Showing 21001 words to 24000 words out of 83936 words

Chapter 8 - KUSKUREN SO Book Complete by Feedohm.txt

Feedoms   

21 Sep 2025

1709

waje na ba, na lumshe ido yayin da na tuna da kalaman Sufyan ƙwanaki da ya ce "_Ba dole su riƙa daddofar zuwa gun ki ba, sun ga gida duk tiles da Ac, ga fridge tamƙame da kayan alatu._"

Na ja gajeran numfashi, a raina na ayyana kuma wallahi haka ne, idan da ace gidan talaka nake aure babu mai zuwa gurina, Fannata ta katse ni ta hanyar watsa min harara tana faɗin "Dan Allah ni bani hanya in wuce, kin tsaya kallona kamar baki sanni ba."

Wani sa'in mutunci da hallacin Fannata na ke tunawa a rayuwata, amma wallahi da bazan barta ta shiga ba tunda mijina baya son zuwan ta, itama kuma da shegiyar zuciyar ta kamar wacce kare ya cinye..

Babu yabo ba fallasa na ɗan ja jikina baya, zuciyata na dakan uku uku, yayin da hankalina gaba ɗaya ya koma ga ƙofar bedroom ɗin, ta samu kujera ɗaya ta zauna tana kallon yaran da suka maida kallon su ga cartoon.

"Ƴaƴan mijinki ne?" Ta faɗa idon ta na kan Aira.

Gabana ya faɗi, na watsa mata harara "Wane irin ƴaƴan shi, yaran Sister ɗin shi ne."

"Sister kuma? Hmm, amma dai kam kamar an tsaga kara da Sufyan ɗin." Ta miƙawa Safna hannu tana faɗin "Fine baby, ya sunan ki.?"

Na ɗauke kai ina faɗin "To sai su ƙi kama? Na ce maki fa ƴaƴan Sister ɗin shi ne, the same father and mother."

Safna ta ce "Safna Sufyan.."

Fannata ta kalle ni tare da waro ido waje ta ce "Wow, ita fa waccen.?"

Caraf Aira ta amshe "Nima Aira Sufyan."

"Why Sufyan? Ya sunan Dadyn ku?" Ta ɗauki Safna ta ɗaura a cinya.

Aira ta ce "Momyn mu ta ce sunan shi Sufyan."

Na katse su "Dan Allah ki bar wannan ƴan maganganun, tankar fa uba yake gare su, so don sun kira shi Dadyn su ba wani abu bane." Na cigaba da magana ƙasa ƙasa "Idan kuma gulma ta kawo ki dan Allah ki tashi ki bar min gida."

Da alamu bata ji abinda na faɗa daga ƙarshe ba, ta taɓe baki da alamu dai bata yadda ba ta ce "Ok, Maama ta ce min baki lafiya.?

Na ɗauke kai na ce "Uhmmm.."

"Me ya same ki?"

Na lashi laɓɓana na bita da kallo sheƙeƙe na ce "Bangane ba?"

"Eh, Me ya ke damun ki?"

Na furzar da iska tare da lumshe ido na ce "Ikon Allah, yanzu me kike so na ce maki? Tunda dai an faɗa maki bana lafiya ba shikenan ba?"

"Allah ya baki haƙuri."

Na amsa da "Amin." Tare da addu'ar ta tashi ta tafi kafin ma ya ji ta ya fito.

Amma sabida masifa irin ta Fannata sai ce min ta yi "Ƙwanaki A'i Abu ta zo ta ce...

Na dakatar da ita "Sai ki ce bayan ganina har da gulmar mijina kika zo min da ita? To ai na sa ni ta zo ya kore ta, sai kuma me Fannata?"

Kai tsaye ta ce "Sai kika ji kunya, daga yin auren ki har kin fara wulaƙanta mutane."

Kafin na bata amsa sai na ga kamar an buɗe ƙofar bedroom ɗin an kulle, na zuba ido gun cikin tsananin damuwa ina fatan Allah ya sa idona ne ke man gizo, jim kaɗan sai ga Sufyan ya fito daga shi sai pant a jikin shi, gaban nan yayi him cikin wandon, wani abu ya daki zuciyata na kalle shi na kalli Fannata da ta yi kamar bata san da shi ba a gurin ba, na miƙe da sauri na ƙarasa kusa dashi murya ƙasa ƙasa na ce "Baƙuwa muka yi, dan Allah koma ka saka kaya kar ta gane min kai haka." Don wallahi a zatona ko bai san da zuwanta ba.

