Showing 6001 words to 9000 words out of 83936 words

Chapter 3 - KUSKUREN SO Book Complete by Feedohm.txt

Feedoms   

21 Sep 2025

1694

tuntuɓe na juyo na watsa mishi hararar ƙauna, domin har ga Allah ni kaina na san macece, ina zubi da sura mai ɗaukar hankali, jinkirin aurena ba daga rashin ƙyau bane, Allah ne ya ƙaddara.

Sai da mukayi raka'a biyu kafin ya dafa kaina ya riƙa zubo min addu'a ta neman tsari daga shaiɗan , da kuma ƙwanciyar hankali haɗi da zuriya ta gari.

Kafin ya tausasa murya ya riƙo hannuna ya kira sunana cikin wata irin siga "Nafeesa."

Ban ɗago ba na amsa a sanyaye "Na'a."

"Banda bakin godiya gare ki, ta yadda kika jajirce kika nuna min ƙauna, nagode ƙwarai insha Allahu nima zan saka miki dai daga da abinda kika mini zan ƙyautata miki, sannan na maki alƙawarin zamu rayu a tare har abada, na maki alƙawarin zaki kasance ke ɗaya tal a gidan Sufyan da kuma zuciyar shi, Nafeesa zan so ki na tarairaye ki fiye da tunanin ki, insha Allahu ba zan baki damar kuka ba muddun bana shagwaɓa bane, zan kula da yayan ki na zame masu uba na gari."

Na lumshe ido a hankali duk cikin maganganun shi babu wacce ta min daɗi fiye da alƙawarin da ya ɗauka na ni ɗaya tal a gidan shi da kuma zuciyar shi, duk da na sha jin ana faɗar namiji ba ɗan goyo bane, sannan bai da tabbas, sai dai ni ina da tabbas akan Sufyan ɗina, ina tabbacin zai riƙe alƙawarin shi fiye da yadda ya ke kafin auren mu.

Hannun shi na ji bisa kumatuna, yayin da ya zuba min ido, ciki wata narkakkar murya ya tambaye ni "Me kike tunani?"

Ban san lokacin da na furta "Ina da buƙatar tabbaci daga kalaman ka!"

"Baki yadda da Sufyan ba ne? Nafeesa duk abinda na faɗa na sani kuma zan cika, na san kina shakku don nace zaki zauna a gidana da zuciyata ke ɗaya kawai ko? Kina ganin kamar daɗin baki ne ko?"

Na girgiza kai a hankali ina kallon ƙwayar idon shi dake fidda tsantsar gaskiyar kalaman shi.

Ya lumshe idon shi bayan ya sarƙe shi cikin nawa "Da gaske na ke Nafeesa, na maki alƙawarin ba zan taɓa miki kishiya, halaccin da kika min kin fi ƙarfin haka, domin duk macen da zata jajirce ta aureka bai ci ka haɗata da wata ba, dan Allah kar ki shiga sahun matan da...

Na ɗaura hannuna bisa bakin shi, cin ƙwarin guiwa na ce "Na yadda da kai Sufyan."

Ɗan murmushi ya jefa min mai kashe min jiki, yayin da ya janyo ledar da ya shigo da ita, ya cure min hijabi tare da ware ƙafafu ya janyo ni tsakiya, sannan ya soma ciyar dani cike da ƙauna.

Bayan mun gama shi da kan shi ya tattara gurin, sannan ya kama hannuna muka je muka yi brush, ya haɗa min ruwan zafi yace na watsa na na samu ƙarfi.

***

Hmm rayuwar aure aƙwai daɗi, maƙaryata ne ke faɗar wai babu komai a cikin shi face haƙuri, sai yanzu ma na lura da baƙin ciki ya sa suke faɗar haka sabida kar kaima ka yi auren ka ji wane daɗi suke ji, wallahi duk abinda ake a novel ana yin shi a zahiri, kuma na tabbatar gurin Sufyan, domin ririta ni yake tamkar ƙwai yana nuna min soyayya, 3 days kenan bai taɓa ɓata min rai ba, ko abu yayi ya ga raina zai ɓaci yanzu ya rungume ni ya hau bani haƙuri.

Na murmusa ina kallon agogo 12pm ta kusa, a hankali na kai hannu na ɗauko wayata dake aje bisa hannun kujera, na ƙura mata ido ina kallon hoton mu rungume da juna dake a screen ɗina.

