Showing 51001 words to 54000 words out of 83936 words
na yanke alaƙa ta da ita, amma hakan ba zai yiyu ba, Fannata ta daban ce, sai na zabga mata harara na ce "Aniyar ki ta bi ki wallahi, ai sai yanzu na fahimci daɗin rabuwa ta da Sufyan kike ji."
Ta ɗaga min hannu "Ya isa dan Allah, a batun Sufyan na daɗe da miki uzuri, faɗa min me ya ce miki.?
"Yana cikin tashin hankali, daga jin muryar shi kin san baa daidai ya ke ba, Ina tausaya mishi Fannata, bai yi dacen Uwa ba, so ta ke ta kashe min miji, ce wa fa yayi idan ya mutu ni ce sanadi, ina ƙyautata zaton ciwon zuciyar shi ya tashi shiyasa bai kirani ba duk tsawon lokacin nan. "
Ta kalle ni sheƙeƙe ta tambaye ni "Ikon Allah, yana asibiti ko gida?"
"Ban sani ba.." Na furta har da ƙananan ƙwallana.
"To ya maida auren ku?"
Na girgiza kai ina ƙwalla, ita fa da alama burin ta bai wuce kar a maida shi ba, ba ta san cewa ina matsayin matar shi ba har ranar da na haihu.
Sai na ga ta murmusa tana faɗin "Har yanzu ba ki san shu'umancin namiji ba Nafeesa? Wallahi Sufyan ƙarya ya ke miki...
A fusace na ce "Dakata dan Allah, kar ki ƙara ƙaryata min miji Fannata, har gwamma ki ce ni ke ma ki ƙaryar ba shi ba, sannan da kike maganar shu'umancin namiji ina ce na fiki sani, sabida ko ba komai ni na yi auren na zauna dashi a inuwa ɗaya, ke fa? Har yanzu ba ki yi ba, baƙya wancen inuwar baƙya wancen.
"Da irin tsinannen auren ki ai gwamma babu.."
Na kalle ta da sauri raina a dagule, a hankali na ce "Auren nawa ne tsinanne?"
Ta gyaɗa kai "Eh."
"To ke ma kiyi tsinannen idan kin isa, kin ga dan Allah ta shi ki tafi gidan ku, ina ce ba gidan uban ki bane nan, ke duk yadda mutun ke son ku yi mutunci sai kin ɓata mishi rai sabida tsabar bakin ciki da hassada, to ki je don kan ki."
Ta ƙwashe da dariya tana kallona, sai na fahimci so ma take ta cinna min hauka, na maka mata harara lokacin da ta kai min duka a cinya tana faɗin "Daɗi na da ke gori ƙawata, kuma kin san me? Ni fa wallahi na daɗe da miki uzuri, idan akan Sufyan ne, komai is allowed, yanzu faɗa min me ya ce miki?"
Ɗan siririn tsaki na ja sannan na ce "Wai na je na bawa Ummana shi haƙuri."
Ta kalle ni sheƙeƙe tana tambayar "To me kika mata?"
Na taɓe baki "Me fa? Aikin asiri ne kawai."
"Kuma za ki je?" Ta kafe ni da ido.
Ya kalli cikin idonta, da alamu kalmar aa take son fita daga bakina, na murmusa, lallai bata san girman SO ba, bata san soyayyar da muke ma juna ba, ko da ya ke ina zata sani tunda ba aure ta yi ba.
"Faɗa ɓacin baki, tare zamu je.."
Ta ƙwashe da dariya tare da miƙewa ta ɗauki hijabin ta ta mayar, sannan ta saɓa jakkar ta, tana min wani banzan kallo kamar yadda nima shi na ke mata.
"Wata ƴar ƙaramar zawara ya kamata ki nemo ta rakaki ba ni ba.." Ta furta tana kashe ni da murmushi.
Zawara? Har ga Allah kalmar ta min ciwo, a hankali na ce "Zawara fa kika ce Fannata?"
Ta ɗaga gira ɗaya still da murmushi a fuskar ta ta ce "Eh mana sakin wawa.."
