Showing 66001 words to 69000 words out of 83936 words

Chapter 23 - KUSKUREN SO Book Complete by Feedohm.txt

Feedoms   

21 Sep 2025

1708

daga baya zaki yi danasani.."

Sai na ji ma ya bani haushi, na daure na girgiza mishi kai ina faɗin "Insha Allahu bana tare da ita.."

"Ok.."

"Mahaifar zaa cire?" Na tambaya har lokacin idona na kan shi.

"Aa, zaa dai tsayar da haihuwan baki ɗaya."

"Me yasa ba zaa cire ba?" Na tambaya har lokacin idona a kan shi, don sai na ke ganin tamkar baya son aikin sai ka ce jikin shi, sai ma na ga kamar dama da gayya ya bama Sufyan shawarar mu raba aure, ƙyila ma aƙwai wani munafircin a zuciyar shi

"Ba shine mafita ba.." Ya bani amsa tare da umurtar nurse ɗin ta taho tare dani....

Ban san me aka min ba amma dai bamu ɗauki lokaci ba aka dawo da ni ɗakin da nike suka ƙwantar, ni dai da ido na ke bin su, yayin da zuciyata ta yi duhun gaske, hawaye ma su zafi na bin gefen kunne na, sai na ke jin tamkar na tafka kuskuren da har abada ba zan taɓa gyara shi ba, sai na ke jin dama ban aikata ba, sai na ke jin dama rabuwar na nema, sai dai kuma ba zan iya rayuwa babu Sufyan ba, kamar yadda ba zai iya rayuwa babu ni ba...

Wayata ta ɗauki ruri, na juyar da kaina ina kallon ta, a karo na farko na ji bana son Magana da shi, kuma wallahi ban san dalili ba, amma dai na san baya rasa nasaba da wannan babbar sadaukarwar da na mishi, kuma na san nan da ƴan mintuna na huce.

Sai da ya min kira ya fi uku sannan na ɗauka na kanga a kunne, samun kaina na yi da faɗin "Bazan haihuwa ba Sufyan, ba zan ga ɗana ba..." Na fashe da wani irin mahaukacin kuka.

"To sai me Nafeesata? Ɗiyan da zan samu gaba ba su ishe mu rayuwa ba? Dan Allah ki ƙwantar da hankalin ki kin ji ko? Na san yadda kike ji, insha Allahu komai zai wuce." Ya ƙarashe maganar a tausashe.

Na yi shiru ina kukana, yayin da ya cigaba lallashina da kalaman soyayya masu rikita kai, har sai da na samu natsuwa, har sai da na ji tamkar babu abinda ya faru, sannan ya cigaba faɗin "Kin ji ni shiru ko.?

A sanyaye na ce "Har yanzu ba su sallame ka ba.?

"A'a tunda asuba Umma ta kira ni, yanzu haka na shiga Kano....





#UWAR SUKUM
[6/14, 8:33 PM] RN Feedohm: 💧💧 *KUSKUREN SO.*

FREE BOOK

*HASKE WRITER'S ASSO.*

   *FEEDOHM*
Wattpad@Feedohm

  _Ga ba ɗaya littafin nan sadaukarwa ne ga NAFEESA Muhammad SULE, maman jinjiri, Alherin Allah ya kai maki a duk inda kike._

_Ina kike Aunty Zainab Abubakar Kotorkoshi? Ke ma ina maki fatan alheri._

*039*




Kano? Na maimaita a raina, yayin da ƙunci ya mamaye zuciyata, sai na ke ganin tamkar bai min adalci ba, sabida ya san ina asibiti ina tsananin buƙatar shi kusa dani, amma zai tsallake ya tashi ya tafi kiran uwar shi, alhalin shine silar rabani da nawa ƴan uwan, na share guntayen hawayen da suka zubo saman kuncina, yayin da wani sashe na zuciyata ya tunatar da ni ba laifin shi bane, tsabar iskanci ne na uwar shi, to wai ma uban me zata mishi? Na faɗa a raina, a fili kuma wasu ɗumammun hawaye suka gangaro min, na yi shiru ba tare da na ce mashi komai ba.

"Nafeesa.." Ya kira sunana a tausashe.

"Uhwummm..."

Cikin mayaudariyar muryar shi ya ce "Kina jina kika min shiru? Kin san dai ba haka kurum zan tafi in barki ba ko? Bai kamata ki yi fushi ba."