Message na shiga na tura mishi ɗan gutun saƙo _I miss you Milky_

Cikin seconds ya maido min _I miss you too Honey._

Da yake ina kiran shi Milky yana kirana Honey.

Ina riƙe da wayan sai ga wani saƙon _Ana son ganina?"_

Wani lallausan murmushi ya suɓuce mini, ina mamakin yadda baya iya good 2hours bai ganni ba, to idan ya koma aiki fa? Duka fa hutun 2weeks aka bashi office.

_No!_ Na tura.

" _To ni ina so, ina so nayi enjoying company ki._ "

Hmm na faɗa, ya cika jaraba wallahi, a time ina gani a facebook wai miji sai yayi 2weeks bai kusanci matar shi ba, sai yanzu nake ganin sakaci da iskancin matan ne da basu san yadda zasu kula da mijin ba, da kuma kan su.

_Call?_  Ya kuma turo min.

Kafin ma na bashi amsa har ya kira, ina ɗaukan kiran kuma ya soma da zolayana "Honey ba class, daga ringing sai picking.

"Haka ka ce ko? Bara to na kashe idan ta yi ringing ɗin na ɗauka."

"Sorry sorry, wasa nike, kar ki aje please."

"To bani haƙuri." Haka fa nike, ko nike da laifi dama tun kafin auren shine ke bani haƙuri, so yanzu ma bai canza ba, haka nan ake cewa wai namiji na canzawa bayan aure, kawai ƙarya ce.

"Ai na bayar." Ya katse ni

"Ban ji ba."

"To ayi haƙuri, gimbiyar Mata"

Na murmusa, ina jin kaina isassa, sai da na mula sannan na ce "Na yi."

"Thank you, me zan taho da shi?"

Na yatsina fuska "Wai har zaka dawo?

"Yes, i miss your company." Ya faɗa kamar mai raɗa

"Uhmm, duk abinda ka zo dashi."

"I love you."

"I love you too." Na furta, kafin ya sumbace ni ta wayar ya kashe.

Nan da nan na miƙe na shiga wanka, na sille jikina da ruwan ɗumi, sannan na fito na yi turare da turaren jiki na ƴan Maiduguri, sauƙi ma ina da coal, kuma baida matsakar haɗuwa.

Na bi ɗakin da airfreshner, sannan na ci ƙwalliya da wata body hug mai hannu ɗaya, na fahimci yana masifar son ƙananan kaya sabida yadda wanshekaran auren mu ya kawo min su, wai baya so ya sa a lefe a yi ta magana, nan da nan na ɗame cikin mini siket na tamke gashina baya, duk da ba wani make up na yi ba, amma ni kaina na san na yi masifar ƙyau.

Ina tsaye Fannata ta kira ni, na yi picking da sauri na soma da faɗin "Aure daɗi ƙawata!"

"Ke banza..!" Ta bini da tsaki.

"Wallahi kuwa, Fannata kin ga yadda yake treating ɗina? Yo duk wani kula a waje wallahi na banza ne, ai yanzu na san menene so."

"Uhmm ki ce ana ta lobewa?"

"Ke dai bari, abin sai wanda ya gani."

"Allah mu ma ya bamu na gari."

"Amin ƙawata, wai kin ma san wani abu?"

"Sai kin faɗa."

"Ya min alƙawarin ba kishiya."

Ban rufe baki ba, ta ƙwashe da dariya, ina jin yadda ta dage tana ɓaɓɓakawa kamar wata Mahaukaciya, ni kam ban ga abin dariya ba a maganata, don haka raina ya soma ɓaci na katse ta "Meye abin dariya?"

Ta guntse ta ce "Ba dole in miki dariya ba, don namiji yace ba zai miki kishiya ba a stage ɗin da kuke shine har abin faɗa? Kin ga kar ma ki sama kan ki dan Allah, ke dai kiyi addu'ar ku zauna lafiya."

Raina ya soma ɓaci na ce "Me kike nufi?"

Kai tsaye ta ce "Wallahi ƙarya ya ke miki, duk namijin da zai zaunar dake yana faɗar ba zai miki kishiya ba, wane da wane, wallahi ƙarya ne, ke dai ki sama ranki bautar Allah kika je, amma maganar kishiya bai taso ba, idan ma yayi, shi ya sani, idan bai ba wahadas, amma kar ki sake faɗawa kowa, don zaki iya jin kunya."

