Showing 63001 words to 66000 words out of 83936 words

Chapter 22 - KUSKUREN SO Book Complete by Feedohm.txt

Feedoms   

21 Sep 2025

1699

Asiya?Ni ce fa Nafeesa.....

Ya saki wani ja'irin murmushi ko gezau babu a fuskar shi, ya dafa hannuna da ke bisa ƙirjin shi yana faɗin "Nafeesata... Bara na miki dalla dalla, ina matuƙar son ki Nafeesa, amma ba zan yadda na haifi yaran da basu taɓa yafe mun ba har abada, yaran da kullun suka kalle ni sai sun ji takaicin kasancewata mahaifin su, ki sani yanzu duk yaron da aka haifa da sikila laifin iyayen shi ne, kuma zasu san da haka, sabida lokacin bamu sani ba ya wuce, sannan ba zan yadda na zauna da ke ba tare da na samu zuriya ba, Alhalin Allah ya bani yadda zan same ta, Nafeesa ina son haihuwa sabida bana da masu min addu'a yanzu, Allah ya karbi abin shi, kuma lafiyayyu yara nake so waɗanda zasu yi alfahari da ni, ba waɗanda zasu wahala ba, Nafeesa idan duk baki yadda da wannan ba, na baki zaɓin rabuwa, babu tilas a ciki."

Hawaye ya ɓalle min, na ƙura mishi ido cikin rawar murya na ce "Amma duk baka san da wannan ba sai yanzu Sufyan? Me yasa tun ina budurwa baka min wannan karatun ba? Me yasa sai yanzu da ka mayar da ni ƙaramar zawara? Me yasa sai yanzu da ka tabbatar da bazan iya rayuwa babu kai ba?"

Kai tsaye ya ce "Sabida nima ba'a ce min za'a karɓe su Aira."

Na girgiza kai "Amma ka bani mamaki Sufyan ka bani mamaki wallahi."

"Shiyasa na baki zaɓi biyu Nafeesa, kina da lokacin da zaki yi shawara da duk wanda kike so.."

Ya fice daga ɗakin, yayin da na zube ƙasa na soma rairai kuka, wallahi ko a mafarki ban taɓa zaton Sufyan zai faɗi haka ba, ban taɓa tunanin zai iya rabuwa da ni ba, anya kuwa ba asirin aka mishi ba? Anya ya kamata na miƙe kafa na zauna? Ina! Nima ina buƙatar shiga inda Asiya ta je, nima ina buƙatar mijina, wallahi ba zan iya rayuwa babu shi ba, dole na karkato da hankalin shi, ko ta wacce hanya ce.

Har magrib babu Sufyan babu dalilin shi, yayin da kunci ya zamana aminina, sam na kasa samo madogara, ban san gidan malan bare boka, bare har na kai can, gashi banda wani abokin shawara, ban da wanda zai lallashe ni, sabida har lokacin ɗakin ni kadaice babu wanda zai zauna bare ya taya ni jimami.

Abun duniya ya ishe ni, shegen kukan ma ya tsaya cak, gashi wani mulmulallen abu ya tokare min maƙogwaro mai ɗacin gaske, wayar Maama na sake kira a karo na babu adadi, cikin sa'a ta dauka, da ƙyar na ce "Tun ɗazu nake kiran ku shiru."

"Eh ban lura ba." Ta bani amsa kamar bata so.

Na lumshe idona "Ina asibiti an ƙwantar da ni Maama."

"Allah ya sawaƙe."

"Dan Allah ku taho mun da ruwan zafi, nan ne teaching hospital, ɗakin haihuwa."

Ban yi zato ba sai ji na yi tana faɗin "Allah ya bada lafiya, sai ku siya anan kam."

A firgice na ce "Ban gane ba? Me zamu siya?"

"Ruwan mana, anan kam bana tunanin zaa samu mai zuwa." Ta bani amsa cikin halin ko in kula.

"Wallahi ni kaɗai ce bani da mai jinya, kuma da alama sai na kai gobe, dan Allah ku taho."

Maama ta ce "Ina Sufyan ɗin?"

"Ya fita, shi ya ce in kira gida wani ya zo."