Muryata ba rawa na tambaye shi "To mai zan yi Sufyan? Kana dai ganin jiya ni kaɗai na ƙwana asibiti..

"Subhanallahi, ina su Maama.?"

"Sun ce ba zasu zo ba."

A hasale ya ce "To sabida me? Ke ba ƴar su ba ce? Su fa mutane ba sa ma kan su adalci wallahi, ta ya kina asibiti tun jiya, kuma sun sani amma su ƙi zuwa sabida tsabar rashin mutunci? Wato gidan ki ne da zaa ci bulus kawai ne gurin zuwa?"

"Ni dai ya ishe ni haka nan.." Na furta cikin kuka mai kama da tsawa.

Sai na ji yayi shiru, kamar yana mamakin furucina, amma sai ya canza maganar "Ance anjima za'a sallame ki, sai ki wuce gidan ku ko? Tunda kin ga ba yau zan dawo ba, ko zaki iya zama ke kaɗai a gidan.?"

"Me yasa ba yau ba.?"

"Ina da uzuri ne Nafeesa, dan Allah kar ki min tada min hankali, kin san dai ko ina nake ina tare da ke ko?"

Na yi shiru zuciyata na ƙona, ina jin wani raɗaɗi a cikin ta, a lokacin idan na kuskura na buɗe baki wallahi uwar shi zan zaga, kuma dai na san makomar aure na.

"Kin yi shiru."Ya katse shiru na.

"Me zan ce?"

"Gidan ku zaki wuce? Ko kina iya zama har ke kaɗai?"

"Ba zan je gidan mu ba.."

"Ok ba damuwa, kin ci abinci ko.?"

Kamar na ce ubanka ya kawo min, sai kuma na fasa sanin me ka iya biyo ba, na haɗiyi mulmulallen abinda ya tsaya min a maƙoshi ina faɗin "To ka kawo min ne?"

"Ya salam, Allah ya baki haƙuri, kin kasa fahimta ba, bara in tura miki 10k account ɗin ki, sai ki samu wani ya siyo miki kin ji ko? Dan Allah ki yi haƙuri, na san dole ran ki ya ɓaci, amma ya na iya babyna? Nima tilas aka mun, ki yi haƙuri kin ji ko? Wallahi duk inda nike ina tare da ke..."

Takaici ya saka na yanke wayar na fashe da kuka, na rasa wanne irin abu zan kira wannan? Shin wulaƙanci koko me? A ce ba za'a bar mijin ka yayi jinyar ka ba, ni wallahi na san ba laifin shi ba ne, don haka kurum ba zai iya wofitar da ni ba, kuma wallahi sai na ɗauki matakin da basu taɓa zato ba..

Ina jin kuɗin suka shigo, ni takaici ma suka bani ko wayar ban kalla ba, na ja tsaki na cigaba da kuka na, sai na ke jin kaina tamkar marainiya, ga wata yunwa da nike ji, gashi ni kaɗai ban san wa zan aika ba, na ƙwanta ina kallon sama da tunanuka barjit a raina.

Ganin dai bani da mafita ya sa na sake kiran Maama , amma matar nan wayar ta a kashe, ba abun na kira Baaba ba don babu waya a hannun shi, sabida ta hannun shi ta samu matsala, ba kuma dauke waccen

Wajen 12 tunani ya ƙwance min, bisa tilas na kira number Fannata yayin da gabana ke faɗuwa don ban san wane irin rashin mutunci zata shuka min ba, koma dai me zata yi, na tabbatar dole idan ta ji halin da nike ciki ta zo wallahi, kai idan ma bata zo ba, ai sai na kira Uwar ta, ita kam dole zata zo..

Kira ɗaya ta ɗauka sabida bata da number, Layin da Sufyan ne ya siya min ya ce kar na sake na bawa tarkacen ƴan gidan mu.

"Assalamu alaikum.." Ta faɗa kamar wacce ke cikin annashuwa.

A sanyaye na kira sunan ta "Fannata.." Yayin da kunya ta min dirar mikiya, don fa ko da ta yi aure ko ɗan guntun message ban tura mata na fatan alheri ba, kuma na san ta san na sani, sabida su Maama da Teemah su ne iyayen biki..