Ya kalle ni ya watsar sannan ya ce "Baƙuwa kika yi dai."

Na sassauta murya tare da kamo hannun shi "Yi haƙuri dan Allah, zuwa ta yi ta adubani, dan Allah ka koma sako kaya Surgarty, bana so ta gane min miji."

"Sabida baƙuwarki sai in ƙi zama yadda nake so? Shin ban hanata shigo min gida ba?" Ya faɗa cikin ɗaga murya.

"Yi haƙuri, yanzu zata tafi, nima ban san da zuwanta ba, gidan mu ta je Maama ta faɗa mata bana da lafiya shine ta zo dubani."

Ya fincike hannun shi yana faɗin "Sabida ɗimin masifa irin naku rashin lafiyar ma sai an ta faɗa ma mutane? Ko da yake laifin ki ne da baki da sirri."

Duk da na ji zafin kalmar ɗimin masifar da ya faɗa, sabida Mama na ce ta faɗa ba wani ba, amma na daure na ƙasa sassauta murya na ce "Yi haƙuri dan Allah ka koma ka saka kaya." Wallahi babu macen da zata so a ga mijinta a yadda Sufyan ya fito.

Kai tsaye ya ce "Wallahi babu wani kaya da zan sako, ni da gidana a hanani sake wa yadda nake so, ai na faɗa miki bana son bimbinin masifa irin na dangin ku, amma tunda basu ganewa sai na yi masu yaren da zasu fi fahimta." Ya zagaye ni ya wuce falon, ya haye bisa doguwar kujerar da ke facing Fannata ya yi ɗaiɗai ƙafar shi ɗaya bisa hannun kujerar ƙafa ɗaya bisa majinginin kujerar, har ga Allah idan na ce maku kishi bar turnuƙe ni ba ƙarya na ke, gashi bana iya ce ma Fanna ta tashi ta bar min gidan, ga shi ita kuma taƙi tashin sai ma ta yi kamar bata ganshi ba.

Ina tsaye gefe zuciyata na azalzala na sani sarai taƙi tashi ta tsaye ne ganin gudun ruwan shi, shi kuma sai wani jan su Aira yake da fira har da ɗage ƙafa ɗaya sama yana tuntsura dariya, na lumshe ido lokacin na ke ganin tudun aliyar shi sosai, wani fat fat nake ji a zuciyata, samun kaina na yi da kallon Fannata rai a ɓace ina faɗin "Dan Allah ki tafi nagode tunda dai kin ga jikin da sauƙi."

Ta murmusa ta ce "Haba ke kam ƙawata, ai ƙya bari mu ƙara gaisawa."

Na ɗaga mata hannu ɗaya "Ni dai ki ma girman Allah ki tashi ki tafi, wai baki da hankali ne Fannata, baƙya gane haram da Halal? Baƙya ganin mijina na buƙatar shan iska a gidan shi?"

"Idan da kan ki aka fara aure da an shiga uku Nafeesa."

Na lumshe ido tare da jan iska mai zafi na furzar waje, dai dai lokacin Sufyan ya miƙe ya canza channel ya maida irin ta yarabawan nan, ya soma juya ɗuwawu yana tsalle wai duk cikin wasa ne da su Aira, wallahi ban san lokacin da na ce ma Fannata "Fannata wai baƙya ganewa ne? Baki da hankali? Na ce ki tashi ki bar min gida dan Allah, ina dalilin wannan baƙin nacin da miya ta? Ke kam wace irin mayya ce ƙwanaki kin zo an kore ki, yau kuma kin ƙara janyo ƙafa kin zo sabida jaraba, to dan Allah tashi ki tafi, ina ce babu ko sisin uban ki a ginin gidan nan, Haba ina dalilin masifa, kin bi kin liƙe min kin nane min sai kace mayya, kuma ku je kuyi auren ku mana, amma kun ƙi kun yi ƙwantai, sai bibiyar wasu kuke a gidajen mazajen su kun hana su sukuni da natsuwa, tunda ance ba'a so ki zo ba sai ki haƙura ba, ba dangin iya ba na baba kin bi kin liƙe daga abota? To wallahi bani iyawa, ki fice min daga gida, kuma kar na ƙara ganin ki, idan auren banza ne ki je kiyi mana ki ji yadda ake jin miji.....





