Showing 15001 words to 18000 words out of 83936 words
da kama hannuna da hannun shi guda, ɗayan hannun kuma ya dafe marata, yana jera mun sannu.
Tun ina jin ciwon marar nan kaɗan kaɗan har ya soma fin ƙarfina, na soma kuka kamar raina zai fita, don wallahi tunda ni ke ban taɓa ciwon mara mai tsananin wannan ba, gashi shiru shiru babu Dr AA babu dalilin shi, cikin kuka na ce "Dan Allah ka kaini asibiti, mutuwa zan yi Sufyan, kar mu tsaya jiran wani Doctor."
Cikin tashin hankali ya ce "Ki yi haƙuri Nafee, yana hanya insha Allahu yanzu zai zo, ko mun je asibitin ba zaki samu kulawar da zai ba ki ba, insha Allahu ba zaki mutu ba, babu abinda zai same ki, ina tare da ke, dan Allah ki daina kukan nan.."
💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
Ina kuke? Ina kuke?
Ku matso kusa dan Allah, shin kin san mun shirya tsab domin NISHAƊANTAR da ku a cikin wani ƙayataccen littafin mu? Kin san littafin gamayya ne na shahararrun marubutan da alƙalumman su suka yi shura? Kin karanta ƘADANGARUWA? ƘWAƊAYI fa? DUHU? ISHARA? RUƊANI fa? Na san ko ban faɗa ba kin canki marubutan.
SLIMZY
FEEDOHM.
TAGWAYE BIYU.
Hmmm, tafiyar daban take, hakan salon ma daban ya ke, Labarin Nadiya! Nadiya...... Labari ne da aka gina bisa halin mu na yau da kullun, ba kuma gama garin labari ba! NADIYA, matar aure, yayin da ƙaddara ta afka mata to soma soyayya da wani mutun daban, wanda ta ke jin inda babu shi, ba zata taɓa rayuwa ba, gefe guda kuma Sadeek, wanda ya mutu a kan ƙaunar ta kuma ƙani ga Alaji....!
Bai taɓa haihuwa ba! Hasali ba zai haihu ba! Kwatsam sai ga ciki daga matar shi? Shin ɗan waye? Hmmm m... Soyayya, tausayi, cin amana, duka a littafin DAMA ACE.....
Kin shirya?
Ki biya kuɗin ki domin tafiyar da ke, tafiya ce da zata jijjiga zukatan makaranta, Naira 500 9994468172 Access bank fiddausi musa tare da shaidar biya ta 08036953516 ko 07042277401.
Kuma kin san wani abin ɗaɗin, ba zamu dakata da posting RUƊANI da KUSKUREN SO ba, ko da ace saura basu samu ba, ina tabbatar maku da waɗanda suka biya zasu same shi.
#SLIMZY
#FEEDOHM
#DAMA ACE...
*******
UWAR SUKUM.
[5/17, 8:18 PM] RN Feedohm: 💧💧 *KUSKUREN SO.*
FREE BOOK
*HASKE WRITER'S ASSO.*
*FEEDOHM*
Wattpad@Feedohm
_Ga ba ɗaya littafin nan sadaukarwa ne ga NAFEESA Muhammad SULE, maman jinjiri, Alherin Allah ya kai maki a duk inda kike._
_Ina kike Aunty Zainab Abubakar Kotorkoshi? Ke ma ina maki fatan alheri._
*010*
Bamu je asibitin ba, haka ban kuma samu sauƙi ba, ina ƙwance ina nuƙu nuƙu har sai da Sufyan ya ga jini ya ɓalle mun, tukun ya ƙara ɗaukar wayar ya kira shi a karo na biyu.
Wannan karon Doctor AA bai wani ɗauki lokaci mai tsawo ba ya yi mashi waya ya ce yana bakin gate, kai tsaye kawai Sufyan yace shigo ciki.
Bayan ya ga halin da ni ke ciki, ya balbale Sufyan da faɗa "Ya kake haka? Sai ka ce mara ilmi? Haba da Allah me yasa tun farko ba ku tafi asibiti ba ko kuma ka kira ni in zo?"