Ina jin sautin murmushin ta sannan ta ce "Gaskiya anan kam baki da mai zuwa Nafeesa, sai dai ko can gidan su ya ke nufi."

Cikin tashin hankali na soma salati "Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un, wallahi nan ya ke nufi Maama, wa na ke dashi a gidan su da zai zo jinyata, ko da kirana babu wanda ya yi fa, kuma sun san banda lafiya, ni dai dan Allah ki taho Maama."

"Ikon Allah, Nafeesa na zo na ɓata muku aure? Ki dai kira su Umman shi."

Wani kuka ya taho min, na hau mata magiya "Dan girman Allah Maama ki yi haƙuri ki zo, wallahi ni kaɗai ce, duk duniya banda wanda zai zauna min sama da ke, dan Allah ku rufa min asiri na tuba na bi ku ba, dan Allah ki taho, idan ma ba zaki zo ba, ko ƙanwata Teemah ki turo."

Ai ban ma kai aya ba, ta yanke wayar ta, na bi wayar da kallo hannuna na rawa, yayin da komai na duniyar ya dagule mun, cikin rawar jiki na ƙara kiran wayar amma sai na ji ta ma switch off, na kira Teemah shima a kashe,  sai ga hawaye na bin kumatuna, na ji komai na duniyar ya ƙwance min, na ɗaga labule na ga yadda iyalan marasa lafiya suke yawo a harabar asibitin, wasu fa har da tabarmi aka shinfiɗa, wannan ya zo wannan ya tafi, ga ƙwanukan abinci kala kala, jikina ya cigaba da rawa, na sa hannu na share zufar da take min, Allah na ya taimake ni ɗakina daban da ace cikin mutane ni ke da ban san yadda zan yi ba.

Na kai hannu hawaye na bin kumatuna na ɗauko ayabar da ya kawo min ɗazu, wallahi har na gaji da cin fruit, abincin da ya kawo min bana buƙatar shi, kunu na ke so ko ruwa mai zafi, sannan ina buƙatar wanda zai lallashe ni na ci, na fashe da kukan takaici, sai ka ce bana da kowa? Sai ka ce marainiya? Ai ko wanne irin laifi na masu bai kamata su barni ni kaɗai ba.

Ina zaune har 10pm daga ni sai halina, sai kuma damuwa da takaici da ta zamana aminiya ta, na kai hannu na janyo wayata na kira number Sufyan, yayin da na ji shi waiting, wallahi sai da gabana ya yi mummunar faɗuwa, ko baa faɗa min ba na san da Asiya ya ke waya, nan da nan hawaye suka ɓalle min, na soma ɗauke su da hannu, bayan minti goma na sake kira, still dai waiting na ji ta "Na shiga uku.." Na furta tare da dafe kaina da hannu ɗaya ina jin wani irin jiri na ɗibata.

Bayan minti ashirin sai ga kiran shi, jikina har rawa ya ke gurin ɗaukar wayar "Da wa kake magana?"

"Bangane ba?"

Cikin kuka na ce "Ai na kira ka waiting da wa kake waya Sufyan.?"

Cikin halin ko in kula a muryar shi ya ce "Wani abu ne?"

"Ina so na sani?"

"Sabida ke ce wa?" Ya furta a tausashe.

Wata irin bugawa zuciyata ta yi, na dafe ƙarfen gadon da hannu ɗaya ina faɗin "Sufyan? Ni?"

"Yeah, a yanzu ban san status ɗin ki ba Nafeesa, because baki yanke shawara ba, kin ga kam dole na tambaye ki a wane matsayi kike min waɗannan tambayoyi.."

Wani kuka ya kubce min, na kifa kaina a cinyoyina da wayar a kunne na, na kusa minti biyar ina rera shi, ba tare da ya yanke wayar ba, kafin na ji yaja numfashi, cikin narkakkar muryar shi ya ce "Komai yana hannun ki Nafeesata, ke ce zaki yanke mu yi rayuwa tare ko akasin haka, ke ce ke da alhakin raba zukatan da suke mallakin juna ne, ke ce mai alhakin watsa farin cikin zukatan mu..

"Ta yaya Sufyan.?"

