Showing 24001 words to 27000 words out of 83936 words
ke kusa da ita ya zauna kan shi a sama, babu yabo ba fallasa ya ce "Kun zo lafiya."
Maama ta ce "Lafiya lau, ya muka same ku?
"Lafiya. "
Auta ya gaida shi ba tare da ya amsa ba ya miƙe ya fice yana kaɗa makulli, ya ɗauki wani ƙaton padlock dake bisa window ya fice yana fito fitttt...
#UWAR SUKUM.
[5/17, 8:18 PM] RN Feedohm: 💧💧 *KUSKUREN SO.*
FREE BOOK
*HASKE WRITER'S ASSO.*
*FEEDOHM*
Wattpad@Feedohm
_Ga ba ɗaya littafin nan sadaukarwa ne ga NAFEESA Muhammad SULE, maman jinjiri, Alherin Allah ya kai maki a duk inda kike._
_Ina kike Aunty Zainab Abubakar Kotorkoshi? Ke ma ina maki fatan alheri._
*015*
Daga ni har Maman da kallo muka bishi, ina ganin lokacin da ta girgiza kai ta ce "Allah ya ƙyauta." Sannan ta juyo gare ni tana tambayar "Me ke faruwa tsakanin ki da mijin ki? Na ga kamar da matsala duk da na so ya tsaya don tafiyar ma tashi ce."
Na sadda kaina ƙasa na ce "Bakomai wallahi, lafiya lau mu ke zaune, kuma shima na san yana busy ne"
"Allah ya ƙara daidaita ku, amma me yasa idan anzo gurin ki kuke korar mutane Nafeesa?"
Kai tsaye na ce "Shine baya so ana zuwa."
"Ko aƙwai abinda aka mashi ne?"
Na girgiza kai "Aa ra'ayin shi ne kawai."
"Ra'ayi?" Ta tambaya a sanyaye
Na gyaɗa kai alamun eh
"Allah ya ƙyauta, shikenan sai a daina zuwan ko? Idan ta kama ayi zumunci sai ayi ta waya? Kema haka kike so ko?"
Na yi shiru tare da sadda kai ƙasa.
"Dama na ɗauka aƙwai abinda ke faruwa shiyasa na zo inji."
Na ce "Babu wallahi, matsalar zuwan ce kawai."
"Allah ya ƙyauta, yauwa sai na biyu kuma ina so in ji yaushe kika yanke auren Fannata?"
Da mamaki na ce "Bangane ba? Aure zata yi?"
"Eh mana, tunda kin fara mata gorin aure ai kin ga alamu sun nuna kin samo mijin kin shirya komai."
Na yi shiru na maida kaina ƙasa, ta yi ƙwafa ta cigaba da faɗin "Ban san baki da wayau ba Nafeesa sai yanzu, banda kina shashasha ko zaki yi ma kowa rashin mutunci ai Fannata ta wuce haka gurin ki, amma yarinya ta tako don ganin halin da kike ciki ki ci mutuncin ta? To wallahi ba zan lamunta ba, idan har na isa da ke, ki tambayi mijin ki kije har gida ki bata haƙuri, shashasha da ke." Ta mun Faɗa sosai, don ta Inda take shiga bata nan ta ke fita ba.
Sannan ta miƙe ta ce Auta ya tashi su tafi
"Dan Allah ku tsaya in gama abincin ku ci. "
"Aa Mungode. " Har ta juya ta kalli su Aira ta ce "Ƴaƴan shi ne?"
Na girgiza kai da sauri, ban san me yasa mutane ke masu kallon ƴaƴan Sufyan ba, kai tsaye na ce "Aa na sister din shi ne"
"Madallah."
Na miƙe na rakata, sai dai abin mamaki lokacin da muka isa bakin gate ɗin sai muka ji shi a rufe, na ja na ja ya ƙi buɗewa na koma ciki da sauri na ɗauko makulli na sa amma ya ƙi, daga ƙarshe muka fahimci ƙwaɗo aka sa ta waje a ka rufe, nan da nan zufa ta soma wanke ni, lokacin da Mama ta kalle ni ta ce "Ai da cewa yayi in bar mashi gidan shi akan ya rufe ni ta waje Nafeesa."