Ban bata amsa ba na yanke wayata, wato ma maimakon ta tayani murna shine take faɗar wai kar na sama raina? Ƙarya ya ke min! Tab, ikon Allah, ni wallahi ta bani mamaki, don sai na ga kamar ma baƙin ciki ta ke min, yo ai sai yanzu ma na gane dalilin da yasa idan mutun yayi aure ya ke watsar da ƙawayen shi na gida, ai baƙin ciki ke shigowa a harkar.




*UWAR SUKUM 08036953516.*
[5/17, 8:18 PM] RN Feedohm: 💧💧 *KUSKUREN SO.*


FREE BOOK.


*HASKE WRITER'S ASSO.*



*FEEDOHM*
Wattpad@Feedohm




_Wannan littafin gaba ɗaya sadaukarwa ne ga NAFEESA ABDULLAHI SULE Alherin Allah ya kai maki a duk inda kike._




*005*




Har Sufyan ya dawo gida sukuku na ke, takaicin maganganun Fannata ya ƙi saki na, ɗan oyoyon da ni ke mashi ma a ranar bai samu ba, ina zaune bisa doguwar kujera ya shigo, ya zauna gefena tare da tsura min ido cike da soyayya da kulawa, kafin ya sake min mintsinin ƙauna a gefen kumatu.

Ganin ban ce masa komai ba, sai dai zunɓurar bakin da nike ya sa ya kamo hannuna ya soma murzawa yana faɗin "Waye ya taɓa min Shalele ta?"

Kai tsaye na ce "Fannata."

"Huh? Me ta maki? Ta zo gidan ne?" Ya jeho min tambayar yana murmushi.

Girgiza kai na yi na ce "Aa, waya mu ka yi."

Ya langwaɓar da kai yana kallon "A wayan ta taɓa miki? To ina bada haƙuri a madadin ta, banda abinta ita wa ya faɗa mata ana ɓatawa amarya rai? Faɗa min, me ta maki?"

Kai tsaye na ce "Don na faɗa mata maganar da muka yi jiya, shine ta ce ƙarya kake min, wai maza baƙwa da tabbas, kar na yadda da kai."

Sai na ga ya ɗaure fuska ya na tambayar "Me kika faɗa mata?"

"Ka ce bara ka min kishiya ba."

"Shine kuma ta ce miki ƙarya na ke? To ta shiga zuciya ta ne ta gani?"

Na girgiza mashi kai a sanyaye, sabida yadda ya yi maganar alamun bai ji daɗin abinda ta faɗa ba, sai nima na ji dama ban sanar mashi ba, ko da ya ke babu wani ɓoyo a tsakanin mu, mun ri ga mun zama ɗaya, na kalle shi na ce "Me zan ce mata? Kawai na ji haushin da ko kunyata ba ta ji ba, ta ƙarya ta min miji."

"Hum ku fa dama mata matsala gare ku, Nafee daga yau kar ki kuma ɗaukar wayar ta, irin su ne masu zuga mutane su kashe su masu aure don su ba su samu mai so ba, kuma ki faɗa mata kar ta yi gigin zuwan gidana, ta je gidan wanda ba maƙaryaci ba."

Na kalle shi dososo ya wani haɗe rai, bai bani damar wata magana ba, lumshe ido na yi a sanyaye ina jin bata cancanci wannan hukuncin ba, na san halin Fannata ta faɗa ne kawai amma bata da zuciyar zugani bare ta kashe min aure, a karo na farko sai na ji haushin kaina, na yi ya kacake ban faɗa mashi ba, sai yanzu na tuna da huɗubar Mamana, da ta ce bakomai zan faɗa ma miji ba, haka ba komai zan ƙwaso ba idan ya min na faɗa a gida, ni zan iya yafe mashi amma na kusa dani bai zama tilas ya yafe ba, haka shima zai iya yafe min amma bai zama tilas ya yafe ma na kusa da ni ba.

"Baby sai in ga..." Na faɗa a shagwaɓe.

