Showing 81001 words to 83936 words out of 83936 words
na shi ba sai me.?
Duk yadda na kai ga nuna mishi bana so sai ya ƙi saurara ta, ya danne ni ya min ɗan ƙaramin fyaɗe, sai da ya samu natsuwa sannan ya soma jera min tsaki yana mita "Dama kin san baki gyara ba kika sa na ɓata lokacina?"
Takaici goma da ashirin suka haɗe min, ga dai wata irin tsanar kaina da nike da ƙyanƙyamin haɗa jiki da Sufyan ga kuma wani iskancin da ya ke niyyar yi min, kamar na yi shiru na ƙyale shi, jin mitar ta yi yawa ya sa na tambaye shi "Me kake nufi?"
Ya maida kayan shi yana jefa min wani mugun kallo, kai tsaye ya ce "Salaf, babu ko taste, abu kamar ƙorama....."
Raina idan ya yi dubu ya ɓaci, takaici ya hana ni magana, har ya fice falon ya na mita, a tunanina idan ya shiga falon zai yi shiru, amma sai na ji yana faɗa masu banda dandano, abin nawa kamar rijiya, ba wani gardi, wallahi ban san lokacin da na ƙwasa da gudu na shiga falon na yi kan shi na shaƙe shi na hau dura mishi zagi ta uwa ta uba, shima a fusacen ya zaro waya ya cigaba da lafta min, duka ta ko ina yana yi yana zagina "Banza ɓallagaza, ƙarya aka miki, an ce Salaf babu ɗanɗano, abu kamar rijiya idan kin isa kiyi duk abinda kika ga dama."
Ina jin ƙarshen wulaƙanci duniya kenan Sufyan ya min, na juya na kalle su suna dariya ƙasa ƙasa, tare da ƴan maganganu idan ka cire Asiya da ta shige ɗaki tana tako ɗaya bayan ɗaya
Cikin wata irin murya na ce "Allah ya isa, yadda ka wulaƙanta ni kaima Allah ya wulaƙanta ka Sufyan, kuma wallahi sai ka sake ni.."
"Sakin na ki wata burauba ce? Ki je an sake ki saki ɗaya.." Ya wani fizge ni kamar kayan wanki ya fice da ni daga gidan ya jefar ƙofar gidan yana huci.
******************
BAYAN TSAWON LOKACI.
Ba laifi na ɗan maro, domin bayan na faɗa ma su Maama abinda ya faru ba su wani daɗe suna fushi da ni ba, sai dai faɗan da na sha sosai, amma fa har lokacin ban manta da abinda Sufyan ya min ba, ban warke daga ciwon takaicin ɗa namiji ba, ba na kuma jin zan warke ɗin har abada.
A ɗan datsin ne Fannata ta haifi yaran ta ƴan biyu ƙyawawa lafiyayyu masu kama da mijinta, sai abin ya dawo min sabo, na ci kuka na sake nadamar abinda na aikata, sai dai kuma na san ba zan iya canza ƙaddara ta ba, ba zan iya canza ƙaddarar ba zan taɓa ganin gudan jinina ba, ba zan canza ƙaddarar ba zan bar mai min addu'a bayan raina ba, ba zan canza ƙaddarar daga lokacin da na rasu an mance da babi na ba, babu wanda zaa kalla a tuni da ni, babu wanda za'a kalla a min addu'a...
Yaran Fannata suka ci sunan Nafeesa da kuma Aisha, tabbas ta min kara da kawaici, tabbas Fannata ƙawace da kowa zai yi fatar samun irin ta.