Wato Sufyan ne wawa ɗin? Ban san lokacin da na miƙe a fusace ba, sai dai kafin na bata amsa ta fice ɗakin da gudu tana dariya, ina jin tana ma su Maama banƙwana a tsaitsaye sannan ta fita.
Ni kam bisa katifa na koma daɓas na zauna, yayin da maganganun shi suka dawo min a ƙwalwa, dama Fannata ce ta hanani tunanin shi, na janyo wayata na sake kiran wayar shi, amma still taƙi shiga, dibarar tura mishi saƙo ta zo min, don hana na hau typing..
" _Dan Allah ka kira ni, Ina so na san halin da kake ciki mijina._"
Ni fa na ji a raina, tuni Sufyan ya maida auren mu, kawai faɗa min ne bai yi ba, so ya ke dai in je in bawa Umman shi haƙuri, kuma zan je ɗin, ai ba don ita zan yi ba, don mijina zan yi, na lumshe ido, yayin da wani sashe na zuciyata ya tunar min, ai kamar ma ba ni ya dace na je ba, Maama ce ya kamata in lallaɓa su je su yi magana ta furfura da furfura, na san hakan ba ƙaramin farantawa Sufyan zai yi ba, sai na samu kaina da sakin ja'irin murmushi, murmushin da rabon iyi shi tun bayan da na baro gidan su..
Jin shiru bai kira, yasa na yi tunanin ko dai ciwon na shi ya tashin da gaske, ko dai mutuwa zai yi ya bar ni, na miƙe jikina, a sanyaye, gashi dai rabon ma da na gaishe da Maama wallahi na yi sati, ko magana bana mata, ban san yadda zan yi na lallaɓa ta ba ta je ta bawa Umman Sufyan haƙuri.
A sanyaye na fita tsakar gida, na saci kallon su, suna zaune ita da Teemah suna jefa fira, sai na ji kunya ta lulluɓe ni, cikin dauriya na ƙarasa bisa tabarmar na raɓa kaina a ƙasa, ina ji a jikina dukkanin su kallo suka bi ni da shi, na ɗan zakuɗa murya ƙasa ƙasa na ce "Maama."
Sanin ba zata amsa min ba, ya sa na cigaba da faɗin "Dan girman Allah ki taimaka ki yafe min duk abinda ba yi, wallahi na san na yi kuskure dan Allah ki gafarta min, ba zan sake ba." Na fashe da kuka ƙasa ƙasa sai ka ce gaske, nan kam ba su san nima tawa ta kawo ni ba.
Ta zuba min ido, abinka da uwa, cikin sanyin jiki ta ce "Shikenan, Allah ya yafe mana baki ɗaya."
Na ƙara sautin kukana "Dan Allah ki ce kin yafe min Maama, ko na ga daidai a rayuwata."
"Na yafe miki Nafeesa, Allah ya yafe mana baki ɗaya, yayi maku albarka tare da ƴan uwan ki."
Na ƙara ƙasa da kaina, har ga Allah sai na ji wani sanyi na ratsa ni, da ƙyar na daure na kalli Teemah na ce "Ke ma ki yi haƙuri."
Sai na ga ƙwalla na zuba daga idon ta, ta rungume ni tana faɗin "Nima ki yafe min Yaya.."
"Baki min komai ba Teemah.."
Muka yi shiru baki ɗaya, kamar waɗanda ruwa ya cinye, ina so na mata ainahin maganar da ta kawo ni ina jin kamar ba yanzu ya kamata ba, tunda dai ko zan je, sai zuwa gobe, don haka na miƙe a sanyaye na hau tattara ƙwanukan wanke wanke, ina jin Maama na faɗin "Ki bar shi Teemah zata yi, baa so kina yawan jijjiga jikin ki."
Na ce "A a Maamana, Ummana, Momcyna, Sweetie na, ai daga zaune zan yi, kuma na daɗe ban yi ba."
Ta murmusa, yayin da Teemah ta zo ta taya ni, ta min ɗauraya, muna tsaka da yi na kalle ta na ce "Sufyan fa ya kira."
Ta jefa min kallon tuhuma "Shine dalilin da yasa kika zo kika bawa Maama haƙuri?"