Sai na ji hawaye sun soma ambaliya a fuskata, komai ya dagule min, wata kunya da takaici suka taru suka min dirar mikiya, na kalli Mama da ƙyar na ce "Ki zo mu koma ciki dan Allah, wallahi mantawa yayi kina ciki ya kulle."
"Dama ta waje ya ke kulle ki."
Kai tsaye na ce "Eh." na mata ƙarya don na kare shi.
Ta girgiza kai "Allah ya ƙyauta, kira shi a waya ya zo ya buɗe ni in tafi."
Na ce "To, mu koma to dan Allah."
Mama ta girgiza kai, da alamu bata yadda da abinda na ce ba, na ruga da gudu na ɗauko wayar na kira number shi sai na ji ringing din na fitowa daga cikin gida, hankalina ya tashi na koma yayin da na tarad da wayar bisa gado, kuma na tabbatar da ba mantata yayi ba, wallahi da sanin shi ya barta, na fashe da kuka na koma gun mama da ke tsaye bakin gate ɗin na ce "Ya manta wayar a ɗaki."
Ta cije laɓɓa fuskar ta ɗauke da ɓacin rai ta ce "Ɗauko min kujera na sa anan kafin ya dawo to."
"Dan Allah ki yi haƙuri ki dawo ciki.
Ta tamke fuska kamar bata taɓa dariya ba ta girgiza kai "A'a, ki dai bani na zauna anan na jira shi ai ba komai."
Duk yadda na so ta koma wallahi ƙi ta yi, bisa tilas na ɗauko mata kujera ƴar tsugunno ta zauna a haraba gidan auta na gefen ta, nima gurin na yi zaman dirshan ina hawaye, ba ta kuma bi ta kaina ba, sai ma carbi da ta fiddo daga cikin jikkar ta ta cigaba da lazimi.
A wannan matakin idan na ce raina bai ɓaci ba, wallahi ƙarya na yi, ina son mahaifiyata kuma bana ƙaunar abinda zai taɓa mutuncin ta, ina jin zan iya yi ma Sufyan komai akan abinda yayi ma Maama, don wallahi sai ya ga ƙaramin haukana, na soma ƙiyasta yadda zan ci nashi mutuncin, na gwammace ko sakina sai dai ya yi, na gaji da rashin mutunci, a ce mahaifiyata ma bata tsira ba? Abinda na yi ma Fannata ma ya dame ni, kuma wallahi ba wani mantawa da yayi, tsabar wulaƙanci ne, ya san dai bai isa ya ƙore ta ba, kuma bai isa ya fito da pant ba, shiyasa yayi mata kora da hali.
In taƙaice maku muna nan zugum zugum abu tun 11am na safe Sufyan bai dawo ba har bayan isha'i, kuma Maama bata koma cikin gidan ba, a nan wajen ta yi sallah, ta kuma ƙi cin abincinmu, haka ta hana Auta ya ci.
Ni kam wuni na yi rusar kuka, haka ko ta su Aira ban bi ba, ƙarshe shiga nayi na rusa masu zagi, don sai da mamaa ta ce in basu abinci tukun na zuba masu, muka cigaba da zaman makokin da babu gawa.
Wajen 10pm muka ji ana ƙoƙarin buɗe ƙofar, na yi tsalle na isa bakin ƙofar, yana shigowa na ci ƙwalar shi, mama ta gifta mu ta wuce bata ko kalli inda muke ba, shi kam sai ya dafe kai yana yana faɗin "Dan Allah ki yi haƙuri, wallahi na manta da kina ciki Mama." Bata ko nuna ta ji ba, don ranta yayi masifar ɓaci, ya sa ƙafa ya tura ƙofar yayin da yayi sama da ni yana wata dariyar banza.
Zillewa nake ina kuka ina faɗin "Ashe baka da kirki, mahaifiyata zaka wulaƙanta?"
Bai dire ni ko'inw ba sai bisa gado, ya danne ni da dukkanin ƙarfin shi yana faɗin "Har cikin ranki kina zaton zan yi ma Maama haka dan wulaƙanci? Wallahi baki yi min adalci ba Nafee, wato kin nuna ke kaɗai ta haifa."
Cikin kuka na ce "Ni kaɗai ta haifa mana, da ace ta haife ka da baka yi mata haka ba."
"Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un, dan Allah ki yi min adalci mana Nafeesata, wallahi shaf na mance da tana gidan na kulle, dan Allah ki yi haƙuri yadda na ke son ki ba zan taɓa yi ma Maama abu makamancin haka ba, dan Allah ki yi haƙuri." Sai na ga ƙananan ƙwallan a idon shi, yayin da jikina yayi masifar sanyi, gaba ɗaya na nemi ɓacin ran na rasa, ya tallabo fuskata da hannuwan shi biyu ya cigaba da faɗin "Ki yadda da ni, ba zan aikata haka ba cikin sanina baby."
"Amma kuma ai a falo ka barta."
Ya lanƙwashe murya "Ba dai ki yarda ba kenan."
Ban ce komai ba, ya ɗagani, ya sa hannu ya ɗauke mayaudaran ƙwallan shi, ya buɗe drawer ya ɗauko min hijabi yana faɗin "Tashi mu je in bata haƙuri."
Na girgiza kai tausayin shi na ratsa ni na ce "Ka bari sai da safe yanzu ranta a ɓace ya ke."
Ya dawo ya zauna ya kamo hannuna "Amma kin yadda ban aikata hakan da gangan ba ko?"
Kamar dai ba zan yadda ba, amma zuciyata ta tirsasa ni da ba zai taɓa min ƙarya ba, na gyaɗa mashi kai a sanyaye, ya rungume ni sosai tare da sumbatar goshina yana tambayar "Ya akai waɗancan yaran ba su bacci ba?"
"Sabida hankalina baa kan su ya ke ba."
Sai na ga ya ɗaure fuska "To su meye na su a ciki?"
Ban kula shi ba ya miƙe ya fita, jimawa kaɗan sai gashi ranshi a ɓace, ya yi min tsaye bisa kai yana faɗin "Me suka yi maki da zaki zage su?"
"Zagi?" Na maimaita, don wallahi na mance ma da na zagen su.
"Eh, sun ce kin zage su, kuma kin san ba zasu yi maki ƙarya ba."
Na lumshe ido tare da gyara ƙwanciyata, sai lokacin na tuna da zagin da nayi masun, ya ƙara fusata jin na ƙi kula shi ya cigaba da faɗin "Bazan lamunci ɓata masu rai ba, ki kiyaye, akan su babu abinda ba zan iya yi ba."
Still dai bance mashi komai ba, na lumshe ido kamar mai bacci, ina tunanin halin da Maama ke ciki, na tabbatar a ƙarshen wulaƙanci zata ɗauki abinda Sufyan yayi mata, ba zata taɓa mishi uzurin ya manta da tana ciki ba.
**********************
Cikin tashin hankali Teemah ta tare ta tana faɗin "Wai Maama lafiya yanzu kuka dawo? Kuma ana ta kiran wayar ki baki ɗauka?"
Kafin ta bata amsa Auta ta yi karaf ya ce "To mijin Yaya ya kulle mu ta waje, sai yanzu ya dawo ya buɗe mu."
"Kutmar uban can.." Ta danƙaro ashar ta auna mashi, tana kallon Mamar, sai yanzu ma ta lura da yadda idanun ta suka ƙanƙance suka yi jawur da alamu ma kuka ta yi a hanya, a take sai ta ji ta nemi duk wani farin ciki ta rasa.
"Wallahi sai na ci Kutmar uban su su duka, ashe rashin mutuncin shi har ya kai ya kulle ki a gidan shi? Ita kuma sakarar wawiyar take zaune har yanzu a cikin gidan shi?"
Mama ta katse ta "Bana son sakarci, ai ya ce ya manta da ina ciki."
Kai tsaye Teemah ta ce "Wallahi ƙarya yake, idan uwar shi ai ba zai ce ya manta da ita ba."
Auta ya amshe "Kuma ina jin bayan mun taho yana dariya."
Ranta ya kuma ɓaci, ta ja hijabi ta saka zata fita, Mama ta tare ta "Ina zaki je?"
"Wallahi zuwa zan yi na ci uban su su duka, ba su isa su wulaƙanta min uwa ba." Ta bata amsa tana share ƙwallan dake fita daga idon ta.
"Dawo ki zauna, ba ki ji me na ce ba, mantawa ya yi, a mashi uzuri, kuma itama uwar ta ce ni, baki kaita jin zafin abinda yayi min ba, sabida wuni ta yi tana kuka."