A kuma datsin ne Teemah itama ta yi auren ta, gida na mutunci da kamala, mijinta mai tsananin son ƴan uwanta, mai daraja iyayen ta, mijin da bai iya ɗaga ido ya kalli mahaifiyar ta, dukkanin su da na ke ma gorin aure sun yi auren su a lokacin na nawa auren ya mutu, na Teemah Ja Ji Jo Ju Je, na lokacin na tabbata jawara, jawarar da bana jin aƙwai wanda zai yadda ya ƙwasa, don duk wanda zai zo gurina zan faɗa mishi banda mahaifa, kuma ko da ya aure ni ba zan haihu ba, don bana so na je na sake dawowa, kuma da zaran na faɗa ma mutun haka sai ya ce min "Nafeesa burin mutun yayi aure ya hayayyafa domin annabi yayi alfahari da shi ranar ƙiyama, ki yi haƙuri ba zan yaudare ki ba, amma ina son zuriya.. "
Wannan shine abinda yawancin maza ke faɗa min, kuma shine abinda ke hanani bacci, gashi a lokacin ina ganin tsananin ƙosawar iyayena akan na yi auren shine ma dalilin da yasa har na ke sauraren maza, amma idan raayi na ne, ni da aure har abada, domin na yi ban ji da daɗi ba..
Ina zaune da la'asar aka min sallama, na kalli Maama sannan na ce ma yaron "Ke ka ce bata na."
Maama ta tsayar da shi "Aa je ka ce tana zuwa ka ji ko."
Yana fita ta kalle ni cike da tausayawa ta ce "Sabida me?"
Na saki murmushin yaƙe ina faɗin "Kowanene Idan na je ma ba zai yadda ya auri juya ba Maama."
Ta runtse idon ta gam, idan na fahimce ta tana jin takaicin cire mahaifata kamar dai ni, a sanyaye ta ce "Ki je ki gani kin ji ko? Bawa ba ya fidda rai da rahama, ba zaki zauna haka."
Daƙyar ta lallaɓa ni na fita, sai dai mamaki ya kusa daskarar da ni, na murmusa ina kallon shi, don yana daga cikin jerin mutanen da ba zan taɓa mantawa da su ba, na kalle shi sosai ina faɗin "Likita kai ne kuwa.?
Ya gyaɗa kai yana murmushi "Eh kin yi mamaki ne?"
Na gyaɗa kai "Ba dole ba, Allah ya sa lafiya? Ko ɓatan hanya ka yi."
"Eh to, zuwa na yi in faɗa miki an samu mahaifar ta roba idan kina so.." Ya ƙarashe maganar cikin sigar zolaya.
Na saki siririyae dariya ina girgiza kai, a sanyaye na ce "Ai da saura likita, sai kuma a samo babyn roba ko?"
Sai na ga ya tsura mun ido, sannan ya murmusa ya ce "To bara in cire maki wannan award ɗin, da alamu an wuce level ɗin , tunda kika fahimci mahaifa roba sai babyn roba."
Na murmusa tare da rusunawa na ce "Ina wuni? Ya aiki ya iyali? Ya akai ka gano ni?
"Duka lafiya lau Alhamdulillahi, gano ki kuma ai bazai yi wuya ba, ko kin manta aƙwai address ɗin ki a file ɗin mu, both na gidan ki da gidan iyayen ki."
"Masha Allah."
Ya ɗan waiwaiga kamar mai son gano wani abu, sannan ya juyo yana ɓata fuska ya ce "Gurin Baaba na zo kuma da alamu baya nan ko."
Na gyaɗa kai "Eh baya nan, Allah ya sa lafiya.?"
Kai tsaye ya ce "Aure na zo nema.."
"Aure.?
Ya jefa min wani lallausan kallon da na kasa gane kan shi, sannan ya ce "Eh ko ba zaa bani ba?"
"Ba haka bane, ai bamu da mace anan gidan yanzu."
Sai na ga ya ciro hular shi ya miƙo min yana faɗin "Ayya, Malan Nafiu me yasa kake sa kayan mata? Ai sai ka ruɗa dangi ko?"
Na ƙwashe da dariya ina kallon shi, "Nafiu fa.?" Na tambaya ina ƙoƙarin tsaida dariya ta.
"Eh mana, tunda kin ce babu mace, kin ga kam ai bai kamata kina sa kayan mata ba." Ya tsura min ido.
Na dakata da dariyar ina kallon shi, domin aƙwai wani saƙo da ya ke ƙoƙarin isar min ta cikin ƙyawawan idanun shi, sai na ga saki lallausan murmushi, kai tsaye ya ce "Ke na ke so Nafeesa.."