"Na'am, da wa nake magana.."

"Nafeesa.."

"Nafeesa." Ta furta kamar mai son tuno sunan, don na tabbatar bara taɓa tunanin zan kira ta ba.

"Eh."

"Wai Nafeesar Sufyan?"

"Eh Fannata."

"Ikon Allah, baiwar Allah dama kina da number ta?"

"Uhmm."

"Ok.."

Na yi shiru ina tunanin ta inda zan fara, yayin da na tsinkaya ta tana tambayar "Lafiya dai ko?"

"Da sauƙi Fannata."

"Allah ya sauƙaƙa."

Ban amsa amin ba, na cigaba da magana kai tsaye "Ina teaching hospital an ƙwantar da ni Fannata."

"Allah sarki, ba ki da lafiya ne.?"

"Eh, abinda ke cikina ya mutu shine aka fitar dashi. "

"Allah ya bada lafiya, ina miki sannu." Ta yanke wayar ta.

Sai na ji hawaye sun zubo min, na sake kiran wayar ta ɗaga cikin ƙosawa tana faɗin "Wai lafiya Nafeesa?"

Na fashe da kuka "Dan Allah ki kawo min abinci Fannata.."

Cike da mamaki ta maimaita "Abinci kuma.?

"Uhmmm."

"Bangane ba? Ina Sufyan ɗin? Don ba zan tambaye ki su Maama ba."

"Ni dai dan Allah ki kawo min." Na faɗa muryata na rawa.

"Ai ko babu dama, wallahi baki da kunya, wato yanzu na ke da amfani gare ki shine zaki kirani, ba'a faɗa miki nima aure na ke ba? Ko ke kaɗaice kika san darajar auren ki? To nima banda wannan lokacin Nafeesa..."

Na fashe da kuka na hau mata magiya, amma sai ta yanke wayar ta, sai na ji duka duniyar ta min zafi, na birki ce na cigaba da rera kuka na, a karo na farko da na ji na tsani kaina da har na biye na Sufyan na wulaƙanta na kusa da ni, da yanzu suna rige rigen zuwa gare ni, da yanzu suna zagaye da ni cikin kulawa da ƙauna, wallahi da na tabbatar Fannata a baki zata ciyar da ni, amma na wulaƙantan su, a kan wanda ya tafi ya barni lokacin da na fi buƙatar shi, duk da dai bai laifin shi bane, na uwar shi ne..

Wajen 1pm sai ga Fannata da ƙaton basket, ban ma san yadda aka yi ta gano inda ni ke ba, wallahi mamaki da daɗi ya sa na zuba mata ido, ta maka min hararar takaici tare da dungure min basket ɗin a gabana tana kallona, ban san me yasa ba, sai na ga ta ɗauke kai tana ƙoƙarin goge hawayen da suka taru a idon ta.

"Ya jikin.." Na ji zazzaƙar murya ana gaishe ni daga bakin ƙofa.

Na ɗaga kai a razane don ban yi zaton tare ta ke da wani ba, sai na ji gabana ya yi masifar faɗuwa, na kalle ta na kalle shi, a lokacin da ya aje min ledar fruit, na tabbatar da tare su ke, sabida yadda ya gogi jikin ta ba tare da Shamaki ba, sai na ga ya leƙa fuskar ta, ya ja mata hanci yana tambayar "Why are you crying?"

"Allah shi ƙyauta, fa shi na ke ba.." Ta faɗa tare da zunɓuro baki.

Ya lakaci hawayen ya dungure mata kai ya ce "Mai ƙarya.."

Ta zabga mishi harara cike da ƙauna, yayin da na kasa ɗauke idona a kan shi, ko a mafarki, ko a tunani ban taɓa zaton Fannata zata samu miji irin wannan ba, idan na ce miji ina nufi ko ina zam zam, wallahi tallahi ban taɓa katari da ƙyaƙyƙyawan namiji irin shi ba, ba wai fari ba ne tas, aa wani irin skin gare shi, wacce ta gaji da hutu, ga ƙyau iya ƙyau, sai ka ce shi ya ƙera kan shi, sai na ga Sufyan tamkar 1 ne a cikin 10 mijin Fannata, sannan daga sutura da ke jikin su zaka tabbatar da kuɗi na magana a gurin.