#UWAR SUKUM.
[5/17, 8:18 PM] RN Feedohm: 💧💧 *KUSKUREN SO.*

FREE BOOK

*HASKE WRITER'S ASSO.*

   *FEEDOHM*
Wattpad@Feedohm



  _Ga ba ɗaya littafin nan sadaukarwa ne ga NAFEESA Muhammad SULE, maman jinjiri, Alherin Allah ya kai maki a duk inda kike._

_Ina kike Aunty Zainab Abubakar Kotorkoshi? Ke ma ina maki fatan alheri._



*014*



Cikin tsananin ɓacin rai Fannata take kallona, yayin da idanun ta suka yi jawur, ban yi zato ba sai na ga ƙwalla na bin kumatun ta, yayin da na ji kamar an zare min lakka, na sani idan aƙwai abinda ke ɓatawa Fannata rai bai wuce gorin aure ba, na lumshe ido ina nadamar abinda na faɗa, yayin da kuma wani sashe ke nuna min ba komai bane illa kishin mijina, kuma kishi Halal ne, don haka na ɗauki wannan jahilin sashen, na tamke fuska ina kallon Sufyan da har lokacin yake tiƙar rawar shi da su Aira kuma sabida tsabar ya ban haushi har dafa kujera ya ke yana baya baya da ɗuwawu yana zakuɗa su.

Na lumshe ido lokacin da na ƙarasa jikin ƙofa na buɗe mata ina faɗin "Dan Allah ki tafi, kuma kar ki sake dawowa bana buƙatar ziyarar, zuwan ki ba zai ɗauke min ciwon ba, ke ni fa ko mutuwa na yi na yafe zuwan ki."

Da ƙyar ta buɗe baki ta ce "Insha Allahu, gidan ki ko aljanna ake rabawa na yafe."

Ta juya tana ƙoƙarin tsaida hawayen da ke fuskar ta, amma sun ƙi bata haɗin kai, sai da ta dafa ƙofar sannan ta kalli cikin idona ta ce "Ban taɓa zaton da jahila nake abota ba sai yanzu, Allah ya isa abota ta, Kuma ki sani da aure da mutuwa duka lokaci gare su, ke ma da kika yi auren bake kika bawa kanki miji ba, kuma wallahi da na auri miji irin wancen gwamma na mutu ban yi aure ba, abu na biyu kuma, waɗancan yaran da kika gani ɗiyan mijin ki ne, ko ki ƙi ko ki so ƴaƴan sa ne na cikin sh......

Bata ƙarasa ba na buga ƙofar da ƙarfi na dawo baya na zube bisa kujera tare da dafe kaina da hannu biyu biyu ina sauke numfashi sai ka ce wadda ta yi faɗa da katti, sashe ɗaya kuma kalaman ta ke barazanar tarwatsa ƴar ƙaramar zuciyata, na zubawa yaran ido ina son gano wani abu, yayin da gaba ɗaya zuciyata ke ƙaryata Fannata, na sani ƙarya take, ƙarya take, Sufyan ba zai taɓa yi min ƙarya ba, bai taɓa aure ba, ƴaƴan yayar shi, kawai don suna kama? Shin dan yarana sun yi kama da Teemah sai ace dole ita ta haife su? Shima haka ne ga Sufyan, da uwar su da shi uwa ɗaya uba ɗaya, kawai baƙin ciki ne da hassada irin na Fannata, da dole sai ta birkita min tunani, dole sai ta hanani ƙwanciyar hankali a gidan mijina, dole yadda bata samu miji ba nima sai ta kashe min nawa auren mun koma mun jeru da ita, kuma wallahi bata isa na lumshe ido har lokacin zuciyata na bugawa da ƙarfi.

Ɗuwawun Sufyan na ji a fuskata yana goga mun, na janye fuskar raina a ɓace tare da buɗe ido ina aika mashi da wani banzan kallo, ya ƙwashe da dariya tare da zama bisa cinyata yana faɗin "Ashe Sweetie tana kishi na."