#UWAR SUKUM.
💧💧 *KUSKUREN SO.*
FREE BOOK
*HASKE WRITER'S ASSO.*
*FEEDOHM*
Wattpad@Feedohm
_Ga ba ɗaya littafin nan sadaukarwa ne ga NAFEESA Muhammad SULE, maman jinjiri, Alherin Allah ya kai maki a duk inda kike._
_Ina kike Aunty Zainab Abubakar Kotorkoshi? Ke ma ina maki fatan alheri._
*031*
Ta jefa min kallon tuhuma "Shine dalilin da yasa kika zo kika bawa Maama haƙuri?"
Shegiyar yarinya da saurin ɗago abu ta ke, na girgiza kai da sauri na ce "Aa wallahi, kawai dai ina yawan mafarkin abubuwa marasa ƙyau, shine na ga ƙara in nemi yafiyar uwata."
"Humm.." Kawai ta faɗa, da alamu bata yadda da maganata ba.
Ranar ni da kaina na yi mana girki, da daddare na zubo mana a plate na zauna kusa da ƙafar Maama ina matsa mata yatsun ta, kafin ta janye mu fara cin abincin a tare, kamar yadda mu ke yi kafin aure ya maishe ni mara kunya, bayan mun gama na miƙe zan ƙwashe ƙwanukan ta riƙe min hannu cike da tausayi irin na uwa ta ce "Bana so kina yawan girgiza jikin ki, dawo ki zauna ƙanwar ki zata yi."
Auta ya amshe "Wai yaushe yaya ta dawo kamar da, ko an ƙarashe kashe auren baki ɗaya.?
Na fakaici idon Maama na zare mishi ido ina hura hanci, alamun zai ci uwar shi idan bai yi wasa ba, kafin na maishe da kallona gun Maama ina faɗin "Maama dama ina so in faɗa miki Sufyan ya kira."
Sai na ga ta saki murmushi tana kallona, kafin ta ja siririn tsaki ta ce "To."
Na yi shiru ina karantar yanayin ta, sai na ga kamar itama ɗin ta gano wani abu daga tubana, na ƙara sadda kai ina faɗin "Ya ma maida ni."
Babu komai a fuskar ta ta ce "Abu ya yi ƙyau, sai a fara shirin komawa, dama haka ake so."
Na sosa ƙeya na cigaba da faɗin "Kin san na yi ma Ummar shi rashin kunya sosai Maama, shine ta ce sai an je am bayar da haƙuri."
Ta ƙura min ido, kai tsaye ta ce "Ƙarya kike, baki isa ki ma uwar shi rashin kunya ba Nafeesa, shi ba sakarai ba ne irin ki, sai dai wani abu."
Na kalle ta da sauri ina faman rantsuwa "Wallahi tallahi, ai rashin kunyar da na yi mata ne yasa ta ce sai an je an bata haƙuri tukun zata bari ya maida ni."
"Amma kin ce ya riga ya maida ki.?
Na hau inda inda "Ai da yake bata sani ba, wallahi...
"Ya isa haka nan, yanzu ya kike so a yi? Wa zai je ya bata haƙurin? Ni ko Baban ku?" Ta ƙura mun ido.
Wani daɗi ya ratsa ni, sam ban yi tunanin zata amince da wuri haka ba, kai tsaye na ce "Ke Maamana.."
Sai na ji sun ƙwashe da dariya baki ɗaya har da Auta, mamaki ya kashe ni, na zuba ma sarautar Allah ido, ina kallon su ɗaya bayan ɗaya, har sai da suka gama mai isar su, sannan Maama ta ce "Kai, Allah ubangiji ya mana maganin abinda ba zamu iya ba, Nafisatu ni ce zan je in bada haƙurin kenan?"
Na daure fuska tare da gyaɗa kai na ce "Eh." Gani ni ke abin ma na neman ya koma rainin wayau.
Maama ta ƙara ƙwashewa da dariya tana faɗin "To Allah ya ƙyauta."