Azabar ciwon da nike ciki bai hana na ɗaga ido ba da ƙyar na kalli Sufyan, ina fa jin kamar ɗazu ya ɗaga waya ya kira shi? Gashi yanzu kuma Doctor ɗin ya ce bai kira ba, kenan ɗazu wayar ƙarya ya yi? To akan me? Ko baya so na je asibitin ne? Marata ta ƙara hantsinawa, na cije laɓɓa tare da dafe ƙasan, ina jin lokacin da Sufyan ya karkace ya ce "Na kira wayar ai not rechargeable wallahi."
"Ok, network ne, amma ai da kun tafi asibiti tunda ka san morning na ke."
Daga haka ya buɗe wani ɗan ƙaramin box, ya ɗauko hand gloves ya saka a take ya shiga dubani, kafin ya ɗago ya tambayi Sufyan "Garin ya haka ta faru?"
"Me ya faru Doctor?"
"Ta samu miscarriage ne, kuma duk yadda na so tsaida shi bai yiyu ba, sabida kafin na zo ya fita sosai."
Sufyan ya dafe kai kamar ya fashe da kuka yana faɗin "Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un."
"Amma ya nuna kamar da ƙarfi aka fitar da shi? Ko ta sha wani abu ba tare da ta sani ba?" Doctor ya jeho mashi tambayar tare da kafe shi da ido.
Sufyan ya ɗago ya zuba min ido, yayin da annurin fuskar shi ya ɓace, ya maida kallon shi ga doctor yana faɗin "Bana tunanin haka."
"Ok, Allah ya sawaƙe."
Ya min allura ya rubuta magunguna sannan suka fita da Sufyan ɗin, ya raka shi ya dawo ya zo ya tsugunna kusa dani ya kamo hannuna yayin da na zuba mashi ido don pain ɗin ya ragu sosai sosai.
Sai da ya shafi goshina sannan ya ce min "Sannu."
Na yatsina fuska ba tare da na ce komai ba, sabida har ga Allah zargi ne fal a raina, abinda yayi yanzu na ƙin kira Doctor da kuma kaini asibiti sai na ji ina zargin shi da zubewar cikina, na buɗe baki da niyyar tambayar shi. Sai na tsinkaye shi yana faɗin "Me yasa kika zubar min da ciki?"
"Kamar ya?" Na zaro idanu waje.
"Kin fahimce ni Nafee, Abdoul ya ce an zubar da cikin ne ta ƙarfi da ya ji, ba fitar Allah ba, kin ga kam dole na tambaye ki."
Sai na ji raina ya dagule, na zuba mashi ido ina faɗin "Kenan ni ce na zubar dashi?"
"To wa? Daga ni sai ke cikin gidan nan, wa ye zai... Sai kuma yayi tsit yana kallona kamar yadda ni ke kallon shi, don abinda na yi niyyar tambayar shi ma ya fice a kaina.
Sai da ya sassauta murya sannan ya ce "Kin je gida Nafee? Babu abinda aka baki acan ki ka ci?" Na tsinkaye shi yana faɗa ciki ciki idon shi a kaina.
Hawaye na ji yana bin kuma tuna kenan yana zaton a gidan mu aka bani abinda zai zubar mashi da ciki?, na ɗauke kai daga kallon shi ba tare da na bashi amsa ba, sai na ji yana kuma faɗin "Shiyasa bana son fita ko'ina da wannan ƴan janye janyen, don wallahi na san sai dai ko acan kika ci wani abun, ko kuma wannan ƴar iskar Fannatar ta baki shawarar ki zubar tunda tana baƙin ciki kin yi aure kun barta."
"Ya isa haka nan Sufyan." Na faɗa can ƙasan maƙoshi.
"Bangane ya isa ba? Kenan kar na yi magana an zubar min da gudan jini na? Nafeesa anya ba ma da ra'ayin ki hakan ta faru ba? Ki ji tsoron Allah, wato kina tsoron ki haifi sikila shine kika nunan da fari kamar kina so don ki ji me zan faɗa, bayan na gwada hankalin ki na ce a zubar shine kika zubar da kan ki? Baki min adalci ba. "
Ni dai rufe idona na yi gam ina kukan, ban kuma bin ta kan shi ba, har ya gama ƴar surutan shi sannan ya miƙe kamar ba shi ba, ya kamani ya kaini toilet, inda ya cire min kayan da na ɓata, ya sa mun diaper a pant na saka, da ya ke tuni na daina aiki da pad, sabida diaper ɗin ya fi min daɗi.