Ya ɗaura hannun shi saman laɓɓana "Shiiiii." Ya kashe min idanun shi masu matuƙar ƙyau da zautar da ni, kafin na yi magana ya rungumo ni jikin shi, yana sinsinar wuyana, tare da zame ribbon ɗin dake a kaina, ya soma yamutsa min gashi da ke fitar da sihirtaccen ƙamshin man da ke gyaran gashi na LEEDAH yana lumshe.

Ban san lokacin da muka zame bisa doguwar kujerar ba, sai dai ganin shi na yi bisa kaina, ya haɗe bakin mu guri ɗaya, yana aika min da wani mayunwacin kiss mai kashe jiki, yayin da ya ke wasa da sassa na jikina, ai nan da nan na mance da wata Fannata, na ɗauki laifi na ɗaura mata, na bawa mijina gaskiya.

Sai da ya kashe min jiki, sannan ya tashi tare da lakace min hanci yana kallon pant ɗina da ya jefar gefe ɗaya, kafin ya ɗauko shi ya kai a hanci ya sunsuna tare da yamutsa fuska ya toshe hanci yana dariya.

Ban san lokacin da nayi kukan kura na amshe abina ina hararar shi, sai kuma nima na kai hanci don tabbatar da abinda na gani a fuskar shi, lokacin guda ya ƙwashe da dariya yana faɗin "Wasa na ke, ina son ƙamshin."

Na bishi da dukan wasa, yayin da ya yi ɗaki da ɗan gudun shi yana dariya.

Ya ja towel ya faɗa toilet ya rufo, yayin da na zube gefen gado ina murmushi, wai a haka za'a faɗa maka aure ba daɗi, a haka zaa faɗa maka aure cike ya ke da ƙalubale, yo ƙalubalen uban wa, banda bakin ciki da son kaima kar ka yi auren ka ji me ake ji.

"Shalele." Ya ƙwala min kira tare da buɗe marfin ya leƙo ƙan shi.

Na murmusa "Ba wani Shalele, kar ka min na Sameer da Zainabu mana."

"Ni na isa, please zo ki cuɗan bayana." Ya langwaɓe kai.

Maƙe kafaɗa na yi, tare da kawar da kai gefe ɗaya, ban yi aune ba, ya fito ya sunkuce ni muka faɗa toilet ɗin a tare, inda komai ya canza salo.


******************

Sai da na gyara ko'ina na yi mopping sannan na shiga kitchen don haɗa mana abincin rana, ina ƙoƙarin kunna gas wayata ta soma ringing, na fita da sauri na ɗauke ta daga inda ta ke charge, na murmusa tare da yanke kiran sannan na sake kira.

"Daga aure sai yarinya ta mance da maman ta?" Mama ta faɗa bayan ta amsa gaisuwa ta.

Na murmusa na ce "Ni na isa? Ko jiya na kira da daddare wayan a rufe."

"Eh, lokacin ta mutu ba charge, ya gidan?"

Na ce "Lafiya lau Alhamdulillahi Mama, ina nan na yi kewar ku."

"Masha Allah, har kun fara fita ne Nafeesa?"

Na ce "Me kika gani Mama?"

"Jiya Ƙanin ki ya zo gidan yayi ta knocking shiru, har ma ya juya sai ga Sufyan ɗin ya buɗe sai ya ce baƙya nan."

Na yi tsit kamar wacce ruwa ya cinye, mamaki ya kama ni, a lokacin da ake knocking muna tare a falo, har zan je na buɗe sai ya ce aa wai ƴan takura ne a rabu da su, da na ji knocking ɗin ya yi yawa, shine na roƙe shi yaje ya ga waye, kuma da ya dawo sai ce mani yayi almajiri ne ke neman inda zai yi aiki a bashi abinci, sam bai faɗa min Ƙanina ba ne.

Muryar Mama ta katse ni "Na faɗa miki bana son ƴan yawace yawacen nan da kika saba anan Nafeesa, ki shiga hankalin shi, yanzu ba da ba ce, ba ko'ina zaki riƙa fita ba, ace ko sati biyu ba ki haɗa ba, amma har kin fara fita? Baƙya jin tsoron zancen mutane.?

A sanyaye na ce "Ayi haƙuri Mama, ba zan sake ba."

"Shikenan, dama kayan ki na anko da Habiba ta saka ta aiko dashi, idan an samu mai zuwa a kawo maki."