Na jefa mashi harara tare da ɗauke kai, ya ja karan hancina ya ce "Ni kike harara? Don na gwada sikilena?"

"Ban ji daɗi ba, kana neman ka sa zuciyata ta buga." Na ƙarashe maganar kamar zan fashe da kuka.

Ya tuntsire da dariya "Haba? Ai haka zan riƙa miki, tunda baƙya jin magana ta, wata rana ma da gudu zan fito ba wando ina ce wa Sweetie sosa min sosa min..." Takaici ya sa na kai mashi duka ya kauce yana dariya, na bishi ya ruga da gudu yana zagaye falon, daga haka abin ya koma wasa.

Kafin yayi tsalle ya damƙe ni ya nufi bedroom da ni yana faɗin "Faɗi abinda ke ran ki."

"Kamar me?"

Ya murmusa ya ce "Ba na ji ƙawar ki na faɗa maki su Aira ƴaƴana bane na cikina?"

Na ɓata fuska "Dan Allah mu bar wannan maganar."

"Hmm, kin fahimci me nake faɗa miki game da Fannata ko?"

Na haɗe bakin mu guri ɗaya, don wallahi bana son maganar baki ɗaya.

******************

Bangaren Fannata kalamai na sun yi masifar ɓata mata rai, don haka daga nan gidan mu ta nufa tana kuka, ta samu mama zaune Teemah na lallaɓe mata kai, kusa da Maman ta zauna tana faɗin "Wallahi ba zan ƙara zuwa gidan Nafeesa ba har abada, ba zan kuma ba Mamaa."

"Me ya faru?"

Teemah ta amshe "Itama zarafin nata suka ci."

Mamaa ta maka mata harara "Ke na tambaya?"

Ta juya ga Fannata "Yi shiru ki faɗa min abinda ya faru Fanna."

Cikin kuka Fannata ta ƙwashe duk abinda ya faru ta faɗa ma Mamaa.

Mamaa ta sauke lumfashi cikin ɓacin rai, ta zubawa Fannata ido har sai da ta kai aya tukun ta ce "Ki yi haƙuri, kar ki ce zaki rabu da ita Fanna, duk duniya bata da ƙawa mai faɗa mata gaskiya irin ki, bata ƙyauta ba, ta biye ma miji ta aikata rashin wayau, ki barni da ita, anjima da kaina zan je gidan sai na ci mutuncin ta, idan ita ke bada mijin sai ta fiddo min shi in taho dashi."

Maama ta bawa Fannata haƙuri sosai, tare da yi mata nasihar kar ta ce zata bar Nafeesa, domin har ga Allah ta sani duk duniya ƴarta bata da ƙawar da ta kai Fannata, idan kuma ta rabu da ita tayi asara babba, sun ɗan taɓa fira tana lallashin ta, tukun Fanna ta masu sallama ta tafi, sai dai a wani bangaren Teemah ta fi jin zafin abinda aka yi ma Fannata fiye da wanda aka yi mata, kuma ta ɗauki alwashin duk ranar da Nafeesa ta zo gidan sai ta zazzage mata abinda ke ran ta, ta yi ƙwafa Mamaa ta tambaye ta "Lafiya?"

"Ina fa Lafiya, haka kurum mutun ya rabamu da Yaya?"

"Au laifin shi ne? Ai sakarcin na gare ta, da tun farko ta nuna mashi darajar nata da hakan bai faru ba, ni bana ganin laifin Sufyan sai na Nafeesa, sannan kema babu ruwan ki da shi."

Ƙwafa Teemah ta yi, auta da ke gefe ya ce "Itama fa Yaya bata so aje gidan ta, sai ka ce ita ta fara aure a duniya."

*******************

"Fisabilillahi waɗannan yaran ba su faɗa miki basa son jallop rice ba?" Yadda ya ke maganar sai ka ce na kashe mashi wasu.

Na tamke fuska na ce "Bangane ba? Idan basa son abu sai na ƙi yin shi? Sufyan ba fa ci bane basa yi, aa so ne basa shi amma suna ci idan an yi."

"To dole sai an yi?"