"Amin, gobe zaki je?" Na tambaya fuskata a ɗaure, don wallahi raina ya ɓaci da wannan dariyar rainin wayan, kar fa su ga na basu haƙuri su maishe ni banza, yanzu sai na koma ƴar gidan jiya, don wallahi akan na koma gidan mijina babu abinda ba zan iya ba.
Maama ta murmusa "Wato Nafisa ban ƙara sanin ke shashasha ba ce sai yanzu, ni zan je na bawa uwar Sufyan haƙuri? Shi lokacin da ya min iskanci kin bashi shawarar ya zo ya bani haƙuri? Ai shegantaka biki ce, to ba zan je, shi bai san darajar iyayen ki, ke ce kika san ta shi, don baki da kunya kin ƙwaso jiki kin bama uwar ki haƙuri ashe da biyu? Ba don Allah kika yi ba, ai dama tun da na ga kina maƙure maƙure na san wallahi da wata a ƙasa. "
" Dan Allah Maama.. " Na faɗa kamar zan fashe da kuka.
Ta tamke fuska tare da watsa min harara tana faɗin "Tashi ki bani guri."
Ƙwallan takaici suka zubo min, na yi wanke wanke, shara, girki a banza babu biyan buƙata, sannan har Teemah na bawa haƙuri duk a banza, na ja majina, wallahi da aƙwai yadda zanyi da na karɓe neman gafarar da na mata yanzu, raina a dagule na ce "Allah ya taimake ni ina da ƙafa biyu kamar yadda kike da shi, idan ba zaki je ba ni sai na je."
Teemah ta riƙe haɓa "Sadaƙallahul azim, rashin kunya fil a ƙwali, anya Maama baa canza miki Nafeesa ba a asibiti lokacin da kika haife ta.?
Ban saurare su ba, na wuce fuuu kamar zan tashi sama, yayin da Maama ta bini da kallo sai dai babu alamun damuwa a fuskar ta, da alamu ita ma ɗin ta min uzuri kamar yadda Fannata ta min.
A lokacin da na koma ɗakin na yi tunanin zan iske kiran Sufyan birjit ko kuma messages ɗin shi, amma babu ko ɗaya, hankali ya ƙara tashi na faɗa bisa katifa na shiga rizgar kuka.
Tunda Safe Baaba ya tayar dani da warning wai ance mishi ina da niyyar zuwa gidan su Sufyan bama uwar shi haƙuri, to kar na sake na taka ƙafata muddun ba Sufyan bane ya maida auren mu, sannan ya bani iznin zuwa bama uwar tashi haƙuri, wallahi takaici ya hanani ce mashi komai har ya kaɗa babbar rigar shi ya fice daga gidan, dan Allah ku ji fa son kai, yau da ace mahaifiyar shi ce Maamar mu tayi mata laifi haka zai ce? Na share guntayen hawayena ina jin babu ubanda ya isa ya hanani zuwa gyaran aurena a cikin su, tunda babu mai aurena cikin su idan nawa auren ya gantale.
Na koma cikin tashin na hau shirina, sai da na kintsa tsab sannan na tura mishi message don na lura message ɗin na shiga, lafiyar maido wa wace babu.
_Zan iya yin komai a kan ka Sufyan, dan Allah ka kular min da kan ka, insha Allahu yau zan zo na bawa Umma haƙuri MIJINA._
Na miƙe na leƙo tsakar gida, na koma na zauna, yayin da tunanin inda zan samu kuɗin mota ya min kaca kaca a raina, don wallahi ko naira biyar bana da ita, ina nan zaune shawara ta zo min, dole in je ɗakin Maama ko Babaa na samo kuɗin mota, na san dai idan na tambaya ba bani zaa yi ba, don haka abinda ban taɓa yi ba tun ina yarinya shi ya kamata in yi, abinda na sani, abinda bature ya ce a Mistake is not a mistake, but to repeat a mistake is a mistake, kuma ni ai ba zan yi fatan maimaitawa ba, na miƙe na fice cike da ƙwarin guiwa, suna nan dai a gantale tsakar gida suna suyar ƙosai.