Sai na ji gabana ya faɗi, na jinjjga kai alamun mamaki, a hankali na maimaita kalmar "SO...... ?
Ya murmusa "Ƙwarai, kuma auren ki zan yi."
Ban wani tsaya tunanin komai ba na ce "To ka turo..."
"Da gaske? Za ki min mahaukacin son da kika ma wancen mutumin?"
Na tsura mashi ido, da mamakin ya akai ya san na ma Sufyan mahaukacin so? Na lumshe idona.
"Ba zaki tambayi sunana ba?" Ya kuma faɗa kamar mai raɗa.
Na ɗan murmusa "Ba buƙatar sanin sunan ka likita, ka ce kana sona, kuma aurena zaka yi, maganar Allah bana son ka, amma zan aure ka, idan ka yadda ka turo, daga baya zan san sunan na ka, amma ina fatan baka mance yadda na ke ba.."
"Ta ya zan mace Nafeesar Sufyan, mai buƙatar mahaifar roba..."
Ban ce komai ba na juya na koma gida, ba wani buƙatar na tsaya mishi ƙarin bayani domin ya san komai, sannan ni kuma bana buƙatar wani soyayya, sabida babu muhalli ta a zuciyata, domin tuni Sufyan ya tarwatsa wannan fagen, abinda ya sa zan yi auren ma sabida iyayena, na fahimci babban burin su bai wuce na matsa ba, ba kuma wai don sun gaji da ni ba, aa sai dan suna buƙatar farin cikina, suna buƙatar na zauna gidan mijin tamkar ƴar uwata, kuma na fahimci basu taɓa fidda rai da samun haihuwar ba, ni kaina kullun cikin addu'a ni ke, Allah ya ya zaɓa min rayuwa mafi alheri, kamar yadda iyayena suke min.
Bayan na koma na sanar da Maama, "Allah ya tabbatar da Alkhairi." kawai ta faɗa.
A cikin satin ne iyayen likita suka zo, Likita da ban san sunan shi ba, kuma bana buƙatar sani, suna zuwa da niyyar neman aure, ashe ma Baaba ya san iyayen shi, tsofaffin abokai ne shekara da shekaru, maimakon neman aure sai na aka ɗaura aure, da mijin da Nafeesa bata san sunan shi....
Sai dai sadakin shi da ya zo a hannuna, na karba ina jujjuya wa, tare da hawaye a ƙwayar idanuna, da fargabar wanne irin miji zan faɗa mawa, sauƙin ina jin shi a raina, sabida tun daga ranar da ya zo Maama ta sa na yi istihara a kan shi, kuma ba laifi ina jin natsuwa a tattare da shi, ba kamar Sufyan ba, a lokacin da tace in yi istihara cewa na yi, ai na ma tabbatar da alheri ne, ashe sharri ne a tare dani, sharrin da ya min katanga da ganin ƴaƴana......
Ban ƙara jin ɗuriyar likita ba domin ba ma da wata hanyar tuntuɓar juna, baya da number ta bana da tashi, gidan mu ma ban san ya aka yi ya zo ba, sai a bakin Baaba na ke jin wai zai zo ya ɗauke ni, wai ashe har Baaba ya canza mun kayan daki an kai, ba tare da sani ba, lallai iyaye rahama ne, duk wanda ya wulaƙanta su zai ga ba daidai, nima Allah ne ya soni da rahama shiyasa ya dawo dani hanya na roƙi gafarar su, har abin ya zo min da sauƙi, sabida har da alhakin su ke bibiyata.
***************************
Da mamaki na ke kallon shi, yana riƙe da bututun mai yana matsawa jerin motocin da suka bi layi, na sauke glass ɗin ina bin shi da ido, kamar dai bashi ba, kamar ba Sufyan ba ne sanye da kayan gidan man ɗanmarna, goye da mutun a bayan shi, na murje idona a lokacin da na ji hannun doctor HAISAM a cikin nawa, yana matsawa a hankali alamun na samu natsuwa, HAISAM da ya canza min rayuwa, Haisam da ya buɗe wani sabon shafi na halastacciyar soyayya, Haisam nawa, Haisam da ya haska mun gobe na..