Cikin wani irin salo ya kira sunana "Nafeesata.........ba zaki iya sadaukar da mahaifar ki, domin farantawa mijin ki? Shin zaki zaɓi zama cikin ƙunci fiye da zama cikin farin ciki.

"Wane farin ciki Sufyan? Bayan ko da na yadda da cire mahaifar ba dani kaɗai zaka zauna ba."

"Wa ya faɗa miki, ke ce kaɗai a zuciyata Nafeesa, wallahi ba zan iya haɗa matsayin ki da na wata ba, ki yadda dani, ko da na maido Asiya wallahi tallahi zuciyata na tare da ke, zan maido ta sabida ta haifa mana yara Nafeesa, idan kin so zaki iya ɗaukar ta a matsayin mai raino..

Na lumshe idona ina auna kalaman shi a sikeli, anya na yadda da shi kuwa? Ya katse ni "Ki yadda dani Nafeesa...

Ban san lokacin da na ce "Ka yi alƙwarin ba zaka taɓa juya min baya ba?"

"Na miki alƙawari Nafeesata..."

Na lumshe idona har ga Allah ina jin tamkar KUSKUREN SO na yi, sai dai ya zan yi, ina son shi, ina buƙatar rayuwa da shi, ina so mu rayu har abada a tare, ciki sanyi da kasala na furta "Na amince..."

"Kin amince ki tsayar da haihuwa?"

"Eh..."

Ya saki ihun farin ciki yana faɗin "That My love, I Love You Nafeesa, I really love you.."

Na aje wayar ba tare da na bashi amsa ba, ina jin wata irin fargaba da ɗaci a raina, ban san ya zan yi rayuwa babu ɗiya ba, Alhalin shi ina ganin shi tare da na shi, na lumshe idona tare da ƙwanciya na yi rigingine ina kallon ceiliing, sai na ke jin tamkar tun farko ba yi KUSKUREN SO ne, na lashi laɓɓana lokacin da wata zuciyata ke tunar min ban yi KUSKUREN SON Sufyan ba, domin shima yana sona kuma zai iya sadaukar da fiye da abinda na sadaukar akan shi! Wata zuciyar ta tambaye ni, to don me ba zai iya haƙura da haihuwa ba kamar yadda na haƙura da ita?

Sabida shi namiji ne, yana da iko akan ƴaƴan da ya haifa, zai iya karɓe su a hannun Asiya idan ta haifa ya maishe su hannuna, Ya Isa.....! Amma ni ko da na yi wani auren ba zan iya amso ɗiyan ba...! Wata zuciyar ta tunatar da ni, dan haka na lumshe idona...


#UWAR SUKUM.
[6/13, 9:14 PM] RN Feedohm: 💧💧 *KUSKUREN SO.*

FREE BOOK

*HASKE WRITER'S ASSO.*

   *FEEDOHM*
Wattpad@Feedohm


  _Ga ba ɗaya littafin nan sadaukarwa ne ga NAFEESA Muhammad SULE, maman jinjiri, Alherin Allah ya kai maki a duk inda kike._

_Ina kike Aunty Zainab Abubakar Kotorkoshi? Ke ma ina maki fatan alheri._


*038*


Har 12am babu Sufyan babu dalilin shi, na kifa kaina a filo ina kuka ƙasa ƙasa, na yi zaton amincewa zata saka ya zo gare ni a ɗimauce, na yi zaton girman sadaukarwa ta zaya sa ya ƙwana tare da ni yana shi mun albarka, na yi zaton abinda na yi zai sa wannan daren ya zama farin dare gare mu baki ɗaya, sai dai kamar ba haka ba, kamar baƙaƙen dararen da suka shuɗe a gidan mu, na sa babban yatsana na share hawayen da suka gangaro gefen kunnuwana, yayin da na ƙurawa globe ɗin ɗakin ido, ni kaɗai ƙwal kamar mayya, shigowar nurse ce ta sa na maida hankalina gare ta, na yunƙura na miƙe da ƙyar ina aika mata da murmushin yaƙe, sabida ɗazu har da ita wajen bani kulawa, ta kalle ni cike da tausayi tana tambayar "Hala ba ƴar garin ba ce ke?"

Na saki murmushin yaƙe "Me kika gani?"