"Kukan munafunci? Me yasa bata biyo ki kuka taho ba?"
Auta ya ce "Ai ta yi tsalle ta ci ƙwalar shi."
Dal ya ji mari a fuskar shi, ya dafe kunci yana tunanin ta inda marin ya fito, ya kalli Teemah da alamu daga gare ta ne, ta kuma tabbatar mashi ta hanyar faɗin "Ko kuma ta rungume shi ba? Sakarai banza, uban me ya hana ka yi masu ruwan duwatsu."
"Allah ya ƙyauta, kuma kar na kuskura na ga kin fita daga gidan nan, sannan kar na ji ko da wasa kin faɗa ma Baban ku abinda ya faru." Mamar ta faɗa tare da shigewa cikin ɗakin zuciyar na tafarfasa.
Tana shiga ciki Teemah ta fiddo wayar Mamar daga jikkarta da ta aje, ta kira Nafeesa tana tauna irin mugayen zagin da zata auna mata.
#UWAR SUKUM.
[5/17, 8:18 PM] RN Feedohm: 💧💧 *KUSKUREN SO.*
FREE BOOK
*HASKE WRITER'S ASSO.*
*FEEDOHM*
Wattpad@Feedohm
_Ga ba ɗaya littafin nan sadaukarwa ne ga NAFEESA Muhammad SULE, maman jinjiri, Alherin Allah ya kai maki a duk inda kike._
_Ina kike Aunty Zainab Abubakar Kotorkoshi? Ke ma ina maki fatan alheri._
*016*
Takaici goma da ashirin ya haɗe ma Teemah, jikinta har rawa ya ke yi, tana buƙatar ta amayar da abinda ke ranta amma da alamu babu dama sabida ƙin ɗaga wayar da na yi, sai ta yi min kira ya fi goma amma shiru, don haka ta yi ƙwafa ta fara rubuta messages.
_Wallahi kin ji kunya Yaya, wai har mijin ki ya rufe mahaifiyar ki cikin gidan ki, amma ki kasa ɗaukar mataki, wallahi kin yi asara._
Ta kuma tura wani message.
_Ai aure ba hauka bane, kuma kowa da na shi matsayin, amma ke duka kin ɗauka kin bawa mijin ki, na rantse da Allah zan iya ɗaukar komai amma banda cin zarafin mahaifiyata, ki guji ranar da zamu haɗu._
_Ashe girman banza gare ki babu wayau. _
Haka ta riƙa tura mata messages kala kala, duka kuma sunyi delivery amma babu reply.
Ta maida wayar ta aje, a lokacin Baaba ya leƙo yana tambayar "Wai har yanzu basu dawo ba Fatima? Kin kira Nafeesar? Ko dai wani gida suka wuce? Don na san ba zasu zauna gidan ta ba har yanzu."
"Sun dawo Baaba." Ta amsa rai ɓace.
Ya ƙarasa shigowa ɗakin, ya wuce uwar ɗaka yayin da Maama ta yi sauri goge guntayen hawayen da ke bin fuskar ta, ta samo guntun murmushi ta yafa a laɓɓan ta.
Gefen gadon ya zauna cikin kulawa yana faɗin "Lafiya daga zuwa ki dawo muka ji shiru? Kuma an kira wayar baki ɗaga ba?"
Ta juyo tana fuskantar shi, kai tsaye ta ce "Da yake wayar silent ta ke ban san an kira ba, daga baya kuma na ga missed call to babu kati a Layin."
Ya gyaɗa kai "Amma duk tsawon lokacin nan kina gidan Nafeesa?"
Ta girgiza kai da sauri "Na manta in faɗa maka zan je gidan Hajiya zainab na gano jikin ta, a can ne ma na ɗan jima."
"Ba laifi, suna dai lafiya ko? Ya kuka yi dasu?"
"Lafiya lau suke, mun yi magana komai ya wuce da iznin Allah."
Babaa ya ce "Alhamdulillahi, babu dai wata matsala ko.?
Mama ta gyaɗa kai "Insha Allahu."
Ya zuba mata ido, kafin ya riƙo hannun ta na haggu ya ce "Me ya samu idon ki?"
Ta jefa mashi murmushi "Wallahi wani abu ne ya faɗa ciki."