Dakin Mamaa na fara shiga na buɗe jikkar ta, Allah ya taimake ni na samu 10k da ƴan canji, shima ina da tabbacin kudin islamiyya yara ne, sabida ita ce shugaban makaranta kuma ita ke aje kudin, ban damu na na ƙwashe su tsab, na san zasu kaimu Kano mu biyu, don kar ma Fannata ta ce bata da kuɗi, don wallahi na gama yankewa ko tana so ko bata so tare zamu tafi, na saka su cikin hijabi na fito ina zunburar biki, na saci kallon Maama da dan ba ta ni ta ke ba, kuma na tabbata ba zata yi tunanin wani abu na je yi mata a daki ba, har zan koma ɗaki sai kuma na yi tunanin bai kamata na je hannu biyu ba, ko ɗan wani abu ya kamata in riƙe, don haka kai tsaye na nufi ɗakin Baaba ina zunɓure zunɓure, na kai ƙofa na tsinkayi Maama na tambaya ta "Me zaki mashi a ɗaki."
Ciki ciki na ce "Mutun da ɗakin uban shi idan zai shiga sai ya nemi izni?" Na zunɓuri baki na faɗa ciki ina ƴan ƙananan surutai.
Cikin rashin saa ban iske kuɗi ba, takaici ya rufe ni, har zan fita na yi tozali da wayar shi, ya maƙalata a caji, da ya ke idan baida caji gida ya ke barin ta, ya tafi da ƙaramar, babu tunanin komai na ɗauke ta ina faɗin "Na ran ta..." infinix ce hot 8 pro, na tabbatar sai ta kai 38k ko sama, na zunɓuri baki, duk dai su suka ja ma kan su, dan Allah da aƙwai mutunci da ba kuɗin zan tambaye su ba, su bani in tafi rai a sanyaye? Ko da ace su ba zasu je ba? Na ja tsaki, haka kurum sun sakani ƙaramar sata.
Kuma fa kar ku ce sata na masu wallahi ko ɗaya, rance na yi, kuma ai kuna jin a gaban ku da zan ɗauki wayar Baaba na ce na rance, don haka kar ɗan Alanguburon da ya kira Nafeesa ɓarauniya, na tabbatar idan na koma gidan Sufyan a ranar zan samu linkin ba linkin su in biya su.
Na koma ɗaki na ƙwanta irin kamar na bar maganar, ban sake fitowa ba sai da na bari Umma na wanka, na zura hijabi na da ke aje na fice sadaf sadaf, ina jin Teemah na faɗin "Maama ƴar riƙon ki zata fita."
"Uban ƴar riƙo......" Na bata amsa lokacin da na kai zauren gidan..
#UWAR SUKUM.
💧💧 *KUSKUREN SO.*
FREE BOOK
*HASKE WRITER'S ASSO.*
*FEEDOHM*
Wattpad@Feedohm
_Ga ba ɗaya littafin nan sadaukarwa ne ga NAFEESA Muhammad SULE, maman jinjiri, Alherin Allah ya kai maki a duk inda kike._
_Ina kike Aunty Zainab Abubakar Kotorkoshi? Ke ma ina maki fatan alheri._
*032*
Tafiya ni ke ina hawayen cike da takaicin mutanen nan, wato su suna zaune gidajen mazajen su lafiya lau cikin ƙwanciyar hankali, sai ni sakara suke so na yi wasa da na wa aure? Ni banza da bata san ciwon kanta ba? To wallahi su je dan kan su, insha Allahu sai sun yi mamakin Nafeesa, sai aurena ya zama abin ƙwantance, daga haka har na isa gurin mai siyar da wayoyi, da ya ke bamu da ni sa da shi sosai, bayan na miƙa mashi wayar ya jujjuya ta, ya cire cewa cover sannan ya tambaye ni "Malama Nafeesa, nawa zaa bar min wayar nan?" Ya sanni sosai gaskiya.
"Ni fa ba siyarwa zan yi ba, jingina nake so ka amsa, ka bani kuɗin ta ka aje wayar, idan na maido sai ka bani wayata." Na faɗa maku ni ba ɓarauniya ba ce.
Ya miƙo min wayar, na ja baya ina girgiza kai, yayin da ya ke faɗin "A'a gaskiya."
Na yi jim ina