Haka ya dawo falon ya goge kujerar fes, sannan ya gyara ko'ina ya haɗa min tea ya zo ya tallabo ni yana jera min sannun da kisses masu zafi, wai ba zai yi fushi da ni ba, ya fi so na akan babyn da na zubar, amma please na mashi alƙawarin ba zan kuma ba, ai kam nan da nan na mance da wani ɓacin rai, yayin da zuciyata ta wanke shi fess, na shiga tunanin abinda na sha cikin ya zube ba tare da na sani ba, maganar kuma bai kira Doctor AA ba, na samu katanga na katange mijina a zuciyata, inda na sa ma raina wani doctor ya kira daban ba wannan ba.
Washe gari na warware ras, babu wannan ciwon marar, sai dai zubar jini, har Mama ta turo Teemah ta taya ni hidimar gidan tunda ban jin daɗi, da ya ke su Teemah sun dawo hutun second term.
"Wai yaya me yasa kika yadda Yaya Fannah?"
Na kalle ta na ɗaure fuska ina faɗin "Ita ce ta faɗa maki na yarda ta?"
"Eh, jiya ta zo guda tana faɗa ma Mama."
Na ce "To ta je dan kan ta, amma wallahi kar ta kuma zuwa ta kai ƙarata."
Teemah ta taɓe baki ta ce "Hmm, to wani abin ta maki?"
Na sake tamke fuska na ce "Eh, zuwa take tana min ƴan maganganu shine Sufyan ya ce in rabu da ita."
"Tab, amma a gaishe ki, ke don namiji ya ce ki rabu da wacce kuka taso tun kuna ƙanana shine sai ki rabu da ita Yaya?"
Na dalla mata harara, wani sa'in fa Teema ta fini wayau wallahi, ban sani ba ko don ina ƴar fari ce, ta cigaba da faɗin "Ki Harare ni amma gaskiya na faɗa maki, wallahi a ƙawaye baki da kamar Yaya Fannata, ki tuna fa yadda idan kina ciwo take jigila da ke lokacin kuna school, san..
A hankali na ce "Dan Allah ya ishe ni, nima fa babu abinda zan iya yi Teemah, Sufyan ɗinnan dai ƙarƙashin shi na ke, dole na yi duk abinda ya ke so na bar wanda bai so..
"Kenan ko Mama ya ce ki rabu da ita sai..
Sallamar Sufyan ta katse mu, ya zubawa Teemah ido daga bakin ƙofa tare da ɗaure fuska yadda ka san bai san ta ba, Alhalin kafin muyi aure bai da mutuniya irin ta, sai na ji ɗar ina addu'ar Allah ya sa bai ji ta ba, duk da dai na san da ƙyar ne.
Ko a jikin ta, sai ta ɗan zamo daga kujera ta ce "Yaya ina wuni?"
Ba yabo ba fallasa ya ce "Lafiya."
Yadda ya amsa ya sa rai na ya sosu, na kalle ta ta wani taɓe baki tare da turo kallabinta gaba, dama fa Teemah ba dai tsiya ba, a hankali na ce "Baka gane ta ba? Teemah ce."
"And so?"
Teemah ta riƙe haɓa "Toooohhhh, and so...."
Na kalle ta na kalle shi, nima na ɗauke kai na cigaba da faɗin "Wai kam ina Senoir Hasana Tukur? Ta daina laƙume maki abinci."
"Yo ta ma isa, tunda aka mata repiting ta shiga tai tayin ta."
Sufyan ya gifta ya wuce, ko ɗakin bai kai ba ya soma ƙwala mun kira "Nafeesa, Nafeesa.
Kafin na amsa Teema ta ce "Baban ki na kira."
Na kalle ta cike da mamaki, ta wani waske, don haka na jefa mata uwar harara na ce "Ban san iskanci, yanzu na ci ubanki wallahi, kuma ki tashi ki bar min guda.
Ta yayibi jikka ta miƙe "Yanzu fa, wannan shegen kallon da ake min ai dole in tafi."
Na riƙe jikkar "Ke wasa ni ke, ba Mama tace ki ƙwana anan ba, babu inda zaki je, kin ga ɗaki can, ki je ki huta kafin na dawo, ni fa har kitso nake so ki man."
"Allah ya sa baban ki ya bari, don na ga baya maraba da baƙo."
Ina kuke makaranta?
💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
Ina kuke? Ina kuke?