Ta ƙarewa ɗakin kallo sannan ta ce "Bana tunanin tunda aka kawo ki wani ya leƙo ki, idan ba mijin ki ba, sai kuma na yi tunanin ke ko ba ƴar garin ba ce ai baƙya rasa abokan arziƙi ba."

Wasu hawaye suka zubo min, na ja majina a raunane na ce "Ba ƴar garin ba ce." To na isa na faɗa mata uwata da ubana duka suna zaune a garin ne?

"Ayya, Allah sarki."

Na maida kaina ƙasa ina wasa da hannuna, ta katse ni "Da alama ke kaɗai zaki ƙwana."

"A'a, mijina zai zo." Na bata amsa cikin rashin ƙwarin guiwa, domin bana da tabbacin zuwan na shi ko akasin haka.

Bata ce min komai ba, ta min abinda ya kawo ta sannan ta juya ta fita, yayin da ta barni da tunani, anya na ma kaina adalci ace zan ƙwana asibiti babu uwata bare ƴar uwata? Laifina ne ko na su? Idan har na wa ne to ni kam wane irin laifi na masu da har na cancanci wannan wulaƙanci? Na saki murmushin takaici.

Ganin da gaske fa ni kaɗai zan ƙwana ya sa na kira wayar Sufyan, wannan karon ma wayar ya ke, sai dai kirana ya shiga yana katse wancen ya ɗauka yana faɗin "Sweetie kin jini shiru ko?"

"Uhmmm."Na faɗa zuciyata na azalzala da son sanin da waye ya ke waya a daidai wannan lokacin, sai dai bai bani damar tambaya ba.

Ya tausasa murya yana faɗin "Dan Allah ki yi haƙuri kin ji ko, tun da muka gama waya na taho amma ƴan road safety suka kama ni, wai takardun motata ce sun yi expire tun last year, kawai dai kuɗi suke so na basu, kuma ba zan bayar ba ko da zamu ƙwana anan, kin san ƙasar ta ɓaci da corruption, kuma ina ta kiran friend ɗina dake aiki dasu wayar shi a rufe dare ya yi."

Na lumshe idona, dama na san sai dai idan wani uzuri ya zo mishi, amma ba zai iya wofitar dani ba wallahi, na lashe laɓɓana ina faɗin "To ka basu mana. "

"Kin yadda mijin ki ya bayar da cin hanci.?"

Na lumshe idona, kafin na ce wani abu ya cigaba da faɗin "Kar ki damu, ina tare dake kin ji ko? Insha Allahu da sun sallame ni zaki ganni komai dare, idan kuma kika ji shiru kar ki damu kin ji ko, ina lafiya, sai dai ke ki kula min da ke, insha Allahu da safe da wayar shi ta shiga zasu rabu dani, i missed and love you alot, please take good care of your self my love..... "

Na ciji laɓɓana na ce "And you.."

"Insha Allahu, muahhhhhh"

Ya kashe wayar, yayin da na ji raina wasai, har na samu na ƙwanta, to mai zai dame ni, yana sona, yana ƙauna ta, and hes ready to sacrifice anything for me, yaran da ya ke faɗa masu lafiya, don ni ya ke yi, because na tabbata da ta haihu zai iya amshe su hannun ta ya maido su gare ni, baya son ta, sai na ga babu amfanin bin bokan ma, su kuma ƴan gidan mu da ba su zo ba, kawai su je don kan su, ai ban ma san lokacin da bacci ya yi awon gaba da ni ba.

***********************

"Na kasa bacci Fatima...." Maama ta faɗa a sanyaye.

"Me yasa Maama? Yaya ko? Ko in tafi?"

Maama ta girgiza kai a sanyaye tare da ɗauke hawayen da su ka biyo mata a kumatu tana faɗin "Barta Fatima, idan har zata cigaba da yin abu muna yafe mata nan da nan ba zata taɓa hankali ba."

Teemah ta ƙura mata ido tana faɗin "Kina nufin baki yafe mata ba Maama? Kina nufin har yanzu fushi kike da ƴar ki?"

