi ƙwafa tana faɗin "Ko uban wa ya ce mashi dama shiga zamu yi.?"

"Bani son sakarci." Maama ta ƙwaɓe ta.

Bata kuma cewa komai ba, sai ƴan ƙananan hawayen da suka biyo fuskar ta, suka yi tsaye cirko cirko kamar waɗanda ke jiran gawa.

Sufyan na shiga ya iske ni gaban madubi ina shafe jikina da turaruka masu sanyayyen ƙamshi, wanda rabon da na shaƙi ƙamshin su tun ranar da muka yi wannan baƙar tafiyar, na lumshe ina sunsunar hamatata, shi fa gidan miji daɗi gare shi wallahi, ya rungume ni ta baya yana shinshinar wuyana, ya ciji kunnena sannan ya raɗa mun "An zo bikon ki."

Wallahi sai da na ji gabana ya faɗi, na dafe ƙirji ina tambayar "Ni? Su waye dan Allah.?

Ƴar dariya ya yi mai sauti sannan ya ce "Su Maman ku da mara kunyar ƙanwar ki, wallahi da ita kaɗai ce da tuni na karya mata ƙafar dama..

Na dafe ƙirjina yayin da na ji wani ɗaci ya gauraye tun daga cikin ƙirjina har zuwa baki na wato ba zaa barni na huta ba? cikin ƙunar zuci na ce "Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un, wai da gaske.?"

Ya tuntsure da dariya "Wai wannan firgicin na me ye?"

Na shagwaɓe fuska na ce "Ni dai dan Allah idan wasa kake min bana so."

"Allah, wai sun zo su tabbatar da gidan mu kika je, ko wani gurin kika yi."

"Wato sai ka ce mai yawon banza ko?" Na faɗa kamar zan fashe da kuka, don har ga Allah raina ya ɓaci, banda salon su ɓata min suna ta ya zasu yi tunanin ba can na je ba? To dan Allah ina zan je?

Na yayibi hijabi na fita ina kumfar baki, har na kai ƙofa na dawo na ce " Sweetie ka na da 50k dan Allah?" Na san dai zasu iya mun maganar kuɗin su, ƙara kawai tun kafin su tambaya na basu, don suna iya ɓatan suna a gaban shi, ni kam Allah ya sani ba sata na yi ba.

"Yeah." Ya faɗa sannan ya manna mun kiss, ya shige bedroom ɗin mu da murmushin da na kasa gane dalilin shi, sai gashi da rapper 500 guda ɗaya, ya miƙa mun, yayin da na yi gaba ina surutai ƙasa ƙasa, wato dai na baro gidan nasu amma ba zasu barni na sarara ba ko? Na ja tsaki, ina zuwa na buɗe ƙofar a fusace don so ni ke na tabbatar masu da ban ji daɗin zuwan su na, ban sani ba ko tsorata suka yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login