Ban sani ba ko kallon da nike mishi ne ya ishe shi, sai ya ce mata "Idan kin gama call me.." Ya manna mata kiss zai fice.

Ta wani kamo hannun shi, shegiya da wata taɓaɓɓar fuskar ta, ta shagwaɓe tana faɗin "Ba fa daɗewa zan yi ba..

"Uhmmm.." Ya wuce yana mata dariya.

Sai lokacin na dawo hayyacina, na sauke ajiyar zuciya ina saƙe saƙe a raina, wallahi da na san gorin auren da nike mata Allah zai bata miji irin wannan da ban yi ba, don har ga Allah yadda na fi Fannata ƙyau da diri ban taɓa zaton zata auri wanda ya fi Sufyan ba, na sauke ajiyar zuciya ina kallon ta, ta wani ɗaure tana zuba min kunun gyaɗa a cup.

"Karɓa, wallahi ba dan halin ki na zo ba.." Ta dungure mun shi a hannu.

Na murmusa "Ba wani, don wa kika yi?"

"Mtsss, idan dan ke za'a miki abu da ba'ayi ba, darajar su Maama kika ji."

A tausashe na ce "Ni dai dan Allah kar ki cikani da ɗumin asara."

Ta dalla min harara tare da ɗan ƙaramin tsaki "Ba dai zaki canza ba."

Na jingina da gadon ina kurɓar kunu na a hankali ina lumshe ido, yayin da ta turo min chip har lokacin dai harara ta ta ke, irin kamar an mata dole nan sai ta zo, ni kam har wani lumshe ido na ke.

"Shi Sufyan ɗin akan me zai tafi ya barki da yunwa asibiti bayan shine ulmul'aba'isin ƙin zuwan su Maama?" Na tsinkaye ta tana faɗa ranta a ɓace.

"Uzuri ne ya ne ya kama shi."

"Uzurin banza, har ya fi lalurar ki? Kalle ki fa? Wai ma me ya same ki ma?"

Na slsalla mata harara "Kar dai ki zagar min miji, na san dai yanzu kin san darajar aure."

"Ba zan taɓa sanin irin darajar da kika sani ba Nafeesa."

Na taɓe baki ina faɗin "Na ji, na faɗa miki abinda ke cikina ya rasu, shine aka fitar da shi."

"Yau?

"Tun jiya."

"Da wata matsalar ne da har yanzu basu sallame ki ba.?

Na girgiza kai "A'a."

Ta kai hannu ta ɗauki card ɗin dake aje bisa tarkace na, sai na ga ta dafe ƙirji a razane tana kallona "Ƙarya kike, haihuwa kuka tsaida Nafeesa.?

Na fizge katin ina faɗin "Malama dan Allah ba ni kayana."

Ta zuba min ido kamar wacce bata taɓa gani na ba "Haihuwa kika tsaida?"

Cikin halin ko in kula na gyaɗa mata kai "Eh."

"Shine ya ce?

"Mu duka muka yanke."

Ta lumshe idon ta, sai ga hawaye na bin kumatu ta, murya a dakushe ta ce "Kin yi kuskure Nafeesa, wallahi kin yi kuskuren da har abada ba zai taɓa gyaru wa ba."

Na kalle ta sheƙeƙe lokacin da na miƙa mata cup ina faɗin "Dan ƙaro min."

Ba buge cup ɗin ƙasa a fusace tana faɗin "Ba zan ƙaro ba, ashe baki da hankali? Baki da ilmi? Kika tsaida haihuwar da baki riga kin yi ba? Nafeesa.

Na dakatar da ita "Ni fa abinci na ce ki kawo min ba faɗa ko shawara na kira ki ba.....



#UWAR SUKUM....
[6/18, 11:30 AM] RN Feedohm: 💧💧 *KUSKUREN SO.*

FREE BOOK

*HASKE WRITER'S ASSO.*

   *FEEDOHM*
Wattpad@Feedohm

  _Ga ba ɗaya littafin nan sadaukarwa ne ga NAFEESA Muhammad SULE, maman jinjiri, Alherin Allah ya kai maki a duk inda kike._

_Ina kike Aunty Zainab Abubakar Kotorkoshi? Ke ma ina maki fatan alheri._

*040*

Ta zuba mun ido har na kai aya, sannan ta fara tattara kayan ta tana hawaye ba tare da ta ce min komai ba, na sani duk duniya bayan iyayena babu mai ƙaunata irin Fannata, kuma nima a da na so ta fiye da tunani, auren Sufyan ne ya canza mun komai.