Ku matso kusa dan Allah, shin kin san mun shirya tsab domin NISHAƊANTAR da ku a cikin wani ƙayataccen littafin mu? Kin san littafin gamayya ne na shahararrun marubutan da alƙalumman su suka yi shura? Kin karanta ƘADANGARUWA? ƘWAƊAYI fa? DUHU? ISHARA? RUƊANI fa? Na san ko ban faɗa ba kin canki marubutan.
SLIMZY
FEEDOHM.
TAGWAYE BIYU.
Hmmm, tafiyar daban take, hakan salon ma daban ya ke, Labarin Nadiya! Nadiya...... Labari ne da aka gina bisa halin mu na yau da kullun, ba kuma gama garin labari ba! NADIYA, matar aure, yayin da ƙaddara ta afka mata to soma soyayya da wani mutun daban, wanda ta ke jin inda babu shi, ba zata taɓa rayuwa ba, gefe guda kuma Sadeek, wanda ya mutu a kan ƙaunar ta kuma ƙani ga Alaji....!
Bai taɓa haihuwa ba! Hasali ba zai haihu ba! Kwatsam sai ga ciki daga matar shi? Shin ɗan waye? Hmmm m... Soyayya, tausayi, cin amana, duka a littafin DAMA ACE.....
Kin shirya?
Ki biya kuɗin ki domin tafiyar da ke, tafiya ce da zata jijjiga zukatan makaranta, Naira 500 9994468172 Access bank fiddausi musa tare da shaidar biya ta 08036953516 ko 07042277401.
Kuma kin san wani abin ɗaɗin, ba zamu dakata da posting RUƊANI da KUSKUREN SO ba, ko da ace saura basu samu ba, ina tabbatar maku da waɗanda suka biya zasu same shi.
#SLIMZY
#FEEDOHM
#DAMA ACE...
*******
*Uwar sukum.*
[5/17, 8:18 PM] RN Feedohm: 💧💧 *KUSKUREN SO.*
FREE BOOK
*HASKE WRITER'S ASSO.*
*FEEDOHM*
Wattpad@Feedohm
_Ga ba ɗaya littafin nan sadaukarwa ne ga NAFEESA Muhammad SULE, maman jinjiri, Alherin Allah ya kai maki a duk inda kike._
_Ina kike Aunty Zainab Abubakar Kotorkoshi? Ke ma ina maki fatan alheri._
*011*
Kallon ta na yi tare da sakin ƙwafa na maka mata harara, a cikin raina na maimaita Babana? Ban san yaushe Teema ta raina ni haka ba.
Na juya na shige bedroom ɗin, Inda na iske shi har ya shaƙa, don ina shiga ya soma masifa "Tun ɗazu nike kiran ki amma sai yanzu kika ga damar zuwa don kin raina min wayau? Nafee ƴar uwar ki ta fini?"
Na ƙarasa kusa dashi, na rungumo shi ina murmushin yaƙe, cikin kunnen shi na raɗa mashi "Allah ya baka haƙuri, bana jin aƙwai wanda ya fika Sugarty, kai fa aljanna ta ce." Na manna mashi kiss a ƙuncin shi na dama.
"Humm.." Ya zagaye ni da hannun shi, tare da janyo ƙuguna ya matse da jikin shi yana kallon ƙwayar idanuna cike da soyayyar shi.
Mun fi minti goma a haka, sannan ya ɗaga ni na zagaye ƙugun shi da ƙafafuna na zauna daram a jikin shi ina dariya ƙasa ƙasa, a hankali ya ce "I cant imagine my life without you Nafee."
"Same."
"Me kika aje min?" Ya ƙanne min ido guda.
"Komai aje ya ke Sugarty."
"Har ke?"
Na gyaɗa mashi kai ina aika mashi da lallausan kallon da na san yana kashe mashi jiki, yayin da ya yi kan gado dani ya ƙwantas, ya bi ya haye jikina sai dai bai ɗaura min nauyin shi ba, ya soma kissing lips ɗina har zuwa gefen wuyana, a cikin kunne na ya raɗa min "Ke nake buƙata."
Na saki dariya ina kallon shi, kafin ya ɗage min gira ɗaya ya tashi zaune, ya soma kiciniyar cire kayan shi, kamar na dakatar dashi sabida Teema da na san tana tsumaye na, sai kuma na ga kamar hakan bai dace ba, na gyara ƙwanciyata cikin siga ta jan hankali, alamun a ko da yaushe jire nake domin shi.