"Mu gani?" Ta haske fitilar ɗakin ya sa hannu biyu ya buɗe ido tare da hura mata iska, suka ɗauki dariya gaba ɗaya, ya lakace mata hanci yana faɗin "Ƴar tsohuwa." Sannan ya miƙe ya fita.
Bayan ya fita ta janyo Pillow ta ɗaura a cinyarta, zuciyarta na tafarfasa, tunda take ba'a ɓata wulaƙanta ba irin haka, ta kasa tsaida hawayen da ke bin kumatun ta, a gidan ƴar ta? Kuma surukinta? Ko a mafarki, wannan shine ƙarshen cin zarafi, ta sani sarai babu wani mantawa da yayi tana gidan, kawai dai kora ya yi mata da hali wacce tafi ta takalmi zafi, kuma da iznin Allah ita da gidan Nafeesa har abada, ba dai zata hana yaranta zuwa ba, amma ita kam anyi na farko an yi na ƙarshe, a daren sam bata runtsa ba, ƙwana ta yi juyi kamar yadda Teemah itama ta ƙwana.
********************
Abu kamar wasa Sufyan bai ƙwana bedroom ɗin mu ba, sai ya koma ɗakin da aka ware ma su Airah ya ƙwana tare dasu, har ga Allah abun yayi masifar ɓata min zafi, wato ni banza duk abinda ya min na huce na yafe mashi amma shi akan na zagi yara shine har da ƙaurace min ɗaki, wato shi mai ɗiyan ƴan uwa? Allah ya taimake ni da ya kasance nima ba juya ba ce, na lumshe ido hawaye na bin kumatuna, a daren ranar ban yi bacci ba, ƙwana na yi juyi, kuma bana jin zan iya zuwa na same shi, don ban ga abin fushi ba.
Da asuba na ɗauko wayata na taras da missed call da messages na Teemah, don na tabbatar da ita ɗin ta turo su da number Mama, na yayibo ashar na auna mata ina faɗin "Har ni za ta zaga dan ubanta? Fi na sanin darajar uwar ta yi? Koko Mamar bata faɗa mata yadda raina ya ɓaci ba? Lallai gaskiyar Sufyan Teemah bata kunya wallahi, ni ban ma san inda ta samo rashin tarbiyya ba, ai kam zan je na same ta, wallahi sai na ci ubanta, wato so ta yi na kaso auren na koma gidan mu zauna ƙugu da ƙugu, shiyasa fa aka ce ko ciki ɗaya kuke da mutun wani sa'in hassada tana shigowa, yo ba gata ba, banda Teema na hassada da aurena ta ya daga wannan misunderstanding ɗin zata ce na wulaƙanta mijina? Wallahi hassada ce, na yi aure na barta, cin ƙwalar da na mashi ma na ce bai ƙyauta ba Auta bai bata labari ba? Ko kuma ya bata duk da hakan bai mata ba.?
Na yi ƙwafa na cigaba da faɗin "Itama ma Mamar bata faɗa masu cewa mantawa yayi tana ciki ba ya kulle? Shikenan ba za a amshi uzurin shi ba? Ni wallahi na yadda mantawa ya yi, don yadda Sufyan ke sona ba zai taɓa wulaƙanta mahaifiya ta ba."
Na ƙara karanta messages din, a fusace na kira number Teemah amma a rufe, don haka na tura messages masu zafi idan ta buɗe wayar ta gani kamar yadda ta turo min.
Da safe na yi wanka na shirya, na shiga kitchen ina fere doya ya shigo, ya wani rungume ni ta baya kamar babu abinda ya faru, yana faɗin "You look good."
Na yi watsi dashi, don da alamu so yake ya manna min hauka, sai ya guma min baƙin ciki sannan ya zo ya nuna min kamar babu abinda ke faruwa.
Ya ciji kunnena "Ni kike sharewa?"
Ban dai ce komai ba, ya ɗaura kan shi a kafaɗata tare da zagayeni da hannayen shi, ya cigaba da faɗin "Wato an maki yaji bara ki je biko ba ko? To ni na kawo kaina."
Sai lokacin na taɓe baki na ce "Hmmm."
"Hmmm ko? Ke da ya kamata ace kina police station yanzu amma na barki gida, shine dan zaƙewa har da fushi.?"
"Ni dai dan Allah ka sake ni na yi abinda ya dace."
Ya shafo marata yana faɗin "Kula miji bai