"Daga yau, kar ki sake nema har abada Nafeesa, dan girman Allah, ki manta da mun yi rayu a tare, na ɗauka ke mutun ce, ashe dabba ce a cikin shiga irin ta mutane, ashe ba mutane kaɗai kike cuta mawa ba har da kan ki."Ta furta har lokacin ƙwalla bai daina zuba daga idon ta ba.

Wallahi ban san ya akai ba, sai samun kaina na yi da fashewa da kuka ina faɗin "To ya zan yi Fannata, nima bana so wallahi, ba'a son raina ba..

Ta zuba mun ido "Me yasa?"

Na kifa fuskata a bisa tafukan hannaye na, ni kaina na san na tafka kuskuren da har abada ba zai taɓa gyaruwa ba, fatana Sufyan ya riƙe alƙawarin shi shine kaɗai zai rage mun raɗaɗi a rayuwa ta "Ina son shi, ina son Sufyan, ban zan iya rayuwa babu shi, zaɓi ya bani Fannata, mu rabu ko na tsaida haihuwa."

"Me yasa ba ki zaɓi rabuwar ba kika tsira da haihuwar ki? Wallahi wallahi ba zai taɓa zama da ke a haka ba, a tunanin ki abu ɗaya kika zaɓa, biyun babu kika yi Nafeesa."

Na hau girgiza mata kai "Ba zai rabu da ni ba, ba zan iya rabuwa da shi ba, mutuwa zan yi Fannata, ina son shi so na gaskiya.."

Ta girgiza kanta cike da takaici tana faɗin  "A haka ma kin mutu Nafeesa, wallahi kin kashe kan ki."

Bata kuma sake saurare na ba, ta tattara kayan ta ta fice daga ɗakin ina ƙwala mata kira, sai na ji duniyar gaba ɗaya ta min zafi, sai na ji ina ma na mutu na huta da wannan rikita rikitar, na shafi mara ta, wasu zafafan hawaye suka fito daga ƙwayar idona, shikenan ba zan haihu ba! Shikenan ba zan ɗauki abinda ya fito daga cikina ba? Me yasa na yanke wannan ɗanyen hukuncin? Na sake rushe wa da kuka, a dai dai lokacin nurse ta shigo ta bani sallama ta, ta juya zata tafi, har ta kai bakin ƙofa na ƙwala mata kira "Sister..."

"Na'am."

Na ɗauke hawayen dake fuskata da babban yatsa ina faɗin "Me aka min?

"Bangane ba?"

"Haihuwar aka tsayar mun ko cire min mahaifar aka yi baki ɗaya?"

Ta kalle ni a nutse tare da sakin ja'irin murmushi ta ce "Mahaifar aka cire...!

Wani haske na ga ya gifta cikin idanuna, yayin da kaina yayi masifar sarawa, na dafe shi da hannu biyu biyu ina wani irin kakari, cikin halin ko in kula ta miƙo min gorar ruwa tana faɗin "Abinda kuka zaɓa kenan da mijin ki, me yasa zaki shiga wani hali kuma? Na ɗauka murna zaki yi..."

Ni dai ban ce mata komi ba, hasalima ban fahimci me take nufi ba, ina dafe da kaina har ta fice daga ɗakin tana faɗin "Ku ƴan daɗi miji, baƙwa tunanin abinda zai je ya dawo, macace kaɗai zata juri dukkanin halin da miji zai shiga, amma su maza ba zasu jure ba..."

Na ɗau tsawon lokaci a haka, tun na miƙe don gaba ɗaya asibitin ta fice a kaina, na tattara kayana na fita, a daidai ƙofar ɗakin na ci karo da wata matashiya kamata tare da wata wacce na ke ƙyautata zaton uwar ta ce, ta goyo ta zata kaita wanka, ga kuma kuma jaririnta a bayan ƴar uwarta riƙe da bedin wankan, da alamu haihuwa ta yi kuma bata jin daɗin jikin ta.

Na bi su da kallo idona cike da ƙwalla, sai na ke ganin tamkar ni da Maama da kuma Teemah da abinda na haifa, na lumshe idona yayin da abubuwa bila

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login