Ya ranƙwafo saitin kunnena cikin sanyin muryar shi ya na faɗin "Anga tsohon sweetie, shine kike ƙoƙarin bi ta ƙarfen motar."
Na watsa mishi hararar ƙauna tare da kulle glass ɗin ina kallon shi, yayin da ya sumbaci hannun nawa, dai dai lokacin da layi ya zo kan mu, ya sauke glass ɗin gefena, ban sani ba ko da gayya ya yi maganar, ni dai na ji ya ce "Malan Sufyan barka da rana.."
"Likita.." Sufyan ya juyo a wahale da murmushin babu a fuskar shi, sai maganar ta tsaya, ya zuba min ido yana nuna ni da hannu, kafin ya murmusa ya ce "Likita ina ka tsinto min Nafeesa ta.."
Haisam ya kalle ni sannan ya kalle shi ta ce "Matata ce, bana faɗa maka na yi aure ba."
Ya yi baya baya tare da ware idanu waje yana tambayar "Matar ka?
Haisam ya jijjiga kai tare da ƙara damke hannuna ya ce "Eh...
Sai na ga ya ja baya yana huci, yayi da doctor ya zuge glass ɗin, ban san me Sufyan ya ke faɗa ba, sai dai bugun motar mu da ya ke yana masifa, ina ganin abokan aikin shi suka janyen shi, sannan aka bawa Haisam haƙuri aka sa mana mai muka ja muka tafi..
Sai da muka yi nisa sannan Haisam ya ke sanar da ni, ashe duk tsawon lokacin nan Sufyan yana dakon na neme shi, a duk tsawon lokacin nan yana jiran na neme shi na roƙe shi ya maida ni gidan shi, ashe har lokacin a tunanin shi ina dakon soyayyar shi, ashe lokacin da ya ce a cire min mahaifa sai da likitan ya bashi shawara a tsayar da haihuwar kawak, sai ya ke faɗa mashi idan na tsayar da haihuwar wai zan iya rabuwa dashi na auri wani, shi kuma so ya ke mu dawwama tare da shi, so ya ke na zauna dashi shi ɗaya, so ya ke duk inda zan tafi in dawo na dawo gare shi, wai yana sona! SO FA! Shima ya yi KUSKUREN SO, ba so bane, sha'awa ce da burgewa, da kuma yana jin duk duniya babu macen da zai mulka kamar baiwa irina, KUSKUREN SO Sufyan ya yi, ga asalin so na ga Haisam ɗina.
"Amma kin same.? Na tsinkayar shi yana faɗa bayan ya yi parking gefe ɗaya
Na girgiza kai, ya jefa min murmushi ya cigaba da faɗin "Ban cire miki mahaifa ba Nafeesa, banda zuciyar Mugunta, na tabbatar wannan mutun ba sonki ya ke ba, so ya ke ya more ki."
Sai na ji hawaye sun ɓalle min, na zura mishi ido cikin son ya tabbatar da abinda ya fada..
Ya kuwa tabbatar min "Eh, na kulle bakin mahaifar nan, domin duk lokacin da kika buƙaci haihuwa, lokacin da kika buƙaci gyara kuskuren ki na ƙwance miki, sabida na tabbatar sai kin dawo, ashe ban sani ba kaina na taimaka."
Na fashe da kuka tare da rungume shi ina godiya ga Allah, sai na ji komai ya goge daga gare ni, sai na ji wani irin farin ciki da ƙaunar shi na yawo a zuciya ta, lallai Haisam mutun ne, lallai Namiji ne amma ba irin mazantakar ta Sufyan ba, wannan shine asalin so..
Ya ɗago fuskata tare da lakace hawayen da suka wanke min fuska ya ce "Muje na ƙwance? Kin shirya ƙarɓar babyn mu.?