Ta saki murmushin yaƙe "Ni fa uwa ce Fatima , ta ya zan riƙe ƴata a zuciya da fushinta har tsawon minti ɗaya? Bayan na san ba ni ke da rayuwata ba? Bayan na san kowanne lokaci Allah na iya karɓar rayuwata, ba zan so na mutu da fushin ɗaya daga cikin ku ba, Alhalin na san irin mummunan hukuncin da Allah ya tanadar wa wanda iyayen shi suka rasu da fushi shi....

Teemah ta ƙura mata ido hawaye na bin kumatun ta, har ga Allah tana son mahaifiyar ta fiye da zato, domin samun irinta sai an tona, ta kamo hannun Maama tana faɗin "Mungode Allah, dan Allah ki ƙara haƙuri, aƙwai lokacin da Yaya zata gane girman kuskuren da ta aikata...

"Allah ya nuna min.."

Teemah ta amsa da "Amin."

Shiru suka yi na ƴan mintuna, sannan Teemah ta katse shirun ta hanyar faɗin "Wai Maama kin ga gidan Yaya Fannata kuwa?"

Maama ta girgiza mata kai da ɗan ƙaramin murmushi a fuskar ta tana kallon ta.

"Wallahi ya haɗu Maama, aljannar duniya kenan, kin san ya fi na Yaya Nafeesa sai goma? Gashi mijinta mai shegen mutunci, shi fa ya kawo mana drinks da muka shiga Yaya Fannata na wanka.."

"Shegen mutunci Fatima.."

Teemah ta dafe baki "Astagfurillah, musulmin mutunci Maama, wallahi ta yi dace."

Maama ta murmusa "Allah ubangiji ya basu zaman lafiya, ya ci da ƴan baya."

Teemah bata amsa amin ɗin ba, sai ta sunne kai ta ce "Yauwa, dama Najib ya ce in faɗa maku wai dan Allah zai turo..."

Maama ta zuba mata ido "Har ya dawo?"

"Uhm, ai course ɗin na 18month ne.."

"To ki bari in yi magana da Baaban ku tukun."

*************************

Ban farka ba sai da nurse ta shigo, na kalle ta a tausashe ina tambayar "Ya fita ne?"

"Wa?"

Kai tsaye na ce "Wanda ke zaune kusa dani mana." Don na tabbatar Sufyan ya zo.

Ta taɓe baki "Ban gani ba.."

Nima bakin na taɓe mata, da ya ke ba ta jiya ba ce, wannan kam babu alamun mutunci a tattare da ita, kuma ta je don kanta, nima ba mutuncin ba ne da ni.

Na kai hannu na taɓa flask na ruwan zafi na ji wayan babu, gashi bana son saka ma kaina ruwan zafi, na maka mata harara ƙasa ƙasa ba tare da ta gani ba na ce "Dan Allah zan samu ruwan zafi?"

Ta mun banza ta fice, na bita da harara, ba don na so ba haka na shiga toilet na sawa kaina ruwan sanyi, na fito, na zauna gefen gado ina goge fuskata da hanky, kafin na ɗaga labulen ɗakin ina bin waje da kallo, hopely na ga Sufyan wata ƙyil ya fita samo mana breakfast, amma ko mai kalar shi ban gani ba, don haka na sauke labulen a sanyaye ina jin ɗaci a zuciyata, sai kuma na soma tunanin ko dai ba lafiya ba? Ko dai sun tafar min da miji, gabana yayi mummunar faɗuwa, ina ƙoƙarin ɗaukar wayata na kira shi sai ga nurse din ta dawo da doctor, muka gaisa fuskar shi ɗauke da murmushi, sannan ya sanar min sun yi waya da Sufyan ya ce mun yanke shawarar ai tsayar min da haihuwa baki ɗaya, shin da amincewa ta? Na gyaɗa mishi kai don har ga Allah hankali ma baa gurin su ya ke ba, ya sake nanata min shin na amince? Na ce mishi eh.

"Kina ganin hukuncin ki daidai ne?" Ya kuma tambaya ta kamar irin bai gamsu ba.

Na maido ƙwayar idona bisa fuskar shi, yayin da dada ɗan kalaman Sufyan ke yawo a ƙwalwa ta, ban san lokacin da na ce "Na ce maka eh, na amince menene na maimaita magana doctor?"

"Bana so ki yi abinda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login