Na ce "To Nagode."

Mun ɗan jima muna fira, tana min nasihar haƙuri da biyayya, sannan muka yi sallama, yayin da zuciya ta ka kasu biyu, ɗayan ɓangaren na mamakin dalilin da ya sa Sufyan ya hana Amadi shigowa, wani sashen kuma yana dariyar kalaman mama na wai in yi haƙuri, ni kam banga inda kalmar ta shigo ba.

Ina ƙoƙarin cigaba da aikina aka yi knocking don haka na sa ƙaramin hijabi na fita na buɗe gidan, dattijuwa ce sai ƴar budurwa wacce ta ci gayu da doguwar riga ta less, tana taunar cingum abin ta.

"Bismillah." Na faɗa ina ƙoƙarin shaida su, na san dai ko ba'a faɗa ba, daga dangin su Sufyan suke, domin dattijuwar na tsananin kama da shi, ita kam Budurwar hanya ko ta rafi.

"Nan ne gidan Sufyanu ko?" Dattijuwar ta tambaya tana bina da kallo.

Budurwar ta amshe da "Haba ke ma Umma, an ce maki nan ne fa, me ye na kuma tambayar ta." Ta ɗauke kai tare da sakin siririn tsaki.

Ni dai mamakin cin maganin ta ni ke, na taɓe baki ina masu iso ciki, yayin da budurwar ta yi gaba da alamun ta san gidan.

Na ɗauko masu ruwa da drinks na basu, sannan na koma na zauna muka sake gaisawa da Dattijuwar, inda ta ke min bayanin ita ce Maman shi.

Sai na ji kunyar ta kama ni, na sunkuyar da kai muka sake sabuwar gaisuwa.

"Sufyanun baya nan?" Ta tambaya.

Na gyaɗa kai cike da kunya na ce "Eh, amma bara in ki....

Kafin na rufe baki na tsinkayi muryar budurwar tana faɗin "Yaya Sufyan, na kawo Umma gidan ka, kuma baka nan.." Ta ƙarashe maganar a shagwaɓe.

Na bita da kallo, yayin da wani abu ya daki zuciya ta, sai na ji tamkar na kifa mata mari wallahi, amma na daure na haɗiyi fushi na, na maida kai ƙasa ina wasa da yatsuna.

Ban san me ya faɗa mata ba, sai na ji ta ƙara narkar da muryar tana faɗin "A'a anan zamu ƙwana."

Gabana ya faɗi ras, na ɗago na kalle ta, lokacin da Umma ta ce "Ƴar nan baki gama abinci ba?"

Na miƙe da sauri ina faɗin "Eh Umma, amma aƙwai fura a frigde da snacks bara in kawo miki kafin na gama."

Ta bini da kallo ta ce "To kina me Nafisa?"

Na sunkuyar da kai ƙasa, ta taɓe baki ta ce "To dan Allah a yi maza."

Na ce "To."

Har na fara tafiya ta tsaida ni "Me kuke dafawa ne?"

"Faten doya."

"To dan Allah ni ayi min saƙwara."

Na gyaɗa kai na wuce kitchen ɗin, da tunani barkatai a rai na, ina jin lokacin da take ce ma budurwar "Hanifa kin ganta ƙyaƙyƙyawa ko? Allah ya nuna min ƴan jikokina haka."

Hanifa ta yatsuna fuska ta ce "An fa ce ba zasu haifi lafiyayyun ƴa ƴa ba, ko sun haifa sai dai su mutu, ko kin manta Kawu ya faɗa miki diramar da aka yi kafin auren amma suka liƙewa juna, Umma sikila fa ce."

Umma ta ce "In ji uban wa? Hanifa bakin ki ya sari guntun kashi, fatan da zaki min kenan? Kina ganin wancan shayyayen har yanzu matar shi bata haihu ba, kuma ya ƙi ƙara wata, a nan na sa ran ganin ƴan jikokina kafin na mutu, shine zaki faɗa min ko an haifa mutuwa zasu yi? To wallahi ki kiyaye ni. "

Hanifa ta ce "Ba fa ni na faɗa ba, ah to, sikila ce dai."

"Ƙarya kike, an ce kariya ce."

Na dafe ƙofar kitchen ɗin ina jin wani abu na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login