Tsigar jikina ta tashi, na hau gyaɗa kai ina hawaye cikin tsananin farin ciki, yayin da tarin buruka suka dawo, yayin da asalin so yayi sallama a zuciyata, sai na ji na tashi daga NAFEESAR SUFYAN, na kuma asali NAFEESAR HAISAM, mutum da zai taimake ka ba tare da sanin ka, mutumin da zai taimake ka ba tare da wata alaƙa ba, wannan shine MASOYI, tabbas da na yi KUSKUREN SO, amma yanzu na gyara kuskure na...
Shittttt ya ɗaura hannun shi bisa bakina, sannan ya miƙo min wayata "Maama na kira...
" Ɗauka, ka faɗa mata Nafeesar Haisam na mata al ishirin da samun jika.."
"Ba ruwana. "Ya kan ga wayar a kunne, sannan ya ɗaukar har da rusunawa ya gaida ta, cikin ɗabiar sa da na ke so, ɗabiar mutunta iyayena, ya na jin tamkar su suka haife shi, ban san irin wannan daɗin da ake ji idan an daraja iyayen ka, ban san irin wannan mutuntar ake ji ba...
Sai da ya gama wayar sannan ya miƙo min muka gaisa, bayan na aje na ke tambayar shi "Na ga baby a bayan Sufyan.."
Anan ya ke faɗa min, ashe Sufyan ɗin tsohon abokin shi ne, ashe bayan mun rabu Asiya ta haihu, rashin saa yarinyar ta zo a sikila, bayan bincike aka tabbatar da ƴar ba ta shi bace, DNA din su bai zo ɗaya, anan asibitin su Haisam aka yi case ɗin, suka ci mutuncin juna, ƴan uwan Asiyan suka naɗa mashi dukan tsiyan bayan ya mari Asiyar a gaban su, suka ce ya wulaƙanta ta, ya jefe ta da zina, da ƙyar aka kashe case din, kuma an bashi ƴar shi, sabida ta haihu bayan maida auren su da wata baƙwai kuma a addinance dole ya riƙe yarinya, sabida muddun aka haifi ƴa wata shidda da aure ta mijin ce, sai dai idan uwar ta tabbatar ba tashi ba ce, to kuma Asiya ta kafe a tashi ce, sannan fa da ta tashi tafiya sai da ta ƙwashe komai na shi ta, bata bar mishi komai ba, sai kayan sawa, duka wata uku da suka wuce ta yaye ƴar ta maido mishi ƴar sa, kin sa crisis na masu sikila, yau asibiti gobe gida, gashi Umman shi ta ce ba zata amshi ƴar ba, sanadin baya zuwa aiki sosai shine inda ya ke aiki company suka sallame shi, dole kuma ya kula da ƴar because duk bayan 2weeks ya ke kaita police station a ga lafiyar ta, sabida Asiyan ta shiga da report zai kashe mata ƴa....
Kin san me? Ranar da na zo gidan ku shi yace dan Allah na zo na ga ko lafiya kike, na baki shawara ki neme shi ku rufawa juna asiri ki koma, so bayan na zo sai na ga nima ina buƙatar mata irin ki, kawai sai na shigar da kaina, na koma na ce mishi kin ce zakiyi tunani, kafin nan har na aiko, wannan haukan da kika ga yana yi, tsine min ya ke, wai na ci amanar shi....
Maimakon na ji tausayin shi, ai sai dariya ta ƙwace min, na cigaba da tuntsura abina son raina....
Alhamdulillahi..
Alhamdulillahi...
Nan ma kawo ƙarshen littafin KUSKUREN SO, INA FATAN KU ƊAUKI DARASIN DA KE CIKI KU YI WATSI DA SHIRMEN DA KE CIKI, SANNAN DUK WANDA NA ƁATAWA YA YAFE MIN....
IN SHA ALLAH ZAN FARA SAKIN SABON LITTAFINA, GA WANDA KE SO A YI MASHI DISCOUNT GA NUMBER TA NAN 08036953516 YA MUN MAGANA NA YI Saving ta shi tun kafin na fara.
UWAR SUKUM.
Oum Farouk......