Daga fuskar shi na gane yadda ya ji daɗi, don wata wawar runguma da ya kai mani har sai da na saki ƴar ƙara, sannan muka cigaba da farantawa juna rai, ban kuma saurara ba har sai na tabbatar da na gamsar dashi iya ƙwarewa ta, sannan ya koma gefe yana ƙwarara min addu'a.
"Me aka sha?" Na tsinkaye shi yana tambaya cikin sigar zaulaya.
Na kalle shi sama da ƙasa na dunƙule gira ɗaya haɗe da gyaɗa kai sama alamun ƙarin bayani.
Ya kuwa birkita ya karkace yana faɗin "Komai ya ji, how could i put it? Kin san agwaluma?"
Na gyaɗa kai har lokacin ina idona na kan shi, ya wani lumshe ido sannan ya ce "Kamar agwaluma a gurin mata." Ya nuna ƙasana haɗe da ɗaga gira biyu.
Dukan wasa na kai mashi ya kauce yana dariya, na tashi na shige toilet na yo wanka tukun na dawo har lokacin yana ƙwance, ban yi zato ba ya fizgo min towel yana faɗin "Zo na ƙara."
Na amshe towel ɗin lokacin har ya bar jikina, na kai mashi doka ina dariya don na san da wasa ya ke, ya kuma miƙe ya shige toilet shima ya wanko jikin shi, ya dawo ya iske har na zura doguwar riga ina ƙoƙarin fita bedroom ɗin.
"Sai ina? Bara ki jira mu fita tare ba." Ya dakatar dani.
"Zan ɗan fita kar Teema ta ji shiru, ka sa na manta da ita."
Yanayin fuskar shi ya canza, yadda kasan bai taɓa dariya ba, babu yabo ba fallasa ya ce "Bata tafi ba dama?"
Mamakin sauyawar shi ya kama ni, na daure na ce "Yanzu fa ta shigo, don ba ta daɗe ba ka dawo, kuma mama ta turo ta ta taimaka min da ƴan aikace aikace kafin na warware."
Ya dafe kai yana faɗin "Wai har kin faɗa masu Nafeesa? Don masifa har kin sanar da su baƙya lafiya?"
Na gyaɗa kai ina cije laɓɓana.
A zafafe ya ce "Ohhh, me yasa dan Allah? Meyasa baki da sirri? Komai sai kin faɗa a gida? Me ye haka Nafee?"
"Sufyan idan na faɗa ma mamana banda lafiya laifi ne?"
"Ni banda maman? Meyasa bana faɗa mata?" Ya ƙarashe maganar cikin ɗaga murya.
Rai ya dagule, na jefa mashi wani banzan kallo ina faɗin "Kai ka ji zaka iya Sufyan, amma ni duk abinda ya same ni sai na faɗa ma Mamata, kuma ai ba sirrin gidan ka na ɗauka na faɗa ba, ban kuma sanar mata cikine ya zube ba.."
"Haka kika ce?"
Na ɗauke kai sama ina ƙoƙarin maida hawayen da ke niyyar zubo min.
Ya tako har ina iya jin hucin lumfashi shi, cikin kunnena ya raɗa min "To bara ki ji, ban yadda ba wallahi, ban yadda ki riƙa ƙwashe matsalata ba kina kaiwa wani guri, idan kuma kika sake duk abinda na maki ke kika janyo, wannan wace irin masifa ce.?
Na dakatar dashi a tsiwance, don wallahi ya kusa kai ni bango "Ni fa ban ɗauki matsalar ka na, abinda ya shafe ni ne na faɗa mata, ah to."
"Ke ba a gida na kike ba? Ke sirrina ce Nafee, idan kuma kika ƙara fidda min sirri Allah ya isa.."
Na yi banza dashi, bana jin Allah ya isan shi zata bini, don ban fidda mashi sirri ba, bana kuma fatar na fidda sirrin gidan shi har abada, ya cigaba da faɗin "Ki je ki sallame ta."
Da sauri na tambayi "Wa.?
"Waccen yarinyar."
"Fatima ce fa? Ƙanwata? Uwa ɗaya uba ɗaya, shine kake kiranta wacce? Baka san sunan ta bane Sufyan?"
A gatsale