Na taɓe baki na cigaba da yanka carrot ɗina ba tare da na ƙara bin ta kan shi ba, don na lura yadda ya ke ji da yaran nan ko ni baya ji da ni, sai ka ce shine uban sun, sannan ma don rashin mutunci har yau uwar su bata kira ba, bare ta ji halin da muke ciki, kuma ko ba komai ya dace ta kira ɗin,  sanin ɗiyan nata basa ji.

"To wallahi sai dai ki dafa masu wani abin daban." Ya faɗa ran shi a ɓace.

Kai tsaye na ce "Ba zan iya ba gaskiya, su ci abinda ya samu."

"Ni kike faɗa ma haka Nafeesa? Sabida ba ƴan uwanki bane ko?"

Na aje yankan carrot ɗin na juyo na zuba mashi ido ina faɗin "To ai ka hana ƴan uwan nawa zuwa Sufyan, ko ka manta?"

Kafin ya bani amsa muka ji magana sama sama, na baza kunne don ƙara tabbatar da kamar muryar Maamata na ke ji tana tambayar su Aira ina masu gidan? Na sauke numfashi cikin tsananin farin ciki, yayin da wani sashe na zuciyata ke rawa, duk da dai na san uwata ta fi ƙarfin wulaƙanci a gidan Sufyan, na kalle shi a ɗarare na ce "Maama ce."

Babu yabo ba fallasa ya ce "Tah.."

Na fice da sauri fuskata a sake, na ƙarasa kusa da ita na rungume ta ina faɗin "Oyoyo.."

"Sake ni kar ki ƙarasa ni." Ta faɗa da alamun jin daɗin gani na.

Na shagwaɓe fuska "Ya zaayi na ƙarasa ki." Na jata muka zauna bisa kujera ina faɗin "Sannu da zuwa, da kin faɗi min zaki zo da na maki special tarba."

Mama ta murmusa ta ce "Ai ba zama zamu yi ba."

Na narke murya "Kai dan Allah, ba fa ki taɓa zuwa ba, gaskiya ƙwana zaki yi."

Ta yi murmushi "Ni banga gun ƙwana ba."

Auta yayi caraf ya amshe "Wallahi sai dai mu ƙwana police station."

Mamaa ta jefa mashi harara "Bana son shashanci."

Ƴar siririyar dariya na saki na miƙe na koma kitchen, har lokacin yana tsaye inda na barshi sai cika ya ke yana batsewa, na kalle shi na watsar, na ɗauki plate na buɗe fridge na ɗauki ruwa da lemu zan juya ya tare ni, ya kalli lemun ya kalle ni sannan ya ce "Kin san dai wannan lemun ni nake shan shi ko?"

Na dafe kai ina faɗin "Au, sorry." Ban ɗauki hakan komai ba, na sake buɗe fridge dine na maida na ɗauki wani, ya kuma sake dakatar da ni "Wannan kuma ai na su Aira ne ko kin manta ne."

Raina ya so su, na maida lemun baki ɗaya na kulle fridge ɗin ina faɗin "Allah ya ji ƙan lemu." Na fito na kawo masu ruwan na aje ina murmushi yaƙe, yayin da zuciya ta ke tafarfasa, ina jin muddun Sufyan ya aikata wani abu ga Mamata wallahi sai na nuna mashi ɓacin raina.

Na zuba mata ruwan a glass cup na miƙa mata ina murmushi na ce "Ni dai dan Allah a riƙa faɗa min idan za a zo yadda zan maku tarba mai ƙyau."

Kafin ta ce wani abu Sufyan ya fito, ya wuce bedroom abin shi, ba tare da ya kalle ta ba, sai na ji na kasa haƙura na bishi kamar zan tashi sama, ina shiga na soma faɗin "Kamar na faɗa maka mahaifiyata ce ta zo,  shine sai ka gifta ta...

Ya dakatar da ni "Ni na ce maki ba zan zo na gaishe ta ba? Shin dakata ma, kin faɗa min zata zo ne koko ganin ta kawai na yi? Dan Allah malama ki barni na ji da abinda ya ishe ni.

"Idan zata zo gidan ƴarta sai ta bada notice?

"Haka dai ya kamata." Ya faɗa kai tsaye, kafin na bashi amsa ya fito waje, ya samu kujerar da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login